Skip to content
Part 5 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Ya bude zip din jakar shi ya rufe ya kai sau goma sha biyar ko fiye da hakan, da ba sabuwar jaka bace ba shi kan shi yasan zip din da ya samu matsala. Ba tunani yake ya manta wani abu ba, amman jakar tayi mishi kadan, abubuwan da yake son dauka sun girmi wajen da ya rage a cikin jakar. Daya daga cikin misalin abubuwan ya hada da Khalid da yake tsaye ya jingina bayan shi da bangon dakin.

“Har yanzun fushi kake mun Hamma? Jirgi zan hau, komai zai iya faruwa…”

Kallon da Khalid ya watsa mishi yana saka sauran maganar koma mishi, sai da ya hadiyi yawu kafin ya sake cewa,

“Idan kasan zakayi kewa ta har haka me yasa da Daddy yace mu tafi tare kaqi?”

Numfashi Khalid ya sauke, shi bai taba tunanin barin gida da sunan karatu ba, asalima banda jami’ar Bayero babu wani waje da yake sha’awar zuwa da sunan karatu. Shima fannin ilimin kimiyya da fasaha ya karanta, baiyi tunani mai tsayi ba da ya tashi neman gurbin karatu wajen cike bangaren magunguna wato Pharmacy a matsayin zabin shi na farko. Duk lokacin da zai ma Nawfal din zancen zabin makaranta sai yayi kokari wajen canza maganar kamar baya son amsawa.

Shisa ya kyale shi, a zaton shi Nawfal na daya daga cikin mutanen da sukan kasa tsaida hankalin su waje daya akan zaben makaranta ko kuma fannin da zasu karanta. Akwai su a ajin su, dan da yawa har suka siyi Jamb suna tararrabin abinda zasu cike, wasu suna da zabi fiye da biyu, wasu kuma basu da ra’ayin kansu ne sai abinda iyaye suka cusa musu tun tasowa. Ya san Nawfal baya daya daga ciki, banda shi baya tunanin wani ya taba tambayar shi abinda yake son zama ko inda yake son yin karatun shi.

Nawfal ya sani, shine mutum na karshe da zaiki goyon bayan shi akan duk wani zabi da zaiyi, in har zabin ba wanda zai cutar da shi bane ba. Zai karya idan yace jin zancen zabin Nawfal din daga wajen Julde bai mishi ciwo ba.

“Kasar waje Bajjo yake son tafiya, ko zaka duba makarantar kaga idan akwai abinda kake son karanta sai ku tafi tare, bana son ya tafi shi kadai.”

Shine abinda Julden ya fadi da Khalid bai ma bari ya karasa ba ya fara girgiza mishi kai.

“Daddy ni bana sha’awar zuwa ko ina, anan zan zauna. Shi Bajjon da ya zabi tafiya Allah ya taimaka, ba yaro bane ba, na tabbata zai iya kula da kan shi.”

Amsar da ya ba Julde kenan yana mikewa yabar wajen zuwa bangaren su. A ranar ko da Nawfal yabi bayan shi ya bude baki bai barshi ya furta komai ba.

“Kar mu fara maganar nan Nawfal, baka so in sani ba, Daddy bai san baka so in san tsarin da kayi wa rayuwar ka ba shisa ya fadamun, karka damu, in da akayi maganar nan na barta…”

Rubutun shi ya ci gaba da yi duk da a lokacin in zaka saka mishi wuka baisan me yake rubutawa ba, Nawfal ya dade a tsaye kafin ya fita daga dakin. Duk wani shirye-shiryen tafiyar Nawfal din da ake tayi baya saka baki a ciki. Kwanakin dai ne bai kula suna ta gudu tare da su a ciki ba sai yau da tun safe yake jin zazzabi ya rufe mishi jiki ganin Nawfal na ta hada jaka. Zazzabi ne mai hade da dana sani na satikan daya dauka yana fushin da ya ga rashin amfanin shi a yanzun.

