Ta gyara zaman mayafinta ta kama hanyar fita na bi ta a baya. Hajjon ma har mun kusa inda motar da aka kawo Mami take sai ga ta ta fito ta ce za ta ɗauki kayanta, aka buɗe Boot ta ɗauka.
Na tsaya naɗe da hannu har sai da motar ta fita gidan muka koma ciki Hajjo na bayana, a falo na zauna ta wuce ɗaki ta ajiye kayanta ta fito ta zauna a ƙasa muna kallon Film ɗin da nake kallo.
Ana buga sha biyu na miƙe na shiga kitchen, ina fara aiki ya Safwan ya. . .