Skip to content
Part 6 of 9 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

MISFORTUNE

Babu wanda ya kula da halinda yake ciki, sakamakon kacamewar da wurin yayi da hayaniya saboda albishir d’in da akayi.

Numfashinshi yaji ya na seizing tamkar zai tafi gaba’aya, yayinda yake tambayar kan shi ‘why Yaya Islaam?, of all people why him?’ A gefen Burhaan kam duk k’wak’warka ba ka isa ka gane halinda yake ciki ba, fuskar nan ce tashi ta yau da kullum blank and plain.

Babu ko d’igon emotion balle kayi tunanin ya amsa ko bai amsa ba, while a ran shi wani irin rad’ad’i da k’unci yake ji. Macen da yafi so da k’auna ita ce aka baiwa wanin sa? Wanin ma ba kowa ba but ElSadeeq his own blood to wai ma yaushe suka fara soyayya ne har suka amince da auren juna ba tare da sanin shi ba?  Kalaman Baban yake ji suna replaying a kunnuwan shi kamar yanzu yake fad’in su ” cikin ikon Allah da kuma yanda suka nuna so yarda da kuma amincewarsu da juna, an sanya auren Bakura da Ummu Suliemah…” A iya nan ya iya ji duk sauran bayanan bai iya jin su ba.

Ji yake kamar ya sanya ihu ko duka wurin zasu iya jin halinda yake ciki, but he can’t shi d’in mutum ne mai b’oye damuwar shi hakan ne ma yake cutan shi akan muradan shi. Ashe tun d’azu Abba ke magana amma ko d’aya bai ji ba Yaya Mutallib dake gefen shi ne ya d’anyi tapping d’in shi a kafad’a hakan yasa ya d’ago cikin k’ok’arin saita kan shi. Wani kallo Abban ya jefa mai yana mai cewa ” da fatan dai kaji maganar da aka fad’a saboda na tabbatar mun isa da kai kuma zaka zamto mai yin biyayya ga zab’in mu?”

Kai ya gyad’a yana cewa ” in shaa Allah Abba” Masha Allah ya furta yana mai duban Lele da kanta yake k’asa ta shiga wani duniya da bata tab’a expecting zai faru kusa ba? Shin Hajjah ce ta basu umarni ko kuma sune suka tsara bata da mai bata amsa. Amma kuma a k’asar ranta wani mugun tsoro ne ya mamayeta, ita da ya kamata tayi farin cikin cikar burinta. So take ta kalli gefenshi amma ta kasa jin yanda ya amsa tamkar bai da damuwa ko d’aya a ran shi tabbas ba da zuciya d’aya ya amsa ba jikinta ya bata hakan.

“Nadeefatou shin kin amince?, kar ki k’wari zuciyarki in kinada wanda kike so ki sanar ba za a miki dole ba.” Kafin ta bada amsa Abbu ya cab’e da cewa ” ai ba ta tata akeyi ba shi ne mai gidan kuma a gaban kowa ya amince so bin nata bai taso ba.” Jin zancen shi ne yasa shi kallon su cikin son d’ago mai suke nufi da kalamansu, Abba yace ” Aa Amb. ita ma tana da hak’k’i a cikin maganar tunda ita zata zauna da shi, shin kin amince?”

Cikin raunin murya cikin kanurinta mai sirki da larabci da turanci kad’an tace ” Abba ai bani da hurumin yin musu ga muradanku, ko ina da wani soyayya ta bata kai daraja da girman umarninku ba ni d’in abun ikon ku ce babu neman zab’i ko ra’ayina in shaa Allahu a kullum zaku sameni mai yin biyayya dai-dai iyawata.” Kowa ya yaba da yanda tayi maganar Abba har da shi mata albarka haka su Baba ma amma, banda shi da yaji tamkar ta yarfa masa wuta a zuciya.

Wata muguwar tsananta yaji a rai da ruhinshi sai yanzu ya gane inda suka dosa, kam bala’i a rasa wa za’a aura mai sai wannan abun? Wai shi me yayi musu ne da zasu hana shi wacce yake so fiye da komai wacce yake burin yin rayuwar auren shi ta din-din-din da ita a had’a shi da Nadeefah, yarinyar da duk duniya ba ma family ba bai tab’a jin akwai macen da ya tab’a tsana kamarta ba? Ya ma za’a yi ya zauna a inuwa d’aya da ita, me yasa ba a had’a ta da Farhaan ba ko kuma Safwaan da ya tabbaatar duk duniya ba wanda ya kai shi sonta sai shi.

