Washegari daga islamiyya na wuce gidan Gwoggo Maryama, can na wuni tana ta faɗin kyan da na yi Kano ta karɓe ni.
Sai yamma liƙis na koma gida ina isa kwanciya na yi don wata muguwar kasala da ta lulluɓe ni, sai ga wayar Hassan yana tambaya ta dalilin da ya sa ban shaidawa Inna zan wuce unguwa ba ta wuni da yunwa. Jin muryarsa cikin zafi ya sa na kwantar da murya na bayar da haƙuri, bisa tilas kuma na fito na ɗora girkin don kasalar da nake fama da ita har lokacin, ga. . .