Skip to content
Part 62 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Wata ranar lahadi da ba fita ya Safwan yake ba yana gida, yana tare da Mashkur don ni ina daki sanyi ma nake ji a haka ya shigo dakin da Mashkur a kafadarsa.

Yana sauke shi yaron ya rugo da gudu ya haye ni, daga inda yake ya ce “Ya kika rufa kuma? Na ce “Sanyi nake ji.” “To ko za mu koma Hospital din ne? Na girgiza kai “Ba ciwo ba ne sanyin dai nake ji.” Ya kira Mashkur ya sauka daga jikina ya ruga ya dane shi shi kuma ya daga shi sama ya ce “Bari mu dan sha iska a baya ko za ki fita? Na ce “A’a. Suka fita na ci-gaba da kwanciyata.

An yi minti ya yi talatin ya kuma shigowa “Wai me ya sa idan na zauna kike turo min yarinyar nan? Cikin rashin fahimta na ce “Wace yarinya na turo maka? Waccan yarinyar mana da idan na zauna kike ba ta ruwa ta kawo min.” Na ce “Wai Sha’awa? Ni ba abin da nake ba ta ta kawo maka.”

Ya jinjina kai “To ba na son tana zuwa inda nake.”

Kaina ya ƙulle sai ban yi magana ba “Bari mu je gidan Mami cin abinci me za mu taho miki da shi? Na ce “Shawarma.”

Suka fita maganar da ya faɗa min kan sha’awa ta hana ni sukuni sai na miƙe dama sanye nake da riga da wando masu kauri har da hularsu, na zura silifas na fita.

Ba kowa falon na wuce dakin su Hajjo muryarta na fara jiyowa tun ban shiga ba tana ma Sha’awa faɗa ta ce ta dafa mata indomie mai dan yaji da romo ta ce ta gaji ta kara da cewa “Ke wallahi Innarmu ba ki bari mutum ya huta, na gama aikin da ke ce za ki yi kuma in miki girki? Ta hau zaginta tana faɗin “Amma in hidimar yaron nan ce ba ki gajiya sai tawa ko? Ta ce “Ai shi ina son shi.” Ta ce “Ni kuma ba ki so na ko? Sai na ji ta yi shiru na kama handle ɗin na shiga da sallama suka dube ni a tare Hajjo na kwance duk ta ɗashe, Sha’awa na zaune gefen katifar tana latsa waya gabaɗayan su suka fara min sannu Hajjo ta ce “Har kin ji ƙarfi Haj kin fito? Na ce “Alhamdulillahi na ji sauki ya naki jikin? Ta ce “Da sauƙi.”

Sha’awa ta ce “Ke dai Innarmu kin ƙi yarda a kai ki asibiti, kalli cikinki yadda ya kumbura.”

Na kai idona kan cikin Hajjo ta yi saurin jan mayafi tana faɗin “Shegiya kumburin uban me ya yi masharranciya.”

Duk da ni ma na ga ya kumbaran amma daga ba ta so a fadi sai na yi shiru na dubi sha’awa da ke zaune da wani ɗan bakin skirt sai riga ƙarama fara manya manyan na fulaninta a fili na ce “Ina kika samu babbar waya haka ta yi murmushi na juya na fita daki na koma na kwanta har ya Safwan ya dawo ya kuma matsa min sai na fito falo cikin kujera na kwanta na dunƙule ina cin Shawarma, Mashkur na wasan shi jin motsi na tashi zaune sai na juya bayan kujerar da nake Sha’awa na gani a yadda na gan ta a dakin su wani abu ya taso min na dubi ya Safwan da ke danna wayarsa ai mantawa na yi da sanyin da nake ji na dira na nufe ta, har ta shiga kitchen ta buɗe fridge tana shirin ciro nama na kira sunanta da karfi ta waiwayo ta amsa cikin ladabi “Yaushe kika fara fitowa haka? Ta ce “Yi haƙuri Haj zafi nake ji.” “Don kina jin zafi sai ki fito haka? Ta kara cewa ki yi haƙuri ta kama hanya za ta fita na ce “Ina za ki? “Zan sanyo ne.” Na ja guntun tsaki “A haka Daddyn Mashkur na nan za ki fita? Bari in kawo miki.” Hijab na fita na dauko mata a dakina na koma na ba ta har ta sanya naman a wuta za ta yi blending kayan miya na ce “Wai me za ki yi ne? Ta karyar da kai yadda Hajjo kan yi “Daddy zan yi ma girki.” Ya Safwan take nufi don haka nake koya ma Mashkur kallon ta kawai na tsaya yi saboda al’ajabi “Dama ke ke mishi girkin ko wa ya saka ki? Na matsa na kashe gas din don har naman ya fara tafasa kuma ya fara hawa kaina, don da an fara girki na ji ƙamshin shi na dinga kwara amai.

