Skip to content
Part 43 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Kamar yadda na saba haka na farka da na yi sallah komawa na yi na kwanta har ban san sa’adda Afnan ta farka ta fita ba.

Na farka ne na ga Mami tana kwalliya na tashi zaune ta waiwayo ta dube ni “Kin tashi Bilkisu? Na yi ɗan murmushi ina waigen inda zan samu abin da zan rufe jikina tuna yadda na zo ya sa na haƙura sai dai na kasa miƙewa zan gaishe ta aka yi knocking ta bayar da iznin shigowa muka dubi kofar a tare ya Safwan ne.

Na yi mamakin abin da ya kawo shi tunda safe na kai idona ga agogo karfe tara ne har da kwata na yi sauri na sauko gane duk saurin da zan yi sai na makara, bathroom na mike na shige da na ƙare abin da zan yi wanka na yi na fito don jin shiru na yi tunanin sun fita, sai dai Mami ce ta fita shi yana zaune bakin gado yana latsa wayarsa.

Ya ɗago muka haɗa ido na wuce gaban mirror shafe-shafena na yi kafin na miƙe don mayar da rigata in je in sanya kaya a ɗakina sai ji na yi ya ruƙo ni zuwa bakin gado cikin siririyar murya na ce “Ina kwana? “Kin tashi lfy? Ya ce yana taɓa cikina.

Na raba jikina da na shi na miƙe “Bari in sanya kaya zan makara.”

Daga haka rigar na mayar na fice ban haɗu da kowa ba har na shiga ɗakin abaya na sanya na yane kaina da gyalen ta na ɗauki Hand Bag na fito, ban koma dakin ba a falo na gan shi tsaye Mami na zaune na gaishe da ita na tambaye ta Daddy ta ce yana falonsa.

Na shiga na gaishe shi ya min nasiha da in kula da kaina, na taso a kunya ce gane in ma da Mami ba ta faɗa mishi zancen cikina ba tona min asiri da ya Safwan ya yi jiya ya sa ta faɗa don maganganunsa kan cikin suka nufa.

Ya Safwan na ji yana fadi wa Mami Antenatal ya zo kai ni ta ce “Makaranta za ta tafi da ka bari sai ranar da ba za ta shiga Sch ba.”

Ya ce “Bar Sch ɗin nan Mami, ni ta fara ma isa ta.”

Ta kama baki ya wuce na ce ma Mami sai na dawo na bi shi.

Har ya shiga mota get man ya iso ya ce wani mutum ya zo ya ce ya Safwan ya turo shi ya sanya Ac kai ya ɗaga mishi ya ce ya shigar da mutumin wurin Mami ya daura Ac kafin ya dawo.

Yana tukin shi na saci kallon shi “Don Allah ka bari ba yau ba, yau ka sauke ni Sch.

Bai ce min komai ba ballantana in gane ko ya ji roƙon da na yi mishi, sai dai na ga ya shiga wata specialise hospital, likitan da ya je gida ya duba ni kuma na gane yana cikin abokansa da suka je gidan Aunty Farha lokacin ina gidan.

Muna tare da shi aka bude min file bayan kammalawa muka fito kiran shi kawai ake ta yi a waya don haka sauke ni kawai ya yi ya juya.

Tun ranar duk yadda ya so fita da ni sai na kauce ma afkuwar hakan, fitowa ma idan ya shigo gidan na bari dai dai in ya shigo daki ya same ni, duk da miskilancin shi sai da na gano damuwar shi.

Ya zo ya roƙi Mami ta hakura da tafiya bikin in tare kawai don ko da aikin bai kammalu duka ba ya gama gyara inda zan zauna. Ta ce a’a ya bari ya kammala a nutse ya ce to ta hakura da tafiya da ni saboda halin da nake ciki ba zan ji dadin zaman mota ba.

Ta ce Ka fita idona Sadauki rashin kunyar da kake min ta ishe ni. Dole ya tashi ya tafi.

Na amso dinkunana Mami kuma ta sanya shi ya kawo min kayana na gidan Aunty Farha.

Ana gobe za mu tafi ya shigo da daddare a daki ya same ni kuɗaɗe masu yawa ya bani na yi godiya.

Daga ni sai Mami sai direba muka dau hanya.
Gidansu Mami na Safana gida ne na yan boko kuma nan ne gidan su Baba da Daddy kasantuwar ubannin su maza duka uwarsu daya ubansu ɗaya.

Gida ne na yan boko da suka watsu garuruwa daban-daban sai dai kusan kowa da part ɗin shi a gidan.

