Skip to content
Part 31 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Tace “yauwa Alh dama yakamata ace kana nan don kaji abinda ke faruwa”. Ya lalubi kujera ya zauna Yana kallon Kabir yace ,” meke faruwa Kabir”. Haj Salma tace ” ina fatan Ka Kula da yadda Kabir ya canja ya rame ya fita hayyacinsa”. Yadan numfasa yace ” Na Lura Kuma harna Kira Shi na tambaye Shi damuwarsa amma yace min babu abinda ke damunsa, Wanda na bishi da haka ne kawai saboda Bana son na takura masa yin abinda baiyi niyya ba , na dai yarda da cewa komai daran dadewa zai biyoni da damuwar sa.”

Kabir yayi kasa da kansa cike da damuwa ayayinda Haj Salma tace ” matsala gareshi Alh gagaruma’ daganan sannu ahankali ta Gama labarta masa komai ta kara da cewa ” to ni bansan abinda zance ba ” Alh Musa ya numfasa Yana kallon Kabir kamar daga sama Kabir yaji Alh Musa yace “Ka rabu da ita Ka nemi wata.”

Gaban Kabir yayi mummunan faduwa ya dago da sauri Yana kallonsa.

Sannan yace “kawu ina sonta matukar so ina tausayinta idan nace bazan aureta ba bansan halinda zata shiga ba.”

Alh Musa ya jinjina kai yace “Kabir idan har da gaske ne yarinyar nan bata da asali azahirin gaskiya sai dai kayi hakuri domin kasan halin mallam Hamza matukar ya kafe akan abu to baya janyewa balle Hafsatu da idan ta tsani abu babu me iya tankwara ta, bayan haka Kuma babu Wanda baya son yayi aure agidan mutunci Kuma wannan abin Kada Ka manta yaduwa yake yi Yana bin zuria, Kuma da kake maganar kana Jin tausayinta babu Wanda ya hanaka Ka taimaka Mata kayi Mata komai na kyautatawa amma banda aure.”

Kabir ya Kara tsunduma cikin tsananin tashin hankali yace ” kawu kune kadai karshen fatana idan Baka Goya min baya na Bana Jin Zan samu abinda nake fata domin nasan akwai kyakkyawar fahimta tsakaninka da Baba zai iya tsayawa ya saurareka kilama har ya yarda da abinda na zo da Shi.”

Alh Musa yace ” yanzu me kake nufi kenan” yace ” ina nufin Ka taimakeni kaje Ka yi magana da su Baba Ka fahimtar dasu irin son da nake ma muhseena da ràshin haramcin aurena da ita, kila zasu sakko su gane bata da wani laifi aduk rayuwar da ta shiga ciki.”

Alh Musa yace “ta yaya kake tsammanin zanje na fahimtar dasu bayan nima ban fahimta ba domin dai ni Kaina Bana goyon bayan Ka aureta don haka zaifi maka Ka hakura kabar wannan maganar Ka nemo wata Ka aura gasu nan da yawa sai wacce Ka zaba.”

Wani irin bakinciki ne ke Kara ratsa zuciyarsa Yana Jin wani abu nayi masa yawo acikin kirjinsa fahimtar da Haj Salma tayi ne na mugun yanayin daya fada yasa tayi saurin kallon Alh Musa tace” Amma Alh da an bi abin ahankali idan har Kabir ya dage ayi hakuri a Goya masa baya ya aureta” yayi Mata kallon tsaf yace” ya auri yar shege?, Ai abu daya ne zaisa na Goya masa baya shine idan har an bincika yarinyar ba cikin shege bace shine kawai Zan aminta da bukatarsa don haka da Kaina zanyi binciken nasabarta idan ya tabbata abinda ake jifanta dashi gaskiya ne to ya Zama dole kayi hakuri da ita.”

Haj Salma ta dubi Kabir Wanda gaba daya nema ma yake ya fita hayyacinsa tace ” to kaji Kabir kawunka zaiyi bincike Ka kwantar da hankalinka tare da adduar Allah yasa ba gaskiya bane abinda ake fade” ya kasa cewa uffan illa doddogarawa da yayi ya tashi ya fice Yana gauraye hanya inda yake tsammanin zai Sami sauki da goyon baya nan ma kofa a kulle take shin yaya zaiyi da ransa?

