Skip to content
Part 11 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Tunani ya hana ƙwaƙwalwarsa hutawa. Da ya rufe idanu sai ya hango surarta a cikin kayan barci. Babu, wani abu da ta saka na kariyar ƙirjinta, hakan yasa idanunsa suka gano masa wasu abubuwa masu ɗaga hankali. Duk da a lokacin da ta faɗo masa yana cikin halin tashin hankali, bai hana shi jin wani abu ba.

Duk yadda yake zaton abun ya wuce tunaninsa. Ya cusa kai a cikin sumar kansa yana cakuɗa shi, tamkar wanda zai cizge sumar. Cinyoyinta masu haske da ya gani a lokacin da ya kwantar da ita sun saka masa wani matsanancin sha’awa, wanda har ya kasa riƙe kansa. Idanunsa suka yi jajir. Ya shiga mawuyacin hali, wanda ya saka masa numfarfashi kamar wanda ransa zai fita. Duk yadda ya yi, domin ya daina tuna surarta abin ya faskara.
Duk yadda zai, wassafa yadda halittarta yake abin ya wuce hakan. Lemon tsami ya nema ya matse kusan guda biyar, ya shanye yana ajiyar zuciya.
A gado ya faɗa yana mayar da ajiyar zuciya. Lallai ya yarda da wani abokinsa da yake ce masa, “Duk yadda kake tunanin shu’umancin mata abin ya zarta tunaninka. Kada ka yarda ka faɗa cikin tarkon ƙaunar mace, ko sarki ne sai ya ajiye sarautar.”

Ya lumshe idanu, ‘Ina ma kana raye? Allah ya jiƙanka abokina.’

Ya furta a zuciyarsa yana jin kewarsa fiye da kullum.
‘Allah ya jiƙanka Zayyad Mohammad Hashim.’

Zayyad ya furta tare da girgiza kai da ƙarfi. Haƙiƙa har ya koma ga Allah ba zai taɓa mance wannan mutuwa ba. Mutuwa ce da ta ɗanɗana masa ɗaci fiye da na maɗaci. Ta zo masa a daidai lokacin da bai taɓa zata ba, bai kuma shirya masa ba.

Sai da garin ya yi haske tar! Sannan Munaya ta farka, haɗi da azababben ciwon kai. Da ƙyar ta yunƙura. Anti Zuwaira ta yi saurin dakatar da ita.

“Sannu Munaya. Ya jikin?”

Munaya ta, shafa kanta, ta dinga tariyo abubuwan da suka faru jiya ta runtse idanunta. A hankali kuma, sai ta fahimci mafarki ta yi. ‘To idan mafarki na yi, me ya sami kaina?’

Ta waiwayo da, sauri ta ce,
“Anti ciwon nan yaushe na ji?”

Ta ɗan riƙe kafaɗunta,

“Ni dai jiya na ji kina ta ihu, na, shigo ɗakinki da sauri ina riƙeki kika, bangaje ni, kika yi hanyar ƙofa. Anan ne kika buga kanki, kasancewar idanunki a rufe. Sannu kin ji? Ki dinga yin addu’a ne idan ba haka ba, shaiɗanu za su yi ta binki.”

Sosai Munaya ta yarda da maganar Anti Zuwaira. Ta tabbata dai mafarkin ta yi. Anti Zuwaira ta yi ajiyar zuciya, sannan ta, tashi ta nufi ƙofa,
“Idan kin kimtsa sai ki fito ki karya, tunda yau babu Makaranta.”

Munaya ta zuba tagumi tana kallonta har ta fita. Tabbas da Abbanta zai ga irin yadda a test ɗin da suka yi, ake rubuta mata ƙaton zero da ya fi kowa shiga tashin hankali. Duk da karatun Biology akwai wahala, amma kuma ita a, wurinta mai sauƙi ne, yanayin matsalolin da ta, tarar a gidan Anti Zuwaira ne kaɗai matsalarta.

Farar takardar da ta gani a gefen gadonta ta ciro tana jujjuyawa. A hankali ta buɗe.

