Skip to content
Part 18 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Jin qarar tsaida motar ya sa ni dawowa daga duniya tunanin rayuwata da na fa’da Yaya Samir na ‘dago na kallah nima ni yake kallo a daidai lokacin,kafin na maida kallona bakin titi dan duk tunanin da na fa’da na tabbatar rabin Kano ma ba muyi ba,a daji Yaya Samir ya tsaida motar,na sake kallonshi da yanayin tsoro,saboda rashin tsaron da ke qasar a ‘bangaren Katsina abun yafi tsanani,na fara magana ga Yaya Samir da tsoro qarara fuskata
“Yaya Samir naga ka tsaya daga nan,ko babu mai ne?”

Kai ya girgiza min,”Ko ‘daya Sumayyah natsuwarki nake so ne,Dan Allah ki daina tunani ko baki fa’da min ba nasan ki nayi bazan iya ciro zuciyarki ba da nacirota na cire miki tunanin,dan Allah Sumayyah kiya haquri da abunda ya faru Samir na tare da ke ki yafema Abbah mu masa addu’a Allah yasa ya gano gaskiya,abun nashi ba yamin da’di banda Ummi ma sai yafi haka Sumayyah inaji ne ina ma Abbah Abdullahi da Ummi Hauwa’u iyayena duk rayuwarku zan jureta hakama ina tayaku rayuwar,Sumayyah ina sanki ko badan  halinki ba da Abbah Abdullahi,umminku ma kin cancanta a so ki aso zama dake a qarar da komai dan samun ki,inaji dan ko baki dauko halin iyayenki duka ba kin dauki wani bare ma nasan Sumayyah kin zarta su ma,dan Allah Sumayyah ki yarda dani,karki manta da rayuwata ki kar’bi wani komai da’dewa Sumayyah,ni ne ke,ke ce ni”

Kallonshi nayi ina hawaye,tare da rasa me zance nayi qarfin hali na ce”Dan Allah Yaya Samir ka ja motar mu tafi haka ina tsoron wani abu ya samemu anan,bansan amsar da Zan baka ba ba abinda ke min da’di ,bare har nayi tunanin gano cancanta da kake gani kai da Halima kuna ta cemin NA CANCANTA,har yau banganeta ba,Dan Allah karku qarama zuciyata ra’da’di ku barni haka,nafi yarda da maganar Abbah Hashim ne,ban da wata cancanta,inama rantsuwa da Allah mu talakawane abincin yau da gobe kullum muke nema,na yarda da Kai ne na biyoka nan na tsallake mutane mafi daraja a bayan iyayena amma ga makomata anan haba Dan Allah me zance wai…..”kuka kawai na fashe da shi to me Zan ce ne wai wata jin wani zafi nake daga zuciyata zuwa kirjina

Lallashina ya fara”Haba Sumayyah dan Allah ki bar kukan ka da kisa nayi nasan komai Sumayya nasan nayi laifi dan Allah kada kisa zuciyata ta qara qunci banajin da’din abinda ya faru ina sanki Sumayyah, duk duniyar da Kika shiga zan tayaki shiga ne Sumayyah,ni ma fa Katsinan ba tamin da’di bana jin zan sake komawa katsina Sumayya Nima na barota saboda ban cika alqawarin da na daukarma Abbah Abdullahi akanki ba”

Da kallon mamaki da goge hawaye nake kallonshi”Yaya Samir ni din fa na yafema,Nima Mai laifi ce,amma karka tafi ka bar Ummi dan Allah ina zakaje Yaya Samir”

Murmushi na ga Yaya Samir yayi kawai”Ai Sumayyah zamana ba shida anfani zanje nima na samu rayuwar da zan tsaya da qafafuna saina dawo na aureki dan Allah,banajin da’di nima dama ina Shirin barin katsinan abokina ya kirani zan samu aikin da yafi nanan,Allah Sumayya banaji zan iya zama anan babu ke din,dan Allah ki bawa wancan haquri Sumayyah”

Daganan yaja motar muka cigaba da tafiya,shirun kurame ya cigaba da ratsa tsakaninmu,na rasa gane duniyar tunanin da zan fa’da duniyar batamin da’di abubuwan sun cunkushewa zuciyata, qarar taka burki ya sa na farka daga barcin da nayi a motar a lokacin na kallo agogon dake jikin motar 4:00pm dai dai ta window nake kallon mutanan da ke alwala suna shirye shiryen tafiya masallaci sai sannan na gano inda nake mun qaraso layin gidanmu muna gefen gidanmu daidai qofar gidan Alhaji Yassar Makama masallacin jikin gidansa ake ta shiga sainaga unguwar tana  sauyawa a idona maganar Yaya Samir ta katseni

