Skip to content
Part 42 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Gidan hamshaƙin gini ne mai matuƙar girma ko da ya zam ba a kammala shi ba kuma da sauran aiki.

Mun zagaya ko’ina bisa jagorancin daya daga cikin ma’aikatan da muka samu part huɗu ne wadanda suka zam falo ne ya raba su ma’ana step aka yi guda biyar da za ka taka ka shiga kofar da za ta shigar da kai part ɗin.

Mun gama har za mu shiga mota ya iso ban mishi magana ba kamar yadda ya gwada bai ma san da wanzuwa ta a wurin ba.

Suka gama maganar su muka shiga mota motarsa na bayan tamu muka fita layin.

Da daddare ina daki muna waya da Gwoggo Maryama kiran ya Safwan ya shigo muka yi sallama da ita na amsa kiran shi “Ki fito ki ba ni abinci.”

Abin da ya ce kenan ya katse kiran, na janyo mayafina da nake ajiyewa kusa saboda gudun ko ta kwana Mami na shigowa in ɗauka in rufe jikina.

Na fita, na gaishe da Daddy da suke hira da Mami na wuce kitchen na haɗa abinci na kawo mishi ya ce in zuba mishi, ina cikin zubawar na ji muryar shi cikin kaina kamar me raɗa “Ki zo mu tafi gida.” Na ɗaga ido muka dubi juna na yi saurin mayar da kai na gama zuba mishi na koma kitchen lemon tatacciyar abarba da kwakwa da na yi da yamma na tsiyayo na kawo mishi na fito daidai Mami na cewa “Me ya haɗa ka da matar taka har ta bar gidan?

Ya ce “Ban mata komai ba Mami, ganin dama ta yi ta tafi.”

Maganar banza haka kawai ba a yi komai ba sai ta tafi?

“Ni ban yi mata komai ba.” Ya ƙara tabbatarwa “Shi kenan sai ka je gidan na su ka ji.”

“A’a fa Mami, don Allah kar ki sa ni zuwa, ni ba abin da ya haɗa mu.”

Ban ji Mami ta ce komai ba har ya gama na kwashe kwanonin na mayar kitchen na kuma zo na wuce su na tafi daki.

Har na kwanta kiran shi ya shigo wai zai tafi in ce ma Mami zan koma murmushi kawai na yi na gyara kwanciya.

Na daɗe kwance yau ma cikin kewar shi kafin barci mai daɗi ya ɗauke ni

Abin da ya yi ta faruwa kenan kullum sai ya Safwan ya zo da daddare sai kuma ya yi min tayin komawa har aka yi sati guda Mami kuma da kanta taba in riƙa yi mishi abincin da zai ci idan ya zo.

Ranar da aka cika satin ne ya zo zaune suna magana da Mami wayarsa ta yi ƙara ya ɗaga sai da suka gaisa da mai kiran ya ce ga shi nan zuwa ya kashe wayar ya mayar aljihu ya dubi Mami “Zan wuce Mami, Auntyn Farha ke nema na.”

Ta dubi abincin da na zuba mishi bai kai ga fara ci ba aka kira shi ta ce “Amma sai ka gama cin abincin ko? Ya dubi agogon da ke ɗaure a hannunsa “Zan tafi kawai Mami.”

Ya miƙe ya mata sai da safe na dubi tulin abincin wani takaici ya ƙulle ni na miƙe na haɗa kayan na kai kitchen.

Sai washegari na dawo makarantar nake jin Aunty Farha ta koma gidanta tun kuma daga ranar ya Safwan bai ƙara takowa gidan ba har aka yi sati zai zam ƙarya nake idan na ce abin bai dame ni ba wani lokacin har hawaye nake idan na tuna saboda matarsa ta dawo ya watsar da ni, kullum dai da safe yana kira na ya tambaye ni lafiyata.

Bikin da Mami ta ce za mu je Safana yana ta matsowa na yi shawarar kwasar kayana in kai ɗinki.

