Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

Malam Rabi’u ya ɗago ya kalli su Baffa yana faɗin “Mahaifiyar Sadauki na ɗauke da cikin Bobbo wata ɗaya cif , a wannan daren Aljani Mazbandala ya saka ƙwanshi a cikinta “, Baffa ya ce “Tabbas Mamman Sadauki ta wahala matuƙa cikin Sadauki , a lokacin tagwaye ta haifa ɗaya ya zo ba rai ɗaya kuma ya tsaya shi ne Sadauki “, Malam Rabi’u ya ce “Wanda ya mutu shi ne ɗanku , ya mutu ne saboda jaririn ɗanku bazai iya rayuwa tare da Sadauki ba ” , hawaye na bin kuncin Mamma ta miƙe tsaye , Malam Rabi’u ya kalle ta cikin tausayawa ya ce “Zauna na fahimce ki , Mahaifiyar Sadauki ta riga ta san sirrin tun Sadauki na shekara bakwai duniya , dalilin da yasa ta ƙirƙiri tafiya zuwa Zuru ganin wani malami , malamin ne ya sanar da ita halin da Bobbo yake ciki , anan ne aka rage mishi ƙarfinshi na halittarshi , wannan dalilin yasa Mamman Sadauki bata so a san gaskiya “, Arɗo ya ce “Amma Mamma bai kamata kiyi shiru ba  , ina amfanin baɗi ba rai “, cikin kuka da faɗa Mamma ta ce “To ko ka ƙi ko ka so Bobbo ɗan uwanka ne , daga Cikina ya fito kuma ni na shayar da shi ,kuma ina sonshi”, Arɗo ya ce “Ai bazan guje shi ba ko da ba komai Bobbo bai taɓa ƙin girmama ni ba ” , Baffa ya ce “Yanzu malam ya za a yi “, Malam Rabi’u zai yi magana Mamma tayi karaf karɓi zance da cewa “Ba wani abun da za a yi , in duk duniya zata taru babu mai Rabani da Sadauki ” jinjina kai Malam Rabi’u yayi tare da faɗin “Tabbas babu wanda zai raba ki da Sadauki sai Allah , a taƙaice ma asalin mahaifin Sadauki ya mutu a Farmakin da Sarki Zawatunduma ya kaima garin Mubanuwa ” ,  Bobbo sai jin su yake yi amma shi abunda suke yi bai dame shi ba .

Nahad dake tsaye ta ce “Malam shi ne Nawa ɓangaren ka bar mu tare da shi “, Malam Rabi’u ya ce “Ki fito a siffar da bazai wahala ba  ” , Baffa ya ce “Ya kamata a kare aikin da aka mishi saboda ya samu yayi rayuwa irin wadda Allah ya mishi ba mai kauce ƙaddararshi ” , Mamma dai yanzu hankalinta ya kwanta dan dama duk fargabanta bai wuce a ce yau an raba ta da Sadauki ba , ko kuma za a raba ta da shi ba .

Nan Malam Rabi’u da Arɗo suka shiga da Sadauki bisa umurnin malamin . Baffa ya bi bayansu aka Bar mamma da Asama zaune .

Nahad kuma na tsaye.

*****

Ɓangaren Hajiya Maryam kuwa ta tashi tun safe tana mai mugun jin kunyar Alhaji Sulaiman , haka yasa ta yi wanka ta shirya tsaf cikin wata ƙyatattar riga wadda ta zauna a jikinta , kitchen ta shiga ta ɗora mishi abinci da ya fi so fiye da kowane abinci wato Shinkafa da wanke da miyar kifi da salat ,  wanda ta yanka ziri-ziri ƙanana-ƙanana tare da Albasa da tumatur .  Ta haɗa mishi zoɓe wanda ya ji haɗin kayan ƙamshi da yaji , ya kuma ji cucumber Dan ƙamshinta Sai tashi yake yi , sannan ya zuba a basket da plate da cup ,  ta kai mishi har ɓangarenshi .

