Skip to content
Part 30 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Haka Haj murjanatu ta dinga kokarin boye damuwa da takaicinta agame da komawar mujaheeda gidàn Taufiq domin bata son damuwar yarta ba Kuma ta son ta San abinda take kullawa acikin zuciyarta.

Dawowar Alh Mustapha labaran guda gaf da magriba ya Kara bakanta ran Haj murjanatu domin dai tasan dalilin dawowarsa don tana Jin lokacin da mujaheeda take yin waya da shi tana gaya masa batun komawarta bayan sallar magriba shine ya wani kunkumo ya janyo jiki ya dawo saboda tsabar ràshin aikin yi.

Hakan yasa kamar kullum ko kallon arziki ba tayi masa ba.

Mujaheeda ta Kara yin wanka ta kintsa cikin wata hadaddiyar doguwar riga me ruwan siminti sabuwa ce dal domin zamanta a gidan duk sabbin Kaya aka sayo mata Wanda har yau bata gama sa su ba.Rigar tayi matukar amsarta tayi kyau kwarai matuka idan Ka debe yar ramar da fuskarta tayi.

Ana ko idar da sallar magriba Taufiq yana shigo da motarsa cikin get din gidan Wanda da alama sallar magriba din ma a masallacin kusa da gidan yayi saboda tsabar kaguwa ya zo wajen mujaheeda domin dai ta ji ajikinsa ya fahimci Yana fa son mujaheeda ya Kuma Saba Zama da ita duk da zaman doya da manajan da suke yi to fa yayi matukar rashinta Yana bukatarta acikin rayuwarsa sosai yayi nadamar komai ya Kuma yarda da cewa duk me turo masa hotunan nan so ya ke ya raba shi da matarsa Wanda ayanzu ya katange duk wata Kofa da hakan zai Kara faruwa domin dai ayanzu ya riga ya tusama Kansa yarda da mujaheeda dari bisa dari domin duk Wanda zai bada shaidar kamalarta hakika ya yarda bayan shine domin dai shine mutum na farko da ya Fara sanin ta a matsayin ya mace .

Kai tsaye Taufiq ya shiga cikin gidan a falon kasa ya sami daya daga cikin kujerun falon ya zauna, bai dade da zaunawa ba Alh Mustapha labaran ya fito domin ya riga yasan da isowarsa kasancewar ya hango tsayuwar motarsa ta windon sama.

Yana shigowa Taufiq ya zamo kasa ya zauna Yana kokarin gaishe shi ya amsa bayan ya zauna akan kujerar Yana ce masa Ka tashi Ka zauna Kan kujera mana, ya girgiza Kai yace ” aah nan ma ya isa.”

Yana rufe bakinsa Haj murjanatu ta sakko daga sama fuskarta babu yabo ba fallasa mujaheeda na binta abaya babu komai ahannunta da alama ba zata tafi da komai gida ba duk abinda asaya mata bayan zuwanta gidan babu abinda ta dauka.

Cikin walwala mujaheeda ta zauna ganin Taufiq zube akasa yasa itama ta zauna akasa.hakan kuwa ya kara bakanta ran Haj murjanatu haka ta zauna rai abace Taufiq ya gaisheta daker ta amsa. Sannan Taufiq yace “Nazo Zan tafi da mujaheeda ne nagode Allah ya saka da alheri ina kuma neman afuwar duk abinda ya faru.”

Alh Mustapha labaran zaiyi magana kenan Haj murjanatu tayi karaf ta amshe maganar tace ” gata nan zata koma sai ka cigaba daga inda ka tsaya,bazance ka daina ba kayi ta yi.”

Alh Mustapha labaran yace “ya isa Haj don Allah ayi hakuri komai ya wuce Allah ya daidaita tsakaninsu ya kade duk wata fitina.” gaba dayansu suka ce Amin banda Haj murjanatu.

Àlh Mustapha labaran yace ” don Allah ku zauna lafiya ku hada kanku kada wata baraka ta kara fitowa atsakaninku” Taufiq yace “in sha Allah babu abinda zai kara shiga tsakaninmu sai alheri.”

