Gaba ɗaya Zayyad ya hana a shigo a dubata, kasancewar baya son wani ya tasheta. Yarinyar gaba ɗaya tausayi take bashi. Ya ci ciwon yadda aka bari wanda ya bugeta ya gudu, hakan yasa ya fito ya rufe su Hajjo da faɗa kamar zai dake su. Duk zafi irin na Hajjo haƙuri kawai take bashi. Bai nemi aje a siyo wani magani ba, da kansa ya kira waya ya ce a kawo. Ya hana kowa shiga ɗakin sai shi kaɗai. Yana nan riƙe da hannun, yana jin da akwai yadda zai yi, da babu shakka sai. . .