Skip to content
Part 14 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Gaba ɗaya Zayyad ya hana a shigo a dubata, kasancewar baya son wani ya tasheta. Yarinyar gaba ɗaya tausayi take bashi. Ya ci ciwon yadda aka bari wanda ya bugeta ya gudu, hakan yasa ya fito ya rufe su Hajjo da faɗa kamar zai dake su. Duk zafi irin na Hajjo haƙuri kawai take bashi. Bai nemi aje a siyo wani magani ba, da kansa ya kira waya ya ce a kawo. Ya hana kowa shiga ɗakin sai shi kaɗai. Yana nan riƙe da hannun, yana jin da akwai yadda zai yi, da babu shakka sai ya cire mata ciwon nan ya mayar jikinsa. Wata zuciyar tana sanar da shi kawai ya gudu da ita a nemeta a rasa.

A hankali take buɗe idanunta har suka buɗe tar! Ya kafeta da kyawawan idanunsa masu tsananin kwarjini. Abin mamaki duk suka sakarwa juna murmushi.

“Sannu ya jikin?”

Ta ɗan yi shiru.

“Uncle Zayyad kai ne?”

Ta yi maganar cikin yanayi na marasa lafiya. Ya kafeta da idanunsa babu ko ƙyaftawa.

“Ni ne Munaya. Ya jikinki?”

“Babu sauƙi.”

Ta yi maganar kamar mai, shirin yin kuka.

Ya ɗan ware idanu,

“Me ya sa babu sauƙi? Wani, abu yana maki ciwo ne?”

Ta gyaɗa kai,

“Eh.”

“Faɗa mini me ne ne ke maki ciwo?”

Ta ɗaga hannunta mai lafiya ta dafe zuciyarta. Sai kuma hawaye,

“Ka tausaya mini ka daina guduwa kana barina. Zuciyata ciwo take yi mini, kullum a cikin tunaninka nake. Bana fahimtar karatu. Na zama daƙiƙiya a dalilin rashinka. Ka tausaya mini ka tafi da ni. Duk abin da za ka yi min na yarda in dai za ka dinga kulani. Ka dinga zuwa muna hira. Idan kuma kaima ka kasance matsafi ne kamar Anti Zuwaira ka gaya mini dan Allah.”

Wannan karon kallon da yake yi mata ya sauya salo,

“Idan ni matsafi ne za ki iya haƙura da ni?”

Ta kauda kanta hawaye suna ci gaba da tsiyaya,
“Idan kai matsafi ne, zan yi maka nasiha har ka daina muyi aure. Ka daina kiran kanka matacce kana raye, tunda ga ka a kusa da ni muna magana. Iyayenka suna kewarka. Ka daina saka mana kwakwanto a cikin zuciyarmu.”

Shiru ya yi yana wani nazari. Daga bisani ya ce,

“Idan kin warke zan ɗaukeki in kaiki gidana. Ina sha’awarki fiye da tunaninki. Za ki iya mallaka mini kanki domin in kashe raɗaɗin da nake kwana a ciki? Wannan taimakonne kawai za ki yi min ki ceto tawa rayuwar. Sannan dole sai na kwanta da ke, sannan zan dawo cikakken mutum wanda kowa zai iya ganina.”

Munaya ta shiga ruɗani da kalaman Zayyad. Ta kasa magana saboda tsananin mamaki da tashin hankali.

Ya yi murmushinsa mai tsayawa a rai sannan ya, shafi kanta ya kuma yi mata Kiss a goshi. Ya matso daf da ita ya ce,

“Na barki lafiya. Ki natsu ki kwantar da hankalinki. Idan kika yarda duk ranar da na sake bayyana a gabanki ko a cikin kasuwa, ko a gidan iyayena ki gaya min kin amince. Daga ƙarshe ina so ki sani, Zayyad Mohammed Hashim ya jima da rasuwa. Sai mun sake haɗuwa domin karɓar amsata. Idan muka haɗu baki bani amsa ba, ina tabbatar maki ba za ki sake ganina ba har abada…”

Ya juya kawai. Saura kaɗan su ci karo da Hajjo, ta ɗan kauce masa haɗi da cewa, “Sorry.”