Bayan fitarsa Haj Salma ta dubi Àlh Musa tace ” Alh yaron nan fa yayi nisa , Yana son yarinyar nan sosai Baka ganin Hana Shi aurenta zai Zama matsala.”

Alh Musa yace “hakanan zai warware ya hakura amma ba zai yuwu ya aureta ba bana cikin wannan maganar, kullum ana adduar ya Sami Mata yayi aure sai Kuma yazo da wannan maganar mara dadi.” Ya Mike Yana cigaba da maganganunsa ya shige bangarensa yayin da Haj Salma ta buga tagumi duk abin baiyi Mata dadi ba Sam Sam bata son damuwar Kabir domin jinsa take tamkar Dan da ta Haifa a cikinta.

Muhseena dawowarta daga islamiyya kenan ta shiga gidan. Ande Dije na tsaye a tsakar gida tana aikin zazzagama Hajara fada cikin matukar fusata da bacin rai take cigaba da cewa ” har kina da bakin da zaki mun wa’azi ke ai yakamata ayima wa’azi da har yanzu kika kasa fahimtar da yarki cewar Umar ba ubanta bane a yaron banza da wofi kika Samo ta akan neman duniya kika je kikayi barin mutuncinki kika Samo ta” cikin hawayen takaici Hajara tace ” ni ban Samo ta a yawon banza ba ki daina jifana da wannan mummunar maganar” cikin daga murya tace “Da Aina kika samota idan baa yawon banza ba, gashi nan kin dorama da na wahala kullum Yana cikin wahalarki ke da yarki me ake da zuria irin taki don haka ni har abada bazan taba kallon muhseena da wata nasaba ba don babu abinda na hada da ita babu ruwan biri da gada,” cikin hawaye masu dumi Hajara tace ” yanzu duk tsawon rayuwar da mukayi tare ba zaki iya kallon muhseena amatsayin jikarki ba” tace ,” don me Zan kalleta amatsayin jikata bayan ba jikata ba ce babu abinda na hada da ita” cikin fushi Hajara tace ” Shi yasa Allah ya Hana ki Samun jikar.” Ande Dije ta Kara fusata tace ” in dai daga gareki Zan Sami jika to Bana bukata.”

Jikin muhseena na rawa komai ya tsaya Mata duhu take gani sosai zuciyarta tana matukar suya da karfi tace ” don Allah kuyi shuru kuyi hakuri Kada kusa zuciyata ta fashe.”

Agigice Hajara ta dubi inda muhseena take tsaye abinda take gani acikin idonta Shi ya tabbatar Mata da cewa ta ji duk irin maganganun da suke yi. 

A hankali ta ratso cikin tsakar gidan tana yima Ande Dije wani irin kallo tace cikin hawaye “Ande aiya rayuwar da mukayi tare ya ci ace ko yaya ne kin so ni ko da ace ina da lefi balle ace Bani da lefi Akan duk wani zargi da kuke ma mahaifiyata , haka zalika ina da tabbacin ko da ace ta wata hanyar aka same ni nayi Imani mahaifiyata ba a yawon banza ta Samo ni ba sai dai ta wani dalilin da ban, Amma don Allah na rokeki ki sassauta mana haka ki fita acikin rayuwar mu”. Tana Gama fadan haka ta juya tayi ma Hajara wani kyakkyawan kallo tayi wani bushasshen murmushi sannan ta wuce daki.

Ande Dije ta kasa cigaba da fadan maimakon haka ma itama dakinta ta shiga ta saki labule.

Hajara komai ya kwance Mata faduwar gabanta ta tsananta yau dai muhseena ta ji abinda take son sani daga bakinta ta yaya zatayi ta kauda wannan tunanin daga zuciyar muhseena.

Daker Hajara ta iya Ciba kafarta tamkar wacce bata da laka a jikinta ta shiga daki.

Zaune Akan katifa ta tadda Muhseena ta hada Kai da guiwa sosai sautin kukanta ke fita. Hajara ta dawo gefenta ta zauna tana kallonta tace ” don Allah Kada kisa damuwa aranki duk abinda kika ji ki barshi a matsayin arashi kada ki.?” Muhseena ta katseta cikin kuka tace “aah Inna Kiji tausayi na ki gaya min gaskiyar lamarin nan , domin yau itace rana ta farko da na yarda na Kuma gasgata cewa Baba bashi bane mahaifina saboda Ande ta Fadi haka agabanki amma bski Musa ba illama amsarki data Kara tabbatar da cewa abinda Ande ta fada gaskiya ne.”