Ai ko bata sab’uwa don auren nan abu ne da ba zai tab’a yiwuwa ba, ya tabbatar wannan aikin Hajjah ce wato duk kashedin da yayiwa yarinyar nan sai da ta sanarwa Hajjah gashi ta had’a kan ‘ya’yanta ta zartar da umarni saboda cikan burin jikar so ko? K’wata yayi ya na mai k’udurewa ran shi a yau ba sai gobe ba zai yi wa tufkar hanci don shi dai bai ga abunda zai sa shi aurenta ba, a bar shi da ciwon da zuciyarshi takeyi na rasa Suleim mana wannan ai shine ga mari ga tsinka jaka. Har aka gama meeting d’in ba zai d’aurar da abunda aka tattauna ba duk ElSadeeq ya na hankalce da shi, ko da aka fita don ai sallah a dawo cin abinci daga masallacin bai dawo ba gida yai wucewar shi da k’afa ko inda motar shi take bai kalla ba.

A wahalce ya k’arasa gidan ya na mai had’a hanya ba wai don hanyar tayi masa nisa ba, sai don yanda zuciyar shi take k’una da tururi da wani jiri da yake kwasan shi. Sai dai da yake jarumi ne ya daure haka ya fad’a gidan kamar an jeho shi, yanayin shi ya tsorata masu gadi dake wajen bai ko kallesu ba ya nufi part d’in su dake farkon gidan d’akin shi ya shiga ko takalmi bai iya cirewa ba ya cilla kan shi kan gado har ya na bigewa da board d’in amma ko a jikinshi farat d’aya zazzab’i ya kawo masa bahaguwar ziyara and before he knows it ya fara kakkarwa yana mai jin kamar zai bar duniya ne gabad’aya.

Ko da aka dawo daga sallah had’uwa akayi a dogon table dake wurin, inda maids suke ta aikin serving d’in su. Sai lokacin aka lura da rashin shi a wajen ko da Abba ya tambaya ElSadeeq ne yace ” kiran gaggawa ya same shi ne daga clinic.” Ok kawai yace aka cigaba da cin abincin cikeda natsuwa. Sanda aka kammala kuma k’asa aka koma kan carpets ana hiran zumunci, na wasshe gamo musamman wainda basu a garin da iyaye da yaran ba wariya sai sambarka. Basu suka rabu ba sai la’asar inda kowa ya nufi gida cike da murna da jin dad’i.

Juyi yake yi kawai yayinda hak’waran shi suke mugun had’ewa da juna, zai iya cewa bai tab’a jin zazzafan zazzab’i irin na yau ba. Ya na jin dawowarsu gidan amma ko motsi ya gaza yi daga inda yake, har kiran da Abba ya din ga masa ya gaza d’agawa don bai da k’arfin magana. Sallah yayi a zaune don bai iya tsayuwa, bud’e drawern shi yayi ya nemo PCM ya had’iya. Sai dai kamar an k’ara masa ciwon ne, a hanzarce ya janyo k’aramar wayar shi wata numb yayi dialing yana sawa a hands free.

Ringing biyu aka d’aga ” Man dem” haka aka furta daga d’ayan side d’in, bai amsa ba sai nishi da ya sake masa. A rikice ya kuma cewa ” Guy, what’s wrong ?”, cikin muryar shi da ta sake cushewa da takaici da kuma ciwo yace ” I’m sick!” Ai da sauri ya taso ya na cewa ” where are you right now?”. Home kawai ya iya cewa ya na kashe wayar.

Cikin abunda bai fi 30 mins ba akai knocking k’ofar, ya na ji ya kuma san Dr. Adnan ne ya iso and ya rufe k’ofar. Sai dai bai da k’arfin tashi daga inda yake, kiran shi yayi ya d’aga a wahalce ” ka daure ka bud’e min k’ofar please Buddy.” Ajiyar zuciya ya sauke sannan cikin dafa bango ya isa parlorn, bud’ewa yayi yana mai dafe kan shi. Da sauri Adnan ya rik’e shi ganin zai fad’i saboda jiri da yake gani, da taimakon shi suka koma bedroom d’in.