Abin da ya fi burge ni fillancin da suke don su ɗin Fulani ne Usul.

Mun yi waya da Zainab ta ce Najib ɗinta ya hana ta zuwa ya ce saboda cikinta ya fara girma yanzu wata shida yake.

Na shafa nawa mai wata huɗu amma tamkar ya yi shidan, sai Mama da Khadijah za su zo.

Ana ta nuna ni ga dangin nasu masu tarin yawa.

Ranar ɗaurin aure da safe Daddy ya iso haka ma Baba da Mama sai dai ba Khadijah wai yaronta ya tashi da zazzaɓi ana gobe za su taho.

Daga Baba har su Daddy kowa na da wurin shi a cikin gidan.

Ni dai ina gaishe su na bar sasan zuwa na matar ɗan yayar Mami da tun zuwan mu take yawan shigowa tana ja na da zance da gayyata ta zuwa part ɗinta.

Ina shiga ta tare ni da abubuwan taran baƙo muka yi ta hira kamar mun daɗe da sanin juna, ta faɗa min ita yar Bauchi ce aiki da ya kai mijinta can ya auro ta, a can suke zaune ta kare da tambaya ta watarana za mu kai musu ziyara ko? Na yi murmushi na ce “In sha Allah.”

Anan na yi wanka na yi kwalliyar biki cikin wani rantsattsen less, bubu ce ga adon gwal da ya ƙara haska kwalliyar tawa sai ƙyalli nake sai dai kan dole na zuba rigar don uban zafin da nake ji.

Ina zaune a falo Raihan tana ciki ba ta ƙarasa kwalliyarta ba, ta rufe kofarta don haka ba wanda ya shigo.

Maganar maza na ji tana kusanto ni na gyara zama sai gani na yi suna shigowa gogaggun maza ne cikin shiga ta alfarma kallo daya na yi musu na haɗe su na ce musu Sannu. Karaf idona ya shiga cikin na ya Safwan wanda ban taɓa sanin zai zo ba, na mike na shiga ciki.

Har lokacin tana gaban mirror tana ƙara gyara adonta.

Na yi murmushi. “Wai kwalliyar nan ba za ta ƙare ba Madam?

Ta mayar min da martanin murmushina “So nake in yi ko rabin kyan da kika yi.”

Na ce “Ya yi na gode da zagi.”

Ta kara murmushi”Ba zagi gaskiya ce zalla.” Zan yi magana aka murɗa handle ɗin kofar aka shigo a tare muka dubi wurin daya daga cikin mazan da suka shigo ne wanda na hakikance shi ne mijinta don akwai hotonsu shi da ita a falon haka ma a dakin barcin na ta.

Daga bakin ƙofar ya tsaya “Wai me kike haka ? Ki fito ki ba mutane abinci. Ga barrister Auwal ya ga baƙuwarki jiran ki yake ki fito ya ce da ke zai kama ƙafa.”

Ta buɗe ido daga inda take tsaye “Wace baƙuwar tawa?

Ya nuna ni “Ga ta nan zaune “Ta ce “La’ila! Ina Sadaukin Abuja? Ya ce “Muna tare a falo, don Allah ki yi sauri.”

Ta ce “Ai baƙuwar da kake magana ita ce amaryar da ya yi.”

Ya dafe kai “Subhanallah ki ce an yi abin tsiya, amma miskilin yana ji ko kai bai ɗaga ba.”

Ta ce “Sai ka ce makafi mace har da ciki shi bai gani ba?

Ya dube ni “Ashe amaryarmu ce kina lafiya.”

Na amsa muka gaisa ya fita ita ma ta gama gyara daurin dankwalinta ta fita.

Wayata na ci gaba da taɓawa zaman wurin duk ya ishe ni sakon ya Safwan ya shigo *”Ki fito ina jiranki a bayan part ɗin su Mami*

Na ƙara duba sakon sai na ƙara minti biyu kafin na miƙe na yane mayafina na fita.

Suna zaune suna cin abinci amma ba ya Safwan, duk da faɗa musu da Hamza mijin Raihan ya yi ni ɗin matar aure ce sai da suka bi ni da kallo.

Na fita ko’ina ka kalla taron jama’a ne sai da na isa inda ya ce in same shi na gane hikimar shi ta yin hakan wurin ba jama’a.

Yana tsaye cikin shigar farin kaya da hula yar uban su da ta zauna a kan shi take ta sheƙi haka takalminsa da agogonsa.

