Skip to content
Part 17 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

Kai tsaye gida ta, shigo. Babu wanda ya kula da ita a, sakamakon hayaniyar biki. A in da ta taɓa ganin Anti Zuwaira ta ajiye key anan ta duba taga babu. Hankalinta ya ƙara tashi. Anti Zuwaira tana can tare da ƙawayenta duniyar ta yi mata daɗi. Dan haka Munaya ta afka ɗakinta. Duk duban duniyar nan ta yi babu makullin nan. Gaba ɗaya ta yi zuba ta jiƙe sharkaf. Ta yi rantsuwa da Allah idan bata ga makullin nan ba, zata tashi hankalin kowa, za ta tona mata asiri a gaban duk wata halitta da ke cikin gidan.

Har ta juya jikinta yana tsuma, ta ji ta taka wani abu. Dole ta ɗan sarara ta duba. Jikinta yana kyarma ta durƙusa ta ɗauka. A lokacin ta ji alamun buɗe ƙofa. Cikin gaggawa ta ɓoye a bayan gadonta, ta runtse idanu tana addu’a. Anti Zuwaira ce ta zo ɗaukar jaka. Har ta ɗauka sai kuma ta dakata tana zazzare idanu. Jikinta ya, bata akwai matsala a ɗakinta.

Ta juya da nufin zuwa wurin gadon, aka bankaɗo ƙofa. Hauwa ce ta shigo ta fizgo hannunta da sauri suka fice. Cikin gaggawa Munaya ta fice tana haki.

Addu’a ta yi sosai sannan ta cusa kanta bayan ta buɗe. Tafiya take tana addu’a tana shafawa jikinta. Ita ta sani, ba aljani ba, hatta matsafan ta fi ƙarfinsu. Ta yi tafiya mai nisa babu komai. Can ta hango wani ɗaki kamar yana ci da wuta. Ta ja ta tsaya tana leƙe. A lokacin taga mutum a gabanta. Za ta yi ihu ya saka hannunsa ya rufe mata baki.
“Ka da ki yi ihu ni ne Zayyad.”

Ta ware idanunta da, suka kumbura ta kalle shi. Sai kuma ta faɗa jikinsa tana kuka mara, sauti,

“Uncle sun, sun tafi da da kuruwar Daddy.”

Anan ma ya sake kwantar da kanta,

“Ki yi shiru babu lokaci.”

Sannan ya janyeta daga jikinsa yana kallon cikin ɗakin. Sai da suka yi addu’a sannan suka sa kansu a ciki.

Zayyad ya fara magana da kakkausar murya,

“Zuwaira! Kina nema, ki wuce iyakarki, kina nema ki kai kanki in da asirinki zai tonu. Kin kasheni, baki haƙura ba, shi ne kike nema ki ɓatar mini da ahlina? Za ki iya yin komai in ƙyaleki, amma kada ki yi kuskuren taɓa dangina. Ki bani kwalbar nan tun kafin in kassara rayuwarki a wannan daren.”

Zuwaira tana zaune a, kusa da Umma da dangin mahaifinta da kuma Hajiyarta. Tana jin dukkan maganganun da ake yi, hakan yasa hankalinta ya yi mummunan tashi. Idan zata miƙe sai a dankwafar da ita a hanata.

Wani baƙin kare ya dinga tunkarosu. Zayyad ya yi amfani da wannan ƙwandalar ya dinga haskesu da shi. Suna ihu. A ya yin da Munaya ta tafi kai tsaye ta ɗauki kwalbar nan ta yi hanyar fita da gudu. Zayyad ya dawo da ita, sannan ya nuna mata hanyar da za, su bi. Abin mamaki sai gashi sun ɓullo a waje. Ta sake cika da mamaki. Bata taɓa sanin akwai wata hanya da za a iya ficewa ba sai yau. Suna ficewa suka afka motar Hajara, suka fice a gujen gaske. Sai da suka yi nisa sannan suka tsaya. Munaya ta buga kwalbar nan a ƙasa. Sai kuwa abun ciki ya ɓace ɓat! Kwalbar ta tarwatse.

