Skip to content
Part 32 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Tun da yabar ɗakinta a yammacinnan bata ƙara ganinsa ba, har aka wayi gari. Ta leƙa tsakar gida ta windonta ya fi sau goma ko za ta ga giftawar Mukhtar, amma ko alamarsa bata gani ba.

Ranta ne ya ƙara ɓaci. Minti ɗaya biyu sai ta ɗaga hannu ta shafi lafaffen cikinta. Ita kaɗai take sakin murmushi akai-akai idan ta tuno tana ɗauke da cikin Haskenta.

A jiya da lamura suka ɗakko kwaɓe mata har suka ziyarci gidan Maman Murad zuciyarta cike take da nadama mai tarin yawa. Amma bayan tabbatuwar ciki a jikinta daga bakin da bazai mata ƙarya ba sai duk wani ɓurɓushin nadamar da ta fara yi ya kau. Ta san zama tsakaninta da Mukhtar a yanzu ba alfarma bace, dolen dole ne. Ga ta ɗauke da gudajin jininsa me zai sa shi sakinta? Ita fa ta riga ta san tun da Fareeda ta haifi ƴaƴa biyu wataƙila ita da ƴan uku za ta fara a gidan.

“Hehehehe! Shagali! Wa ka ganni da ƴaƴa uku rigis a gidannan? Hmmm! Na rantse da girman Allah Fareeda za ki gane shayi ruwa ne.”

Ta faɗa a fili tana dariya irinna bosawa.

Agogo ta kalla taga ƙarfe bakwai da kwata na safe. Tsam ta miƙe tsaye ta shige cikin ɗakinta, doguwar rigar barcin da yake jikinta ta cire, ta ɗauki wata ɓingilar riga da gajeren wando ta saka.

Ta ɗauki Hijabi iya gwuiwa ta saka. Gaban madubi ta ƙarasa ta ɗan goga powder a fuskarta ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin.

Ɗakin baƙi inda Mukhtar yayi ƙaura ta nufa, tafiyarta lafiyar Allah take yi a tsakar gidan.

Amma tana isa ƙofar ɗakin tasa hannuwa biyu ta dafe mararta, ta duƙe ƙasa kaɗan, ta takwarkwashe fuska sosai, tsawon minti ɗaya tana matse-matsen idanu daƙyar ta samu nasarar matso hawaye daga cikinsu. Nishi ta fara sas-saukewa sauri-sauri. Daƙyar tasa ƙafa ta tura ƙofar, ta faɗa cikin ɗakin a galabaice.

Bawan Allah Mukhtar yana kwance akan darduma a tsakar ɗakin. Ga Alƙur’ani da casbaha ajiye a gefe ɗaya, daga irin kwanciyar da yayi za’a gane irin barcin nan ne da ba’a shirya mishi ba ya samu nasarar ɗauke shi.

‘Wani abu da Mukhtar ya daɗe baiyi ba shi ne tashi a tsakiyar dare yayi sallah. Ko a can baya a mafiyawancin lokuta yana ji da zarar ƙarfe huɗu da rabi na dare yayi Fareeda za ta raba jikinta da nashi, ta shige bayi ta ɗauro alwala ta fara nafila, shi kam sai dai ya gyara kwanciya.

A daren jiya bayan shafe awoyi cikin tunani kyakkyawan alwala ya ɗauro ya fara jero nafilfili. Zuciyarsa cike da tunanin rahamar Ubangiji ga bayinsa. Shi Ubangiji mai gafara ne mai jin ƙai, duk yawan saɓon bawa sai dai in bai nemi gafara ba, abinda kawai ake so shi ne bawa yayi tuba cikakkiya da niyyar bazai ƙara komawa ga irin laifin da yake aikatawa ba.

Bayan cikakkun awoyi uku da suka shafe shi da Ibrahim suna tattake guri akan matsalolinsa. Ibrahim ɗin ya sake jaddada masa kacokan abubuwan da suke faruwa da shi a yanzu na rashin daɗi shi ke da kaso tamanin bisa ɗari na faruwar komai. Ya kuma jaddada masa matuƙar bai ɗauki hanyar gyara ba tabbas bai ga komai ba, ya shirya ganin taɓarɓarewar al’amura ninkin ba ninkin na yanzu da yake gani.