Ranar da na fito da su Mami ta ce “Ba za ki kira shi ya kaiki wurin ɗinkin ba? Na yi shiru ta ce “Amma ki tabbatar kin tambaye shi kuɗin ɗinkunan.” Kai na ɗaga mata na wuce.

Direba da ya hango ni da ƙatuwar jaka ya zo ya karɓe ni.

Ina zama a mota na share hawayen da suka ziraro min na shafa cikina wanda duk ɓoye shi da nake yi a yan satittikan nan abin yana son cin tura don ƙara turowa yake.

Na lumshe idona ina jin wani abu na taso min ta ƙasan zuciyata.

Sai da muka fara zuwa na bayar da ɗinkin Direba ya sauke ni a makaranta,wayar da muka yi ta yi da Zainab kafin ya sauke ni tana shaida min haihuwar matar Najib ita ta sanyaya min zuciya a raina na ƙudura idan muka tashi zan tsaya in saya ma matar Najib kayan barka ina shiga aji kamar sun hada baki matan da muke gaisawa suka rufe ni. Wai ke amaryar nan sai yaushe za ki tare? Idan mun ce za mu zo sai ki ce ba ki tare ba?

Asma’u Manga ta kwashe da dariya “Naku wasa ne, wace tarewa kuke magana ango har ya san inda dare ya yi masa.”

Suka kama dariya su duka suna ce mata Don Allah? Ta ce “Ba ku ga yadda take ƙyallin goshi ba? Suka ƙara barkewa da wata sowa.

Ni dai na ƙara jan hijab ɗi na ina cewa

“Sharrin ku dai ku zai kashe.”

Ban samu suka ƙyale ni ba sai da mrs Sunday da za ta ɗauke mu darasi ta shigo.

Muna fitowa na doshi inda direba ke jira na na shiga sai na shaida mishi inda nake so mu biya.

Mun kusa isa ya ce “Kamar wata baƙar mota tana bin mu. Na waiwaya na dubi motar da yake faɗin, sai na ba shi umarnin shiga wani kantin sayar da kayan yara da na gani a gefen hanya ya raɓa ya shiga wurin ya yi parking na fita na shiga wurin, riguna masu matuƙar kyau da tsada na zabar wa yarinyar Najib, ina zaɓen kuma ina tuna gwagwarmayar da muka sha da shi a zama na gidansu wani abin na tuna in yi tsaki wani in yi murmushi.

Na koma na zaɓi tarkacen yara sai na isa wurin biyan kudi ATM ɗi na na ciro zan miƙa ƙamshin turarensa na fara ji kafin muka yi ido hudu, ban fasa miƙawar ba sai dai da na miƙa, mai amsar kuɗin an riga an ba shi ATM ya cire abin da na ɗauka sanin waye me biyan na maida nawa jaka ina cewa “Ina wuni ya Safwan?

Wani kallo yake min ya kamo hannuna
bayan ya karɓi Atm ɗinshi.

Da muka fito ban ga motar da na zo ciki ba sai bakar motar da direba ya yi zargi tana bin mu ita ɗin ya nufa da ni ya buɗe gaba ya cusa ni, sai da ya rufe ya zagaya ya shiga, wanda ya riƙe min kayan da na saya ya iso shi ya karɓa ya ajiye, ya yi mata key muka bar wurin.

Bai yi min magana ba haka ni ma har ya tsaya wani haɗaɗɗen hotel.

Bari na ya yi ya shiga ciki kafin ya dawo ya ce in fito na fita na bi bayan shi wani daki mai lamba takwas ya shigar da ni, da shiga ta zama na yi ya sa aka kawo abinci ban tsaya jan aji ba na ci don ƙamshin abincin da na ji ya sa na ji ina jin yunwa sai da na koshi ya dawo kusa da ni “Me na yi miki kika guje ni? Shiru na yi na ƙi magana wayata da ke jikin jaka ta hau ƙara.