Tana kallon lokacin da Hajjo ta dubu fuskarsa, sannan ya ratsa ya wuce. Hajjo ta bi bayansa da harara ta yi sauri ta zauna,

“Ya jikin naki? Wannan dokto ɗin ya cika masifa. Ya hana kowa zuwa wurinki yana ta gaggaya mana magana akan wai mun bar direban da ya kaɗeki ya gudu. Mu muna ta lafiyarki ce ko kuwa ta guduwar wani direba. Bari in je in biyasu kuɗinsu mu je gida.”

Munaya da ta yi mutuwar kwance ta dinga zazzare idanu tana mamaki. Kafin ta tafi Anti Zuwaira ta shigo a gigice.

“Sannu Munaya. Allah ya baki lafiya kin ji? Da na kama wanda ya kaɗeta Wallahi da sai na kai shi gidan yari. Tayaya zai buge mutum kuma ya ce zai gudu. Kuma zan ji in da aka ce a dinga gudu a cikin kasuwa.”

Munaya dai ta sanƙare. Allah-Allah take Anti Zuwaira ta fice. Tana fita ta jawo gyalen Hajjo. Ta dubeta,

“Lafiya?”

“Yanzu Hajjo baki gane wa ne ne wannan likitan ba? Haba Hajjo. Me ya sa kuke son mayar da ni zararriya ce? Me na yi maki Hajjo?”

Tausayinta ya ratsa Hajara. Ta dawo tana dubanta,

“Wani abu ya yi maki ko? Shikenan ya kashe mu. Shi ya sa ya hanamu shigowa wurinki? Bari in yi sauri in je Office ɗinsa ai nasan Office ɗinsa.”

Munaya ta ce,

“Uncle Zayyad ne fa. Shi, ne likitan da ya dubani. Ya za ayi ki ce kin ga Uncle Zayyad amma baki gane shi ba?”

Hajjo ta ce,

“Me ya ke damunki ne Munaya? Wannan gajeren mutumin ne Uncle Zayyad? Ko dai zafin ciwo ne? Ki kwantar da hankalinki dan Allah. Kin ga su Umma duk za su zo bikin nan, bai kamata su dinga ganinki a cikin wannan yanayin ba. Ki mance da wani Zayyad ki fuskanci abin da ke gabanki. Idan har kina so ki tsira da wannan karatun to ya zama dole ki ajiye komai.”

Munaya ta rufe idanunta ba tare da ta sake furta komai ba. Ta tabbata ko Office ɗin ta ce aje ƙarshe su sake mayar da Ita mahaukaciya. An je biyan kuɗin asibitin aka ce masu Dokto ya biya. Anti Zuwaira ta nemi jin wani dokto ne? Aka kaisu Office ɗinsa ita da Munaya. Tabbas gajeren mutum Munaya ta gani a zaune yana rubuce-rubuce. Ganinsu yasa ya ɗago yana kallon Munaya da jajayen idanunsa. Bata san lokacin da ta, watsa masa wani mugun kallo ba.

“Sannu Munaya. Ya jikin? Ku dinga lura wajen tsallaka titi direbobin nan sam basu da hankali. Suna tuƙi ne kamar za su tashi sama.”

Munaya ta kauda kanta saboda tsantsar takaici. Anti Zuwaira ta yi masa godiya, ya nuna babu komai. Har suka kai gida bata iya furta uffan ba. Tana jin ana mayar da magana amma ko tari bata yi ba. Kalaman Zayyad kaɗai ke ɗaga mata hankali. Ta yi ƙoƙarin ta mance shi, kamar yadda Hajara ta bata shawara, sai dai hakan ba mai yiwuwa bane, sai dai idan an zare mata numfashi.

