Skip to content
Part 22 of 25 in the Series Nawa Bangaren by Queen-Nasmah

His excellency ya numfasa tare da furzar da wani iska mai Matuƙar zafi ya ce “Hajiya Maryam Nayi Matuƙar mamakin jin haka , yau a duniyar nan da a ce wani ya ce min zaki aikata abu makamancin haka wallahi bazan yarda ba , kin fi duka matana addini da ilimi , kuma ga su nan gabansu na faɗa , amma kuma kin aikata babban kuskuren da a cikinsu babu wanda yayi ko da kaɗan ne na abun da kika yi ” , cikin kuka Hajiyar Maryam ta ce “Kayi haƙuri , wallahi ba halina ba ne , kuma ƙaddara ce ta riga fata , dan Allah kayi min afuwa daga cikin ni’imomin da Allah ya maka ” , Numfashi Alhaji Sulaiman ya sauke ya ce “Kul ! Maryam kar ki ma fara danganta hakan da ƙaddara , wannan tsabar son zuciya ne “, “Gaskiya Alhaji mu mun gaji da wannan zancen kawai kayi hukunci , tun ɗazu sai zirititi kuke yi ” Hajiya Mabaruka ta faɗa .

Murmushi ya ɗan yi ya ce “Mabaruka ke nake aure ko ke kike aurena ?”, Mabaruka ta ce “Kai ke aurena mana ” , Jinjina kai yayi ya ce “to wannan ba huruminki ba ne , kar ki sake tsoma baki ” , ai ko maganar His excellency ba ƙaramin baƙantawa Hajiya Mabaruka tayi ba , nan ta ƙara hakincewa sai wani cika take yi tana batsewa .

Alhaji Sulaiman ya ce “Ba halina ba ne saki , kuma ban taɓa ayyanawa a raina zan saki wata ba , har Abada Allah ina roƙonka da ka min tsari da furta kalmar saki ga matana , Hajiya Maryam bazan iya ce miki komai ba sai dai kawai in miki addu’a a matsayina na mijinki Allah ya shirya min ke , ya shiryar da duk wata mace mai irin kuskuren nan ” , “Ameen Your Excellency Allah ya ƙara maka girma ” Hajiya Fulani ta faɗa , murmushi ya mata ya ce “Fulani Allah ya miki albarka mace mai haƙuri da sanin ya kamata ” , Hajiya Mabaruka ta miƙe cikin tsananin ɓacin rai dan ba haka ta so ta ce “Mu da bamu da haƙuri a ce mu bi gari ” , girgiza kai yayi yana ƴar dariya ya ce “Allah ya shirya min ke , Allah ya bar ni tare da ku baki ɗaya ” , bata tanka shi ba ta wuce , sai Fulani ce ta amsa da “Ameen adalin Mijinmu “.

Hajiya Maryam da farinciki ya ƙara sata fashewa da kuka ta ce “Allah ya saka maka da gidan Aljanna , Allah ya haɗa mu baki ɗaya a aljanna ,na gode maka fiye da tuninka , Allah ya ɗaukaka ka ɗaukaka ta ban mamaki , Allah yasa kayi shugaban ƙasa a zaɓe na gaba , na gode Allah ya saka da alkhairi “, His excellency ya ce “Ameen Ya rabbi Amaryata , kowa ma zai iya tashi ya tafi , Allah ya maku albarka “, Nahad ta fara miƙewa ta ce “Kayi ma Ummata Halacci , kuma a yau ka rufa mata asiri , yadda kayi mata Allah ya maka babban alkhairi har abada”, Da ameen ya amsa ,kallon Hajiya Maryam Nahad tayi ta ce “Ana mini kiran gaggawa zan tafi sai na dawo” ɓat ta ɓace da ganinsu .

Kai tsaye Wuro barka ta dira inda tayi wani babban lulluɓi a unguwarsu Bobbo.

*****

Washe gari da safe su Mamma suka duƙufa zuwa gidan Malam Rabi’u . Wani ɗan ƙaramin gida ne a ido amma cikinshi babba ne sosai, mutane sai shige da fice suke yi a gidan kowa da matsalarshi , kasancewar Malam sanannen malami ne , daga garuruwa daban-daban ake zuwa neman magani , kuma alhamdulillahi ana dacewa . Yana zaune kan kujerarshi su Bobbo suka shigo . Wuri suka samu suka zauna kan Wata ƙatuwar tabarma , “Me kike yi tare da su ” ya tambaya , Mamma ta kalli Asama , Asama ta kalli Mamma , malam Rabi’u ya ce “da ta bayanku nake “, juyawa suka yi har su Baffa , banda Bobbo da yake jin wani matsanancin ciwon kai .

“Ina take ?” Mamma ta tambaya , “Gata nan tsaye bayan Sadauki ” Malam Rabi’u ya faɗa yana nuna saiti da inda Bobbo yake , sannan ya ce “Malama ki faɗa min me kika biyo su yi nan ” , Nahad ta ce “So nake a cike min ɓangarena ” ,Malam Rabi’u Ya ce “To zauna ayi magana “, Zama Tayi gefen Bobbo wanda shi yana ganinta kuma yana jinta kusa da shi.

Malam Rabi’u ya ce “A zahirin gaskiya Zan faɗa muku ɗanku ba halitta ba ne kamar ku.” , Baffa ya ce “Ban Fahimta ba . Me kake nufi “, Mamma kuwa tuni ta fara zarar ido , Malam Rabi’u ya ce “Ni ka san mutum ne da Allah ya ƙaddara da tarin Rauhanai haka yasa nake ganin abubuwa “, Mamma ta ce “Malam ni dai bana son sai an faɗa ,ɗana mutum ne kamar kowa ” , Baffa ya ce “ Ki mana shiru wallahi ,na lura duk lokacin da aka zo wurin nema ma Bobbo magani sai kin hana ” , Malam Rabi’u ya jinjina kai ya ce “Dole ta hana , yanzu dai ba wannan ba zan yi bincike ku bani minti biyar ” , idonshi ya rufe ya kira Aljani ya ce “Ka tabbatar min da maganar da nake ji , ka zagaya cikin ƴan daƙiƙu ka dawo min ina jira ” , wannan alhajin ya tashi . Bayan ɗaƙiƙa 30 ya dawo , bayanan daya samo ya zayyanawa Malam Rabi’u , sannan ya ɓace .

Malam Rabi’u ya ɗago ya kalli Su Baffa yana faɗin “Mahaifiyar Sadauki…

<< Nawa Bangaren 21Nawa Bangaren 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×