Cikeda son sanin ta inda zai fara yace ” Tun yaushe ne baka da lafiya?”, a k’asan mak’oshi yace ” today”. Kallon shi yayi da kyau jin yace yau amma yanda ya gan shi kamar wanda ya kai 2 weeks yana jinya, har masifaffun idanun shi sunyi ladab sun fad’a sosai. Cewa yayi ” Today?, what’s actually worrying you?”. Cikin ficewar hayyaci yace ” sun raba ni da ita Adnan!”

“Who?”, ya tambaya da mamaki amsa ya bashi da ” Suleim!” A mugun rikice ya kalleshi don ya san labarin mugun son da yake mata, duk duniya Adnan ne kawai yasan how mad he loves Suleim da kuma irin alwashin da yake sha na aurenta. A hankali yace ” how?, me ya faru?”, a hankali ya bud’e baki ya fara bashi labarin dukkan abunda ya faru a meeting d’in har yai leading d’in shi ga zazzab’i.

Shiru yayi ya zura mai idanu don bai san ta ina zai fara ba, nisawa yayi yace ” amma shi ElSadeeq d’in ya bai gaya maka he’s dating her ba? Ai kaga da tuntuni ka san mai kake ciki, ba ma wannan ba ka san how much nake maka magana about this procrastination da ka fad’a mata tun farko da hakan bai faru ba may be ma ka fara sonta kafin shi.”

A hankali yace ” ElSadeeq bai da laifi don he’s been trying to tell me about his love life sai in ta kaucewa cos I thought he’s dating one of that girl’s friends…..” Katse shi yayi da cewa ” and you will be stucked with her forever.”

Hararar shi yayi bai yi magana ba, murmushi yayi ya cigaba da magana ” yes,,,,,she’s your destiny and you have no choice than to accept it” bai ka ga bashi amsa ba yaji sharp pain na allurar da bai san yaushe ya had’ata ba a cinyan hannunshi.

“You need not to say anything Dr. I know ba ka sonta but ita ce zab’in da Allah yayi maka, gode masa ya kamata kayi” ya k’arashe yana discarding allurar a waste bin na d’akin. A take ya bashi amsa da ” Allah ya kyauta in amshe ta as wife, I don’t love her babu kuma wanda ya isa ya tilasta min zama da abunda bana so.”

Kallon mamaki ya bishi dashi jin yanda yayi maganar kamar wanda aka d’aurawa mugun abu, yarinya irin kalan da kowani namiji yake burin aure yake cewa Allah kyauta. Eh lallai kam Dr, Burhaan kam birkitaccen mutum ne na gaske lura da allurar da yayi ta fara aikinta ya sanya shi cewa ” ka dai bi komai a hankali Man-dem, gudun b’acin rana, now sleep zanyi gadinka har ka tashi”. Ya k’are da d’aukar wayan shi ya na zama a sofa shi ko Burhaan lumshe idanu yayi yana mai tafiya tunani, har ya cimma matsaya don haka da ita zai yi aiki don kamar yanda ya fad’i ba wanda ya isa. (Anya kuwa?).

Bacci mai nauyi ne ya sure shi bai farka ba sai after 7 lokacin har an idar da sallahr Magrib, a gaggauce ya mik’e Adnan baya d’akin bai bi ta kan shi ba ya fad’a toilet wanka yayo da alwala. Bai ko tsane gashin kan shi dake tsiyayan ruwa ba balle ya shafa mai jallabiya ya zura ya tada sallah, zama yayi a kan dadduma bayan da ya idar da sallahn azkarai yayi da adduan Allah ya sa abunda yake shiri ya tabbata. Yana zaune har aka kira isha a d’akin ya sake yi, cire jallabiyan yayi yai combing gashin kan shi tare da shafa masa tsadadden man shi sannan ya shafa lotion a jikinshi shiryawa yayi cikin army green shirt mai laushi na Armani da wandon shi 3quarter na camou soft crocs bak’ak’e ya sanya a k’afan shi turare ya fesa daga sama har k’asa fitowa yayi zuwa parlorn shi.