A sanadiyyar hatsarin da ta yi aka ɗaga bikin Anti Zuwaira. Wanda zai zo daidai da lokacin da za su kammala zana jarabawa, daga nan sai ta bi su Umma su koma Kano tare. Ta ƙosa ta koma gida. Masifun da take gani sun isa su sakata hauka. Tana ji a jikinta anan gaba ba za ta iya tsallake sharrin Zuwaira da Zayyad ba. Ga dukkan alamu dukkansu hatsabibai ne na lamba ɗaya. Tana nan a kwance, ta fara jin sauƙi, kawai ta miƙe ta fice. Kai tsaye gidansu Hajjo ta tafi. Tana zuwa ta sami Amina zuwarta kenan. Bayan ta gaida Mamin Hajjo suka shige ɗaki.

“Hajjo dan Allah ki zo ki kaini gidansu Uncle Zayyad.”

“Wai ke ba za ki rabu da fatalwar nan ba? Na zaci karatu za ki ce mu yi?”

“Ni dai ki zo mu je dan Allah.”

Dole suka tafi gidan. A falo suka sami Hajiya riƙe da Alqur’ani tana karantawa. Bayan sun gaisa ta tambayi yaran gidan, aka tabbatar mata suna Islamiyya. Ta gyaɗa kai.

“Hajiya wai ni kuwa Uncle Zayyad aikin me yake yi?”

Hajiya ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce,

“Babban likita ne a fannin fiɗa. Sai dai baya aiki a ko ina, sai dai yakan je asibitin abokinsa da ke Kano lokaci zuwa lokaci. Kamar yadda Alhaji ya yi maki bayani ne a baya. Zayyad yana da tarin ilimi na ban mamaki. Amma ya ƙi amincewa ya yi aiki da kowa sai a kamfanin mahaifinsa. Ba abin da ya karanta ba kenan, amma abin mamaki. Allah ya yi masa baiwar sanin harkar kasuwanci. Babu in da ba a neme shi ana so a yi aiki da shi ba, amma ko alama bai yarda ba, dan bashi da ra’ayi. Me ya faru?”

Gaba ɗaya sai suka kalli juna. Munaya ta sunkuyar da kanta ƙasa. Ya tabbata ba gamo ta yi ba, Zayyad ɗinne dai ya zo ya dubata.

“Me ya faru Munaya?”

“Dama.. Dama.. Da na ji ciwon nan ne, shi ya yi min aiki a hannuna ya cire min ƙarfe. Kuma…”

Alhaji da ke sakkowa a bene ya ce,

“A’a Munayatu. Duk wanda ya mutu baya dawowa. Idan kika ci karo da shi, ki daina yi masa magana. Ki nuna masa bakya ƙaunar yana zuwa kusa da ke. Aljanu suna yin haka, suna rikiɗewa ta kowacce fuska. Duk yadda kike tunanin hatsabibancin aljani ya wuce nan. Zai iya zuwa wurinki da siffata, ko siffan iyayenki. Ina tunanin akwai aljanin da yake son ya aureki ne, wanda sai an yi da gaske.”

Hawayen da take dannewa suka sakko.

“Daddy Wallahi Uncle Zayyad ba a aljani bane mutum ne kamar kowa. Shi fa ya dubani. Akwai yadda zan yi har ku ganshi. Na yi maka alƙawarin sai ka ga Uncle Zayyad da idanunka.”

Hajiya Nafisa ta haɗiye wani abu saboda tashin hankali ta ce,

“Shi dai Alhaji za ki nunamawa ko? Ni tuni na yarda akwai aljanin da ke son hana ɗana kwanciyar ƙabari.”