Na tsaya kusa da shi ina gaishe shi wata mata ta iso “Dama na ce Dunkum na hango suka yi min musu.”

Ta ɗaga wayarta “Ku zo shi ne.”
Shi dai ido kawai ya daga ya dube ta jin abin da ta ce ya kama hannuna ya ɗau hanyar barin wurin.

Sanin duk inda za mu kutsa jama’a ne danƙam ya sa na zare hannuna a na shi wani part muka shiga na wata tsohuwa da zuwan mu mun shigo tare da Mami.

Tsohuwar Mami ta ce min ita kadai ce abokiyar haihuwar iyayen su da ta rage ita kuma ce autar su.

Tana zaune sai wasu maza da suke yi mata sallama za su fita gaban ta ya zaunar da ni ya zauna ta ce “Maraba da mai gida, jiya da na tambayi Bilki ta ce min ba za ka samu zuwa ba.”

Ya ce “Yau na shirya tafiyar.”

Ya kamo hannuna ya sanya cikin nata sai na ɗora da gaishe ta ta ce “Ita ce kishiyar tawa Sadauki? Ya ɗaga mata kai “Yar wajen Abubakar? Zuri’ar su mutanen kirki ne ka riƙe ta da kyau.

Allah ya kaɗe fitina a aurenku ya sa albarka a yi ta haƙuri,zo mu zauna zo mu saɓa.”
Na ɗaga mata kai don duk maganganun nata ni take kallo.

“Ga aure me albarka an ce har an samu rabo, Allah ya raba ku lafiya.”
Shi ya ce Amin Ni na sunkuyar da kai.

Matar da ta same mu dazu ta shigo har da wasu matan tare da ita.

Ashe su ɗin ya’yan yayan Mami ne suka fara tonon ya Sadauki, suna ja na idan wannan ta kamo ni ta nan sai waccan ta ta ni ta can, shi dai yana zaune ya sa musu ido.

Tsohuwar ce ta ɗaga sandarta da ke gefen ta suka sake ni suka watse ta ce “Ka ga min ja’irai, yarinya da juna biyu kuna jagalgala ta, kai kuma kana zaune kana kallon su?

Tana ajiye sandar suka dawo sai da ya ciro kudi masu nauyi ya ajiye musu suka rabu da ni. Da fitar su ma wasu suka shigo su ma haka suka yi ta fizga ta da ƙyar tsohuwar ta kora su ta ce “Ka ga ka tashi da matarka tun ba su sanya mata ciwon jiki ba ga ta da lalura.”

Tana rufe baki wasu maza suka shigo na yi mamakin ganin cikakkiyar fara’a a fuskar ya Safwan a yayin da yake gaisawa da su.

Ni dai miƙewa kawai na yi bayan mun gaisa na shiga ɗakin tsohuwar da ta nuna min ta ce “Shiga ki yi kwanciyarki.”

Na samu lafiyayyen gadonta na haye barci ya yi awon gaba da ni, don ni dai har yanzu barci bai isa ta tun samun cikin.

Cikin barcin na ji muryar ya Sadauki ban tashi ba sai da Raihan ta zo “Ki tashi amaryarmu, yamma ta yi ana ta shirin tafiya dinner kina kwance.”

Na tashi zaune sai da na wattsake na fito tsohuwar na nan zaune tana goga goronta ta yi min sannu ni ma na yi mata tana faɗin “Kin matse, Sadauki ya gaji da shigowa ba ki tashi ba.”

Na yi murmushi.

Part ɗin su Mami na tafi na dauko kayan da zan sanya na dawo wurin tsohuwar na yi sallah na yi wanka na shirya cikin wata ɗanyar shadda da har ta fi lace ɗin da na cire karɓa ta.

Da na gama na koma kusa da tsohuwa Nene na zauna ina sauraren hirar da take min na tarihin zuri’ar su Babana da ta sani saboda mahaifiyar su Baba (Baban su Zainab) da yayanta ya auro.

Ina ta gyaɗa kai Raihan ta dawo lokacin tsohuwar ta gabatar min da tuwon semo miyar kuɓewa ɗanya da ta ji wadataccen nama da man shanu, ya Sadauki ya shigo a bayanta daidai tana cewa “Gaskiya kar ki ci tuwon nan ki ɓata kwalliyar ki, ki zo mu je wuri ya fara haduwa.” Shi dai yana tsaye ya soke hannunsa a aljihun wando yana kallon mu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 42Mutum Da Kaddararsa 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.