“Ban ki fada maka ina son barin kasar ba dan bana son kasan plans dina Hamma, wallahi ba dan bana so ka sani bane ba…na kasa ne saboda zan dinga hango yau, bana son idan na kalle ka in dinga jin ba kasar nan kawai zan bari ba har da kai…”

Iska Nawfal ya furzar ta bakin shi da yake jin kamar idan yaja numfashi maimakon ya wuce inda ya kamata sai iskar ta dawo tana taruwa cikin bakin na shi, ga zufa da yake ji har a bayan kunnuwan shi da tafukan hannuwan sh.i

“Kuma kana fada, ba zakayi ni sa da gida ba, ko da sunan aiki ba zaka iya barin gida ba shisa kake mamakin yanda bi da Adee muka iya tafiya makarantar kwana, ban san ya zan fara fada maka batare da na roke ka mu tafi tare ba, Hamma ba zan so kaina da yawa ba, dan Allah kayi hakuri…”

Gyaran murya Khalid yayi dan bai yarda da kanshi yayi magana kai tsaye ba, yanda yaga zuciyar Nawfal shimfide a cikin idanuwan shi, ya kuma ganta a karye, idan ya nuna alamar rauni bai da tabbas kan abinda zai faru.

“Me yasa sai wata kasar? Wani garin bai isa ba?”

Dan daga kafadu Nawfal yayi.

“Kullum jina nake kamar tsuntsu, ina da fuka-fukai, amman ina tsare cikin keji tun haihuwata, nasan suna da wani amfani tunda an halliceni da su, amman babu sarari a kejin da nake balle in gwada miqe su har in san ya kamata in tashi…”

Sosai Nawfal yake kallon Khalid, kalaman shi yake zabe iya yanda zai iya, yana so koda kowa bai fahimce shi ba Khalid ya fahimta.

“Hamma ina numfashi kullum, amman bana jin yana kai mun inda nake so, idan ina tare da Daada nakan ji kokawar da nake da numfashi na ya danyi sauki, idan muna tare da kai ko Adee ma haka, ina bukatar in fita daga kejin da nake ciki ko zanji, banda tabbas amman ina ji a jikina barin kasar zai iya cike ramin da yake tare da ni.”

Wannan karin ta baki Khalid yake jan iska yana fitarwa ta hancin shi a hankali, ga idanuwan shi da yake kiftawa da sauri-sauri ko ruwan da yake jin ya taru a cikin su zai koma, babban dan yatsan shi ya kai yana goge gefen idan shi.

“Kamar wani abu ya fada mun a ido.”

Ya furta a hankali, muryar shi na fitowa a karye.

“Ka dauki duk abinda kake bukata kuwa?”

Kai Nawfal ya iya jinjina mishi.

“Sai karfe goma naji Daddy na cewa zamu tafi kaika airport.”

Kan dai Nawfal ya sake jinjina wa cikin alamar eh. Numfashi mai nauyin gaske Khalid yaja yana fitarwa.

“Bari in dawo.”

Ya furta yana juyawa ya fice daga dakin hadi da ja ma Nawfal din kofar. Dan dafe kai Nawfal yayi kafin ya sauke hannun nashi yana mayarwa kan tsintsiyar hannun shi dan ya murza agogon shi, ya riga da ya saba in dai tunani yayi mishi yawa idan yaja iska ya cika bakin shi, to zai fitar da ita ne bayan ya dora hannun shi kan agogon ya dan murza shi, shisa baya daure shi gam gam, lokutta da yawa da shi yake alwala, har wanka ma. Sai ya manta cewa yana hannun shi. Duk agogunan shi haka zaka ga basa aiki, sai da Julde ya bashi wani fari, da alama mai tsada ne.

“Ruwa baya lalata shi, ga ka da agogo a hannu, sai an tambaye ka lokaci kace ba yayi, yan gayun zamani.”

