haɗiye miyau da ƙyar. Ta sakawa kanta za ta daina nunawa Zayyad ko a fuska ta damu lamarinsa. Bare har ya ci gaba da wahalar da zuciyarta. Idanunta ta mayar akan Mubaraak, a can ƙasar zuciyarsa tana tausayin yadda zai zama gawa na huɗu a cikin mazajen Anti Zuwaira. Tasan dangin Mubaraak da son abin duniya. Sannan shi saurayi ne da yake ƙaunar fake life ta sakar masa murmushi ta ce,
"Anti Zuwaira ba dai shi ne sabon angon ba?"
Ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta jawo kujera ta zauna. Shima ya yi fuska. . .