Dariya ta so ta suɓuce masu. Hajiya dai ta kama Allah, ta watsar da maganar jita-jita tun ranar da ta ji alamun ana wanka a ɗakin Zayyad. Munaya ta ce barci take ji. Kai tsaye ɗakin Zayyad ta nufa ta yi kwanciyarta akan luntsumeman gadonsa tana juyi. Maganganunsa na neman amincewarta suka dinga dawo mata kai. Sai wajen Magrib suka baro gidan. Su dai lallaɓa Munaya suke yi kada ta rikice masu. Shi kansa Daddy lallaɓata yake.


Ƙarfe biyun dare tana barci ta dinga jin rurin wayarta da ta danne. Cikin magagi ta ɗauka.

“Kin amince da abin da nake buƙata?”

“Eh na amince.”

Ta furta masa tana magagi.

“To fito ƙofar gate ɗinku.”

Miƙewa ta yi, ta kama hanya hannunta ɗauke da hijabin da ta lulluɓa da shi. Yana nan tsaye a bakin gate ɗin. Mamaki ya kama shi. Bai taɓa tunanin za ta iya fitowa a cikin wannan lokacin ba. Bai taɓa tunanin za ta amsa gayyatarsa ba. Yarinyar nan tana neman ta ƙure shi. Shi kuma so yake ko ta wata hanya ta rabu da shi, ta daina tuna shi. Baya son ya saka ‘yar mutane a matsala. Sai dai duk yadda ya yi mata dan ta ƙyale shi abin ya faskara. Hijabin ya karɓa ya zura mata, sannan ya jawo hannunta suka tafi. Idan za ta tuna wannan gidan shi ne gidan da ta taɓa shiga take nemansa aka ce mata gidan ɗan gwamna ne.

Har suka wuce ɗakuna babu alamun akwai mutane a gidan. Ko da yake dare ne, ba lallai, a ji motsin kowa ba. Akan gadon da ya ajiyeta ranar da ya kawo mata taimako daga karnukan nan ya ajiyeta. Cikin dakewa da addu’a ta cire hijabin jikinta, yana zaune yana kallonta. Ta cire ribon ɗin kanta. Gaba ɗaya gashin kanta suka watso. Tana ƙoƙarin cire ‘yar rigar ya dakatar da ita.

“Bari ni zan cire maki da kaina.”

Gabanta ya yi wani mugun faɗuwa, amma ta dake. In dai da gaske abin da take karantawa a cikin idanunsa gaskiya ce, babu ko shakka babu abin da zai iya yi da ita.

Ya matso kusa da ita kamar zai kai mata sumba, ta yi saurin shigewa jikinsa ta kwanta shiru. Dukkansu suna iya jiyo yadda bugun zuciyoyinsu ke bugawa da ƙarfi kuma babu ƙaƙƙautawa.
Ta saka hannu cikin ƙirjinsa tana jin kamar fitsari zai zubo mata dan tsoro. Da sauri ya kauce yana cewa

“A’uzubillah!”

Ta ɗago tana kallonsa. Wani irin sanyi ya dira a jikinta. Ta yi dariya kawai ta kalle shi.

“Ka, gaya mini wa ne ne kai. Ka gaya mini dalilin da kake son ka guje ni. Ka gaya mini cewa Zayyad ɗina yana raye. Ka faɗa mini ɗayan Zayyad ɗinne ya rasu ba nawa Zayyad ɗin ba. Mutum mai tarbiyya da tsoron Allah shi ne yake yin ƙarya dan kawai ya cika wani muradinsa? Akanka na zama haukaciya. Akanka an wulakantani a gaban mutane, an koreni a cikin aji. Saboda kai na rasa tunanina da hankalina.”

Ta tako gabansa tana ƙoƙarin ganin ta daina kukan, amma inaaa. Ta yi ajiyar zuciya, ta nuna shi da yatsa ta ce,

” Akanka, na jure ƙalubale masu tarin yawa. Sannan dan baka da, tausayi baka da imani, ni kake so ka sake ɗorawa akan wata hanya mai wahala? Na shirya! In dai har idan na baka jikina za ka dawo Zayyad ɗinka, ka koma gidanku ka dawo masu da farin cikin da tun bayan rasuwarka suka rasa shi me zai hana ba zan aikata abin da kake so ba? Na shirya baka budurcina domin kaima ka dawo cikin hayyacinka. Kuma ina so ka sani, daga yau zan yi ta bibiyan rayuwarka har sai ka amsa mini wannan Zayyad ɗin bai mutu ba.”

