Skip to content
Part 10 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Sati biyu kenan. Rayuwa suke ba don tana musu daɗi ba. Suna iya ƙoƙarin su wajen ganin komai da ya faru bai canza yanayin zamantakewar da ke tsakanin su ba.

Sajda ta fi komai ɗaga musu hankali a yanzun. Kamar asibitin da aka kaita ya sake tunzura ciwonta ne. Don yanzun da wuya take samun baccin awa biyu a rana. Abinci ma da ƙyar ake ɗura mata yoghurt, haka ma ruwa, gashi in ba kowa kusa ta fara, haka zata yi ta buga jikinta da kome ta samu. Labeeb na iya ƙoƙarin shi akansu.

Kome suke buƙata ta ɓangaren kuɗi basu da matsalar shi. Ya ɗauke musu duk wannan. Ya dai damu da ciwon Sajda ɗinne shi ma. Kullum sai ya bugo waya ya tambaya jikinta.

Haka satin nan yana dawowa suka ɗauketa shi da Dawud suka mayar da ita asibiti. Zaune su Ummi suke suna jiran dawowar su.

“Da ina da zaɓi zan dawo da ciwon Sajda jikina ta samu sauƙi. Allah kaɗai yasan abinda take ji.”

Tayyab ya faɗi kamar zai fashe da kuka. Kallon shi Ummi ta yi.

“Kar in kuma jin irin maganar nan a bakinka. Addu’ar ku take buƙata. Kamar yadda ka faɗi. Allah kaɗai yasan abinda take ji. Saboda shi ya ɗora mata. Shi kuma zai yaye mata.”

Zulfa ta kalli Ummi ta ce,

“Me ya sameta wai? Ƙawayenta sunata tambayata a makaranta. Na ce musu bata da lafiya.”

Rausayar da kai Ummi tayi. Inda tasan abinda ya ke damun Sajda da ta ji sauƙin abinda take ji a zuciyarta. Bata nunawa ne, amma tare suke ciwon nan da Sajda. Daidai da minti ɗaya bai taɓa fita daga zuciyarta ba balle ta yi tunanin samun sauƙi, don wajen ciwon Sajda daban yake a zuciyarta. Ba tata lafiyar ba har rayuwa da kanta zata iya haƙura da ita in hakan zai samarwa Sajda sauƙi.

“Ban sani ba Zulfa. Kawai bata da lafiya ne.”

Shiru Zulfa ta yi na ɗan wani lokaci kafin ta ce,

“Allah ya bata lafiya.”

Su dukkan su suka amsa da amin.

“Zulfa duba min girkin can a kitchen. In ya tsane ki kashe rishon.”

Miƙewa Zulfa ta yi ta nufi kitchen ɗin, bata jima ba ta fito.

“Na kashe Ummi.”

“Yauwa sannu.”

Tayyab Zulfa ta kalla.

“Yaya ka kunna mana kallo.”

Bai ce komai ba ya miƙe. Don yanzun kwata kwata kallo baya gabanshi. Kunna mata yayi ya dawo ya zauna. Daga shi har Ummi idanuwan su ne kawai akan Tv ɗin. Hankalinsu na can wani waje daban.

****

“No……. Bazan iya ba. Me zance ma Ummi? El bazan iya ba.”

Sai lokacin Labeeb ya ɗago kanshi ya sauke idanuwanshi kan Dawud da ke kai kawo cikin office ɗin.

“Dawud ka zauna.”

Kai yake girgiza mishi ba tare da ya daina kai kawon da yake ba. Yana jin komai na ƙara kwance mishi.

“Sajda bata haukace ba. This is not happening…….”

Yake faɗi ma kanshi. Ganin yadda gaba ɗaya ya rikice ya sa Labeeb miƙewa ya kamo hannun shi ya dawo da shi ya zaunar.

Idanuwanshi sun kaɗa sun yi ja. Ya kalli labeeb da faɗin.

“Ya zanyi ne? Me rayuwa take so da ni wannan karon El? Zuciyata zata tarwatse. Na yialƙawarin zan kula da su, tun ba ai nisa ba na kasa.”

Fuskar shi Labeeb ya kama da hannuwa duka biyun.

“Ka nutsu mana!”

Ture hannuwan Labeeb yayi ya dafe kanshi cikin hannayenshi. Ya ɗauka za a jima kafin hawaye ya sake zubar mishi.

Taya zai fara bari akai Sajda gidan mahaukata? Me zai ce ma Ummi? Ta yaya za su iya bacci basu san halin da take ciki ba.

Numfashin shi har sama-sama yake saboda zafin da ƙirjin shi ke yi. Muryar Labeeb a karye ya ce,

“You have to be strong, wannan shi ne right abinda za ka yi mata. Kana jin Doctor ya ce sati biyu ne.

Ba wai can zata zauna gaba ɗaya ba. Lafiyarta muke so dukkan mu.”

Yana jin hawayen da ke zuba cikin hannayenshi. Kafin zuciyarshi ta fara karanto innalillahi wa inna ilaihir raji’un. A fili ya ci gaba da faɗi har saida ya samu nutsuwa.

