Skip to content
Part 2 of 13 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Ko da wasa bacci bai yi attempt na kusanto inda suke ba, bare har ya iya ɗaukarsu a wannan dare. Kwana suka yi suna kai kokensu a wurin Allah da duk kalar addu’ar da suka iya, domin bala’in da suke ji a rayukansu ya fi gaban kwatanta ce.

Da asuba suna gama Sallah Deena ta ɗauki waya, ba tare da ta yi shawara da Deeni ba ta danna ma number Lalu kira, wanda shi ne kaɗai ƙanensa namiji, sauran ƴan’uwansu duk mata ne.

Shigar Lalu a blanket kenan wayarsa ta ɗauki ruri, “Call, da sanyin asubar nan?”, Abin da ya faɗa a ransa kenan, lokaci ɗaya kuma ya lalubo wayar da ke gefensa, bai yi mamaki da ganin number Deeni ba, saboda akwai maganar kai Hajiyarsu asibiti, wanda aikin Lalu ɗin ne a kowace Monday, har idan Deeni na da uzuri.

Ransa a ɗan ɓace ya ɗaga kiran, saboda wartsake masa baccin da Deeni da aka yi, da mamaki sai ya ji muryar Deena tana faɗin “Uncle Lalu”, Ras! Gabansa ya faɗi asanadin raunin muryarta da ya ji, amsawa ya yi da “Ya aka yi ne Dee-dee.?”

“Dan Allah ka zo gida yanzu, Yaya ne ba lafiya”, ɗan yaye blanket ɗin ya yi tare da tambayar ta “Me ya same shi?”, Shesshekar kukan da take yi ne ya ba shi cikakkiyar amsar da ke nuna Deeni na cikin damuwa, ya buɗe baki zai sake tambayar ta ya ji ta tsinke kiran.

Hausawa suka ce “Babban Yaya Uba”, duk inda hankalin Lalu yake sai da ya tashi, domin ciwon da zai sa a kira shi da sanyin safiyar nan ba ƙarami bane, uwa uba kuma ga ƙauna ta jini ɗaya, musamman da ya kasance Deeni ne ya tsaya masu a komai ba tare da gajiyawa ba.

Zaune ya tashi tare da cigaba da kiran number Deeni, amma har kiran ya tsinke ba’a ɗaga ba. Ransa cike da son sanin a bin da ya samu ɗan’uwansa ya sauko daga kan gadon, sweatersa dake yashe a kan gadon ya ɗauka, akan shirt ɗin jikinsa ya ɗaura ta, lokaci ɗaya kuma ya rufe kansa da hular dake manne da sweater. Key ɗinsa da ke kan bed side locker ya ɗauka, isar sa bakin ƙofa kenan number Deeni ta shigo wayarsa, da hanzari ya ɗaga kiran da sallama, daga can cikin wayar Deeni ya amsa haɗe da faɗin “Lalu, ɗan Allah kada ka bari Hajiya ta san bani da lafiya, kawai ka yi dubara ka fito.”

Lalu bai yi jayayya da shi ba ya ce “Okay Insha Allah,” saboda ya fi kowa sanin Hajiyarsu bata da cikakkiyar lafiyar da za ta iya jure ko da ciwon kai ne na ɗaya daga cikin ƴaƴanta, bare kuma wannan bala’in mai zaman kansa.

Key ya sa ma ɗakinsa, sannan ya nufi ɗakin Hajiyar, don ya san ƙa’ida ne a wannan lokacin zaune take tana azkar, kuma duk dubararsa sai ta ji fitar sa.

Gefenta ya zauna a kan babban abin sallar da take zaune, cikin ladabi ya gaishe ta, bayan ta amsa ne ta ce “Sai ina da sanyin safiyar nan?”, amsa ya bata da “Wani abokina ne ya gayyace ni raɗin suna, shi ne zan je”, ta san shi ɗin na jama’a ne, shi ya sa bata yi musu ba ta ce “A dawo lafiya, amma asibitin fa?”, Tabbatar mata ya yi da a kan lokaci zai dawo su tafi, don ƙarfe tara take ganin likita, yanzu kuma shida saura kaɗan.