“Mazaaaaa!, har anji sauk’i zaa tafi tad’i kenan”, Adnan da shigowar shi kenan ya furta cikeda tsokana. Hararar shi yayi ya na cewa ” zaka wuce mu je ne ko a nan zaka kwana in yi tafiyata?”, juyawa yayi yana cewa ” in kwana in maka mene Kulthum tana can tana jirana.” Tab’e baki yayi bai ce uffan ba suka nufi mai part.

Da sallama a bakinsu suka shiga Umma dake shirya abinci a dining ne ta amsa musu, zama yayi a kujeran parlorn yana sauke numfashi. Shi ko Adnan wurin Umman ya nufa yana cewa ” ni fa Umma abincinki na dawowa wallahi, tun d’azu k’amshi yake cika min hanci”. Murmushi tayi tace ” ai ba had’a fad’a zai yi ba zauna barin kawo maka”, zama yayi a d’aya daga kujerun dining d’in inda ita kuma ta koma kitchen.

Serving d’in shi Alkubus da miyan ganye tayi sai Zobo mai sanyi kafin ta baro dining d’in. Kusa da Burhaan ta zauna hakan ya sanya shi bud’e idanu a hankali yace ” Barka da gida Umma” amsawa tayi da ” Yawwa Babana, lafiyan ka lau kuwa?” A hankali yace ” just headache amma na sha magani.”

“Allah ya sawwak’e, shi ma Safwaan ya na sama zazzab’i ya kwantar da shi sai da Adnan yayi masa allura ” ta furta concerned, shiru yayi a k’asan ran shi ya tabbatar ciwon bai da nasaba da k’ok’arin raba shi da Nadeefah da ake yi. Wanda in dai da ran shi ba zai tab’a barin ya faru ba, yanda shi aka tauye shi ba zai bari a tauye d’anuwanshi ba. Bud’e baki yayi da niyar ya bata amsa sai dai sakkowan da Safwaan yakeyi daga stairs ya hana shi magana, instead tashi yayi ya nufe shi.

Taimaka masa yayi har suka sauko, zaunar dashi yayi a couch yana gyara mai zama. A hankali yake jera masa sannu ba ko k’ak’kautawa ya na amsawa cikin sanyi kai kace ba Safwaan iyayen karad’i ba. A lokacin Adnan da ya kammala ya k’araso parlorn, sake duba shi yayi da kyau kana yace ” zamu je da Burhaan zai kawo drugs d’in shi, zuwa gobe in sha Allah zai warware.”

Godiya Umma tayi masa yana cewa ‘ haba Umma kamar wani bak’o?’, sallama yayi shikuma Burhaan yace bari yaje ya dawo. Aa motar Adnan suka fita a harabar hall d’in ya ajiye shi, shikuma ya d’auki motar shi. Sai da ya fara biyawa Yerwa pharmacy dake wajen estate d’in ya duba drugs d’in Safwaan kafin ya juyo. Instead ya shiga gidansu dake ‘ Tar Goni street’ sai ya nufi ‘ Garwa Zannah close’, kallon gidan yayi yana mai alwashin shiga gidan, ba zai tab’a shiga ba sai an soke maganar auren. Sai lokacin ya tuna da miss calls d’in ElSadeeq, zai kira shi bari ya koma gida.

Honk yayi a k’ofar gidan mai gadi ya bud’e ya shiga ciki, ko kallon side d’in da maigadin dake ta zubo masa kirari bai yi ba ya nufi ciki. Zaune ya iske ta a couch, news take kallo amma hannunta carbi ne tana ja. Washe baki tayi ta na cewa ” ho! D’an nema ka kasa hak’uri kenan sai ka biyota?”

Sake d’aure fuska yayi yace ” nda dubdo ” don wannan murmushin ba burge shi yayi ba, don ya san bai rasa nasaba da auren ‘yar gaban goshinta da aka k’ak’aba masa. Amsawa tayi itama tana saita fuskarta ganin zai kawo mata wargi a parlornta, daga amsawar kuma bata sake magana ba. Ganin tayi shiru ya sanya shi sauka gabanta cikin tausasa murya yace.