Fuskar shi ya ɗago. Ya sa hannayenshi ya goge ta. Hanky Labeeb ya miƙa mishi ya karɓa yana sake goge fuskarshi da shi kafin ya ɗauki takardun da ke gabanshi.

Signing yayi akansu hannunshi na rawa. Sannan ya miƙe, Labeeb na bin bayanshi suka fice zuwa ɗakin da Sajda take. Yau allurar baccin ma sam ta ƙi aiki.

Ihu take tana jijjiga gadon da aka ɗaureta a jiki. Gaba ɗaya ta yi baƙi, ta rame sosai, a hankali Dawud ya taka ya ƙarasa gefen gadon ya tsaya yana kallonta.

A ɗan girman da take da shi za kai mamakin ƙarfin da take da shi wajen girgiza gadon kamar zata karya shi. Juyo da kanta ta yi ta ƙura mishi idanuwa.

A hankali ta ce,

“Yaya…..”

Jikinshi na ɓari ya ƙarasa ya tsugunna kusa da ita.

“Sajda nine. Ki kalle ni, kin gane ni?”

Kallon su Labeeb yake daga inda yake tsaye. Yanayin yadda Dawud ɗin ke mata magana ya karya mishi zuciya, fita yayi ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin.

“Sajda ki gane ni mana…… Don Allah ki gane ni…..”

Ya ƙarasa maganar yana ɗora kanshi a jikin gadon. Wata irin dariya ta yi, ta ci gaba da dariyar kafin ta fashe da kuka. Baisan lokacin da wasu sababbin hawaye suka zubo mishi ba.

Ƙarfen gadonta ya riƙe da hannuwanshi ya tsugunna a wajen. Kuka yake kamar ƙaramin yaro. Muryar shi a dakushe yake roƙon Sajda ta gane shi.

Ya sake jin ta furta Yaya. Ta yi wani abu da zai sa a fasa kaita gidan mahaukata. Amma da alama bata jinshi don dariya take yi, tai kuka, tai ihu tana ƙoƙarin ɓallewa daga gadon.

Yana nan wasu maza su huɗu suka shigo. Belt ɗin da ke ɗaɗɗaure da Sajda suka kama suka kwance. Kamar jira take ta fara ƙoƙarin rugawa suka riƙeta.

Duka take kai musu ta ko’ina, da ƙyar suka riƙe ta dam, kafin wata nurse ta zo tai mata wata irin allura. Ko minti biyu ba a yi ba tai shiru.

Da sauri Dawud ya zagayo, ture sauran da ke tsaye yayi, ya sa hannu yana karɓar Sajda da ke jikin ɗaya daga jikinsu.

Tallabe ta ya yi a hannunshi yana tsugunnawa. Ko numfashi baiga tana yi ba balle motsi. Cikin tashin hankali yake faɗin,

“Sajdaa….. Sajdaaa…..”

Abinda Labeeb ya jiyo kenan, da gudu ya shigo. Tsugunnawa yai gefen dawud yana kama hannun sajda ɗin,

“Allura suka yi mata. Bata motsi wallahi…..”

Dawud ke faɗi cikin tashin hankali. Miƙewa Labeeb yayi ya cakumi wuyan ɗaya yana haɗa shi da bangon ɗakin,

“Uban me kukai mata?”

Da ƙyar aka ɓanɓare shi daga hannun mutumin, don bayajin ihun da nurse ɗin take da faɗin,

“Allurar bacci ce! Tana da ƙarfi ne shi yasa, zata tashi nan da awa ashirin da huɗu.”

Sauke numfashi kawai Labeeb yake, likitan ya shigo. Yanayin su ya kalla ya ce,

“Lafiya dai ko?”

Nurse ɗin tai mishi bayanin abinda ya faru. Kallon su ya yi cike da tausayawa.

“In sha Allah babu abinda ya faru da ita. Allura ita ce taimakon da zamu iya mata. Ku ɗauko ta mu tafi.”

Dafa dawud Labeeb yayi. Ya ɗago ya kalle shi.

“Ɗauko ta mu tafi.”

Bai ce komai ba ya saɓi Sajda a kafaɗarshi yana miƙewa ya bi bayansu. Motar asibitin suka shiga. Labeeb kuma ya shiga tashi ya bi bayansu.

****

Federal Neuro Psychiatric Hospital (FNPH) suka ƙarasa. Duk takardun da ya kamata su ciccike aka basu suka cike. Labeeb ya biya kuɗaɗen da duk ake buƙata.

Tare da su aka je ɗakin Sajda ɗin, suka sauketa kan gadon a hankali, bata san duniyar da take ba. Kallon ko’ina na ɗakin Dawud yake yana jin yadda zuciyar shi tai nauyi a ƙirjinshi.

Ta yaya zai iya bacci sanin Sajda na nan, baisan halin da take ciki ba. Idanuwanshi ya tsayar a kanta, Sajda ce haka, yarinyar da gani daya kowa zai mata ya ji ta shiga ranshi.

