"Har Zayyad ya dawo da Ruma Zuwaira bata bar gidan ba. Shi kuma bai sake bin ta kanta ba, ya ɓare magunguna ya ba Ruma sannan ya tasata a gaba suka wuce ciki. Zayyad bai sake fitowa ba, sai da shirin zuwa Masallaci domin ya yi Magrib. Mamakinsa ya, kasa ɓuya da yaga Zuwaira zaune. Kamar zai yi magana, sai kuma ya fasa ya fice. Tana ganin ya fita ta yi min sallama ta bi bayansa. Akan hanyar yake gaya mini ta so ta tsaida shi da magana, ya dai ce mata sai anjima ya fice.
"Kwanaki biyu Zuwaira ta. . .