“Hajjah na san ke d’aya ce kike da ikon sawa ko hanawa a gidan nan, please ki saka baki a zaluncin da ake shirin yi min”. A mamakance ta kalleshi tana mai cewa ” waye yake shirin zaluntar taka, kuma da menene?”, sake tausasa harshe yayi yace ” auren yarinyar can Nadeefah, wallahi Hajjah bata dace dani ba and I don’t love her I’ve never do.”

“Ashe ba ka da kunya ba kada hankali Burhaan, a gabana zaka bud’e baki ka gaya min baka son jinina?, jinin ma ta d’aya daga mafi soyuwa a gareni?” Ta furta cikin ta’ajjubi. ” Hajjah that’s not what I meant…..” Katse shi tayi da cewa ” me kake nufi if not this eh Burhaan!!, mu zaka wulak’anta?, tarbiyyar da akayi maka kenan? Iyye?”

A yanzu kam ya fara loosing composure d’in shi, meye laifi a abunda ya fad’i. This is his life and his right and he’s so entitled to his right, ya na da ikon zab’ar wacce yake so a koina ne. Amma Hajjah tana shirin d’aura masa laifi saboda cikar muradan shegiyar can, wannan ai rashin adalci ne a doke ka a hanaka kuka me yasa Hajjah bata musu adalci ne ba tun yau take nuba musu tsagwaran bambanci da ita ba. Amma na yau ya tab’a shi don haka yace.

“Ni dai bana sonta ba kuma rashin kunya ba ne duk cikin wainda aka sa ma rana yau ai da son ransu a ka sa sai ni ne kawai da ba’a so, don kawai ki cikawa shalelenki buri?…..” A tsawace tace ” eh lallai ka isa Burhaan Ya Hajjan kake kalla cikin idanu kake gaya ma wainnnan maganganu?” Yamara dake fitowa daga d’akin Hajjah ta fad’i hakan.

Waigawa yayi bai san tana nan ba yace ” ba wani abu na fad’a ba Yamara gaskiya ce dai na fad’a, ba kuma rashin kunya nakeyi ba this is my life ba zan iya zama da yarinyar da ban so ba in kuma aka matsa toh duk abunda zai biyo baya ta kuka da kanta” juyawa yayi ya nufi k’ofa bai jin ko d’ar balle ya ga rashin kyautawar shi, he’s just blinded by hatred. When he said he hate her he means it with every fiber of his being.

A dai-dai k’ofar barin parlorn yayi kicib’us da Lele dake tsaye kasak’e kamar ruwa ya cinyeta. Ganinta a wurin ya sanya shi janyota suka dawo a gadarance yace ” I’ve told you in baki shaida musu ba ni zan fad’a and I’ll repeat it a koina cewa ‘ ban sonki and I’ll never do so ‘ so make your decision now ba sai gobe ba in kin ji kenan,,,,,,,Hajjah I’m sorry in na b’ata miki rai but that’s just the fact”. Daga haka yai wucewar shi zuwa waje motar shi ya figa a guje kamar zai bar duniyar.

Dukansu sun kasa motsi daga inda ya tafi ya barsu, basu tab’a sanin haka yake ba sai yau. “Ko dai ya fara shaye-shaye ne?”, Hajjah ta furta cikin ficewar hayyaci kamar dai figar maganar akayi daga bakinta. Yamara ta bata amsa da “ba wani shaye-shaye iskanci ne kawai kuma ba zamu zuba idanu ba a yau ba sai gobe za ayi wa tufkar hanci zai san waye ya isa tsakaninku, d’an iskan yaro ana mai kallon mai hankali,,,,,,ke kuma zaki tashi a wurin ko sai na sauke fushin a kanki?”

Cikeda sanyin jiki ta nufi d’akin Hajjah nan ta barsu Hajjahn ta na cewa ” wannan duk ba abun rikici bane Amsah, bacin rai ne in ya sauko zamu sasanta”. Kallonta tayi tace ” ba maganar share magana don in aka bar shi lamarin girma zai yi gwara ayiwa tufkar hanci, a daren nan ba sai an kwana ba zai gane ko iyayenshi ba sa sainsa da mu balle shi “. Daga haka ta nufi waje dama da shirinta ko ta kan musabbabin zamanta a wurin bata bi ba, gidanta tayiwa tsinke da alwashin a yau sai ya san shayi a ruwane.

