Skip to content
Part 46 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ta gyara zaman mayafinta ta kama hanyar fita na bi ta a baya. Hajjon ma har mun kusa inda motar da aka kawo Mami take sai ga ta ta fito ta ce za ta ɗauki kayanta, aka buɗe Boot ta ɗauka.

Na tsaya naɗe da hannu har sai da motar ta fita gidan muka koma ciki Hajjo na bayana, a falo na zauna ta wuce ɗaki ta ajiye kayanta ta fito ta zauna a ƙasa muna kallon Film ɗin da nake kallo.

Ana buga sha biyu na miƙe na shiga kitchen, ina fara aiki ya Safwan ya kira lafiyata ya kara tambaya na ajiye wayar na ji alamun akwai mutum a baya na Hajjo ce take famar min fara’a.

“Haj kuma aikin da kanki? Ki kawo a yi.” Na ɗan dube ta “Ki bar shi za ki riƙa min gyaran wuri ne kawai, girki zan riƙa yi da kaina.”
Ta ce “To to to Haj, na gane ba abin da za a yi na ce “E ba yanzu ba.

Ta fita na cigaba da aikina sai da na kammala na fita kallon na samu tana yi na ce “Hajjo.” Ta waiwayo “Na’am Haj.” Na ce. “To zo mana.” Ta amsa “To Haj.”

Ta mike ta bi yo ni dakin da na ba ta na ce “Ki yi wanka, sai ki fito ki karɓi abinci.”
Ta ce To Haj. Tana fara’a na fita.

Sallah na je na yi na koma falon tana zaune tana kallon TV still kayan da ke jikinta ta mayar ban so hakan ba amma sai ban ce mata komai ba, na shiga kitchen na fito mata da abinci ta karba ta fara ci a wurin na dauko nawa na zauna ina ci tana ba ni labarin garin su mijinta ne ya rasu ya bar ta da yara biyar mata uku su ne manya sai biyun maza matan uku duka sun isa aure amma rashin yadda za ta aurar da su ya sa suna nan zaune shi ne ta fita neman kudi ta tara abin da za ta aurar da su. Yanzu ma da ta biyun suka fito ita ma an ɗauke ta aiki wani gidan.

Na yi shiru cikin tausayi sai ma na ji duk abincin ya ishe ni kitchen na mayar na koma daki.

Yau sai da aka yi Isha’i ya Safwan ya dawo tuni na kammala abinci na sheƙa kwalliya muna zaune a falo tare da Hajjo.

Yana shigowa na miƙe na taro shi har sai da ya gota Hajjo ya tsinkayi muryarta tana gaishe shi, ya waiwayo ya amsa sau daya muka wuce sai da muka shiga bedroom ɗin shi ya ce,

“Wace ce wannan ɗin?

Na ce “Mai aiki ce Mami ta kawo min ɗazu.
Amma ba ita ta yi min girki ba ko?
Na daga kai “Ya za a yi in ba wata girkin abiincinka.”

Ya canza kaya muka fita har lokacin tana zaune sai da ya kammala muka dawo kan kujerun falon ta yi min sai da safe ta wuce ɗaki.

Washegari ma sai da na sanya ta ta yi wanka ganin ta kuma mayar da kayan jikinta na yi mata magana, wasu koɗaɗɗun kaya ta sanyo da na gwammace waɗanda ta cire.

Daki na shiga na tsinto mata kayana da za su shige ta don tana da jiki na haɗa da man shafawa da turare na je na ba ta.

Ta yi godiya sosai ta je ta sanya ta dawo tana ta ba ni labari yaranta ma haka suke fama da rashin sutura musamman yammatan.
Kaya sosai na tara na ba ta na ce ta aika musu.

Na yi ta samun baƙi wanda duk yan makarantarmu ne, har Raihan da ba su samu zuwa bikin tarewar tamu ba sai ga su ita da mijinta daga Bauchi suka yi kwana biyu, kwana ɗaya gidan Mami ta yi min kwana ɗaya ranar da ya Safwan bai gidana.

Sati na biyu na dawo makaranta tare da ya Safwan muka dawo, ya yi horn kenan kafin a bude gidan da ke jikin namu wata mota ta fito da alama mai gidan ne da matarsa wadda ba za ta wuce sa’a ta ba.

Ya ɗago ma ya Safwan hannu kafin ya buɗe ya fito shi ma ya fita suka gaisa sai ya dawo wuri na “Fito ki shiga gidan nan Mami, ku gaisa da matar gidan.” Na ce mishi “To na buɗe na fita ita ma fitowar ta yi cikin fara’a ta taro ni muka shiga gidanta a ƙayataccen falonta ta sauke ni ta sanya mai aikinta ta yi ta kawo min abin ciye-ciye har da abinci ruwa kawai na sha muka gaisa sosai ta ce min sunanta Khadijah watanta takwas da yin aure ni ma na gabatar mata da kaina ta ce tana fata za mu yi zumunci na ce in sha Allah.