Amincin Allah ya, tabbata a gareki ƙanwata. Da ina rantsuwa, da sai in rantse maki ba zaki taɓa zama a ƙarƙashin inuwata ba. Rayuwata ta bambanta da ta mutanen da kika sani, kuma kike rayuwa a cikin su. Abu ɗaya nake so ki yarda da shi, kuma ki amince. Ni Zayyad bana raye. Matacce ne, Irin wanda har abada ba za a, sake zama inuwa ɗaya da shi ba. Idan ke musulmace ta gaske, kuma kin yarda ba a mutuwa a dawo, ki sawa zuciyarki haƙuri da kuma gazgata cewa bana raye. Ko kin taɓa ganin idan aka KAMU DA ƘAUNAR MATACCE? Ki cireni a cikin zuciyarki ki yi mini addu’a, sannan ki fuskanci karatunki da kike ta samun matsala duk a dalilina da Zuwaira. Wanda muka zame maki mummunar ƙaddarar da ba za ki taɓa mance mu ba. Ki yi rayuwa da rayayyu kamar yadda kowa yake yi.

Zayyad Mohd Hashim

Munaya ta zabura tana kalle-kalle. Ta riƙe kanta da ƙarfi kasancewar ta mance da ciwo a kanta.

“Idan kana jina, ina so in gaya maka. Mu ma a musulunci bamu da fatalwa. Da jinnu kaɗai Musulunci ta yarda ba fatalwa ba. Idan kuma kai Jinnu ne kake yin kamannin Uncle Zayyad, ka taimakeni ka taimaki rayuwata ka zo ka ɗaukeni ka tafi da ni duniyarku ta aljanu. Wallahi soyayyarka za ta iya kashe rayuwata. Ina jin akan sonka zan iya, sadaukar da rayuwata domin kawai in rayu da kai. Innalillahi Wa inna ilaihirraji un. Na shiga uku ni Munaya.”

Ta kwantar da kanta akan gado tana rizgar kuka. Za ta so ta ga ranar da za ta yi dariya. Tunda ta iso garin nan, bata taɓa yin dariya ba. Ga shi suna gab da fara jarabawa, daga nan za su yi hutun sati biyu. Ta Tabbata a hutun nan ne za ta koma wurin iyayenta. Me za ta gayawa Umma da Abba akan halin da take ciki? Idan suka san komai anya kuwa za su sake barinta ta dawo Karatu?

Ji ta yi an dafa kafaɗarta. Bata ɗago ba, dan bata ƙaunar haɗa idanu da kowa.

“Munaya Lawal lafiyarki ƙalau kuwa? Me ne ne haka? Haka za ki rayu kullum a cikin kuka? Ina tawakkalin da ke garemu? Ina tauhidinki? Dan Allah kada ki bari kina ji kina gani, da lafiyarki da hankalinki ki koma cikin kafirai waɗanda basu taɓa yarda da ƙaddara ba.”

Duk suka zauna daga ita Hajara har Amina. Sai yanzu ta ɗago cikin kuka mai rikitarwa. Amina ta ce,
“Subhanallah! Me zan gani haka? Kin ga yadda idanunki duka kumbura kuwa? Ki sawa kanki haƙuri da tawakkali mana.”

Munaya ta kwantar da kanta a jikin Hajara tana ci gaba da kuka, Irin wanda basu taɓa ganinta ta yi ba. Da ƙyar suka yi ta lallaɓata, har ta amince ta shiga ta yi wanka. Amina Aminu ta ciro mata doguwar riga mai kyau. Ko mai ta ƙi yarda ta shafa haka ta saka rigar. Hajara ta tashi ta ɗauko manta mai gurguwa wanda da shi take amfani tun tasowarta. Ta shafa mata a hannu da ƙafafu da fuska. Ta ɗauko fauda ta shafa mata. Ta saka mata kwalli, sannan ta sami Light jan baki ta goga mata, sannan ta bi da man baki irin mai danƙon nan. Nan da nan ta fito ta yi ras!