“Sumayyah mun qaraso fa muje na sauke miki kayan,ina sauri ne”

Kallonshi nayi ido cikin ido abinda banwai ta’ba yi ba”Yaya Samir ba zaka shiga ka gaida su Umma ba”

Kai ya girgiza”Haba Sumayyah idan na shiga me kike tunanin zan ce musu,bazan ta’ba iya ha’da ido da Ummi Hauwa’u ba,bare Abbah Abdullahi”

Wani hawayen naji yana qoqarin fitomin nayi qoqarin gogesu na bu’de murfin motar na fito da ciwan jikin dukan da Abbah Hashim yayimin sai yanzu jikina kemin tsami dana tashi,Yaya Samir kayana ya fiddomin ina gefe tsaye sai lokacin na lura da qaton jakarshi a gefen da ya ciro tawa,yaja boot din ya rufe,aljihu yasa ya fito da ku’di ya mikomin nayi kamar ba Zan amsa ba ya ha’demin rai na amsa nayi godiya ya kalleni

“Kiya haquri Sumayyah,kowa da yadda rayuwa ke zuwa masa,dama nayi niyyar maidoki gidan,amma naso da shirin na biyamiki ku’din ko neco ce,tunda abokina ya kirani maganar aikin da na da’de inasan samu a saboda ke da na haqura dana Katsinan amma Abba ya kasa fahimta,bazan iya ha’da ido dasu Ummi Hauwa’u ba, nasan na tauyemiki kiya haquri yanzu banasan nayi biyu babu ne baki ba wannan babban aikin da nake saka rai na samu”

Daganan ban ‘dago kaina ba saboda hawaye har na Fara jin qoqarin tashin motar Yaya Samir na ‘dago da sauri ta cikin glass na hango fuskarshi babu gitso hawaye ne fuskar Yaya Samir da bazance yaga zubar su ba murmushi ne kawai ykemin da yafi kuka ciwo ana wa hasashen ga ma zahiri nagani hawayen sun yi nasarar zubo masa,qurar motarshi kawai na gani banyi aune ba gefen kayana na duqa ba kuka nake ba,amma bana yanayi me kyau,Yaya Samir kam mutumin kirki ne sai yanzu nima nafi hangen dacewata da Yaya Samir din dukda AbdulHamid din amma banajin Zan iya barin Yaya Samir ‘din Kuma nayi minti a qallah biyu wajen na daure na tashi da jan jakata,Dan yanzu a fara tanbayar lafiya mutane akwai tanbaya mara anfani anawa tunanin saboda bana yanayi mekyau wani gabana ne ya yanke ya fa’di qofar gidanmu nagani da kwa’do, hakanan naji jikina na bani babu lafiya,na da’de wajen tsaye
“Yaya Sumayyah”naji an anbata,hakan yasa ni saurin waiwaya wa,Haris na gani a tsaye shi nake kallo shima haka,Haris abokin Ahmad ne kuma makwabtanmu ne nayi hanzarin ce wa
“Na’am Haris,inasu Mama sukaje ne na dawo na tarar gidan rufe?”

Haris ya dan dubeni ya kau dakai”wallahi Yaya Sumayyah ai su Mama sunfi sati da barin nan, Mai gidan ya koresu,basu biyan haya,yace idan basu tashi ba kafin gobe a lokacin ,ya ce hukuma zai Kira musu,Ahmad dai yace min gida zasu koma,sai lokacin ya ce min ke dama kin da’de bakinan,wallahi su mamana ma basu ji da’di ba ki qaraso gidanmu mana ki huta,ya ce min kinje katsina”

Ban iya tsayawa cikakken amsawa Haris ba,na ce”A’a Haris nagode nima zan bisu ne”

Kai ya girgiza “Yaya Sumayyah yamma ta fara ki samu wani gidan ki kwana,tunda baza ki shiga namu ba bari na Kira miki napep”

Kai na ‘daga kawai ya wuce to ni ina na nufa kenan,Aunty Asma’u ba zata kar’beni na kwana ‘daya bama zan iya zuwa ba,mama Atika ta fa’domin rai banjin zan iya,zuwa wajen ta inada tabbacin ta watsar da zumunci saboda mama ke bin ta kullum cikin qorafin ayyukan gida ta keyi gidansu Halima ya fa’domin a rai na,da wannan tunanin na ji hawaye masu ‘dumi sun sauka kan fuskata qarasowar su Haris a adaidaita sahun yasani saurin gogewa na kalli Haris da ya fito da ga motar yana
“Yaya Sumayyah ga napep din ki fa’da masa ina zaki bari na shigarmiki da jakarki din”

