Yadda Hassan ya ce hakan aka yi muka haɗu a inda ya ce muka lula Kaduna. Hotel ya kama mana muka yi kwana biyu tunda na shiga garin nake tuna ɗana Amir yana cikin garin nan ko a wane hali yake oho, ina tsoron ya rayu a yadda na rayu ina da uwa amma kamar bani da ita ba wata soyayya ko shaƙuwa tsakanin mu saboda rashin zama tare.
Ya kan fita ya yi harkar da ta kai shi idan ya dawo mu fita tare mu ɗan zagaya gari, sai dare mu dawo.Da muka dawo inda ya. . .