“Mami ce ki ɗaga ki faɗi mata kin koma gidanki.”

Jin da na yi ya ce Mami ce sai na yi zaton ita ɗin ce don haka na kasa na ciro wayar, daga wasannin da yake min abu ya zarce mun dade kafin ya haƙura ya janye muka yi wanka ya tambaye ni lafiyar cikina.

Sai da muka shiga mota na ciro wayata na duba kiran da aka yi min Rahinar Gwoggo Maryama ce sai na kira ta muka yi magana.

A ƙofar gida ya sauke ni bai fito ba ya juya da motarsa.

Da na shiga a wata yar rumfar shan iska na hango Mami tana tare da baƙi na isa na gaishe su ta ce “Sai yanzu Bilkisu? Yau kun daɗe.” Na ce “E Mami.”

Na wuce su na shige ciki

Da yake ban tare da yunwa daki na shiga na hau gado na kira Mamana ina so in ce idan na haihu ko ba za ta zo ba ta turo min ƙannena da ƙanwarta, amma ba zan iya ce mata ina ɗauke da cikin ba.

Kwana biyu aka ƙara bayan nan ya Safwan ya same ni a makaranta ya kai ni hotel din nan, na uku da aka yi ya daɗe tare da ni tun ina ƙorafin yamma ta yi Mami za ta neme ni sai ya ce “To mu wuce gida abin mu kawai.”

Sai in yi shiru.

Ana kiran sallar magrib ya sauke ni zuwa lokacin Mami ta kira har ta gaji na shiga ina ta tunanin ƙaryar da zan mata sai dai ashe na makara da ta gaji da kira na direban da ya kai ni ta kira ya ce mata Oga ya ce ya je kawai.

Ban haɗu da ita ba har na samu na shige daki zane na daura zuwa kirji da na tube kayan jikina na shiga na yo alwala na fito, na ji ana taɓa ƙofa saurin zura hijab na yi Mami ta shigo muna dubi juna ni da ita na ce “Sannu da gida Mami.”

Ta ce “Yawwa ina kika tsaya?

Na buɗe baki zan karanta mata abin da na tsara ta ce “Ba na son wannan sakarcin da kike, yana son kasancewa da ke ya gagara gyara miki gidanki ki koma?

Tana gama fadi ta juya ta fita.

Wata kunya da takaicin kaina suka kama ni na yi ta maza na kabbara Sallah da na idar na yi zugum ban san me ya sa na biye wa ya Safwan ba, gado na tashi na hau sam kasa fitowa na yi saboda nauyin Mami sai da safe da zan fita makaranta ranar ce kuma za mu fara Exam da muka fito kuma na ƙi bin inda zan ga ya Safwan mota na samu na shiga na yi tafiyata kuma sai ga shi yana ta kira na ban daga ba sai da na koma gida na ce ni na koma gida.

Da daddare ina daki ƙishi ya ishe ni don yanzu wani irin zafi ke damu na in rasa inda zan sa kaina yanzun ma daga ni sai zane da na yi ɗaurin ƙirji Ac ɗakina da na dawo da yamma ta ƙi yi.

Na share gumin da ya tsattsafo min a goshi ga dakin ba fanka na isa ma’ajiyar kayana na ciro wata riga doguwa mai laushi sai gefen ƙirji aka yi mata flower na sanya na yane jikina da mayafinta na zura silifas na fita dakin sai dai na yi turus ganin ya Safwan zaune tare da Mami, na wuce su ban gaishe shi ba don idan gaban Mami na gaishe shi ta ƙasan maƙoshi yake amsawa kamar wanda aka yi wa dole.

Ruwan da na sa da har ya fara ƙanƙara na ɗauko cikin farin ciki sai da na dan sha sai na fito zan gifta su ya ce “Ba ni ruwan nan ki ɗauko wani.”