Dariya yayi yana mika ma Julde hannun shi maimakon ya karbi agogon kamar yanda ya miko mishi, da kan shi kuwa Julde ya zagaya agogon yana daura ma Nawfal din. Tun lokacin zai kirga ranakun daya cire agogon daga hannun shi sai jiya da yaje yi wa Daada sallama, dan suna gaisawa yace,

“Dan Allah Daada banda kuka, in kikayi kuka zaki sa inji kamar na tafi kenan, bayan da anyi hutu In shaa Allah zan dawo.”

Yana kuwa ganin yanda take ta kokawa da hawayen ta har ta raka shi bakin kofa, inda kamar fitar su Madina take jira ta karyo kwana jikin ta sanye da uniform din islamiyya. Hango sun da tayi yasa ta taho da gudu.

“Na hanaki wannan gudun Madina, amman ba zaki daina ba.”

Daada ta fadi cikin fada, muryarta dauke da kulawa, dariya Madina tayi, dimples din da suke a kuncinta duka biyun suna bayyana, da murmushin ta kalli Nawfal da yayi dariya mai dan siririn sauti, babu yanda za’ayi Madina tayi murmushi a gabanka baka iya mayar mata ba, ko da kuwa baka santa ba. Da take yar karama tayi haske, amman yanzun a hankali asalin kalarta take fitowa tana nuna alamar cewa ita sam bata dauko hasken fatar da su duka suke dashi ba. Ita ce mutum ta biyu daya sani da take murmushi da duka hakoranta a waje, idanuwanta ba su cika girma ba, idan tayi murmushi sai su kankance, kusan ma baka ganin su gabaki daya.

Yanayin fuskarta idan tayi murmushi shine zai sa fara’a ta kwace maka batare da kama sani ba, sai dai ya dauka kankanta a zuri’ar su zata tsaya ne akan Adee, sai ga Madina kuma yanzun da take son ce musu da duk sun adana tsokanar da suke wa Adee sun jira sun ga yanda nata girman zai kasance in yaso sai su kamanta idan ita kadai zasu tattara wa tsokanar ko kuma zasu rabata ne tsakanin ta da Adee.

“Hamma…”

Ta kira kafin lokaci daya murmushin da yake fuskar ta ya bace, baki ta turo.

“Da tafiya zakayi ba zaka jira in dawo ba?”

Daada ta kalla

“Ko anan zai kwana?”

Kai Daada ta girgiza mata.

“Sallama yazo mana daman, gobe zai tafi makaranta.”

Kallon shi Madina tayi.

“Baka ce ka gama ba?”

Dan murmushi yayi yana mata bayani cikin yanayin da yake tunanin zata fahimta a shekarun ta, yayi mamakin ganin yanda take kallon shi idanuwanta cike da hawaye, wani abu ya taso yayi mishi tsaye a kirji ganin hawayen ta ido daya ya fara zubowa kafin dayan, yanda zubowar su ta budema yan uwan su hanya, muryar ta dauke da wani yanayi da ya kasa barin kunnuwan shi tace,

“Ba zaka dawo ba ko? Shisa baka fada mun ba? Saboda ba zaka dawo ba?”

Kai yake girgiza mata ya juya wajen Daada dan ta taimaka mishi, amman sai yaga tabar wajen da sauri, hakan yasa shi karasawa yana riko hannun Madina da ta fisge ya sake riko shi da sauri, yana ganin yanda take kokarin sake kwacewa.

“Waye yace ba zan dawo ba? Makaranta fa, ko wadda na gama baki ga ina dawowa ba?”

Kafada ta makale.

“Zaka bar kasar, jirgi fa zaka hau, ba dawowa zakayi ba ni na sani.”

Ta karasa tana fashewa da kuka me sauti, baisan yanda zai fara lallashin ta ba, janta yayi yana hadata da jikin shi.