A can gidan Deeni kuwa faɗa ya yi ma Deena a kan gaugawar kiran Lalu da ta yi, zuciyarta a dake ta ce “Haba Yaya, wai me ya sa kamar baka son su sani ne, kada ka manta damuwarka fa damuwar Lalu ce”, ta zabure mashi haka ne, saboda ta fahimci idan ta sa wasa su kaɗai tashin hankalin zai kashe.

Shiru Deeni ya yi na wuccin gadi, kafin daga bisani ya ce “Ki koyi juriya kin ji ko Deena, kuma Hajiya ce bana son ta sani, kin ga ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba”, a yadda ya ƙarashe maganar cikin raunin murya ne ya ƙara mata tausayin sa, take ta sauko daga fushin da ta yi ta ce “Insha Allah ko da Hajiya ta ji zata yi haƙuri, saboda wannan jarabawar ta mai imani ce.”

A hankali ta yi ta ba shi magana, har ya ɗan gamsu da ita, gefensa ta dawo ta zauna tare da kwantowa a jikinsa suka yi shiru.

Ba a jima ba mai acaɓa ya kawo Lalu a estate ɗin, kiran wayar Deeni ya yi tare da tabbatar musu da ƙarasowar sa. Yana cikin hasashen yanayin da zai tarar da ɗan’uwansa ne Deena ta zo ta buɗe, idanunta da suka ƙanƙance saboda kuka ya kalla, lokacin da ta ce “Har ka iso?”, kai kaɗai ya jinjina mata, domin jikinsa ya yi sanyi sosai.

Ciki ya shiga, ita kuma ta rufe ƙofar, yana shirin zama falon ne ta ce mashi “Ka shigo ciki”, bai yi musu ba ya bi bayanta har bedroom ɗin Deeni, zaunen da ya same shi a kan abin sallah ne ya ɗan sassauta mashi bugawar da zuciyarshi ta ke.

Gefenshi ya zauna a kan abin sallar, lokaci ɗaya kuma ya miƙa mashi hannu tare da faɗin “Ya jikin?”, sai da Deeni ya ɗan nisa kafin ya ce “Da sauƙi”, Deena kuwa gefen gado ta zauna, tunaninta wane kalar ruɗu Lalu zai shiga idan ya ji damuwar ɗan’uwansa.

“Wai me ke damunka ne?”, Tambayar da Lalu ya yi masa kenan, domin Deeni bai sake magana ba, duk da har yanzu hannunnsa na cikin na Lalu.

“Lalu bana gani, akwai yiwuwar na maka ce”, tashin hankali ba a sa maka rana, tabbas tunda Lalu ya zauna ya lura da sauyin idanun Deeni, amma sai ya ba ranshi duk zafin ciwo ne ya kawo haka.

Tamkar faɗowar aradu ya ji maganar, mafarin ya ce “Kamar ya ba ka gani?”, don ya kasa gasgata maganar.

Tabbatar mashi da Deeni ya yi cewar ya fa makance, aikuwa ya shiga sallallami da salatin Annabi. Iya ruɗu Lalu ya shiga, Deeni da lalurar ke a jikinsa ne ya riƙa ba shi haƙuri.

Cikin tsananin kuka Lalu ya faɗi similar to abin da Deena ta faɗa “Ta ina zan iya jurar ganin ka cikin wannan halin?”, amsa Deeni ya ba shi da “Ta yadda Allah ya tsaro Lalu, ku ɗauki juriya kawai, amma it feels like this condition is permanent.”

Da hanzari Deena ta tari numfashinsa “Ɗan Allah Yaya ka dena faɗar haka, Insha Allahu you will be fine”, hannu Deeni ya miƙa mata alamun ta matso kusa da shi, hakan kuwa ta yi, ita da Lalu suka sanya shi gaba suna ta kuka.

Shi ɗin dai ne ke ta tausar su da maganganu masu nuna tsantsar dangana, inda ya ce “Toh idan mutuwa na yi fa ya zakuyi? Ku bar ma Allah lamarinsa kawai, na san tsabar ƙaunar da yake mani ce har ya jarabce ni da wannan, ina roƙon sa da ya sa hakan ya zama silar shigar mu aljanna ni da ku.”