Ta ce gidan da ke kallon nawa matar gidan suna abin arziki ita ma duka shekarar ta daya da rabi da aure za ta shigo da yamma idan ina da lokaci sai mu shiga wurin ta na ce ba damuwa na miƙe na ce “Bari in je za ku fita an bar ogan, ta yi murmushi “Ko dai kin bar angon ya zauna gida shi kaɗai?

Na rufe baki “Kai ba haka ba ne, bari in tafi sai kin shigo.

Wani kyakkyawan agogo da ta rako ni ta ba ni ta ce tana business na online tana yin odar kaya daga Dubai da China idan na dawo sai in duba muka yi musayar lambar waya na yi mata godiya na fita.

Ana yin sallar laasar kuma na idar da sallah sai ga ta na tarbe ta da kyau ni ma na karrama ta yadda ta karrama ni da za mu fita kuma na ɗauki haɗaɗɗen turare na ba ta muka shiga gidan wadda ta kira Hafsa ita ɗin ma ba ta wuce shekarun namu sai dai ita mijinta babban mutum ne tana da kishiyoyi har biyu amma suna Sokoto garin mijin, ita kuma iyayenta a Suleja suke.

Ta karbe mu faran-faran muka zauna hira kamar sun dade da sani na tana da yarinya yar wata uku, kuma makarantarmu guda sai dai ita tana shekarar karshe tana karanta political Science.

Ganin yamma ta yi sosai na ce zan tafi gida Khadijan ma ta miƙe ta ce mu je Hafsa ta yi mana addu’a sosai ta Allah ya kauda shaidan a tarayyar mu ya sa mu zauna da juna domin Allah, ya sa taren ta dore mana har aljanna muka shafa ta raka mu har get ɗinta ta ba mu turare na gida.

Na shiga na ga Hajjo tsaye kusa da mai gadi.
Ta washe baki sai ta taho wurina tana “Haj sannu da dawowa.” Na yi ɗan murmushi “Yawwa Hajjo.

Muka shiga ciki tana biye da ni na ce “Me kike yi wurin mai gadi? Ta sosa kanta “Wallahi wayarsa na je ya ara min na kira yara.”

“Ke ba ki da wayar? Ta langaɓe kai “Ana ta kai wa ke ta kaya Haj? Ana ta abin da za a ci ina a ke ta waya? Na kaɗa kai.

“Haka ne.”

“Ina dai da sim shi, lambar da nake kira take ciki.
Jakata na buɗe na ciro kudi na miƙa mata “Kai wa mai gadi ki ce ya sawo min ƙaramar waya.”
Ta karba ta juya cikin sauri, na wuce ciki.

Har na idar da sallar magrib ta shigo ta ce Isya mai gadi yana magana na fita wayar ya ba ni har da canji na ce ya riƙe canjin ya yi godiya ya fita ita kuma na miƙa mata wayar na ce “Ina SIM ɗin da kike kiran yaran naki? Cikin sauri ta kwanto haɓar zanenta na ce sai ki sanya in kin caza wayar ki riƙa magana da su.”

Ta ce “Ban iya ba amma bari in je Isyan ya koya min. Ta fita da sauri.

Da ya Safwan ya dawo yana aikin shi ina ba shi labarin su Khadija da Hafsa yana saurare na, karshe na roƙe shi idan Zainab ta haihu zan je Kaduna. Wani kallo ya yi min “Ba inda za ki ba ki ga abin da ke gaban ki ba?

Na marairaice mishi ina ƙara rokon shi sai cewa ya yi “Oya tashi mu je mu kwanta.

Tun kuma ranar muka shiga hulɗa ta mutunci ni da su Hafsat muna shiga gidan juna mu yi hira ita Hafsa ma muna yawan haɗuwa a makaranta cikin lokaci kaɗan na yi matukar sabo da su.

Wata ranar Laraba na tashi barci jin kamar ana kuka ya sa na buɗe ƙofa na fito, ban ga kowa ba sai na fita.

Hajjo na samu a bayan dakuna tana sharbar kuka shaɓe-shaɓe kiran sunanta na yi ta taho hawaye na zuba na tambaye ta me ya faru tana fyace hanci ta ce yar ta ta farkon ta kira ta wai saurayinta ya ce zai karɓo a karɓar mishi kayan shi daga ba ranar auren. Na ɗan yi shiru sai na ce To ki yi shiru ke kina ta wannan kukan ita ya kike so ta yi? Ke da za ki rarrashe ta.’

Ta share hawaye “To Haj.”

“Ki yi haƙuri in Sha Allah za a san abin yi .”
Na koma ciki.

