Skip to content
Part 12 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

haɗiye miyau da ƙyar. Ta sakawa kanta za ta daina nunawa Zayyad ko a fuska ta damu lamarinsa. Bare har ya ci gaba da wahalar da zuciyarta. Idanunta ta mayar akan Mubaraak, a can ƙasar zuciyarsa tana tausayin yadda zai zama gawa na huɗu a cikin mazajen Anti Zuwaira. Tasan dangin Mubaraak da son abin duniya. Sannan shi saurayi ne da yake ƙaunar fake life ta sakar masa murmushi ta ce,

“Anti Zuwaira ba dai shi ne sabon angon ba?”

Ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta jawo kujera ta zauna. Shima ya yi fuska ya jawo tasa kujerar ya zauna.

“Ka gaisa da ƙanwata da nake ta baka labari. Ga kuma ƙawayenta.”

Duk suka gaisa babu, yabo babu fallasa. Zuciyar Munaya tana ta ingizata akan ta sake kallon in da Zayyad yake, sai dai wannan karon ta ci galaba akan zuciyarta. Ta dage ko kallon in da yake bata sake kallo ba. Mubaraak ya kasa sakin jiki. Dole Anti Zuwaira ta yi masu sallama suka wuce. Munaya ta yi ajiyar zuciya.

“Kunsan waye Anti Zuwaira za ta aura?”

Duk suka zuba mata idanu. Kafin ta yi magana ta hango Zayyad tsaye da wata suna magana. Ta gigice, zuciyarta ta dinga in gizata akan ta je ta wanka mata mari. Akan me za ta tsaya da Zayyad ɗinta? Da sauri ta kauda kanta sannan ta lallashi zuciyarta ta ci gaba da cewa,

“Mubaraak ɗin da nake baku labarin zan aura. Wai shi ne zai auri Anti Zuwaira. Ban san me ya kawo Mubaraak Kaduna ba. Da alamun ajalinsa ce ta kira shi.”

Dukkansu sun cika da tsananin mamaki. Sai yanzu kowacce take tariyo yadda ya shiga ruɗu a farko, da kuma dalilin da yasa Munaya ta miƙe da ta ganshi.

“Munaya ki yi wani abu kai. Kada ta je ta kashe shi.”

Munaya ta girgiza kai,

“Me zamu yi? Mu kira shi mu gaya masa gaskiya ya ce kishi ne? Ko mu sanar a gida, ya zama dalilin tona asirin Anti Zuwaira ta bi mu ɗaya bayan ɗaya ta kashe mu? Mu yi masa fatan alkhairi. Sai ki ga tana sonsa sai ta kasa kashe shi.”

Hajara ta ware idanu,

“Uncle Zayyad mai kyau da zati ta kashe shi bare wani Mubaraak? Wallahi ranar da na fara zuwa gidan Anti Zuwaira ina ganin hotonsa sai da na tsaya na jinjina kyansa. Da farko na zaci kyawunsa ya saka kika tsunduma a cikin sonsa, sai daga baya na gane daga Allah ne. Idan ba daga Allah ba, babu yadda za a yi a, gaya maki cewa mutum ya mutu, amma ki dage ki ci gaba da sonsa.”
Amina Aminu ta gyaɗa kai,

“Tabbas Allah shi yasan me ya ɓoye a cikin wannan sarƙaƙƙen al’amarin. Na tsorata a lokacin da naga wasiƙar da iyayensa suka tabbatar da rubutunsa ce.”

Anan suka yi ta tattaunawa, duk da Munaya tana ganin Zayyad amma ta ƙi gaya masu, sannan ta ƙi damuwa da lamarinsa. Ta ji daɗin fitar da suka yi, wanda sai yamma suka dawo da ita, su kuma suka wuce gidajensu.

A gajiye ta shigo gidan. Mubaraak da Anti Zuwaira suna kallo a wayarta sai dariya suke kwasa. Mamaki yasa Munaya ta ce,

“Wai Anti har an ɗaura auren ne?”

Anti Zuwaira ta harareta da wasa ta ce,

“Baby ka ji zolayar Munaya ko? Ta ya ya za a ɗaura aure ba tare da ke, kin sani ba? Ki bari ki je ki huta ki dawo, sai mu tsara yadda yanayin bikin zai kasance ko Baby?”

Ya ɗan yi yaƙe ya ce,

“Hakane.”

Munaya ta taɓe baki tana jin daɗin yadda Allah ya rabata da Mubaraak, cikin ruwan sanyi. Tana isa ɗaki ta ɗaga waya ta kira Umma. Bayan sun gaisa take ce mata,

“Su Mubaraak sun zo sun karɓi kayansu ne?”

Umma ta ce bata fahimta ba.
“Ba kusan zai yi aure ba?”

Umma ta yi ajiyar zuciya tana mamakin waye ya gaya mata.

“Eh. Sun zo sun yi magana da Abbanki, akan Mubaraak zai yi aure sai ki zo a ta biyu kuma Abbanki ya amince da hakan.”

Munaya ta taɓe baki ta ce,

“Gobe a aika masu da kayansu.”

A razane Umma ta ce,

“Akan me? Kina da hankali kuwa? Dan kawai zai yi aure? Dama zaɓi biyu ya bada, idan bakya so, to ki amince kawai ayi auren ki haƙura da karatunki.”

“Umma kenan. Anti Zuwaira fa zai aura. Yanzu haka ma gashi can a falo na barsu suna shirye-shiryen biki. Zaki amince in zo a ta biyun?”

