Kamar yadda na saba haka na farka da na yi sallah komawa na yi na kwanta har ban san sa'adda Afnan ta farka ta fita ba.
Na farka ne na ga Mami tana kwalliya na tashi zaune ta waiwayo ta dube ni "Kin tashi Bilkisu? Na yi ɗan murmushi ina waigen inda zan samu abin da zan rufe jikina tuna yadda na zo ya sa na haƙura sai dai na kasa miƙewa zan gaishe ta aka yi knocking ta bayar da iznin shigowa muka dubi kofar a tare ya Safwan ne.
Na yi mamakin abin da ya. . .