Wata ranar lahadi da ba fita ya Safwan yake ba yana gida, yana tare da Mashkur don ni ina daki sanyi ma nake ji a haka ya shigo dakin da Mashkur a kafadarsa.
Yana sauke shi yaron ya rugo da gudu ya haye ni, daga inda yake ya ce "Ya kika rufa kuma? Na ce "Sanyi nake ji." "To ko za mu koma Hospital din ne? Na girgiza kai "Ba ciwo ba ne sanyin dai nake ji." Ya kira Mashkur ya sauka daga jikina ya ruga ya dane shi shi kuma ya daga shi sama ya ce "Bari mu dan. . .