Umma ta sa Salati da ƙarfi. Sai kuma ta kashe wayar. Munaya ta saki lalataccen murmushi. Ganin da ta yi wa Zayyad da wata kawai ya isa ya sakata cikin tsananin masifa. Dauriyarta ta ƙare. Ta kwantar da kanta a filo, hawaye suna zuba. Bata damu da ta goge su ba, ta hakanne kaɗai zuciyarta za ta iya rage raɗaɗi.

“Ki daina kuka Munaya. Bansan yayarki ba ce sai yau. Duk da haka ta gaya mini yadda kuke, Allah bai haramta aure a tsakanina da ke ba. Ke dai roƙon da zan yi maki, ki daure ki ɓoye kishinki kada ta gane akwai wani abu a tsakanina da ke. Na yi maki alƙawarin kina gama karatu za ayi aurenmu. Babu abin da ya canza daga irin ƙaunar da nake yi maki.”

Munaya ta ɗago sheƙeƙe, cike da mamakin zuciyar da ta bashi ƙarfin halin zuwa ya lalata mata tunanin Zayyad ɗinta. Da hannu ta nuna masa hanya,

“fice mini a ɗaki. Kai har ka isa in yi kishi akanka? Ba ƙaramin taimakona ka yi ba, kamata ya yi ma in gode maka. Dan Allah malam fice ka bani wuri.”

Sumi-sumi ya fice yana mamakin furucinta. Duk da yasan dama can ba sonsa take ba, amma ya yi mamakin yadda ta fito masa ƙarara ta nuna masa ko a gefen gyalenta. To kukan me take yi?


Yau gaba ɗaya zuciyarsa a hargitse take. Yau ne karo na farko da Munaya ta kalle shi da rashin kulawa kuma sau ɗaya tak! Bata sake kallonsa ba.
Tana nufin ta zo ne ta saka masa soyayyarta sannan ta juya masa baya? Me ya sa farkon soyayyarsa za ta zo a haka?
‘Ko dai ta haƙura ne kamar yadda na bata shawara a wasiƙata? Kai a’a. In dai da gaske tana sona bai kamata ta yi saurin karaya haka ba.’

Hoton surar jikinta ya sake dawo masa cikin kai. Abin da yake ƙoƙarin ganin ya daina tunawa. A hankali ya sake shiga yanayin da ya shiga jiya. Ya kwanta kawai yana juye-juye. Ya yi danasanin ɗaukota a jikinsa. Shi ya sa idan Allah ya haramta abu, in dai za ka tsallake umarninsa sai ka ga ba daidai ba. Ga shi yarinya ƙarama tana neman ta ruguje masa dukkan shirinsa. Ya tsaya da wata dan yaga ta damu, amma abun mamaki babu damuwa a fuskarta. Me ya sa sai da ta bari ya afka cikin tarkonta sannan za, ta juya masa baya?
Ko da yake jinin Zuwaira babu abin da ba za su iya aikatawa ba.
‘Na sake faɗawa tarkon Zuwaira. Bayan ta kasheni, ta sake turo wata cikin rayuwata domin ta hanani ganin duniyar gaba ɗaya.’

Da ƙyar ya iya samun lemon tsami, ya matse ya shanye. Sannan ya nufi banɗaki. Idan kansa ya kulle ruwa kawai yake sakarwa kansa, ta haka ne yake samun sassauci.

Munaya tana juyi cikin tsananin damuwa. Zayyad ma a can juye-juye kawai yake yi cike da tsananin damuwa. Ta jawo filo ta rungume tsam, tana jin ina ma Zayyad zai bayyana a daidai wannan lokacin. A can wurin Zayyad ma yana rungume da filo ya rungume tsam! Yana addu’ar Allah ya kawo hanyar da zai ga Munaya a daidai wannan lokacin.

Haka suka raba dare, cikin tsananin damuwa. Gara shi, ya tashi ya yi wanka sannan ya yi alwala ya ɗauko Alqur’aninsa.

*****

“Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!! Ka fito ka ga wani abun ban mamaki. Innalillahi Wa inna ilaihirraji un.”

Da sauri-sauri ya sauko daga bene, ya nufi in da yake jin muryar Hajiya Nafisa. Duk da bai san me ne ne ba, amma yana da tabbacin duk abin da zai kiɗimata ba ƙaramin abu bane.”

A tare da yaran duk suka cusa kai cikin falon Zayyad, a in da suke jin sautikan Hajiya.

“Me ya faru? Ki yi magana mana.”

Da hannu ta nuna masa cikin ɗakin. Zayyad. Dukkansu suka cusa kai basu ga komai ba.

“Wai me ne ne?”

Daddy ya tambayeta cikin tsawa.

“Kana nufin ba ka ga an kwashe kayan sawan Zayyad an kawo sabbi ba? Ba ka duba wurin hulunansa ba? Takalmansa. An gyara ɗakin. Kuma Wallahi lokacin da na, shiga na ji ana wanka, an ajiye kaya akan gado wanda suke a goge. Kuma.. Kuma..”

Ta zube ƙasa a sume. Gaba ɗaya yaran suka sa kuka tare da taruwa a kanta. Daddy ya rikice, ya ruɗe. Bai taɓa ganin irin tashin hankalin nan kamar irin wanda suke ciki a yanzu ba. Zai iya rantsuwa da Qur’ani da hannunsa ya saka ɗansa a ƙabari. Kuma da ya ce su Munaya su bashi kwana biyu, zuwa ya yi Masallaci ya yi tambaya akan mutuwa da fatalwa. Maganar ɗaya ce, a musulunci babu fatalwa. Haka babu wanda ya taɓa mutuwa ya tashi. Ta ya ya waɗannan abubuwan za su yiwu?

Muje zuwa domin jin yadda zata kaya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 11Na Kamu Da Kaunar Matacce 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×