Zayyad dai idanu kawai ya zuba mata. Duk yadda ta yi magana burgeshi take yi. Bai taɓa tunanin ta iya masifa ba, sai yau ɗinnan. Da alama yarinyar nan ita ce silar wargajewar komai, ita ce silar rusa masa duk wani shirinsa.

“Kin zaci da nace maki ki bani kanki wasa nake yi maki?”

Munaya ta yi banza da shi, tana jin gabanta yana faɗuwa. Amma saboda kafiya irin nata ta ƙi ta nuna ko da a fuskarta.

Zayyad ya runtse idanu yana girgiza kai.

“Ka gaya mini gaskiya. Yau ba zan bar nan wurin ba, sai ka gaya mini abin da ke faruwa a cikin rayuwarka. Wai da, gaske ka mutu ne ko kana raye? Ko kuma Zayyad ɗin biyu ne? Na bincika kaf zuri’arku babu ‘yan biyu. Kuma babu mai irin kamanninka. Ka gaya mini ƙasusuwan waye Anti zata kwasa?”

Ƙasusuwan Zayyad Mohammed Hashim zata kwasa. Sai kuma me kike son sani?”

“Waye Zayyad Mohammed Hashim?”

Ya matso daf da ita.

“Ni ne Zayyad Mohammed Hashim. Iya abin da zan iya gaya maki kenan.”

Munaya ta durƙushe a ƙasa, tana kuka. Duk yadda yaso ya nuna kukanta bai dame shi ba, abin ya faskara. Yana jin kukan yana tsaga dukkan sassan jikinsa. Komawa ya yi ya zauna a kujerar da ke ɗakin. Ya kama kansa.

“Ki daina kukan nan.”

Ta ɗago cikin jajayen idanu ta ce,

“Ka gaya mini komai akan rayuwarka. Na yi maka alƙawarin ko ka kasance aljani ne da gaske ba zan taɓa gudunka ba.”

Ya dubeta ido cikin ido,

“Kina so in gaya maki rayuwata kema ki juya mini baya?”

“Ba zan juya maka baya ba. Ka taimakeni ka fitar da ni daga cikin kokwanto.”

Ya yi shiru.. Daga bisani ya fara cewa,

“Sunana Zayyad Mohammed Hashim kamar yadda kika sani.”

Sai kuma ya yi shiru. Wata zuciyar tana gargaɗinsa. Ya tabbata idan ya gaya mata komai lokacin shigarsa matsala ta zo. Amma kuma idan ya yi shiru ba zai iya jure ganin kukanta ba. Yana sonta fiye da yadda yake son kansa. Bai taɓa yin soyayya ba, bai taɓa sanin yaya zaƙi da ɗacin soyayya yake ba, sai a kanta. Yana so ya cire damuwar fuskarta. Yana so ta zama mai ƙoƙari a cikin ajinsu.

Ya miƙe tsaye domin baiwa maganar da zai yi mahimmanci. Ya dinga kaiwa da komowa. Ya furzar da wani irin huci. Ya dawo gabanta ya tsugunna.

“Idan na gaya maki ba za ki sake kuka ba? Za ki daina zama cikin damuwa?”

Da sauri ta gyaɗa kai tana share hawaye.

“Tashi ki saka hijabinki ki zauna akan gadon nan in gaya maki komai.”

Da sauri ta yi yadda ya ce. Ta zauna ta kafe shi da idanu. Tana kula da yadda ko alama baya son yi mata bayani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 13Na Kamu Da Kaunar Matacce 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×