“Wuce ki koma ɗakinku.”

Ta wuce na bi bayanta da kallo ko da ta sanya hijab ɗin bai hana bayyanar mazaunanta ba suke kuma juyawa cikin hijab ɗin. Na yi ƙwafa na fita.

Har dare ina tare da ya Safwan don tunanin da ke ta yawo a raina da zargin da ke neman samun matsuguni a zuciyata, zan sa a ido a gidana don zaman dakin da na koma ina ganin yana neman ja min illa.

Har dare ya Safwan bai tafi gidan Aunty Farha ba maimakon tafiya Mashkur ya ɗauka ya ce in zo mu fita muna tafiya ina mamaki.

Wani wurin sayar da kayan maƙulashe ya kai mu ya saya mana muka dawo na shiga daki ina shirin barci sai ga shi cikin na shi shirin, ya hau gado ya kwanta.

Na ce “Ya Safwan Aunty Farha fa? Banza ya min “Kashe min hasken nan.” Na kashe na hau gadon ya matso yana laluba ta, nasan ko na ƙara tambayar shi ba faɗa min zai ba sai na ƙyale shi.

Washegari ma nan ya ƙara kwana ban san me ya faru ba sai da na ji yana waya “Ni Farha za ta wulaƙanta? Ta ce tana son yarta na ba ta haƙuri ta bar ma Mamina daga tana wurin ta, ta ƙara magana na ce mata ba zan iya ce ma Mamina ta ba ni Afnan ba.

Kawai sai ta shirya text ta aika musu ita da Daddy, don ta raina ni shi ne suka haɗa kayan yarinyar suka ba ta.

Ni kuma shi ya sa na bar mata gidan za kuma ta daɗe ba ta ji daɗi na ba.”

Jin ya taho na bar inda nake na koma daki,sai dai muryarsa na ji yana kira na na fito abin mamaki Amir ɗi na na gani na isa cikin farin ciki da yake ya fara girma bai zo ya rike ni ba gaishe ni ya yi yana murmushi, na dubi ya Safwan murmushin shi mai tsada ya yi min.

“Na yi magana da kakar shi ana yin hutun na sa Dr Auwal ya dauko shi shi ya sanya aka kawo shi.

Na zauna murmushin ya ƙi ɓacewa a fuskata. Ya tashi daga inda yake yana leƙa Mashkur da ke barci kan kujera.

Na mike zuwa dakin su Hajjo na same ta zaune ta samu sauƙi na jira Sha’awa ta sanya hijab muka fita zuwa kitchen abinci na ce ta dafa ma Amir, da ta gama na je na ɗauko na kawo mishi.

Ya Safwan ya fita ya bar mu, hira na yi ta yi da shi ina jin daɗin karatu mai kyau da yake samu, ya ce min yana son wata makaranta ta haddar Alkur’ani.

Na ce “Zan faɗa wa Daddy idan ka koma zai sanya ka.

Da daddare da na fahimci ya Safwan nan zai ƙara kwana kamar in yi mishi magana sai na r2iy to ya ce ina na ji na ja bakina na tsuke sai da komai ya lafa a tsakanin mu ya matse ni a kirjinsa ya kira sunana na amsa ya ce “Ki yi haƙuri Bilkisu.” Ƙara nutsuwa na yi jin ya ambaci sunana don sai abu mai muhimmanci.

“Ina son ki Bilkisu, kina da matsayi mai girma a zuciyata da zai yi wuya a samo wadda za ta kamo ki kina min ladabi da biyayya kina mutunta ni, kina gamsar da ni kina ciyar da ni daddaɗan abincinki, ina alfahari da ke.

Zan roƙe ki, abin da ba zan ma wata mace ba, in roƙe ta kan abin da nake da iko kuma mallakina ne.”

Ya ɗan yi shiru jin ban ce komai ba ya cigaba “Ina so in ba Mami Mashkur.”

Duk da na ji wani iri amma na ce “Don za ka ba Mami Mashkur sai ka roƙe ni? Ya ce “E don ki gane girman da kike da shi a idona. Shi ya sa na matsa da ɗauko miki Amir don ya ɗebe miki kewa.

Shi kenan washegari ya Safwan ya sani na haɗa kayan Mashkur muka tafi gidan Mami har Amir muka tafi.