“Wallahi zan dawo Madina, kinji na rantse ai.”

Shesshekar kukanta duk da babu sauti yana ji ta yanda jikinta ke amsawa, dagota yayi yana rike fuskarta, amman hawayen da takeyi ya hana ta tsaya ta kalle shi.

“Ki kalleni mana, Madina, na taba miki karya? Zan dawo, me yasa ba zan dawo ba? Wa nake da shi acan din? Dole zan dawo…kina jina, zan dawo.”

Duk da ta saka idanuwan ta cikin nashi yana kallon rashin yarda a cikin su, fuskarta ya saki yana kai hannu ya kwance agogon da yake daure da shi ya kama hannunta ya saka a ciki.

“Ga agogo na ki ajiye mun, idan na dawo zan amsa…”

Ganin ta dumtse agogon yasa shi saurin dorawa da.

“Mai tsada ne, Daddy ya bani, ki adana mun kar komai ya same shi, idan ya fashe cikin kudin kunshin ki na wajen Daada za’a biyani.”

Dan murmushi tayi da yasa shi sauke ajiyar zuciya, hannuwa yasa yana goge mata fuskarta.

“Kin girma ba zaki daina kukan nan ba…”

Hannuwan shi ta ture.

“Da ka tafi baka yi mun sallama ba ko Hamma…”

Dariya yayi.

“Kashe di ne haka Madina? Ni ake ba kashe di yau?”

Wannan karin tare sukayi dariya. Da nauyin zuciya yabar gidan Daada, amman kamar yanda ya fadawa Madina ne, bashi da wani dalili na zama inda zai tafi, bashi da kowa a can, duk wani da yake da kusanci da zuciyar shi yana nan inda zai bari. Jakar shi ya sake budewa yana zira hannu a cikin aljihun da yake daga can gefe ya laluba yana zaro agogon da Adee ta bashi, ita kalar bula ne ta siya, makaranta ma ya same ta dan yayi mata sallama.

“Na rasa me zan siya fa, tunda watan nan ya kama nake tunani, kaga inda karshen tunani na ya kaini.”

Karba yayi yana dariya.

“Kinsan ba sai kin sai mun komai ba.”

Harar shi tayi.

“Kanina zai bar kasar ace ba abinda na bashi.”

Sosai ta bashi dariya, idan wani ya hango su a inda suke zaune zai iya dauka saurayin ta ne.

“Kina da son girma Adee.”

Kallon shi take yi.

“Kasan har goya ka nayi ko?”

Da murmushi a fuskar Nawfal yace,

“Ko da can Adee kafafuwan ki sunyi gajarta su iya dauka ta.”

Duka ta kai mishi a kafada yana rike wajen.

“Ouchh… Hannun ki yayi kankanta ace yana da zafi haka.”

Wani dukan ta sake kai mishi.

“Adee… Da zafi fa…”

Ganin ta daga hannu yasa shi mikewa tsaye yana murza inda ta daka, ganin yanda take harar shi yasa shi yin dariya.

“Yi hakuri babbar Yayaa.”

Itama dariyar tayi ya koma yana zama.

“Sai ka cire agogon Daddy kasa nawa.”

Noqe kafada yayi.

“Me yasa? Zan ajiye naki dai in ta kallo, amman agogon Daddy ai ba zai ciru ba kema kin sani.”

Kai Adee ta jinjina.

“Laifina ne dana bata baki na, bani agogo na tunda ba zaka sa ba.”

Ta karasa tana kama hannun shi daya janye yana saka agogon a aljihu. Da gaske yake a lokacin zai ajiye ne ya dinga daukowa lokaci zuwa lokaci amman ba yanda za’ayi ya cire agogon da Daddy ya daura mishi da hannun shi, bai taba dauka akwai dalilin da zaisa ya cire agogon nan ba sai jiya da Madina ta hargitsa mishi duk wani lissafi da yake tunanin yana tare da shi. Agogon da Adee ta bashi ya daura yana ganin yanda ya amshi farar fatar shi.