Duk suka yi ajiyar zuciya. Zata sake faɗawa jikinsa ya girgiza mata kai,

“A’a Munaya. Babu kowa anan daga mu sai shaiɗan. Zai iya yin amfani da wannan damar ya cusa mana wani tunani.”

Ta yarda da zancensa. Ita kuma dama kuka take so ta yi, dan haka ta kwantar da kai a jikin motar tana kuka mai tsuma zuciya.

“Ki yi haƙuri ki daina kuka. Na sakaki a cikin matsala. A yanzu haka matsalar bata ƙare ba, musamman idan Zuwaira ta gano cewa ke ce silar ɗauko wannan kwalbar. Na gode Munaya. Allah ya nuna mini ranar bikina da ke, in rama maki alkhairin da kika yi mini ta hanyar baki kulawa fiye da kowacce mace a duniya.”

Cak! Ta dakata da kukan, da take yi, ta zuba masa idanu ta cikin farin wata. Dukkansu suka ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu. Bugun zuciyoyinsu ya sauya. Haƙiƙa soyayya ba ƙarya ba ce. Ba za ka gane hakan ba, sai idan ka faɗa cikinta. Ya buɗe mata mota ya ce,

“Ki, shiga ki koma wurinsu Amina. Za ki sami Daddy ya ji sauƙi. Kada ku fita gidanmu sai Daddy ya sanar da ku me ya aikata a rayuwarsa da har su Zuwaira suke kawowa zuri’arsa farmaki. Idan ya gaya maku sai ki zo ki bani labari, domin nima bansan ta yadda laifukansu yake nema ya shafeni ba. Ko kuma in ce ya shafeni.”

Munaya ta shige motar jikinta a sanyaye. Yana kallo ta wuce. Ya yi ajiyar zuciya. Lokaci ya zo da zai cire Munaya a cikin matsalar da take ciki. Motarsa ce ta tsaya a gabansa, bai ce komai ba, ya buɗe kawai ya shiga Bello ya ja suka bar wurin. Munaya kuwa kalaman Zayyad sun ƙarasa kashe mata jiki. Gaba ɗaya gani take yi komai a mafarki suke faruwa.

‘Tayaya zan iya faɗa da matsafa? Tayaya da raina da lafiyata zan faɗo cikin matsala ina gani? Duk, saboda soyayya ce ko kuwa tausayi?’

Da waɗannan tunane-tunanen ta iso gidan. A gujen gaske ta fito ta afka cikin falon da ta barsu. Duk suna zazzaune kamar komai bai faru ba. Farin ciki ya tsirga mata ganin Daddy a zaune. Hajara ta ce,

“Sannu da ƙoƙari Munaya. Umma ta kirani na gaya mata a gidanmu zamu kwana. Ta buƙaci in baki waya na gaya mata kin sha magani kin kwanta.”

Munaya ta gyaɗa kai alamun ta gamsu. Har yanzu hawayen sun ƙi tsayawa daga idanunta. Su Suhaima sai kallonta suke suna kuka. Sun rasa ta yadda za su gode mata. Yau da a ce Munaya bata zo ba, da yanzu duk an kashe su. Munaya ta dubi Daddy ta ce,

“Daddy ka taimaka ka gaya mana ko akwai wata matsala ce a tsakaninka da matsafa? Ko ka taɓa aikatawa wani wata kuskure ne?”

Daddy ya ɗaga kansa yana kallon Munaya. Ya ce,

“Ɗiyata Allah ya biyaki da gidan Aljanna. Yau zan gaya maku abubuwan da ban taɓa gayawa kowa ba. Na taɓa yin wani kuskure a, shekarun baya..