Yana zaune yana taɓa duba wasu takardu Hajiya Maryam ta shigo da sallama a bakinta riƙe da basket a hannunta . Amsa mata yayi yana tattare takardun ya aje gefe ɗaya , Cikin jin kunya ta  aje kwandon abinci , ta ɗago ta ce “ga wannan na san zaka so shi ” , murmushi yayi ya ce “Na gode Amaryata Allah ya miki albarka “, wani nannauyan numfashi ta sauke tare da kallonshi ba tare da ta ankare ba kawai sai ki tayi hawaye na kai kawo a kuncinta , da sauri Alhaji Sulaiman ya tashi ya durƙusa gabanta tare da sa hannun ya share hawayen dake bin kuncinta yana girgiza kai alamar kar tayi kuka , cikin rawar muryar dake nuna mutum na ƙoƙarin shanye hawaye ta ce “Haƙiƙa mijina na tafka Babban kuskure , kuma ina Dana sanin aikata hakan , dan Allah mijina kayi haƙ…” hannunshi ya ɗora kan bakinta ya ce “Shhhhhhh , kar ki ce komai . Mafi alkhairin mutum shi ne wanda yayi kuskure kuma ya fahimci kuskurenshi , ki gode ma Allah da yake sonki da rahamarsa har ya ganar dake gaskiya cikin dubunnin mutane , badan kin fi so ba , amma dai ya zaɓe cikin masu rabo daga rahamarsa , ki ɗauka hakan darasi ne gare ki da kuma ƴan baya ” ,  hawaye suka ƙara gangaro mata .ta ce “Haƙiƙa da ni Maryam ban aure ka ba ban san wane mijin zan aura mai adalci kamar ka ba ,  kai ɗin nan mutum ne mai Matuƙar arziki , idan na ce maka arziki ba wai iya duniya nake gane maka ba , ina hango maka lahirarka ” , ƴar dariya yayi yana miƙewa tsaye tare da ɗaga ta tsaye itama .suka zauna gefen gado . jawo ta yayi sosai ya manna a ƙirjinshi ya ce “Hajiyata mutum baya ganin gobenshi . Ke ɗin nan ba za ki iya gane ɗan aljanna da ɗan wuta ba sai an je can , mutum zai kasance yana aikin lada iya rayuwarshi amma rana ɗaya ya tafka babban kuskuren da zai jefa shi wuta , haka ma mutum zai kasance yana ɓatanci tsawon rayuwarshi , amma Maryam in Allah na sonka da rahamarshi sai ya sa kayi aikin alkhairi ɗaya wanda zai maye maka gurbin kura-kuranka , ke dai kawai kiyi fatan Allah yasa mu cika da imani ” , Rufe ido tayi cikin soyayya ta ce “ba ja in ja na gamsu da duka bayananka mijina ” sai kuma tayi saurin tashi daga ƙirjinshi tana faɗin “Baka ci abinci ba fa “, “Zan ci matata , ki zuba min tare zamu ci ” ya faɗa  , zuba mishi abincin tayi suka ci tare cikin raha da annashuwa.

*****

Bayan awa uku Malam Rabi’u da su Bobbo suka fito daga ɗakin . Nahad ta nufi Bobbo da gudu wanda yanzu ya kasance kowa yana ganinta ta rungume shi , lumshe ido yayi yana ji wani mugun sonta har zuciyarshi . “Mu je muyi shirin aure ” Nahad ta faɗa . Bobbo ya kalli su Mamma ya ce “muna gayyatarku ku kaɗai zuwa aurenmu jibi da misali 2:30 na dare ” , Mamma da Su Baffa suka tsaya turus suna kallon Bobbo ko ya manta su mutane dare lokacin barcinsu ne . Nahad ta ce “Kar ku damu daren jibi zai kasance kamar safiya gare ku ” . Malam Rabi’u ya kalli agogonshi ya ce “Yanzu lokacin dana ɗibar muku yayi zaku iya ci gaba da labarin waje mutane na jira na ” , sosai su Baffa suka gode mishi , Nahad ta mishi kyautar sarƙar Murja ni da lu’ulu’u .

*****

Waje suka fito inda Bobbo ya riƙe hannun Nahad ya ɗaga sama ɓat suka ɓace sai gidansu Nahad . Hajiya Maryam da His excellency Alhaji Sulaiman suna tsaye gaban mota , yayin da sojoji suke tsaye kamar yadda suka saba jerawa duk sun ƙame , kawai kawai suka ji wata gigitacciyar ƙara , nan take duka sojojin suka saita bindinga , iska ya taso ko ina kaɗawa yake yi , “Ummana !” Suka jiyo sautin muryar Nahad , da sauri suka juya yayinda sojojin suka juyar da bindingarsu ga Nahad tare da saita harsashensu . His excellency ya musu umurni cikin tsawa akan su aje bindiga , jikinsu na rawa suka sauke bindigoginsu .

Nahad da idonta suka yi ja ta tunkaro iyayenta tana riƙe da Bobbo , Kallon Alhaji Sulaiman tayi ta ce “ Abbana Na gode , Na gode da zama da ni da kayi duk da na kasance bana ji , duk da na kasance ina janyo maka hasara , Amma duk da haka ka baka gaji dani ba , kayi haƙuri . Ni zan koma Nahiyarmu , asalin inda na fito ” , kanta ya dafa ya ce “ke kamar ƴa ce a gare ni ba sai kin min godiya ba ,Allah ya miki albarka “, “Ameen ” Hajiya Maryam da Bobbo suka amsa , yayinda Nahad ta ci gaba da magana “Abba da Umma ni ɗin nan da kaina ina gayyatarku zuwa wajen aurena da Nawa Ɓangaren , ɓangaren nan da nake yawan baki labari Umma , yau dai burina ya cika , zamu yi aure da shi jibi da misalin ƙarfe biyu da rabi na dare , 

“Daddare fa kika ce ? ” Hajiya Maryam ta faɗa cikin sigar tambaya . Nahad ta gaɗa kai tare da kallon Bobbo, gaɗa mata kai yayi yana murmushi , Alhaji Sulaiman ya ce “Allah ya kai mu , ni bari na wuce , zan yi meeting da ƴan majalisu ” , Hajiya Maryam ta ce “Allah ya tsare hanya ” , da ameen ya amsa , sannan ɗaya daga cikin sojajin ya buɗe mishi mota ya shige , motoci guda biyar kamar kullum suka fita .

Nahad ta ce “Umma zan je in nemo Naheela a yau ɗin nan ” , Hajiya Maryam ta kalli Bobbo ta ce “Ka kula min da Nahad ” . Nahad ta ce “Kar ki damu zan iya wannan ” , Hannun Bobbo ta riƙe tare da rufe idonta Shima yadda ta rufe ido haka yayi , suka ɓace a tare.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nawa Bangaren 22Nawa Bangaren 24 >>

5 thoughts on “Nawa Bangaren 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×