Daga nan Alh Mustapha ya cigaba da yi musu nasiha amma har yayi ya gama Haj murjanatu ba tace uffan ba.ko da mujaheeda ma tayi Mata sallama a dole ta amsa tana kokarin boye bacin ranta.

Amma a lokacin da taga Taufiq yasa mujaheeda gaba sun tafi ji tayi kamar ta rushe da kuka saboda tsananin bakinciki.

Bayan tafiyarsu shima Àlh Mustapha labaran kakkabewa yayi ya haye sama saboda ya Lura da mugun kallon da Haj murjanatu take sakar masa yasan karshe abin ya dawo Kansa ta zazzage masa komai aka.

Jugum ta cigaba da zama afalon takaici na damunta lalle lokaci yayi da Taufiq zai fuskanci hukuncinta sosai take Kara Jin tsanarsa acikin zuciyarta.

A cikin mota kuwa hira sosai Taufiq da mujaheeda suke yi bayan Taufiq din ya bata hakuri ya Kuma cigaba da labarta Mata irin zaman ràshin dadin da yake yi agidan bayan babu ita. Hakanan take jindadin yadda Taufiq yake gaya Mata son da yake Mata da irin rashinta da yayi tabbatas ta fahimci abubuwa da dama da da bata fahimta ba a game da Taufiq, murmushi kawai take yi tana jinta acikin wata sabuwar duniyar da take son kasancewa ciki.

Isarsu gidan mujaheeda ta tadda an gyara komai ko’ina sai tashin kamshi yake yi matuka su kansu masu aikinta sun jidadin dawowarta domin sunyi rashinta agidan.duk wani nau’in abincin da mujaheeda take so sun dafa Mata an cika Kan daining dasu.

Haka Taufiq ya sata agaba har sai data ci abincin ta koshi duk da dai dama bata da yunwa atare da ita.

Awannan dare dai sun cire komai sun nunama junansu tsananin kauna tamkar daren farkonsu mujaheeda ta mallaki mijinta yadda take so, haka zalika soyayyar sa ta kara kama zuciyarta tana fatan zamansu ya cigaba a haka har karshen rayuwa ba tare da fada ko tashin hankali ba.

Washegari kuwa Taufiq da kansa ya dauki mujaheeda ya kaita gidansu domin ya gayá mata yadda mahaifinsa ya damu da ita.

Zuwansu gidan ta kara gamsuwa da irin son da surikinta yake mata don yadda ya nuna murna da jindadin sa afili domin rasa inda zai sata yayi gaba dayama afalonsa ta tare ita dai Haj saratu wannan kauna da fifiko da yake nuna ma mujaheeda abin ya Fara tuke Mata zuciya don bata ga dalilin da ita mahaifiyarta bata kaunar dansu Shi Kuma ya rasa abin kauna sai yarta abin ma har Yana son wuce gona da iri. Domin dai hatta furar da ake Dama masa ranar tare yasa a damo da mujaheeda haka ta Dama ta Kai musu.

Bata kara shiga sabgarsu ba har Taufiq yazo tafiya da ita suka tattara suka tafi.

*****

Tun bayan komawar Kabir Kano muhseena ta fuskanci ya canja saboda yadda yake nacin kiranta awaya ya rage, sai dai kullum sako na tafe hakan yasa ko muhseena tayi tunanin akwai matsala sai Kuma ta saki ranta ta dinga Jin da akwai matsala da sakon ma bazai dinga turowa ba.

Duk da taso taji yayi magana da iyayen nasa ko kuwa har ya koma Bai Sami yin maganar dasu ba domin dai tana cike da son Jin sakamakon amma nauyi da kunya sun hanata tambayar sa.

Tabangaren Kabir kuwa tun bayan komawarsa Kano damuwa ta kara masa yawa sosai yake son muhseena Amma ya rasa hanyar da zai bulloma mahaifansa nan da nan har ya rame baya iya maida hankali akan komai sai tunani Yana so. Muhseena Yana Jin tausayinta ba zai taba iya gaya Mata bazai aureta ba kamar yadda yake Jin mawuyacin abune ya iya rabuwa da ita.