“Sunana Alhaji Mohd Hashim, kamar yadda kowa ya sani. Mu mutanan Katsina ce. Mu uku iyayenmu suka haifa, ni ne babba sai Kabiru, da kuma ƙanwarmu Hama. Bayan na dawo daga Karatu sai mahaifinmu ya sanar mini akan ya yi min aure. Na shiga tashin hankali irin wanda ban taɓa shiga ba, a sakamakon ni ina da wacce na taɓa yiwa alƙawarin aure wato Nafisa. Shi kuma ya dage dole sai na zauna da zaɓinsa Karimatu. Ban yi masa musu ba, kasancewar ban taɓa yiwa iyayena gardama ba. Dan haka na kira wani babban amininsa na roƙe shi, ya je ya sami iyayena idan Karima zata tare, a ɗaura aurena da Nafisa, na amince zan iya zama da mata biyu.

“Da a ka je aka tambayi mahaifina sai ya ce ya amince. Dan haka aka haɗa mini mata biyu suka tare a rana ɗaya. Farko a Katsina muka fara zama, daga baya kuma sai harkar kasuwancina ya cilloni Kaduna. Dan haka na samu gida ɗan madaidaici na siya, na tattara matana muka koma can.”

Daddy ya ɗan dakata yana duban fuskokin kowa. Sannan ya ci gaba da cewa,

“Tunda muka dawo Kaduna matsaloli suka kawo mini ziyara. Karamatu masifaffiya ce ta lamba ɗaya. A ya yin da ita Nafisa take da sanyi. Da farko sharri ta fara yiwa Nafisa, da yake bana zama sai nake yawaita yi mata faɗa. Ita kuma mace ce mai haƙuri, sai dai ta yi ta bani haƙuri ba tare da ta taɓa neman kare kanta ba.

“Na yi wa Nafisa rashin adalci, na juya mata baya. Amma ko da wasa bata taɓa kai ƙarana ba. A ganinta auren soyayya muka yi dole ta yi haƙuri da ni. Ana haka Nafisa ta sami ciki. Na yi murna da wannan ciki, hakan ya jawo nake tausaya mata.

“Wannan lamari ya jawo tashin hankula a cikin gidana. Karima ta dage ta hana kowa kwanciyar hankali. Tsintuwa da Allah ya isa mun sha shi har mun gode Allah.

“Akwai ranar da ina dawowa gida na sami, ta yi wa Nafisa dukan tsiya har ta jawo mata zubar jini. Wannan lamarin ya tashi hankalina. Ko da na kaita asibiti har cikin ya zube. Dan haka na saki Karima saki ɗaya na aikata gida.

“Da kaina na kira mahaifina na yi masa bayanin komai, kuma ya gamsu da hukuncina. Ran mahaifina idan ya yi dubu to ya ɓaci, dan haka Karima tana ƙarasowa gida, ya taka da kansa ya je har gidansu ya yi mata masifa kamar zai rufeta da duka. Daga nan ya ce ba zan dawo da ita ba, tunda har za ta iya aikata mummunan aiki irin wannan.”

Daddy ya sake ɗagowa ya dubi Hajiya Nafisa da ta sunkuyar da kanta ƙasa. Sannan ya ci gaba da cewa,

“Zamanmu ya yi daɗi da Nafisa, bamu da wata damuwa. Watarana ina wurin aiki, mahaifina ya kirani ya ce maza-maza in mayar da Karimatu ɗakina. Na yi mamakin waɗannan kalaman nasa, domin ko da, safe mun yi waya da shi, yana sake yin tir da halin Karima. Kamar yadda na gaya maku ne, haka tarbiyyar gidanmu yake, bamu isa mu tambayi babba dalili ba, bare kuma iyaye. Na amsa masa da shikenan. Har na dawo gida babu walwala.

“Ban ɓoyewa Nafisa komai ba, na gaya mata. Ita kanta ta ta shiga tashin hankali, domin kuwa Karima ta gasa mata gyaɗa a hannu. Amma sai ta dinga ƙarfafa mini guiwa akan in bi umarnin iyayena.