Za mu tafi Mashkur din ya yi barci ta ɗauke shi don zuwa ta kwantar da shi na bi ta a baya tana kwantar da shi na murɗa kofar na shiga da sallama ta juyo da murmushi “Ya aka yi ?

Na ce “Mami kwana uku kenan ya Safwan bai kwana gidan Farha ba.”

Ta cika da mamaki “Saboda me ? Na ce “Ban sani ba.” Ta ce “Mu je in ji.”

Muka fita, har sai da muka shiga mota Daddy ya kira shi a waya ya fita.

Mun daɗe muna jiran shi sai ga shi tun da na ga ya ƙi min magana nasan ya gane ni na faɗi sai da muka isa yana ɗaukar hula a cikin hulunan shi na ɗane bayan shi ina shafa shi tun yana cewa in bari har ya haƙura muka hau gado, sai wajen sha daya ya tafi.

Da safe na tashi nonona kaɗan ya kumbura kuma bai min zafi Mami kuma ta ce kuka kaɗan Mashkur ya yi.

Da wuri ya dawo gidan don Mami ta ce kar ya zo idan Mashkur ya gan shi zai yi kuka. Ina fitowa yau ma ganin Sha’awa na yi da wata yar riga da ta kama ta ta toni asirin komai na jikinta sai zane da ta daura, na isa da sauri yau kashedi na kwakkwara mata na ce idan ta ƙara min haka zan sallame su na koma wurin ya Safwan da ganin na haɗa fuska ya ce “Meye kike ta faɗa? Na ce “Ba komai.

Sai ga Hajjo washegari tana ba ni haƙuri na ce ta gaya mata ta bari ta yi ta ban haƙuri.

Da yammaci ne na dan ji ƙarfin jikina sai na fita waje inda aka jera kujeru don shan iska ina cin Apple ina kallon harabar gidan. Isya ya wangale get, ganin motar da ta shigo gidan abin ya ba ni mamaki Farha ce cikin rawar jiki Isya ya buɗe mata kofa ta fito ya bude Boot ya dauko ledoji guda biyu ya biyo ta da su ina ta kallon ta har ta ƙaraso, na ce “Barka da zuwa Aunty Farha.” Aunty Farha ta yi fara’a “Yawwa Nana.” Na miƙe muka shiga ciki na kira Sha’awa ta kawo mata ruwa ta fito cikin doguwar rigar atamfa da ta zauna a jikinta tunda ta fito Aunty Farha ke duban ta har ta kawo ruwan ta juya ɗakinsu.

“Wace ce wannan Nana? Na ce “Yarinyar Hajjo ce.” A ɗan razane ta ce Yarinyarta kuma? Na ce “E.” Ya Safwan ya shigo ina yi mishi sannu da zuwa ta sunkuyar da kanta ya wuce ciki bai zauna ba na ce mata ina zuwa ta turo min ledojin da ta zo da su “Ga shi nan a ba Mashkur.”

Na ce “An gode ba ki zo min da Afnan ba? Ta ce ba ta dawo Sch ba. Ta mike na ce “Na gode. Ta fita na nufi wurin ya Safwan ina tunanin Aunty Farha kamun ƙafar laifinta take shi ne har da zuwa da kawo ledoji don ko haihuwar Mashkur din wando ba ta bayar ta ce a ba shi ba.

Ya Safwan yana zaune na zauna kusa da shi na ba shi ruwan da na zuba mishi ya sha mur sai na zargi maganar Farha ne bai so in yi mishi sai ban yi ba.

Washegarin ranar ya yi tafiya zuwa Ikko kawai sai na ji ina sha’awar shan dan farfesun kayan ciki ni da ban cin komai ya zauna na fita na ɗora, cikin hukuncin Allah ko da ya fara ƙamshi ban yi aman ba sai ga Hajjo ta kasa ta tsare in kawo aiki ta yi ina gama dahuwar na zuba masu na zauna a falo na gama ci sai ga Sha’awa da gudu Innarta tana ta amai na ce ta je ta gyara ta zan je asibiti yanzu sai mu tafi tare.

Taren muka tafi su na ce su fara shiga na zauna ina jira likitan ya aiko in shigo na shiga Scanning na samu likitan ya gama mata muka ƙara gaisawa na tambaye shi abin da ya same ta, sai da ya ɗago daga rubuce rubucen da yake ya ce ciki ne karami sai ya fara ƙwari za ta samu lafiya. A tare ni da Sha’awa muka haɗa baki wurin faɗin ciki? Hajjo ta sunkuyar da kai

<< Mutun Da Kaddararsa 61Mutum Da Kaddararsa 63 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.