Haƙiƙa tawakkalin Deeni ya kai a buga misali da shi, sosai maganganunsa suka ƙara ma Lalu mugun tausayin sa, tursasa ma Deeni ya yi a kan su yi gaugawar tafiya asibiti yanzu.

Heater Deena ta haɗa, Lalu da kansa ya yi masa jagora zuwa ban ɗaki don ya yi wanka, sannan ya fito ya ba shi wuri. Deena kuma kitchen ta zarce ta haɗa musu Black Tea, don shi kaɗai ne za su iya sha.

Cikin ɗan ƙanƙanen lokaci suka kimtsa tare da fitowa, sa’ar da suka samu kuma ba neighbours ɗinsu ko ɗaya a waje, mai gadi da ke can bakin gate da uban garwashi a gabansa ma bai iya tantance me ke wakana ba. Motar Deeni suka shiga da nufin tafiya, kafin Lalu ya tada motar ne Deeni dake zaune a gaba ya ce “Lalu, ka nutsu ka kai mu asibitin nan lafiya”, kamar ya san abin da ke ransa kenan, don kuwa Lalu tunani yake ta ina ma zai iya driving motar a cikin wannan yanayin.?

“Ok, Insha Allah”, Lalu ya faɗa cike da ƙwarin guiwa, lokaci ɗaya kuma ya tattaro dukkan nutsuwarsa sannan ya sa ma motar key. Mai Gadi na hango motar Deeni ya miƙe tare da buɗe gate ɗin, suna isowa kusa da shi suka gaisa, sannan Lalu ya ja motar suka nufi asibiti.

Lawwali, wanda sunan maigadin ne. Da tunani suka bar shi, don ya lura da sanyin jikin Deeni, “Allah ya sa dai lafiya”, ya faɗa a fili, lokaci ɗaya kuma ya koma kan bencinsa ya cigaba warming jikinsa..

Tunda suka hau hanyar asibiti har suka isa ba wanda ya ce ma wani kanzil. Dama tuni sun sanar da wani Opthalmologist, wanda tsohon friend ɗin Deeni ne, cewar zasu zo, shi ya sa kai tsaye suka nufi office ɗinsa, tun kafin su ƙarasa ya fito tare da yi musu iso a ciki.

Kafin su zauna ne wani mutum ya biyo bayansu a fusace, “Haba likita, tun da asuba muke nan, amma daga zuwan waɗannan ka shigo da su”, gaba ɗayansu basu ji daɗin abin da mutumin ya yi ba. Wani irin kallon ƙuluwa Lalu ya jefi mutumin da shi, kawai dan ba huruminshi bane, amma da ya ba shi amsa dai-dai da shi.

Wannan ba sabon abu bane a wurin likitan, don ya ga mafiyin haka a wurin mutane, mafarin sai da ya daidaita zamanshi a mazauninsa sannan ya dubi mutumin da ke ta huci, sassauta murya ya yi kafin ya ce mashi “Ka yi haƙuri Malam, ka ga kai da ƙafafunka ka shigo nan, shi kuma ba ka lura sai da aka yi masa jagora ba?” 

Kallon Deeni mutumin ya yi, kwarjini da tausayinsa ne suka cika ma mutumin rai, domin duk inda tsayayyen namiji ya ke, toh Deeni ya kai nan, amma sai gashi an riƙe masa hannu kamar ƙaramin yaro. Jikin mutumin a mace ya maida dubanshi ga likitan, kasa magana ya yi saboda kunya, aikuwa likitan ya ƙara jibga kashi wata kunyar ta hanyar faɗin “Yanzu kai da shi wa ya fi bukatar ganin likita?”

“Gaskiya ya fi ni buƙata, kawai yadda ka shigo da shi ne ya fusata ni.” haƙuri likitan ya ba shi, aikuwa ya fice jiki ba ƙwari.