Kukanta ya Karu tace ” meyasa ba zaki gaya min gaskiya ba bayan duniya ta sani ban Kuma tsira daga mugayen kalamansu ba ràshin gaya min gaskiyar Kuma baida duniya ta daina kallona da abinda ake fada ba to don meye yasa ba zaki iya gaya min gaskiya ba bayan nice duk duniya ya dace naji gaskiyar domin magana ce ta rayuwata da makomarta.”

Gaba daya Hajara ta Kara tsunduma cikin tashin hankali zuciyarta na gaya Mata Anya tayima muhseena adalci kuwa na kin sanar da ita gaskiyar labarinta, Anya kuwa lokaci Bai yi ba da zata gaya Mata gaskiyar komai ba.

Muhseena ta dago da idanunta shatkaf da hawaye tace ” Inna don Allah ki fitar Dani daga duhu ki fitar da ni daga fitinar tunani da bakinciki da ke damuna ki gaya min wacece ni daga bakinki ya kamata naji komai Kuma ina tabbatar Miki matukar kika gaya min gaskiyar to ina tare da ke.”

Hajara tasa hannu ta goge hawayenta tana kallonta tace ” muhseena babu abinda sanin gaskiyar zai Haddasa Miki da ya wuce Karin tashin hankali” tace ” tashin hankali tuntuni nake cikinsa idan Kuma kika gaya min gaskiyar to babu bakincikin da zanji Saima na Sami nutsuwa domin ni na yarda da kaddara.”

Asanyaye Hajara tace ” shikenan idan har kina da karfin halin Jin gaskiya to Zan gaya Miki komai ayau Zan gaya Miki duk abinda kike son sani.”

Muhseena ta numfasa tace ” A shirye nake Inna.”

“Kada ki sake wani abu ya fito daga bakinki agame da muhseena ” furucin mallam Umar ya datsema Hajara harshen yin magana, ya karasa magana ya na shigowa cikin dakin fuskarsa cike da damuwa da tashin hankali Yana kallon Hajara yace ” me yasa zaki karya alkawarin da kika yi min?” Cikin hawaye Hajara tace ” mallam Ka gafarceni, amma ina ganin kamar lokaci yayi da ya kamata muhseena tasan komai.”

Mallam Umar ya girgiza Kai yace ” wasu abubuwan zaifi kyau abarsu a boye yadda suke don haka babu wani amfanin gaya Mata wani abu.”

Cikin kuka me karfi muhseena tace ” don Allah Baba Ka Bari ta gaya min Allah ya Sani kuna cutar da ni da tunani na ina bukatar sanin wacece ni waye Kuma mahaifina?”

Ji yayi kamar an caka masa mashi a kahon zuciya yace ” yanzu muhseena Ashe har akwai wata rana da zaki tambayi waye mahaifinki bayan NI duk duniya kina da wani mahaifin da ya wuce ni ne?” Ta jinjina Kai tace ” Bani da wani mahaifi da ya wuce Kai Baba , Amma ina bukatar sanin asalina Ku Gaya min gaskiya na gaji da wannan bakar rayuwar me cike da kyama da ràshin sanin makomata.”

Da karfi mallam Umar yace ” nine mahaifinki ni na haifeki.”

Ande Dije ta dage labulen dakin tana kallonsu tace” Kaine mahaifinta aina,? Kaga Ku gayama yarinya gaskiya wannan abin bazai binnu ba har karshen rayuwa” tana Gama Kara watsama wutar fetur ta saki labule ta koma, ayayinda Mallam Umar ya ji kamar duk an zare masa lakar jikinsa furucin mahaifiyarsa ya Kara bata lamarin muhseena ta watsa musu idanunta tace ” gaskiya ta fada don haka Kuma gaskiyar nake son ji daga gare Ku” ta Kara kallonsu ta fada da karfi ” haka ya isa, shin wacece ni waye mahaifina?”

Gaba daya sun firgita da Jin yadda muhseena ta Fadi maganar cikin karaji da tsananin fusata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 30Nima Matarsa Ce 32 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×