Ta dube ni da sauri! Sai ta tambaye ni cikin kwanciyar hankali "Me yake miki?
Shi ma zuba min ido ya yi na ce "Zuwan nan da Ummu Hani ta yi shi ma wani laifi ne da zai tuhume ni akan shi." Fuskarta ta cika da mamaki "Akan me? Ya hana ni mu'amala da duk wanda ya shafi Hassan."
Wannan shi ne ƙarya Sadauki, akan me? Shi kenan mutum idan aka hore mishi mace, mai ladabi da biyayya sai kuma ya shiga cikin lamarin ta ya hana ta sukuni?
"Ba haka ba ne Mamina."
Ya Safwan ya faɗi. . .