*****

“Malam sake jakar nan.”

Salim ya furta kamar zai kai mishi duka yana fisge jakar daga hannun shi ya wuce, bin shi da kallo kawai Nawfal yayi, bai ma yi tsammanin yana falon a zaune sai da ya fito daga daki, ba dan tafiya zaiyi ba sam ba zai ko kalli inda Salim din yake ba

“Hamma na tafi.”

Shine abinda ya furta, sai da ya dan tsorata da yaga Salim din ya mike, yaga duk yanda ake kiran shi dogo sai da ya daga kan shi sannan ya iya ganin fuskar Salim din daya miko hannu da nufin karbar jakar da take hannunshi, shi kuma ya girgiza mishi kai.

“Ba zaka taho ba?”

Salim ya fadi daga bakin kofa yana saka Nawfal din bin bayan shi da sauri. Duk da haka takun Salim daya shine kusan na shi guda uku saboda kafafuwan Salim din, yanzun da Nawfal ya ke bayan shi sai da murmushi ya kwace mishi, randa Khalid yace,

“Bajjo kaga kafafuwan Hamma? Ban san me yasa ya ke karantar aikin likitanci ba, kaddarar shi na ga aikin nepa, ba sai ya taka komai zai dinga yanke wayoyi ba.”

Dariyar da ta sake kwacewa Nawfal din mai sauti ce dan har sai da Salim ya juyo, sai yayi saurin boye dariyar da yin tari har sau biyu. Duk da haka murmushi bai bace mishi ba har suka karasa wajen motar Daddy da Salim ya zagaya ya bude gidan gaba yana zama da jakar Nawfal din a hannun shi. A bakin motar Nawfal ya tsaya yana dube-dube, ta inda Khalid zai bullo yake nema, da ya kalli hanyar bangaren Saratu sai zuciyar shi ta rage gudun da takeyi a kirjin shi. Kwakwalwar shi ta fara ce mishi ya bude mota ya shiga, amman zuciyar shi sai ta kasa, kamar na umarni tayi wa kafafuwan shi da su fara takawa zuwa bangaren.

Wata murya cikin kan shi tana fada mishi.

“Saboda Khalid da Adee, ko ba dan kowa ba dan su biyun.”

Da ya shiga ma ya ganta zaune a falo, bayan yayi mata sallamar da ta bishi da kallon “Lafiya? Me ya faru?” a maimakon ta amsa abinda yake fadawa kan shi kenan, saboda Khalid da Adee.

“Nanna zan tafi…”

Ya furta a hankali, kallon shi takeyi zuciyar ta na kara tafasa fiye da yanda takeyi kafin ya shigo. Yau kwana na takwas kenan da Julde baya mata magana saboda shi. Akan tayi magana kan tafiyar shi kasar waje.

“Duka cikin yaranka babu wanda kayi tunanin turawa karatu wata kasar? Sai shi? Komai na rayuwar ka akan Nawfal zai kare ne Julde?”

Kai ya daga mata, a karo na farko yana dorawa da

“Akan shi zan kare Saratu, me zai faru? Nace akan Nawfal rayuwata zata kare idan kina da matsala da hakan kofar gida a bude take zaki iya kama gaban ki, ban taba rike ki ba, ban taba hanaki ba, saboda Daada ne ban taba ce miki ki tafi ba, wallahi zaki saukake mun abubuwa da yawa idan kika tafi da kanki.”

Maganganun shi sun mata zafi.

“Nawfal ya fini kenan?”

Wani irin kallo yake mata

“Da hada kanki kike yi da shi? Ban taba fada miki ya fiki ba? Duk tsayin zaman shi a gidan nan ban taba ce miki ya fiki ba daman?”