A matsalarshi da Fareeda baya da yanzu, shi ne ya taka muhimmiyar rawa gurin ɓata komai. A tsakaninsa da Fatima tun farkon fari ba haka ya kamata su faro tafiyar ba.

Da yake a shirye yake da karɓar gyara ta ko wane ɓangare. Bai kawo suka ko ƙoƙarin kare kansa ba, da hannu bibiyu ya karɓi laifukansa, sannan ya buɗe kunnuwa sosai yana karɓan shawarwari daga bakin Ibrahim da yake kallon mace a matsayin wata sassauƙar aba wajen tafiyarwa. Daga ƙarshe ya ƙarƙare da ce ma Mukhtar ɗin,

“Ban ce maka babu hatsabibai kuma shaiɗanun mata ba. Waɗanda idan bawa za ka zame musu wajen hidimtawa da tarairaya baza su taɓa yi maka da daɗi wajen zamantakewa ba. Akwai irinsu da yawa, waɗanda kamar ƙuli-ƙuli suke gurin rashin gane gabansu. Amma ni abinda na yarda da shi shi ne kaso tamanin cikin ɗari na matan da muke aure rashin fahimtarsu ke sa muke fuskantar matsala da su.”

Ya ɗauki aniyar gyara ta ɓangaren Fareeda da Fatima. Amma Fatima ta yi mishi laifukan da baya jin zai iya ƙyale ta taci bulus ba tare da ya ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki da zai sa ta gane lallai tayi ba daidai ba. Tsakani da Allah cikin da aka ce mishi tana ɗauke da shi ko kusa baiyi murna da samunshi ba. Da irin waɗannan halaye na Fatima ta ina mutum mai cikakken hankali zai so haɗa zuria da ita?_

To amma ya ya iya? Rabo ya rantse tsakaninshi da ita. RABON AYI aure ta samu ciki da shi Mukhtar yasa komai ya faru a baya. Lallai wannan shi ake ce ma ƙaddara ta riga fata. Tsakani da Allah ta gama sire masa a cikin zuciya, gaba ɗaya maa jikinsa ne yayi wani irin sanyi da al’amarin rayuwar duniyar. Yana tare da matarsa suna zaune lami lafiya ƙaddara da rashin jin magana irinta Fareeda da rashin haƙuri irin nashi suka ja mishi gora wajen ɗakko ma kanshi ƙajaga. Ko da ya idar da sallah a cikin addu’o’inshi sai da ya saka Fatima, babbar addu’arshi gare ta shi ne Allah ya shirye ta, Ubangiji ya cire mata ƙyashi, hassada, baƙin ciki, ƙarya, munafurci, rashin yin abu don Allah da duk wasu miyagun halaye da take da su. Matar da kuke shirin haɗa zuri’a da ita ko ɗan yaya ne dole ka dinga saka ta cikin addu’o’inka.

Fareeda kam bayan addu’ar Allah ya huci zuciyarta kan fushin da take yi da shi, ya daɗe yana addu’ar Allah ya kawar da shaiɗanin da yake tsakaninsu. Ubangiji ya ƙara musu danƙon ƙauna da soyayya, Allah ya raya musu zuria ya kuma sauketa lafiya. Ya ƙarƙare da roƙon Allah yasa yadda take uwargidanshi anan duniya ta zama uwargidansa a aljannah

Ga kanshi kuma sosai ya ɗauki tsawon awanni yana addu’ar Allah ya sassauta mishi zafin zuciya, kishi, rashin haƙurin da yake ɗawainiya da shi. Ya roƙi Allah ya yaye mishi duk wani hali nashi da yake taka rawa gurin samun matsaloli tsakaninsa da iyalansa. Bai samu nutsuwa ba sai da aka kira sallar assalatu. Ya sallaci raka’atanil fijr a gida sannan ya fice zuwa masallaci. Bayan an idar ne ya dawo gida yayi azkhar, ya cigaba da karatun Alƙur’ani. Jin barci na neman fin ƙarfinsa ne yasa shi ajiye Alƙur’ani da casbahan ya kishingide nan kan dadduma. Shi ne har Fatima ta shiga ɗakin bai sani ba.