“Bayan Sati biyu Karima ta dawo gidana. A lokacin Nafisa tana da ciki, amma bamu gayawa kowa ba, gudun tashin hankali. Kasancewar bata da girman ciki, kuma bata yi laulayi ba, sai asirinmu ya rufu. Sai da cikin yakai wata takwas sannan ta an kare da shi. A ranar Karima ko runtsawa bata yi ba.
Kafin tasan abun yi, har an haife cikin nan. Ta sami ɗanta namiji aka sa masa Zayyad.

“Zayyad yasha baƙar wahala a wurin Karima, kamar ba zai rayu ba. Yana da shekaru shida a duniya wata tafiya ta kamani. Dan haka Nafisa ta ce ita ba zata zauna ba, ga laulayi tana yi, ga kuma izayar Karima. Dan haka na ɗauki Nafisa da kaina na mayar da ita gidan iyayena akan ta zauna sai na dawo. Ita kuma Karima na barta a gidana dake Kaduna. Daga nan na bar ƙasar.

Wasa-wasa har sai da na yi shekaru ɗaya ban dawo gida ba. Amma duk ina waya da su, sannan Nafisa ta sake haihuwa ta haifi Afrah. Mahaifina ya gaya mini yadda yake jin daɗin zama da Nafisa, yana yawaita gaya mini kyawawan halayyarta. Ɗiyata Afrah bata sanni ba, sai a hoto da kuma waya idan na kira, nakan ce a bani ita in yi ta biyewa gwarancinta. Shi kuwa Zayyad ya fara girma ne da ilimi da ya gada a, wurin mahaifina. Yana da farin jini, da kuma kaifin ƙwaƙwalwa, ga wayo da Allah ya hore masa. Da wahala ka haɗu da Zayyad sau ɗaya bai tsaya maka a rai ba.

“A lokacin da na dawo ta Kaduna muka dawo. Na sami arziƙi mai suna arziƙi. Dan haka gidan Karima na fara isa. Me zan gani? Karima na samu ɗauke da ciki haihuwa yau ko gobe. Raina ya yi mummunan ɓaci, na tambayeta me ke faruwa? Waye ya yi mata ciki?

“Sai kawai ta kama kuka tana cewa wai itama tashi ta yi ta, ganta da cikin nan.

“Wannan maganar ba za ta taɓa faɗuwa ba. Na ruɗe. Ban ce mata komai ba na fice daga gidan. A hotel na kwana, washegari na je wurin wanda na ba kwangilar gina mini gida, muka je gidan tare. Ya yi mini amana ya damƙa mini takarduna a hannu. Gini ne na gani na faɗa. Na dinga ganin kiran wayar Karima ina katsewa. Daga baya na ɗaga, anan take gaya min cikin kuka wai ta haihu. Na ja tsaki na, kashe wayata.”

“Na tafi da Katsina na dawo da iyalaina, cikin sabon gida. Mahaifina da dangina suka, zo gidan domin su sa albarka, basu ga Karima ba. Na yi masu ƙarya a karo na farko akan ta tafi gidan ƙawarta suna buki. Na ji tsoron gayawa mahaifina gaskiyar abun da ya faru, kasancewar yana da ciwon zuciya, ina tsoron wacce batasan darajarsa ba, ta yi sanadin barinsa gidan duniya, ko kuma sanadin shan wahalarsa.”

Daddy ya yi ajiyar zuciya, yana jin tamkar kada ya fasa abin da ya faru. Sai dai kuma irin masifun da suke tunkararsa idan bai faɗa ba, ba zai sami sassauci ba. Shi kansa yana kasa barci akan wannan lamarin. Ya ɗago yana kallon yadda duk suka zuba masa idanu. Su Suhaima suna ta mamaki domin basu taɓa sanin mahaifinsa ya taɓa aure bayan mahaifiyarsu ba.

Muje zuwa. Alƙalamin ‘Yar mutan Borno.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 16Na Kamu Da Kaunar Matacce 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×