Al'amura masu tsayawa a rai sun faru a wannan haduwa ta mu. Ya Safwan ya susuce ya nishaɗantu ya gamsu har ya sa da komai ya lafa na fara jin kunyar shi. Fitar da bai kuma ba kenan sai washegari, abinci ne dai ban samu nasara ya ci ba, na yi nadamar yin maganar nan, da na yi haƙuri ban tanka ba, ba ga shi ya wuce ba.
Da zai fita tare muka fita zuwa gidan Mami ya sauke mu ya wuce.
Tun da Afnan ta dawo makaranta tana liƙe da duk wanda ya dauki Mashkur. . .