Wasu hawaye masu zafin gaske ne suka zubo mata, tsaki kawai Julde yaja ya fita ya barta a tsaye. Maganar duniya babu kalar wadda bata yi mishi ba a kwanakin nan, in da take ma baya kallo. A cikin kwanakin wata irin tsanar Nawfal take ji fiye da wadda take mishi a da.

“Kar ka dawo… Dan Allah idan ka tafi kar ka dawo.”

Ta furta tana saka shi tsayar da idanuwan shi a kan ta. Tsanar shi yake gani karara a fuskarta, bai zaci zuciyar shi zatayi mishi zafin da takeyi yanzun ba. Saboda bai taba tsamannin wani abu daga wajen ta ba, ya san ta tsane shi daga ranar farko da kafafuwan shi suka taka cikin gidan ta.

“Me yasa?”

Ya tambaya yau a karo na farko yana saka idanuwan shi cikin nata.

“Me yasa Nanna? Me nayi miki haka? Me yasa kika tsane ni?”

Tabe baki tayi jin yanda muryar shi ta karye a karshen tambayar kamar shi dinne wanda aka yiwa wani abu, kamar zuwan shi bai kara mata matsaloli ba, kamar ita din bai kamata a tausaya mata ba saboda duka laifin nata ne.

“Matsala ka kara mun Nawfal, zuwan ka matsala ya kara mun, shisa bana so ka dawo. In ka tafi karka dawo.”

Iskar dai yaja yana cika baki da ita kafin ya fito da ita a hankali, kirjin shi na kara daukar dumi, juyawa yayi yana cin karo da Salim da ya rike mishi kafadu dam, da yake bai tsammaci zaiyi karo da wani abu ba, da Salim din bai rike shi ba baya zaiyi ya fadi, gefe Salim ya janye shi batare da yace komai ba ya nufi hanyar kitchen, shi kuma Nawfal yana ficewa. Tsaye yayi bakin kofa ya sa hannu ya dafe kirjin shi da yake zafi, anan Salim ya fito rike da robar ruwa.

“Muna ta jiran ka.”

Ya fadi yana wucewa, bin bayan shi Nawfal din yayi har wajen mota. Sai da ya bude baya ya shiga sannan ya ga Khalid a ciki. Zama yayi yana jan kofar ya rufe. Ba zaice ga abinda Daddy yake fada ba dan hankalin shi yayi wani wajen, hannun Khalid da yaji kamar yana saka mishi wani abu a cikin na shi ne ya saka shi kallon hannun na shi yana dago abinda yake ganin kamar wata silver, dubawa yayi, abin hannu ne da ake kira da bracelet a turance, tsuntsu ne ya bude fuffuke a tsakiyar abin hannun, Khalid ya kalla da yaki yarda su hada idanuwa.

“Ya zama mukullin kejin ka…”

Khalid ya fadi cikin sanyin murya

“Fly Bajjo, iya inda zaka iya.”

Kai kawai Nawfal ya jinjina mishi, su duka babu wanda ya sake cewa komai har suka isa Airport din, ba zama sukayi ba tunda jirgin karfe sha daya na dare zai tashi.

“Kana sauka saika samu ka kira ni, ka dai rubuta lambar wayar ko?”

Cewar Julde da alamu suka nuna baya cikin wata nutsuwa mai yawa, dan murmushin karfin hali Nawfal yayi.

“Na haddace fa Daddy, zan kira dana sauka.”

Kai Julde ya jinjina, Nawfal din yana mikawa Khalid hannu, shima hannun ya mika mishi yana jan shi bayan ya rike suka rungume juna, Salim da yake tsaye ya dakuna fuskar shi yana furta.

“Ewww”

Sakin juna sukayi suna dariya, Nawfal ya juya ya kalli Salim din da yake ta bata fuska har lokacin.

“Marin ka zanyi sai ka ga taurari.”

Dariya Nawfal yayi.