Ganin yana barci yasa ta miƙe tsaye daga duƙewar da tayi, harara ta maka masa. A zuciyarta take ayyana yau fa cikon kwana ɗayan girkinta ne, amma maimakon su kwana suna rungumemeniya yana shafa cikinta shi ne ya wulaƙantar mata da kwanan ba tare da ta mori abinta ba.

“Ai wallahi baka ci bulus ba, za ka biya bashi in dai Fatima ce. A yanzu ne zan fito maka da asalin wacece ni tunda mun riga mun ƙarasa haɗewa. Yo me ya rage? Jinina da naka sun gauraya wajen samar da gudajin jinainai da za su zamo rayayyu nan gaba kaɗan ai dole in dama kunu na yadda nake so.”

Tayi maganar ƙasa-ƙasa ta yadda ita kaɗai take jin abinta, laɓɓanta da ke motsi ne kawai za su saka a fahimci maganar ciki take yi.

A ɗan fusace ta ɗauki Alƙur’ani da carbin ta ajiye gefe ɗaya, hijabin jikinta ta cire ta hurga kan katifa, ta ɗaga vest ɗin jikinta zuwa sama sosai sannan ta raɓa ta bayansa ta kwanta haɗe da ruƙunƙume shi tana aikin goga mishi ƙirjinta.

Nishi take yi a wahalce kamar wacce take cikin wani matsanancin ciwo. Idan ba sani aka yi bama yadda take goga mishi ƙirjin za’a zaci irin bugun ciwon nan ne take juye-juye ba tare da saninta ba.

Kamar a mafarki yake jin nishinta, da yake da riga a jikinsa bai farga da abinda take masa a bayansa ba sai daga baya. Ko da ya tabbatar ba mafarki yake yi ba a firgice ya buɗe idanunsa.

Da saurin gaske ya janye jikinsa daga nata ya miƙe zaune fuskarsa a tamke tamau.

“Miye kike yi haka? Me ya kawo ki nan?”

A maimakon ta amsa tambayoyinsa ko kuma ta faɗi wani abu daban kawai sai ta saka kuka. Tasa hannu biyu ta dafe saitin mararta ta cigaba da juyi tana hawaye da shessheƙa.

“Kin ga, idan baza kiyi magana ba salin-alin ki tashi ki fice min daga nan.”

Yayi maganar cikin dakiya da ɗaurewar fuska.

“Has…Aban twince cikina… marata…. bayana ciwo… zan mutu…. wallahi jiya kwana nayi banyi barci ba… har wasiyya na rubuta na aje maka a gefen gad…”

“Kina jin irin ciwukan da kika lissafa ne har kika samu damar rubuta wasiyya?”

Ya katseta da tambayar, a zuciyarsa yake girmama ƙwarewarta a wajen sharara ƙarya.

Ɗif tayi bata amsa ba, can kuma sai ta cigaba da jan shessheƙa.

“Tashi ki zauna.”

Ya bata umarni.

A sakalce ta miƙe ta zauna tana mutsutsuke idanu da tura baki. Har ta fara jan hanci za ta cigaba da kuka ya daka mata tsawa a dole ta haɗiye kukanta.

“Fatima? Wai ke wace irin macece? Yanzu don Allah bayan abinda ya faru jiya har kin samu ƙwarin gwuiwar da za ki iya fuskanta ta da wasu ƙarerayi naki?”

“To ba tun jiya Hajiya ta ce kayi haƙuri ba…”

“Banyi haƙurin ba. Ke saurareni kiji da kunnen basira.”

Ya miƙe tsaye daga ƙasa ya koma kan katifa ya zauna, har lokacin fuskarnan ba wasa.

“Ke bakiyi mamaki da duk irin abinda ya faru jiya me yasa ban sake ki ba?”

Wani irin rugurgujewa ƙirjinta yayi ya buga daram. A tsorace ta zaro idanu tana kallonsa, ta kasa cewa komai.