Cikin rashin jin dadi na isa inda yake na ajiye gaban shi na koma kitchen ɗin, duka ruwan da ke ciki masu sanyi ne na ciro na mayar inda zai yi ƙanƙara na sha mai sanyin ban ji ya gamsar da ni ba jin kiran sunan Mami da yake ƙwallawa kuma kiran da ƙarfi ya sa na gane da ni yake don ba zai yiwu ya yi wa Mamin shi irin wannan kiran ba na fito na tsaya daga bayan kujéra ya ce “Wane irin ruwa kike sha me ƙanƙara, kin manta halin da kike ciki?

Na yi shiru ya juya wurin Mami cikin kwantar da murya “Ki bar ta Mami mu tafi gida, kin ga kina wurin ki tana nata, ba za ki san me take yi ba.
Yanzu wannan ruwan ƙanƙarar da take sha Mamina zai illata abin da ke cikinta.

Wata kunya ce ta lullube ni da ta sa na ji kamar in nutse a wurin na kwantar da kaina saman kujera na rufe ido.

“Ka gama gyaran gidan ne? Ta tambaye shi “A’a Mami.”

To ka bari har sai ka gama ba za ta koma ma matarka gida ba.”

“Gidan ne ba na son rabawa.”

“To sai dai kam ita matar taka ta bi Bilkisu gidanta daga akwai wuri amma Bilkisu ba ta kuma koma mata gida.

Na tada kaina na wuce daki na bar shi yana rokon Mami ta bari mu tafi tare.

Da shiga ta rigar na cire na mayar da zanen don ji nake kamar in yi tumɓur na hau gado zafin da nake ji ya hana ni barci.

Aka turo ƙofa na yi hanzarin juyawa na ba kofar baya ban ji muryar Mami ba da na zaci ita ce sai kamshin turarensa da hannuwansa da na ji ya sa ya tallafo ni rufe idona na yi jin ya sa kaina saman ƙirjinsa ya sa hannu cikin gashina “Wace irin zufa kike yi haka?

Na ce “Ba ka hana ni shan ruwan sanyi ba zafi nake ji.”

Ya dubi inda AC take “Me ya hana ki kunna Ac?

Ta lalace ɗazu.”

Me ya hana ki faɗa wa Mami?

Kin ga duk irin wadannan matsalolin idan Mami ta bani ke muka yi tafiyar mu ba zan bari duk ki fuskance su ba. Yanzu ban da na shigo haka za ki kwana cikin zafi ga ruwan ƙanƙara kina sha da zai illata abin da ke cikin ki.”

Ya sake ni ya mike ya fita sai ga shi ya dawo “Tashi ki shirya ki koma bedroom ɗin Mami ki kwanta.

Na fidda ido ya ɗaga gira “Na yi mata magana ki tashi mu je.”

Na yunƙura zaune kafin na mike wata rigar barci tsawon ta iya gwiwa na dauko na sanya zan sanya hijab ya hana “Ba na son wannan yawo da rufar da kike yi a cikin gida, abin da kike boyewar kina ji dai na gaya wa Mamin.

Haka ya tasa ni ya hana ni daukar hijab ga cikin sosai ya fito cikin rigar.

Ba mu haɗu da Mami ba har ya raka ni ɗakin na kwanta bisa gadonta da na ce zan dauko Afnan ya ce in kwanta ya je ya zo min da ita ya kwantar da ita a gefena sai da ya ba ni peck ya ce “Zan je gida me zan miki kafin in tafi?

Na ce ƙishi nake ji, ka kuma hana ni in sha ruwa.

Ya ce “Ba hana ki na yi ba mai ƙanƙarar ne na hana.

Ya fita ya kawo min mai sanyi kaɗan na sha hakanan na koma na kwanta, ya ja min kofa, sanyin da na samu ya sa ban jima ba barci ya ɗauke ni.

Maryam Litee

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 41Mutum Da Kaddararsa 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×