“A gaban nawa zaka marar mun yaro?”

Daddy ya fadi yana murmushi.

“Allah ya tsare mana kai Bajjo, dan Allah ka kula da kyau kaji ko?”

Julden ya nanata mishi ya kula idan wani yaji saiya dauka yaron goye ne shi din. Kai kawai ya jinjina yana kallon Khalid da yake bin shi da ido .

“Zan kira ku.”

Ya furta su duka suna daga mishi kai, kafadar shi yaji Salim ya dafa yana dan tura shi, hakan na sawa ya juya suka dan taka, kafadar shi Salim ya saki yana kamo hannun shi ya saka mishi jakar shi da yake rike da ita a ciki yana hadiye yawu, sosai yake kallon Nawfal din.

“Abin da Nanna ta fada…”

Yace yana saka Nawfal ware mishi idanuwa dan ko kadan Salim din bai nuna alamar yaji zantukan da sukayi da Saratu ba.

“Kar ka saka su a zuciyar ka, idan nace maka bata nufin abinda ta fada karya zanyi, ka san karya zanyi Bajjo…”

Kai Nawfal yake dagawa.

“Nanna ta fada maka maganganu da yawa, baka saka su a ranka ba, wannan ma ka watsar. Dalilin ta na ce maka karka dawo nata ne ita ka dai, karka watsar da kowa saboda ita.”

Kokari yake kar yayi kuka tun safiyar yau, ya dauka Khalid ne zai saka shi kuka, hakan bai faru ba. Maganganun Salim ne suke karya mishi zuciya, saboda Salim ba mai yawan magana bane ba, asalima Salim baya shiga rayuwar kowa a gidan shisa bai taba tunanin ya damu da ko Khalid ba balle shi, balle ya kula da wani abu daya danganci rayuwar shi.

“Ka yi abinda zaka yi ka dawo, idan zaka zauna ka tabbata ba saboda abinda Nanna ta fada bane ba, saboda kana da naka dalilin ne… Khalid da Adee zasu so ka dawo, ga Daddy ma, ba saina fada maka Daada ba… Ni ma ina so ka dawo saboda in kama ku kuna zagina da Khalid in muku dukan dana dade ina tarawa.”

Yanda ya karasa maganar yasa Nawfal yin dariya, duk da hawaye ne cike taf da idanuwan shi, jakar Salim ya sakar mishi yana fadin,

“Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya.”

Kai kawai Nawfal ya iya dagawa, idan yayi magana kukan da yake tarbewa ne zai kwace mishi. Takawa yayi kawai yana cigaba da tafiya kafin ya juyo ya hange su tsaye, hannun shi ya daga musu, da Khalid da Daddy ne suka daga mishi hannu suma. Salim kai kawai ya jinjina, baya shiga harkar kowa saboda baya son jin wani abu kusa da zuciyar shi, baya son saka kowa da komai cikin ran shi, duk wani abu daya danganci hayaniya baya so. Yau yayi ma Nawfal magana saboda kunnuwan shi sun sha kwaso mishi maganganun Saratu da take yiwa Nawfal din da baya son ji.

Yanda yaron yake rayuwa da wannan hayaniyar har mamaki yake yi. Fata daya ya tsinci kan shi da bin Nawfal da shi yanzun da suka juya hanya. Allah yasa da jirgin su ya tashi ya bar duk wata hayaniya da take cikin rayuwar shi, tafiyar ta samar mishi da wani shiru a rayuwar shi.

Sai dai abinda Salim bai hango ba shine addu’ar shi da ta karbu.

Nawfal ya bar duk wata hayaniya da tafiyar shi.

Ya barta tana jiran dawowar shi.

Dawowar da idan tayi mishi maraba sautin ta bashi kadai zaiji ta ba Har su da suke zagaye da shi sai ta taba.

<< Rai Da Kaddara 4Rai Da Kaddara 6 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.