Suka kamo hannunta bayan ta yane ƙaramin gyale suka fito falo. Anti Zuwaira tana zaune tana latse-latsen waya. Duk ta juyo ta kallesu tana murmushi,

“Haba yanzu naga Munaya. Na rasa me ke damun yarinyar nan, duk ta rame ta ƙare. Har fargaba nake yi ta koma gida, a fara tuhumata. Dan Allah ki dinga saurarawa kanki mana.”

Duk suka zuba mata ido, kowanne da irin zagin da yake yi mata. Ruwan tea kawai Munaya ta sha, sannan suka dubi Anti Zuwaira suka ce,

“Anti ki bamu aronta mu ɗan fita wurin shaƙatawa.”

Ta ɗan ɓata fuska,

“So nake ku ɗan tsaya saboda Munaya taga mijin da zan aura. Amma duk da haka bai ɓaci ba, kuna iya tafiya sai ku gaya min in da kuke ni kuma sai mu ƙaraso da mijin nawa. Ƙila ku ci sa’a ta saki fuskar.”

Duk suka amince da shawararta ta biyu, a sakamakon basu ƙaunar su fita tare. Bayan sun hau titi ne Munaya ta yi magana cikin sanyi,

“Ki fara zuwa gidan Alhaji Mohd Hashim.”

Bata ce komai ba, ta kama hanyar gidan.

“Munaya ki daina damuwar nan dan Allah. Kina ɗaga mana hankali da yawa.”

Ta ɗan musƙuta ta kwantar da kanta a jikin ƙofar mota ta ce,

“Uncle Zayyad ya ce mini shi bai da iyaye. Ya ce mini shi ba Alhaji Muhammad Hashim ne ya haife shi ba. Amma a ƙarshen rubutun wasiƙar da ya yi mini, ya rubuta cikakken sunansa da kuma Alhaji Mohd Hashim. Kaina ya ɗaure. Dan Allah idan kuna da maganin da zaku iya bani, saboda in sami sauƙin soyayyar da nake yi masa, dan Allah ku taimaka mini. Ina shan wahala. Ina tsoron in koma gida iyayena su ganni a haka su hanani karatu. Akwai wanda suka zo suka kawo kuɗin gaisuwa gidanmu, akan ina gama karatu za a aurar da ni agun Mubaraak. Ɗan wani abokin Abbana ne. Duk da ban taɓa sonsa ba, amma irin nacin da yake yi akaina, da kuma mannewa da ya dinga yi, daga ƙarshe ya kai maganar agun Yayan Abba, da kuma shi kansa Abban, suka ce basu ga mijin da zan aura ba, idan ba Mubaraak ba. Na amince ne saboda ban taɓa soyayya ba, ban taɓa kamuwa da son wata halitta ba. Hasalima ina ganin kamar babu soyayya duk shirme ne. Ashe soyayya wahalalliyar kalma ce mai ƙasƙantar da bawa, duk girmansa.”

Anan ma duk suka ɗan yi shiru. Kowa yana tsoron ya gaya mata aljani take gani ba mutum ba.

“Ki tattara komai ki miƙawa wanda ya ƙagi soyayya. Shi bai mance halin da kike ciki ba, kuma shi ya isa ya cire maki wannan soyayyar ba mu ‘yan adam ba.”

Anan ma shiru duk suka yi, har suka iso gidan. Kai tsaye da motarsu suka shige.
Me za su gani? Alhaji Mohd Hashim ne tsaye cikin babbar rigarsa, suskarsa cike da annuri. Da alama fita zai yi, duk yaran gidan suna kewaye da shi. Har da Anti Afrah itama ta zo. Bakin Hajiya Nafisa ya ƙi rufuwa saboda farin cikin yau a karon farko mijinta zai fita cikin walwala tun bayan wasu shekaru da ya yi a kwance babu lafiya.

