Daddy ya sunkuyar da kai, ya ci gaba da cewa,
"Da Nafisa ta tambayeni in da na kai Karima, sai nace mata na raba masu gida ne. Haka na gayawa kowa. Idan Karima ta je Katsina tana ɓoye ɗiyarta ta shiga har gidanmu ta ce muna nan lafiya. Haka muka kwashe shekara guda ba tare da na waiwayeta ba.
"Watarana ina Office sai ga Karima. Na yi mamakin yadda akayi tasan ofishina. Sannan tayaya sakatarena zai barta ta shiga babu izini. Na dubeta rai a ɓace na ce,
"Lafiya kuwa? Me kika zo yi wurina maciya amana. Kin ji kunya. . .