“Hmmm! Bari kiji, ni a tsarina ko? Duk rashin haƙuri irin nawa saki shi ne mataki na ƙarshe da zan bi da mace wajen ladaftarwa. Akwai matakai iri-iri da ya kamata abi kafin rabuwar aure, tunda dai ke mayya ce na kaiki gidanku kin ƙi zama, to ki cigaba da zama anan ɗin. Amma na rantse da Allah na ƙaurace miki kenan har zuwa sa’adda ni a karan kaina zan gamsu da gyaruwar halayenki. Bazan hana ki ci da sha, sutura, gurin kwana da nema miki lafiya ba, hakkinki ne tunda ban sake ki ba. Amma mu’amala da miji, kulawa, soyayya, tarairaya sai dai ki gani a maƙwafta. Idan kin so ki hankalta Fatima, idan baki so ba kar Allah yasa ki hankalta ki gyara halayenki. Abu ɗaya da zan tabbatar miki shi ne daga wannan matakin idan baki gyara ba za mu kai iyaka ne tsakanina da ke. Tashi ki fitar min a ɗaki, kuma daga yau duk abinda kike buƙata ki aika min saƙo ta waya ne, kar ki sake takowa cikin ɗakinnan, idan ba haka ba Wallahi zan shayar da ke mamaki mai girman gaske. Kuma ki saka a zuciyarki ni Mukhtar na jefa ki a cikin layin maƙaryata, daga yanzu har zuwa sadda zan gamsu kin gyara halaye ko baki gyara ba Allah ɗaya kawai za ki ce min in yarda dake. Tashi ki fita tun kafin ki hassalani.”

Haka ta miƙe jiki ba ƙwari za ta fita a ɗakin. Maganganunsa sun daki jikinta ba kaɗan ba.

“Haka za ki fita tsirara? Ko da yake je ki, daman akwai ƙarancin abinnan, fita a yadda kike so.”

A kasale ta juya ta ɗauki hijabinta da ke ajiye kusa da shi ta saka, ta fita a ɗakin ba tare da ko kallonsa ta sake yi ba. Tana tafe tana haɗa hanya har ta ƙarasa falonta, nan kan kujera ta zube tana hawaye, ta buɗe baki za ta kwarma ihu sai muryar Mukhtar ta ji a gefenta yana cewa.

“Duk da nasan ƙarya kika sharara min cewa kin kwana cikin ciwo. Ga dubu biyar nan ki tafi asibiti, na baki kuɗinnan ne kawai don kar Allah ya tuhumeni kin ce ba ki da lafiya ban kula da ke ba.”

Bai jira ta karɓi kuɗin ba ya ajiye a gefenta ya fice daga ɗakin yana jan tsaki ƙasa-ƙasa.

*****

Da matuƙar mamaki ta buɗe baki, sai kuma tayi dariya tana kallon Kamalu da ya kasa haɗa idanu da ita.

“Ɗan ƙanina, wai duka-duka yaushe maganar tayi ƙarfi ne har aka shirya maganar aure a gaggauce haka ban sani ba? Na zaci iyayen Jamilar sun ce sai tayi shekara uku a jami’a sannan za’ayi maganar aure?”

Wanda ta kira Kamalu dai ba baka sai kunne, ƙara sunkwui da kanshi ƙasa yayi cikin kunya yana murmushi.

“Fitsararre, ai dole kaji kunya mana tunda a gaban Fareeda ne. Wallahi a gidan in kika ga yadda ya tasa mu gaba da fitsara iri-iri za ki sha mamaki. Da fa Honey cewa yayi mu bari gobe lahadi mu shiga kasuwa haɗo lefen, amma da ya taso mu gaba da naci har da ƴar ƙwallarsa ai babu shiri muka fito a gatse-gatsen ranar nan. Allah yasa dai bamu takura miki ba Fareeda, duk mun sanki da sanin kyawawan kaya kalar ƴan birni shi yasa muka ce tsinke baza mu siya na lefennan ba sai kina gurin…”

“Au! Wai yanzu kina nufin kasuwa za mu shiga Aunty Kareema?”

“Eh mana babbar Yayata. Don Allah kar ki ce baza ki samu zuwa ba. Ya Mukhtar don Allah kasa baki, Wallahi tun da aka saka bikinnan kullum sai Jamcy ta jaddada min in tabbatar an zuba mata zaɓaɓɓun kayayyaki kuma masu tsada a cikin lefenta.”