Farin ciki ya tsirgawa Munaya. Hawaye suka wanke mata fuska. Da sauri ta ƙaraso wurin Alhaji, sai dai ba zata iya rungume shi ba, dole ta zube a ƙasa ta riƙe ƙafafunsa kawai ta fashe da kuka.
Gaba ɗaya wurin babu wanda bai yi hawaye ba. Shi kansa Alhajin da ya dafe kanta da hannunsa guda, sai da yaji ruwan hawayen yana ta sauka a kuncinsa. Shi ke hana yaransa kuka, yanzu kuma daga shi har su kukan suke yi. Munaya ta shiga tsananin farin ciki irin wanda tunda ta zo garin bata taɓa shiga ba. Hajiya ta ɗagota ta ƙanƙameta suna ta kuka. Afrah da su Suhaima da Rumaisa da Rumasa’u suka ƙanƙameta suna kuka.
Dole Alhaji ya share hawayensa, ya dinga tausarsu har suka amince suka daina kukan. Sai dai ita Munaya lokaci zuwa lokaci tana goge hawayen da suka ƙi tsayawa. Yau ko a haka ta bar Kasu ta ci riba, tunda har ta zama silar sanya babbar family kamar na Alhaji Mohd Hashim farin ciki.

“Munaya kin taimakemu. Munsha wahala akan ciwon Alhaji, bamu taɓa samun nasara ba, sai zuwanki. Dan Allah ki gaya mana duk abin da kike so, ba wai dan mu biyaki ba, sai dan mu ma mu yi maki yaƙi akan ki samu abun, duk wahalarsa.”

Hajiya ta dire maganarta tana kallon Munaya, da tuntuni ta fuskanci tana cikin damuwa. Alhaji ya ce,

“Zo kusa da ni ‘yata. Zo ki gaya mini bayan ciwona me ce ce kuma damuwarki? Zo ki sanar da ni.”

Munaya ta tashi a sanyaye ta zo gaban Alhaji ta zauna a ƙasa, sai kuma ta rushe da kuka. Ta yi alƙawarin sai ta gaya masu duk abin da zai faru sai dai ya faru. Sai dai ba za ta iya gaya masu wace ce Zuwaira ba, har sai lokacin da ya kamata su sani ya yi.

“Daddy tunda na zo garin nan, na haɗa idanu da Uncle Zayyad shi ne.” Sai kuma ta yi shiru. Duk suka dubi juna cike da wani irin mamaki, wanda basu taɓa shiga ba.

Hajara ta ɗan yi gyaran murya ta ce,

“Daddy tunda Munaya ta haɗa idanu da hoton Uncle Zayyad a gidan Anti Zuwaira shikenan ta, kamu da matsanancin ƙaunarsa. Bata sake yin dariya ba har yau ɗinnan.”

Baki duk suka buɗe. Da ƙyar Daddy ya iya cewa,
“To ai Zayyad ya rasu. Tayaya za ki iya kamuwa da son wanda baya raye? Ko baki san ya rasu bane?”

Ta girgiza kanta tana kuka. Hajara ta ce,

“Wallahi ta sani. Wani abun al’ajabi kusan kullum sai ta haɗu da Uncle Zayyad. Ko a kasuwa ko a Makaranta. Sau biyu dai ya taɓa yi mata magana. Ka ji abin da yake ramar da ita. Da ta zo gidan nan ta shiga ɗakinsa ta ɗauki agogonsa, kuma da ta haɗu da shi ta sake ganinsa a irin wannan agogon da ke wurinta. Abubuwa sun faru babu iyaka.”

Dukka ɗakin suka yi shiru suna zare idanu. Tunda suke jin abun firgitarwa basu taɓa jin irin wannan ba.

“Me yake ce maki idan kun haɗu.”

Cikin matsananciyar kuka ta ce,

“Cewa yake yi shi matacce ne. Ba zamu iya rayuwa a tare ba.”

Daddy ya sake gyara zama cike da tashin hankali.

“Kin taɓa ganin in da matacce ya zama rayayye? Wannan kuma wata almara ce, ko in ce sharrin jinnu. Amma nasan Munayata tana da ilimi. Kuma ba za ki taɓa ƙirƙiran abun da bai faru ba. Ko kina da wata shaida da zai sa in gani nima?”