Ganin fiffikan da Yamaran ta fitaa tana yi ne ya sanya tace “Allah ya kyauta ” tana nufa d’akin ta, a zaune taga Lelen ta zuba tagumi. Zama tayi gefenta a ranta ta na cewa ” k’alubale na farko” a baki kuma cewa tayi ” tagumi bai gan ki ba Lele addua zaki cigaba dayi “. Ajiyar zuciya ta sauke ta na cewa ” I’m sorry Hajjah, na tabbatar saboda ni Ya Islaam yai miki haka”.

Girgiza kai tayi tace ” ai ba abun bada hak’uri bane dukanku jikokina ne, kuma ba wanda yafi k’arfin kuskure sai dai ki sani ba abunda ya isa ya hana aurenki da shi sai dai in d’ayanku ne ya rasu don haka sai ki shirya zama da zab’in da kece kika yi wa kanki…….” Fasali ta ja ta na kallonta cikeda tausayawa ta cigaba ” don haka dole ki d’aura aniyar zama da shi and mind you zaman ba zama ne sauk’i ba amma in kika rik’e addua komai zai wuce sai kiga sai labari”

Tabbas zama da Burhaan ba zama ne da zai zo da sauk’i ba, amma ta tabbatar komai zai canja zai zo yana sonta fiye ma da yanda ita take son shi kamar yadda akan yi a novel. Murmushi ta sauke a ranta tana cewa ” ni ba kalar matar da namiji zai iya resisting bane, I’m pretty sure Ya Burhaan will love and accept me as his wife in shaa Allah ” don haka a fili tace ” in shaa Allahu Hajjah ta “.

Kallonta kawai tayi tare da cewa ” a nan zaki kwana ne ko zaki koma gidanku ne?. Girgiza kai tayi tana cewa ” a nan zan kwana I’ve missed you so much Hajjah ta “. Cewa tayi ” ke da zakiyi aurenki ki barni a tsohon gidan mijina”, a shagwab’e tace ” ai kullum zan na zuwa “. Kallon baki da hankali tayi mata ta na cewa ” eh tunda ga mara kai ba, toh kar in ji kar in gani “. Dariya ta sanya kawai amma ita har ranta da gaske takeyi in tayi aure kullum sai tazo gidan Hajjah babu kuma wanda zai hanata.

Zafi zuciyar sa take masa, a d’azu ta sauka amma yanzu it is becoming unbearable for him, ga nutsuwar shi da yayi k’aura daga jikin shi. Hakan yasa ya parker motar shi a dai-dai street d’in gidansu, kan shi ya kifa a sitiyari yana mai yin kukan zuci wanda yake jin tamkar ruwan dalma ake zuba masa a k’irji.

Ba zai ce ga adadin lokacin da ya d’auka a wajen ba , don sai da ya samu sauk’in abunda yake ji ya nufi gida. A sanyaye yayi parking, ya jima kafin ya fito daga motar jiri yake gani. Ya tabbatar harda yunwa a tare da shi amma bai da appetite ko kad’an, har zai yi part d’in shi ya tuna da drugs d’in Safwaan. Ciro su yayi ya nufi main house.

A hankali ya bud’e k’ofar da sallama a bakin shi, da wani azababben kyakkyawan mari aka amsa sallamar tashi bai san sanda magani hannunshi ya subuce ba. Turus yayi da hannu a kunci ya na mai kallon Abba dake tsaye a gaban shi fuskar nan a kinkine a tsawace yace.

“Ni zaka wulak’anta ka tozarta a tsakiyar ‘yanuwana?, ni zaka watsawa k’asa a ido ka nunawa duniya ban isa da kai ba?, Ashe kai mutumin banza ne ban sani ba?!” Wasu kalamai ne masu matukar zafi da rad’ad’i fiye ma da wanda yake ji a baya Nadeefah is a misfortune and bad luck to his life. Tunda yake Abba bai tab’a marin shi ba duk zafin da yake dashi kuwa sai yau yau d’in ma a kanta, hakaza kalaman shi bak’I ne a kunnuwan shi don basu tab’a wanzuwa ba balle har su samu matsuguni. Hakan nema ya sanya shi kasa ko motsi sai kallon Abban da yake yi.