Ya ƙarasa maganar yana kallon Mukhtar da Fareeda a marairaice.

Shi dai Ibrahim ɗan dariya kawai yayi yana kallon ƙanin nasa. Hmmm! Ta yaro kyau take ba ta ƙarko, bai san a cikin rayuwar auren kashi saba’in da biyar na zamantakewar haƙuri ne jagoranta ba.

Mukhtar a tausashe ya matsa kusa da Fareeda yana rarrashinta da tausasan kalamai kan ta daure su shiga kasuwar.

“Ba sai kun jigata kanku wajen gama haɗa kayayyakin ayau ba. Abinda baku siya ba gobe ku leƙa ku ƙaro, jibi haka, har dai ku gama siyan duk abinda ake buƙata.”

“Ni fa ban ce bazan je ba Abee. Tunani nake yi, da mu wahalar da kanmu wajen shiga kasuwa me zai hana Ya Ibrahim ya faɗi iya adadin kuɗin da yake so mu haɗa komai na lefennan, yanzunnan zan kira *Hds jawellerys and more* mu tura musu kuɗaɗen su haɗa mana duk abinda muke buƙata…”

“Hds jawellerys and more?* Su wanene kuma haka?”

Su ukun suka haɗa baki gurin tambayar Fareeda da mamaki a fuskokinsu.

“Hds jawelleries and more business name ɗinsu ne. Kawai abinda za mu yi yanzu shi ne za mu kira Sister Hadiza mace mai haba-haba da iya tarbar jama’a a fili da cikin waya kan lambarta 08144965394. A garin kano suke, adireshin babban shagonsu suna nan kan titin gwarzo unguwar kabuga bayan gidan man AYM SHAFA…”

“Haba Fareeda, duk shagunan da suke nan kaduna sai mun tsallaka kano?”

Kareema tayi maganar tana ɗan ɓata fuska.

“Ke kam Aunty Karima kin cika gajen haƙuri. Ki bari in kaiki mana. Kin tuna kayan da nasa da yamma nayi fitan bikin amaryar Abee da su? Har kina tambayata inda na siya lace da atamfar da sarƙa da ƴankunne haɗe da warwaraye masu kyau  na ce miki Aunty Binto ce tayi min siyayyar? To ai a gurinsu ta siya min. Muna daga nan za mu aika mata da kuɗi gobe zuwa jibi da sassafe saƙonninmu za su iske mu har nan kaduna.

Kuma ko rantsuwa nayi babu kaffara za kuyi mamakin irin haɗaɗɗun kayayyakin da za zuba mana a cikin akwatunan. Ke ni fa na huda ne naga jini, in kunji ana faɗin garanti trust kuma sayen na gari don mayar da kuɗi gida to kayan *Hds jawelleries and more ne*. Kuma ƙarin armashi shi ne idan da kanmu muke so mu zaɓa yanzunnan muna kiranta za ta antayo mana da hotunan sabbin yayi na kayyaki mu zaɓa mu darje.

Suna da group a whatsapp da suke tallata hajojinsu👉🏽

https://chat.whatsapp.com/LpxLzmsKFFfBatQoY8q1jA

Ke ko ruɗewa kikai wajen zaɓin kala da kin tura mata hoton kalar fatarki za ta zaɓa miki atamfa, ko lashi, ko material, ko shadda, ko abaya wanda zai shiga da ke sosai da sosai, duk inda kika shiga da suturan da kika siya gurinsu ayita kallonki ana tunanin ina kika sai wannan ɗanɗasheshen zanin…”

“Taɓɗijan! Ni kam na ga gurin zuwa haɗo lefen Sweet Jamcy my heart. Yaya Ibrahim kawai a kira Hds jawelleries and more su haɗa min lefen amaryata.”

Ango Kamal ya faɗa cikin karaɗin murna.

Nan dai dukkansu suka haɗu kan shawarar a kira Sister Hadiza  08144965394, sun san halin Fareeda ƙwarai. In dai ta yaba da abu, to tabbas wannan abu fa yayi ne ɗari bisa ɗari.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 31Rabon A Yi 33 >>

2 thoughts on “Rabon A Yi 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×