Da sauri ta ɗauko takardar da ya rubuta mata. Cikin ikon Allah tana dubawa sai ta ganta. Ta zaci ko zata nema ta rasa. Ta warware ta miƙa masa. Yana buɗewa ya miƙe tsaye hannunsa yana karkarwa. Hakan yasa itama Hajiya ta karɓa. Rubutun ɗansu ne. Suhaima da su Afrah suka karɓa suka haɗa kai, suka karanta. A take cikinsu ya murɗe saboda tsananin tashin hankali. Tsoro da firgici ya shige su. Daddy ya ce,

“Rubutun Zayyad ne. Amma ta ya ya hakan zai iya faruwa? Mu dai bamu da fatalwa. Mun yarda Allah ɗaya ne, kuma idan an mutu ba a dawowa.”

Da sauri Munaya ta tashi tsaye tana goge hawaye,

“Daddy ka taimaka ka gaya mini ba mutuwa ya yi ba. Ina cikin tashin hankali.”

Daddy ya girgiza kai,

“Zayyad shi ne babban ɗana. Idan har akwai wanda ya fi sonsa ba zai, wuce ni da mahaifiyarsa ba. Mun ɗauki soyayyar duniya mun ɗora masa. A lokacin yana yaro shi yake cin duk wata gasa akan Karatun Alkur’ani na duniya. Har sai da ya girma ne ya gama karatunsa, ya ƙi karɓar aikin da ake ta bashi, ya ce shi a kamfanin mahaifinsa zai yi aiki. Har Saudiyya sun so su riƙe shi saboda tsantsar iliminsa da kuma iya tajwidi. Amma ya nuna masu sam! Ba zai zauna ba. Zayyad bai taɓa yi mini gardama ba. Ko domin biyayyansa a garemu ya ci ace Zayyad yana kwance a cikin ƙabarinsa cikin Rahamar Ubangiji. Kuma da hannayena na saka shi a ƙabari, bare kuma in yi tunanin ko ƙarya akayi bai mutu ba. Tabbas Zayyad ya mutu. Abubuwan da suke faru kamar irin wannan kuma ba zan iya cewa kai tsaye ga dalili ba. Amma ku bani kwana biyu.”

Hajiya ta tsaya tana kallonsa. Shima dai tasan ya faɗa hakanne domin kawai ya kwantar masu da hankali. Amma rubutun nan ya fi komai tsaya masu a rai. Suhaima sarkin tsoro ta fi kowa tsurewa. Sannan ta ga ƙarfin hali da kuma ƙarfin soyayya a wurin Munaya. Idan ita ce ma ai ba zata iya kwana ita kaɗai ba, saboda tsoro.

Haka Munaya suka yi wa su Daddy Sallama akan za su dawo. A cikin motar ma kowa ya kasa magana. Har suka shiga ƙaton wurin shaƙatawar da ke kusa da Gamji Gate. Suna nan zaune aka kawo masu kayan motsa baki, wanda Hajara ta je har wurin ta gaya masu abubuwan da suke buƙata. Munaya ta ɗan sami sassauci dan haka ta ɗan sha abubuwan domin su ji daɗi.

Suna nan zaune sai ga Anti Zuwaira. Abin mamaki babu wanda ta nema da nufin a gaya mata wurin da suke. Tana nufosu da saurayinta har suka ƙaraso wurinsu. Munaya ta ɗago idanunta da nufin ganin waye wannan miji da ake ta zancensa.

A firgice ta miƙe tana kallonsa. Shi kuwa yana tsaye fuskarsa cike da annuri. Ta gigice, ta rasa me za ta yi da ya wuce zura masa idanunta masu tasiri a idanun waɗanda suka kalleta. Ta juya kanta ta rasa me za ta yi ko me za ta ce. Ta sake hango Zayyad yana tsaye. Yau ɗin ma cikin fararen kaya yake. Hankalinsa baya tare da ita, domin kuwa ya tattara hankalinsa ne akan wani Balarabe yana nuna masa abu a ƙaton takarda. Jikinsa ya bashi ana kallonsa, dan haka ya waiwayo da sauri. Suka haɗa da ni. Ya kalleta har yanzu kuka take yi. Ya rasa ta yadda zai iya taimakawa domin ya cire mata damuwar da ke tare da ita, duk da ya fita shiga damuwa.

Mu je zuwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 10Na Kamu Da Kaunar Matacce 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×