Ya tari ya Safwan cikin fara'a da girmamawa, ban tunanin ya san da ni ba sai da ya Safwan ya zagayo inda nake ya ce "Fito mana."
Na buɗe na fita, Najib ya dubi inda nake na ce "Sannu ya Najib." Yawwa kawai ya ce min ya ce ma ya Safwan "Bismillah babban yaya."
Ya bi bayan shi ni ma na bi su a hankali.Ya fara ƙwala kiran sunan matarsa ta fito tana mana sannu da zuwa na karbi yarinyarta da ke hannunta ta kawo ruwa da lemo.
Ni dai ina sauraren su suna magana ina ma. . .