Skip to content
Part 12 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Nayanthara

Sarauniyar kudanci Nayanthara

Samun irin ki tabbas sai an tona

A kudanci ta tabbata ba ki da tsara

Ko a mafarki zaki na firgita ɓera 

Da ke ake yi har yau Nayanthara

Wa ke ta zomo ana batun su ɓauna

Ni ke na hango a sama babu tsara

Gwanar iya aiki ta wuce kyara 

Balo-balon so a zuci tuni kin hura 

Wuta ta bege a ruhuna kin kunna 

Ke ce maza ke shayi, ke suka zaɓa 

Tafiyar ma ta daban ce 

Salon ma na daban ne 

A dole in an gano ki a dare 

Sannu dai a hankali Nayanthara 

Maƙiyanta ku sai ku yi hattara 

Domin idan ko ta ɓara 

Gyaɗar cikin ku za ta ɓara 

Huta lafiya sarauniyar baje aiki

Ja gaba dai muje gandun aiki

Ga ta Vijay da ke akai Bigil

Kin wuce dai a kira ki da ɓingel

Tunda dai tuni an saka lalle. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 11Ba’indiya 13 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×