Murmushi nayi kawai na matsawa Haris ya sa jakartawa ciki na shiga na ce wa mai napep “zoo road zani”

Haris yasa hannu aljihu ya bawa mai napep ku’di ina ce wa
“Haba Haris da ka barshi nima da ku’di hannu na,wallahi”

Kai ya girgiza “Haba Yaya Sumayyah aike yayarmu ce ko ba Ahmad zanyi miki, dandai kin qi ne da kinzo gidanmu da safe sai ki wuce nasan Umma na bata labari ba zataji da’di,a gaishemin da Ahmad da su Mama har Abba ma?,kice wa Ahmad zanzo insha Allah”

Nayi murmushi na ce”Ah bawa Umma haquri zasuji,insha Allah,Muna jiranka,Haris nagode”

Daganan napep yaja Haris na ‘daga mana hannu Haris yaron kirki abokin Ahmad ne sosai ko da yaushe tare zaka gansu ina da tabbacin har kuka Haris zaiyi na rashin Ahmad ko makaranta bencinsu daya da Ahmad kwana ke rabasu da Ahmad watarana ma tare suke kwana da’kin su Haris idan ana ruwa,banda jarabawar rayuwa a lalacewar wannan gidan har a nemi cin mutuncinmu saboda ku’di na haya daidai gwargwado Abba na qoqarin biyansu, dalilin dawowarmu nan din da Abba ka’dai yake zaune shagon da wasu ‘yan garinmu suka Kama haya anan to zaman Mama a gwarzo babu da’di a gidansu Abbah take zaune duk qorar da suka kwaso zasu ce Mama ce ko duk barnar da akayi a da’kin Hajiya mamarsu Abbah to mu ne,haka zamu ci duka ba damar magana,duka Khalil da Aisha mama ta haifa anan din muma munfisan zama gida amma babu muhalli acan ,amma ko ba komai gwaggo na qoqarin mana abinda ya samu mahaifiyar Mama, Mama bisa qaddara take zaune da Abbah kaf ‘yan uwanta ta fisu matsalar rayuwar gidan aure,gurin miji ne kawai bata samun matsala,da wannan tunanin muka qarasa zoo road da kwatance nama mai napep muka qarasa layin gidansu Halima ina ji Ina gani muka wuce qofar gidan Aunty Asma’u duk girman gidan ace ka gaza jan naka a jiki dai dai da minti goma baka so yayi a ciki wannan arziqi bai rana ba na fa’da a Raina kofar gidan su Halima dana ga wani ‘bangaren an fara buga siminti an cire langa langan muka tsaya na fito Mai napep fiddomin jaka ta yayi gaba bani da za’bin da kunyar da ke tare dani ganin qatuwar jaka hannuna bansan yanayin tunanin da iyayen Halima zasuyi ba ganina da jakar ganin kowa yana ta kanshi komai ya canza masu ku’din ma suna kukan tashin kayan masarufin ina ga mu talaka,dukda iyayan Halima ba su da matsala amma sainake jin nauyi da haka na qarasa tura kofar na shiga ciki da sallamata Faisal da Yaya Baffa da suke tsakar gidan suka amsamin,suna
“Mutanan Katsina,yanzu kuke tafe,hala tare kuke da Asma’u ko?,naji Kabir ya ce ta je unguwa”Yaya Baffa ke fa’din haka

Yaya Hakim da Yaya Abdussalam,da suka fito daga dakinsu da alama fita zasuyi suka kalleni Yaya Abdussalam ya ce”wato kinji ranki Halima na zazzabi kenan shine daga saukarku kanki zarce gida Kika zo nan”

Murmushi nayi muka gaisa dasu Faisal ya anshi jakata ya Kai da’ki na bi bayanshi duk hankalina yayi wajen Halima jin tana zazzabi amma jiya fa munyi waya bata fa’da min ba

Faisal ya fito yana
“Kinga bata ma da’kin bari na duba bayan gida ko qila ta shiga wanka ai taji sauqi Mama batanan ta ce kada tayi wankan sai tayi zazzabi ya dawo ta cikamu da raki cikin dare”

Murmushi nayi na zauna saman kujera ina cigaba da tunane tunane..

<< Na Cancanta 17Na Cancanta 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×