Skip to content
Part 15 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Wani irin guguwa ta zo da ƙarfin gaske, wanda shi kansa bai san daga in da ta fito ba. Duk yadda yaso ya lalubo addu’a hakan ya faskara. Dan haka ya runtse idanu kawai yana jiran abin da zai afku. Sai kuma ya ji shiru. Yana buɗe idanunsa ya nemi Munaya ko sama ko ƙasa bai ganta ba. Mamakinsa ya ƙaru. Babu in da bai dubata ba, amma babu ita. Hankalinsa ya gaza kwanciya. Dan haka ya fito a cikin daren ya nufi gidan Zuwaira. A bakin gate ɗin ya tsaya, ya dubi maigadin ya ce,

“Baba Munaya ta dawo ne?”

Sai da ya durƙusa ƙasa sannan ya ce,

“Eh ta shigo Rankashidaɗe.”

Ya gyaɗa kai kawai, ya juya cike da mamakin wannan lamarin.

Ita kuwa Munaya wani irin barci take yi, irin wanda bata taɓa yin irinsa ba.


Kwanaki biyu kamar komai bai faru ba, suka ci gaba da shirye-shiryen biki. A can cikin Makaranta kuwa, an fara jarabawa. Zayyad ya ci burin taimaka mata. Baya ƙaunar dalilin da zai sa ta faɗi jarabawarta. Dan haka kullum sai ya zo Makarantar, kafin su shiga aji zai tura ayi masu bayani akan yadda ake amsa jarabawa. Munaya ta sami sassauci daga cikin irin raɗaɗin da take kwana take tashi da shi. Haka zalika rayuwar ta sauya mata. Su Hajara ma ba a barsu a baya ba, sun taimaka mata a cikin ɗakin jarabawa.

A kwana a, tashi babu wuya. Munaya ta daina yi wa Anti Zuwaira shisshigi. Haka zalika ta daina neman Zayyad. Wanda shi kuma har kwanciya ya yi babu lafiya a sakamakon rashin ganinta.
Abin takaici Munaya ta zaci za a rufe gidan Anti Zuwaira ne a tafi gidansu ayi biki. Sai ita da mahaifiyarta suka nuna sam! Anan gidan za ayi komai, kowa ya, watse. Ɗaurin auren kuma ayi a can gidan mahaifinta. Yadda dai ta tsara haka akayi. Tunda Umma da Hajiya Baraka suka zo, Munaya take yiwa Hajiya Baraka kallon tausayi. Ta haifi wacce za ta kasheta da hannayenta. Bayan Munaya ta zauna da ita da Ummanta sai ta fashe da kuka. Umma tasan akwai matsala dan haka ta ce,

“Munaya. Ki gaya mini me ya sameki? Kin ga yadda kika rame kika lalace? Ko dai Zuwaira tana matsa maki ne?”

Munaya ta girgiza kai tana, share hawayenta.

“Umma na kasa sabawa da garin nan ne.”
Umman ta yi dariya,

“Shi ke nan matsalar? Duk ƙoƙarin da su Hajara suke yi bai sa garinsu ya burgeki ba?”

Anan suka yi ta hira, har take jin zuciyarta ta sami sassauci daga irin raɗaɗin da take kwana tana tashi da shi. Anan suka yi ta shirin zuwa Dinner. Umma dai da Hajiya Baraka sun ce ba za su je ba. Har Munaya ta zo wucewa ta ji Hajiya Baraka tana yiwa ‘yar ta faɗa,

“Haba Zuwaira. Zayyad fa ya rasu. Me ne ne na barin hotonsa a ɗakin nan? Sannan ba za ki je ki dawo da ‘yarki gabanki ba? Me ne ne haka? Kuma shi Mubaraak ɗin nan hankalina ba kwanciya ya yi da shi ba, domin shi ne wanda.”

Zuwaira ta yi saurin dakatar da ita,

“Shi ne wanda Munaya za ta aura ko? To ni Hajiya ina ruwana? Ke baki ga ita Munayar marigayi mijina take so ba? Hakan ya nuna da yana raye za ta iya binsa kenan. Kuma maganar hoton Zayyad ba zan iya cire hotonsa ba. Maganar Islam kuma zan ɗaukota ba yanzu ba. Ki daina zancen nan, domin shi kansa bai taɓa sanin ina da wata ɗiya ba. Ni auren nan kawai yinsa zan yi.”

Ta juya ta fice. Munaya ta runtse idanu ta jingina da jikin bango,

“Na bar maki Mubaraak, kamar yadda ta zama dole nima ki bar mini Zayyad.”

Anti Hauwa ce babbar ƙawar amarya. Abin ma gwanin ban dariya. Tiƙa-tiƙa da su, saboda budurwar zuciya wai suna yin abubuwan ‘yan mata.