Kujera biyu ce a gaban babban table ɗin likitan, Sai da Lalu ya taimaka ma Deeni ya zauna, sannan shi ma ya zauna. A cikin previous memory ɗin Deeni ne ya riƙa kallon fuskar likitan, duk a lokacin kuma zuciya na hakaito mashi yadda suke fuskantar juna.

“Mutane sai haƙuri”, likitan ya faɗa cike da sosuwar rai, Deeni da shi ma ya san halin jama’a ya ce “Wallahi kuwa, Allah dai ya bamu mafita”, sai da Lalu ya yi ƙwafa kafin ya ce “Amiin dai.”

Gaisawa suka yi, tare da jajanta ma juna a kan wannan lalura da ta samu Deeni, daga bisani kuma professional Opthalmologist ɗin ya shiga aikinsa, bayan ya tabbatar da attention ɗinsu na tare da shi ne ya gwada B.P ɗin Deeni, kafin daga bisani ya ce mashi “Faɗa mani duka damuwarka.?”

Rayuwa kenan, sosai hankalin Deeni ya tashi, wai yau shi ne a gaban likita yana mashi tambaya, take ya tun ba a je ko ina ba ya ji kewar aikinsa, don sai wanda Allah ya zaɓa ne ke kaiwa irin position ɗinsu.

Cikin raunin murya ya ce “Lost of vision as you know, before hakan kuma na fara da headache mai zafin gaske, har ina jin kamar idanuna zasu faɗo, kuma har yanzu ma da headache ɗin.” cike da tausayinsa likitan ya jinjina kai, Lalu kuma yadda Deeni ke ƙyafta eyes ɗinsa ne ya ɗaga mashi hankali, hannun Deeni ya dafa, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin sa ma zuciyar Deeni dakiya.

Prescription likitan ya fara rubutawa, “Tsawon wane lokaci ka ɗauka kafin faruwar hakan?” Ya sake jefo ma Deeni tambaya.

Ɗan shiru Deeni ya yi yana nazari, daga bisani ya ce “I can’t remember”, jinjina kai likitan ya yi “Okay, so nake na san meye silar, kafin na yi examine ɗinka.”

Deeni ya ce “Ba komai, go ahead.”, Tambayoyi ya shiga kwararo ma Deeni game da cutuka masu haddasa Sudden blindness, amma Deeni baya da cuta ko ɗaya, idan ma akwai toh bai sani ba, daga ƙarshe ya ce “Am sorry to say kana amfani da kayan maye?”, Ko kusa Deeni bai ji haushi tambayar ba, saboda duk a cikin aiki ne.

“Wallahi Shaheed, ko cigarette bana sha”, ya faɗa tare da girgiza kai, Lalu da ke ta sauraron su ya ce “Wallahi kuwa”, dan tambayar ta taɓa mashi zuciya.

Da ƴar dariya a bakin Dr. Shaheed ya ce “Toh family history fa?”, Nan ne kaɗai ya samu amsar da take “Eh”, domin kusan Family ɗin babansu suna da matsalar idanu, sai dai ba a taɓa samun wanda ya makance ba.

Dr. Shaheed ya ce “Okay, Family history, da hawan jini, sannan kuma da alaƙarka da screen ne abin da na iya samu cikin abubuwan dake haddasa wannan lalurar, though ban yi examine ɗin ka na ga ko akwai wani ciwo cikin idanun ba, kun ga sai mu yi fatan Allah ya sa lalulrar mai iyaka ce”, ya ƙarashe maganar yana duban Lalu, cike da kyakkyawan fata Lalu ya ce “Amiin.”

Ɗaya daga cikin tools ɗin dake kan table ɗin Dr. Shaheed ya jawo, Opthalmoscop ɗin ya daidaita a gabansa, wanda da shi ne zai haska cikin idanun Deeni. Da taimakon Lalu Deeni ya saita kansa a scope ɗin, cike da ƙwarewar aiki Shaheed ya shiga aikinsa na binciken wane hali idanun Deeni suke ciki.

A ƴan tambayoyin da ya yi ma Deeni ne ya fahimci akwai yiwuwar ya warke, indai aka nace da magani.