Cikin ràshin karsashi ya shigo falon cikin sallama Haj Salma ta dago ta amsa tana kallonsa batun yau ba tana ganin damuwa da ràshin nutsuwa afuskar Kabir amma kwanakin nan abin yafi girmama, ” Anti an uni lafiya” Kabir ya fada Yana kokarin zaunawa akan daya daga cikin kujerun da suka cika falon, ta amsa ” lafiya Alhamdulillah, ba dai har Ka dawo daga kamfanin ba”. Ya gyada Kai Yana rufe fuskarsa da hannunsa yace ” Na dawo, bana jindadi ne yau”, ta Kura masa Ido tace ” Naga alama”. Daganan ta taso daga inda take ta dawo kujerar kusa dashi tana kallonsa cike da kulawa tace ‘ Ba ciwo kake ba, damuwa ce kawai ke damunka Kabir”,ya bude fuskarsa Yana kallonta Amma ya kasa cewa komai domin yasan gaskiya ta fada ba Kuma zai iya Musa Mata ba.

Ta cigaba da cewa ” Tun dawowarka daga Durmi nake ganin canji atare da Kai Ka rage walwala baka fara’a kamar da hatta abinci ina Lura wani lokacin yadda aka Kai maka haka ake dakkowa ba tare da Ka ci komai ba,shin meke damunka?”,yayi shuru Yana son ya tattara kalaman da zai gaya Mata, ta kasa hakuri ta cigaba da cewa ” ko kana ganin kusancinmu da babbar alakarmu bai Kai Ka gaya min damuwarka ba.”

Yayi saurin girgiza Kai yace “idan akwai wacce ta dace na gayama damuwa ai bayanki be anti sallama kefa a matsayin Uwa kike agareni ” ta gyara zamanta tace ” uhmmm ina jinka menene damuwarka meya tsayama arai yake kokarin hanaka walwala “.

Sannu a hankali Kabir ya gayama Haj Salma komai ya kara da cewa” Na rantse miki anti yarinyar nan na bukatar kulawa da tausayawa ina matukar Sonta ina jinta araina fiye da Tunaninki bata da wani farinciki arayuwa da ya wuce ni to Anti Salma ta yaya Zan iya cewa bazan aure ta ba bayan girma da kima da mahaifanta suke bani da Kuma ita da bata taba soyayya da ko wane namiji ba sai ni.”

Ya karasa magana tamkar me Shirin yin kuka Haj Salma ta shiga damuwa itama tace ” Duk naji Kabir amma kai Yanzu a tunaninka zaka iya auren yarinyar da ba’asan ubanta ba komai so da tausayin da kake Mata ” yayi saurin daga Kai yace ” Abinda nake son su Baba su fahimta Kenan Anti Zan iya auren muhseena acikin ko wane irin yanayi ko da ace itace ta aikata wannan lefin da kanta to soyayyata zata fanshi hakan balle ba ita ta aikata ba, katamaimaima bana Jin akwai Wanda yasan yadda akayi amma an dauki karan tsana an dorama muhseena idan Kuma har aka hana auren irinsu to ta yaya zaa Sami me aurensu ko kuwa haka zasu Kare rayuwa babu Mijin aure Kenan.”

Haj Salma ta jinjina Kai tace ” Amma fa abinda kamar wuya Kabir ,domin ko ni idan ya tabbata bata da uba bazan iya Goya maka bayan Ka aureta ba amma idan har Ka dage Zan iya yarda Amma ba haka raina ya so ba, balle iyaenmu masu azabar kafiya Anya Kabir ba zaka hakura da yarinyar nan ba.”

Yayi saurin girgiza Kai yace ” bazan iya ba anti ina Sonta idan na hakura da ita zanyi matukar cutuwa ” dai dai lokacin Àlh Musa ya shigo falon ya tsaya Yana kallonsu yace ” me akayi maka da zaka cutu Kabir” gaba dayansu suka dawo da kallonsu Kansa Haj Salma na kokarin yin magana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 29Nima Matarsa Ce 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×