Yau Munaya har da make up, ta yi bala’in kyau sosai. Hajara ta kaita wurin make up ta biya. Sun yi ankonsu su uku. Anti Hauwa ita ce mai bayar da tarihin amarya. A cikin tarihin an tsame aure-auren da ta yi. Wani irin ƙarni da Munaya take ji shi ya sakata jin amai yana taso mata. Da gudu ta yi waje tana kwarara amai. Can baya ta tafi tana aman nan kamar kayan cikinta za su fito.

Yana tsaye ya rungume hannu yana kallonta. Tana gamawa ya miƙa mata ruwa,

“Gashi ki kuskure bakinki.”

Ta ƙarba tana wanke baki. Sai can ta tuna, waye mai muryar. Ta ɗago a razane tana kallonsa. Duk ya rame mata.

“Ka yi ciwo ne?”

“MATACCE baya ciwo Munaya. Wani taimako nake nema a gareki.”

“Ina saurarenka.”

“An haɗa yadda za a kashe mahaifina gobe da ƙarfe goma sha biyun dare, a ɗakinsa. Ba ni da halin taimaka masa. Ke kaɗai za ki iya yi mini sadaukarwar nan.”

Cikin karkarwa ta ce,

“Me.. Me.. Me.. Ne? Daddy za su kashe? Daddy??”

Ya girgiza kai.

“Daddy da Hajiya sun ɗauko masifa da hannayensu sun kawo cikin gidanmu. Rayuwar mutanan gidanmu yana cikin hatsari. Domin kuwa dukkansu an bayar da su a cikin ɗakin tsafi. Lokaci kawai suke jira su ɗauke kowa. Suna so su shafe tarihin gidan Alhaji Mohd Hashim. A cikin waɗanda za su ɗauke har da Rumaisa.”

Tunda yake fito mata, bai taɓa fitowa a cikin tsananin damuwa irin na yau ba. Sai ya ta kula da wani abu. Idan har da gaske Zayyad aljani ne ko matacce me ya sa bai taɓa yi mata wani abu da zai nuna shi aljani bane? Me ya sa bata taɓa ganin ya ɓace ko ya ɓullo ba? Me ya sa ba zai je ya taimaki iyayensa ba? A baya ya ce basu suka haife shi ba.

‘Me ya sa ke kaɗai kike ganinsa?’

Wata zuciyar ta yi saurin an karar da ita. Wannan kaɗai ya isa ya saka ta gane cewa aljanin ne. Ta yi ajiyar zuciya. Tana cikin tafiya ta ji wani irin kuuuwa a hanyar banɗakin. Dan haka ta koma a hankali tana leƙe.

Anti Hauwa ta gani tana feɗe cikin wani mutum da ba za ta iya cewa waye ba. Feɗewa take yi da sauri-sauri. Jini yana ta kwarara. Cak! Ta dakata ba tare da ta juya ba. Hakan yasa hantar cikin Munaya ya kaɗa. Tsananin tsoro ya shigeta. A hargitse ta juyo tare da wani irin kururuwa. Munaya da ƙafafunta suka ɗauki rawa, ta durƙusa ƙasa tana numfarfashi. Hauwan ta juyo da wuƙar nan tana zare idanu. Bakinta duk jini. A daf da Munaya ta tsaya tana zazzare idanu. Ta waiga hagu da dama, tana neman wanda ta ji motsinsa yanzu amma bata ga kowa ba.

Yadda jikinta ke rawa yasa kunnuwan Hauwa suka jiyo sautin bugun zuciyarta. Ta juyo kenan ta sake jin alamun za a shigo banɗakin hakan yasa ta ɓoye a kusa da Munaya. Wani matashi ne ya shigo, hakan yasa yana shiga ya ci karo da mummunan aikin da Hauwa take yi. Zai juya da gudu ta fizgo shi, kafin yasan abun yi, ta caka masa wuƙa a ciki, ta kuma toshe masa baki. Daga bisani ta kafa haƙoranta tana zuƙar jini. Can ta cusa hannunta a cikinsa ta zaro kayan cikin tana cusawa a baki.
Yau ranarta ce, domin ta yi alƙawarin kashe mutane ashirin saboda da su za a yi party na bikin Zuwaira. Ita dai ta roƙi a bar mata kayan ciki, dan haka an bar mata na mutane biyar.

Duk wanda ta gani sai ta kashe shi ta watsa a cikin wani banɗaki. Tsananin tashin hankali Munaya ta ganshi a wannan dare. Ta Tabbata babu yadda za ayi ta fice ba tare da Hauwa ta ganta ba. Allah ya taimaketa wayarta tana gida a kashe, ta cusa a cikin kayanta.
Muryar Hajara ta ji tana takowa tana waya,

“Eh. Yi haƙuri banɗaki zan shiga, idan na fito zan kira.”