Bayan ya matsar da tool ɗin a gefe ne ya ce “Matsalar mai sauƙi ce Insha Allah, yanzu zan baka magani, sannan za a ayi maka Glass, may be idan ka fara amfani da su ka cigaba da gani, idan kuma matsalar bata kau ba, toh theater ce abu na gaba.”

Godiya sosai suka yi mashi bayan Lalu ya karɓi prescription ɗin. Magana mai kwantar da hankali ya faɗa musu cewar lalurar Deeni mai sauƙin magancewa ce, daga bisani kuma ya rako su har bakin motar su.

Shigar su motar ke da wuya wayar Deeni ta fara ruri, Lalu ne ya duba wayar “Hajiya ce ke kira”, sai da Deeni ya furzar da iska mai hucin gaske kafin ya ɗaga kiran, amsa sallamar da ta yi mashi ya yi, bayan sun gaisa ta ce “Yau ne asibiti fa”, bai bari ta sa ran zai kaita ba ya ce “Yau da wuri na fita aiki, amma mun yi magana da Lalu yanzu zai kai ki”, daga can ta ce “Toh shikenan, bana son yin latti ne.”

“Insha Allah ba da jimawa ba zai zo”, ya faɗa cikin juriyar da baya son ta fahimci yana cikin damuwa. A kan jikinsa ya aje wayar bayan sun yi sallama, kwantar da kansa a bayan kujera ya yi, a ransa ya ce “Allah ka dubi raunina, ka ba ni lafiya mai ɗorewa”, hawaye masu kauri ne suka ɓuɓɓugo mashi a Idanun, da ƙarfin hali ya haɗiye kukan, don baya son ɗaga hankalin Lalu, tada motar Lalu ya yi suka tafi, a kan hanya suka tsaya wani babban pharmacy suka sayi magani, glass ɗin ne suka bari sai zuwa anjima saboda uzurin Hajiyarsu.

Da isarsu gida Deena ta buɗe musu ƙofa, sannu da zuwa ta yi musu, inda Lalu ya yi ma Deeni jagora suka ƙarasa Falon gami da zama.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya faɗa musu yadda za a yi amfani da magungunan, kafin daga bisani ya bar gidan da nufin idan ya gama da asibitin Hajiyar zai dawo.

Hajiyarsu kuwa a shirye tsaf ya iske ta a falo, tsegumi ta fara yi mashi “Ku kam kuna wasa da lokaci, tun ɗazu muka yi magana da Deeni ya ce kai zaka karɓi motar, amma shiru sai yanzu”, cikin ladabi ya russuna “Sorry Hajiyarmu, da ƴar tazara a tsakanina da gidan”, sandarta ya miƙa mata, ta karɓa tana dogarawa saboda ciwon ƙafafu, kai tsaye asibiti suka nufa.

Bata wani damu sai ta ga Deeni ba, duk da a asibitin yake aiki, saboda tana da tabbacin aikin gabansa ya ishe shi. Likita ta gani kamar yadda ta saba. Bayan ta fito ne ta dubi Lalu, take ta gane akwai abin da ke damun sa “Lalu, anya kana da lafiya kuwa?”, ta tambaye shi lokacin da suka nufi motar su, da tsiya ya ƙaƙaro yaƙe ya ce “Lafiya ta lau Hajjaju, kawai yunwa nake ji”, ce mashi ta yi “Toh da mun je gida ka ci abinci, ka san bana son ana zama da yunwa”.

Cike da ƙauna gami da tausayin mahaifiyarsa ya ce “Toh Hajiyata, Allah ya ƙara maki lafiya”, ta ce “Amiin.”

Buɗe mata motar ya yi ta shiga seat ɗin baya, shiga shi ma ya yi suka ɗauki hanya.

Sun kusa gida ne ta ji faɗuwar gaban da bata shirya ba, neman tsarin Allah ta shiga yi cikin sautin da ya fito fili.

Lalu da tuni damuwa ta bi jikinsa ya tambaye a “Me ya faru?”, Amsa ta ba shi da “Faɗuwar gaba nake, Allah ya sa ba wani abu ke shirin faruwa ba…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutuwar Tsaye 1Mutuwar Tsaye 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×