“Kana kallona ko ni ma zaka mareni ne?, tunda har ka iya zuwa gaban mahaifiyata kai mata rashin kunya. Ana maka kallon mai hankali ashe hankalin naka a hannun riga yake shashasha mara sanin ciwon kai yarinya k’arama ta fika lissafi,,,,,,,to in ma kayi abunda kayi ne saboda a fasa aurenka to ina son ka sani aurenka babu fashi wallahi ko mutuwa zakayi kuwa kaji nace wallahi”.

Ya furta bai ko had’iye miyau balle jan fasali saboda tsantsar b’acin da ran shi yayi, bai bashi damar tankawa ba don baya buk’atar tankawar nashi ya cigaba ” don haka ka gaggauta cire wasu banzayen tunani a kan ka aurenka da Lele zanen k’addara ne babu kuma makuwa in shaa Allahu sai mun tabbatar da shi and tomorrow first thing in the morning kaje ka bawa Hajjah hak’uri……” Daga haka ya ture shi daga k’ofar yana fita daga parlorn bayan yace wa Umma dake tsaye a gaban staircase ” a kawo min black tea”

Kallon shi tayi ganin kamar a daskare yake ya sanya ta matso gabanshi, hannunshi ta janyo zuwa sofa ai ko ya bita a sakale. Zama tayi kusa dashi tana shafa gashinshi cikin rarrashi tace ” gata ake maka Babana wanda ba zaka san hakan ba sai a nan gaba, ban san aibun da take da shi da ka kasa karb’anta a matsayin wacce aka zab’a maka kayi rayuwa ba but tabbas nan gaba akwai randa zaka gode mana,,,,,,,,and I’m not happy with what you did today I won’t say I’m disappointed in you but I’ve never expect such thing from you don haka ya zama tilas kaje ka bawa Hajjah hak’uri kar kuma ka sake furtawa ko a gaban waye cewa baka son ta kaji?”

Bud’e idanun shi da suke kamar an watsa masa barkono yayi, cikin wata murya yace ” but Umma I don’t, wallahi ban tab’a son yarinyar nan ba and……” Katse shi tayi da ” shhhhhhh,,,,issokay give her love a try wata rana zaka fara sonta na tabbatar don ita d’in abar so ne ga kowa, you inclusive za kuma kace na gaya maka now, barin had’a muku tea ka samu ka sha you need to sleep and rest.”

Ba ta jira cewar shi ba ta wuce kitchen bayan ta tattara maganin da suka watse a k’asa. Hargitsa kan shi yayi cikin rashin mafita, there’s no fucking way he’ll love this girl abunda ya faru yau ma ya k’ara masa tsananta ne mai matuk’ar tsanani. Maganin ya d’auka yana hawa stairs don kaiwa Safwaan.

Duk maganganun da sukeyi yana jin su, hakan kuma ba k’aramin karya masa zuciya yayi ba. Yarinyar da yake mutuwar so ita ce wani yake cewa ya tsana?, yarinyar da yake kwana ya tashi da buri da fatan mallaka ce aka mallakawa wani yake zillewa har da cin alwashi a kanta?. A yau inda ba Yayanshi abun son shi bane da babu abunda zai hana shi yi masa dukan kawo wuk’a, don baida mak’iyi kamar mak’iyinta a wanga duniya amma kaico ba zai tab’a iya tab’a ko farcen Burhaan da sunan cin mutunci da tozarci ba. Hakan ne ma ya sanya hawaye mai zafi zubo masa, bai tare su ba barin su yayi suna zuba son ran su don tun d’azu yake neman d’auki da agajin su basu isoba sai yanzu.

Motsin shigowa ya sanya shi jan blanket ya rufe fuskar shi, tareda jan numfashi. Maganin kawai ya ajiye ya fita don ya tabbata idanunshi biyu bai son takura ne,and he knows what he’s going isn’t easy don he’s also going through it now and  shi ma bai son magana ko d’aya.

Sauk’a k’asa yayi ya tarda Umma har ta had’a tean ta ajiye masa da alamu ma ta wuce wajen mijinta, d’aukan wanda ta ajiye masa yayi da zafin shi ya kwakwad’e ya ajiye cup d’in ya wuce d’akin shi.

Deejasmah

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nisfu Deeniy 5Nisfu Deeniy 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×