Ta katse kiran ta cusa kai. Munaya ta runtse idanu ƙafafunta suna rawa. Ta faru ta ƙare babbar aminiyarta za ta faɗa cikin tarkon Hauwa. Hajara tana sa kai ta yi ido biyu da bayan Hauwa, domin bata juyo ba. Hajara ta zazzaro idanu tana kallon tarin mutanen da ke kwance babu numfashi. Ga uban ƙarni na tashin hankali. Hajara bata ga fuskar waye ba, dan haka ta ce,

“Me zan gani? Me.. Me.. Me..”

Ta kasa ƙarasawa. Saboda tunda Allah ya halicceta bata taɓa ganin masifa irin na yau ba. Hauwa ta gane muryarta, dan haka itama jikinta ya dinga tsuma. Ta ɗaga wuƙar da nufin ta juyo ta caka mata. A lokacin Munaya ta yi wani irin kukan kura ta fizgo Hajara suka yi waje da gudun gaske. Ba su da mafaka da ya wuce ɗakin taron. Dan haka suka tafi ɗakin taro suka zauna a kusa da amarya da ango. Jikinsu babu ta in da baya ɓari. Dukkansu sun kasa yiwa junansu magana.

Har aka tashi wurin taron, babu wanda ya ce wa ɗan uwansa uffan. Bayan, sun isa gida, suka watsa ruwa kowa ya koma ya zauna. Amina ta dube su bayan ta je ta rufe ƙofa ta dawo tana kallon su,

“Wai lafiyarku ƙalau ƙuwa? Ko dai wani abu ya faru ne?”

Munaya ta labarta mata komai, ta ƙara da cewa

“Da yanzu wani labarin ake yi. Da yanzu an, kashe Hajara.”

Ta fashe da matsananciyar kuka. Hajara kuwa tunda ta manne da jikin bango ta kasa ko da tari. Yau da ace gida za ta koma, da sai dai ta kira iyayenta su zo su ɗauketa. Ta jinjinawa Munaya. Ta tabbata da ba dan ita ba, da tuni wani labarin ake yi, ba wannan ba.

Amina ta jinjina kai,

“Abubuwan nan suna daɗa nisa. Wannan wacce irin masifa ce haka? Mutum ɗan adam ake yankawa kamar wani dabba? Saboda kawai neman duniya? Wani irin shagala ce haka da har zai sa ka mance lahirarka? Dama Labaran da ake bayarwa da gaske ne? Kunsan wani abu ne?”

Duk suka girgiza kai,

“Gaskiya har da sakacinmu. Musamman ma ke Munaya, Allah yana kareki. Bansan dalilin da yasa kike wasa da ibada ba, kullum sai an tuna maki sannan kike yi, ana kwana biyu ki mance. Duk da duk abin da Allah ya rubuto akanka sai ya faru, amma fa addu’a yana taimakawa komai ya zo da sauƙi.”

Ta ɗan yi shiru, daga bisani ta ce,

“Idan an gama biki mu je wurin mahaifina sai mu ji me zai ce.”

Munaya ta runtse idanu hawaye na sake fita. Yau da an kashe Hajara ta dalilinta da ba za ta taɓa yafewa kanta ba.
“Gobe zamu koma gida ni da su Umma. Gashi goben za, aje a kashe Daddy.”
Anan ma, sai duk ɗakin suka yi shiru.
“Waye ya gaya maki?”
Amina ta yi tambayar cike da al’ajabi.
“Ba sai na gaya maki wanda ya gaya mini ba. Amma dai tabbas gobe za a kashe Daddy.”
“Tabɗijan. Yanzu ya zamu yi a shawo kan Umma ta bar tafiyar nan zuwa jibi?”
Munaya ta jinjina kanta, ta sake sharce hawayen da suka ƙi tsayawa,
“Bansan ya za ayi ba. Samun mai, shawo kan Umma akan ta ƙara kwana akwai wahala.”
“Ok. Ko zamu je mu zuga anti Zuwaira akan gobe ayi buɗan kai, a cikin gidan nan wanda Umma ita ce uwa dan haka dole za ta zauna har sai an yi an gama jibi sai ku wuce.”
Munaya ta, jinjina kai,
“Mu, gwada mu gani.”
Suna miƙewa Hajara ta yi tsalle ta diro, sai gata a bakin ƙofa. Ta riƙesu tsam jikinta babu ta in da baya rawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 14Na Kamu Da Kaunar Matacce 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×