Kwana biyu na ɗauka ina tunanin abin yi ga wannan baiwar Allah don ta shiga damuwa sosai wannan fara’ar duk babu ko abinci ba ta cika ci ba. Ranar ni ke da girki muna cin abinci da ya Safwan ya tsare ni da ido har na gaji na ce mene ne ? Ya ce “Kin ƙi cin abinci tunanin me kike? Na ja ajiyar zuciya sai na ba shi labarin halin da Hajjo take ciki saboda rashin kayan daki za a fasa auren ɗiyarta, da kuma shawarar da na yanke zan ba ta kudi su je su sayi kayan daki a yi bikin yarinyar.

Har na gama bai ce komai ba sai dai tsare ni da ya yi sai da na ci abincin.

Washegari da na tashi makaranta kafin in wuce gida sai da na tsaya na cire kudi a ATM wadanda nake son ba Hajjo kudin da na san a dai sayayya ta mutumin kauye ta ishe su.

Sai na wuce gida saboda ba ni da girki kwanciyata na yi a daki bayan na ci abinci, da na fito da yamma Main palour na zauna ina latsa wayata chating muke da Zainab, Hajjo ta zo ta zauna a kasa can nesa da ni ta kara gaishe ni sai na tambaye ta yaushe ne bikin yarinyar ta ta? Ta ce ba a riga an sa ba, amma mai auren ya ce aka bari ruwa ya sauka to ya fasa.

Na jinjina kai sai na dauko jakata da ke gefena na buɗe kudin ciki na ciro, ina kallon Hajjo tana mazurai, kamar ta buga tsalle ta sa musu wawa.

“Zan ba ki wadannan kuɗaɗen Hajjo, ki je a saya ma yarinyar ki kayan daki.”

Ƙirji ta dafe.

“Haj kyauta kika ba ni waɗannan uban kuɗaɗen?”

Na ajiye mata ta taso ta ɗauka ƙanƙame su a jikinta sai kuma ta durƙushe ta shiga godiya na ce ta tashi ta je ba komai.

Da ba ta tashin ba tana ci-gaba da godewa ni tashi na yi na koma daki yan gyare-gyare na kama yi a dakin sai na ji shigowar saƙo na duba wayar Alert ne na kudade masu nauyi daga ya Safwan,na kira wayarsa bai daga ba sai na shiga Whatsapp na tambaye shi game da kudin bai ba ni amsa ba har sai washegari da ya dawo gidana mun kwanta na yi mishi maganar ya ce “Ba kin ce za ki yi wa matar can hidima ba shi ne na kawo miki tawa gudunmawar.

Na yi mishi godiya.

Kwana uku da ba Hajjo kuɗaɗen ta same ni wai ƙanenta zai zo ya karbi kudin ya kai wa mahaifiyarta a yi hidimar bikin ita da yarta ta biyu da ke aiki nan ba sai sun je ba saboda aikin su da ba su daɗe da farawa ba.

Hakan aka yi ƙanen nata da suke da matukar kama ya zo ya ya tafi da kudin.

Ranar wata Lahadi na shirya zuwa gidan Mami zuwana kuma na farko tun tarewa ta tare da Hajjo na tafi.

Mami ta yi murnar gani na sai tambaya take muna nan lafiya kamar ba kusan kullum sai mun yi waya ba, na ce Babu.

Da muka keɓe ta ce “Mai aikin da na kai miki ce ta yi fes da ita haka? Lallai kun iya kiwo.”

Na yi murmushi.

Sai yamma sosai muka koma gida.

Washegari da hantsi na shiga kitchen dambun shinkafa na yi mana da ya ji kayan haɗi yana ta ba za ƙamshi na ba Hajjo na mai gadi ta miƙa mishi da ta dawo ta dauki na ta, ni kam sai da na yi sallah na fito na fara ci, ina ci ina kallo Hajjo ta fito inda ta saba zama ta zauna ta zura wa TV ido , tana kuma ta yabon dadin dambun wai ban da gaban ta na haɗa ita kam da ta ce ba ta ga abin da ya hada shi da dambu ba.

Ina sauraren ta aka yi knocking ta miƙe cikin sauri ta tashi ta buɗe zan gani! Aunty Farha ce tana wannan fara’ar ta ta ni ma cikin faraar na taro ta ta zauna Hajjo ta kawo mata ruwa da lemo na yi mata tayin dambu ta ce ta koshi .

Muna nan zaune muna hira har hirar ta ishe ni Aunty Farha ba ta da alamar za ta tafi sai yamma ta ce in kai ta ta ga gidan nawa.

Ban ƙi ba tashi na yi na nuna mata wurina ta ce “To ban ga na ogan ba? Ban ƙi ba na raka ta sai dai muna shiga wanda ya Safwan ke ciki yanzu sai na ga mata ta nemi wuri ta zauna ta dauki remote, ni kam na gaji sai na bar ta na fita na shiga kitchen.

<< Mutum Da Kaddararsa 45Mutum Da Kaddararsa 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.