Ita ce yau da hauka, tsoro ne na gaske yake shigar shi, da wani imani na daban, ya sake yarda ɗan Adam ba komai bane. Kaita abinda kake so don Allah ya baka aron lafiya da hankali.

Ba zaka gane muhimmancin kyautar da kake samu ta komai ba sai lokacin da ka ga wani ya rasa wannan abubuwan da kai ka raina. Ƙarasawa yayi gefen gadon ya zauna.

Ranƙwafawa yayi ya sumbaci goshin Sajda. Muryarshi a sarƙe ya ce,

“Allah ya baki lafiya Sajda. Allah ya yaye miki abinda yake damunki. Na yi alƙawarin kula da ke Sajda, banda zaɓi a barinki wajen nan.

Wallahi banda zaɓi, zuciyata na tare dake ko da yaushe, don Allah ki ji sauƙi da wuri…..”

Kalaman ya ji sun mishi tsaye, ya rasa abinda zai faɗa mata kuma, miƙewa yayi, zuciyarshi na sake karyewa. Ko juyawa bai yi ba ya fice daga ɗakin.

Da gudu-gudu yake fita daga asibitin har sai da ya kai ƙofa, ya ƙarasa inda Labeeb yai parking ɗin motar ya buɗe ya shiga ya zauna, ko rufewa bai yi ba ya jingina kanshi da gaban motar.

Yana jin Labeeb ya rufe mishi ƙofar ya zagaya ya shiga ya kunna motar yana janta, bai ɗago kanshi ba sai da ya ji yayi parking. Buɗe motar ya yi ya fice.

Bayanshi Labeeb ya bi da kallo, yasan suna buƙatar lokaci da junansu, su yi jimamin abinda rayuwa ta zo musu da shi. Don haka ya ja motar shi ya tafi kawai.

****

Da sallama ya tura ƙofar, yana janta daga ciki. Takalmanshi ya cire, hannunshi har lokacin riƙe da handle ɗin ƙofar yana tsaye ya kasa ƙarasawa ciki.

Zulfa ce ta taso daga inda take tana ƙarasowa wajen Dawud.

“Yaya ina Sajda ɗin?”

Kasa magana yayi, komai ya tsaya mishi a maƙoshi. Jin yayi shiru ya sa Tayyab miƙewa daga inda yake zaune.

“Meya faru?”

Ya buƙata muryarshi na karyewa. Ummi da ke zaune ta kafa idanuwanta wkan Dawud. Yanayin da take gani a fuskarshi yasa ta jin wani abu ya dunƙule waje ɗaya a cikinta saboda tashin hankali.

Kafin ɗan da ke cikinta yai wani irin juyi da ya sa bayanta amsawa, bata san lokacin da ta soma faɗin,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, Ya Allah….”

Saboda azabar da take ji ba, dafe bayan ta yi da hannu tana ci gaba da kiran sunan Allah. Da gudu Dawud ya ƙarasa yana tsugunnawa a gabanta.

Su dukkansu zagaye ta suka yi suna mata sannun da ko amsawa ta kasa yi saboda azaba. Gaba ɗayansu sun rikice don Zulfa ma har ta soma kuka.

Bata san iya mintinan da ta ɗauka ba, kafin ta ji sauƙi na samuwa a wajenta a hankali, sauke numfashi ta yi ta ci gaba dayi tana hamdala.

“Ummi ko mu tafi asibiti?”

Dawud ya faɗi muryarshi ɗauke da wani yanayi. Murmushin ƙarfin hali tai mishi tana faɗin,

“Ba sai mun je ba Dawud, yana faruwa a wannan stage ɗin. In sha Allah ya wuce.”

Tayyab ya ce,

“Anya kuwa Ummi? Sannu.”

Murmushi ta sake yi, wannan karon ya fi na ɗazu ƙwari.

“Karku damu fa. Ya wuce ai….”

Ta ƙarasa maganar tana kamo hannun Zulfa ta janyota jikinta.

“Ke komai kuka. Ba na ji sauƙi ba.”

Luf Zulfa ta yi a jikin Ummi tana sauke ajiyar zuciya. Kafin Ummin da Tayyab su maida hankalin su kan Dawud.

Zuciyar shi ya ji tana dokawa da ƙarfin gaske. Yanajin kamar ace yana da ƙarfin ɗauke musu raɗaɗin da za su ji da labarin da zai faɗa musu.

Idanuwanshi ya sauke ƙasa yana jin suna cika da hawaye masu zafi. Muryarshi na rawa ya ce,

“Sajda….. Ummi sajda na asibitin….mahaukata.”

Matsawa Tayyab yayi kamar Dawud ya watsa mishi ruwan zafi. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un Ummi ke jerowa babu ƙaƙƙautawa. Ta kasa tarbe hawayen da take ji.

Kuka take, daga zuciyarta yake fitowa yana gangarowa kan kuncinta da ƙuna mai ciwo. Daga Allah sai wanda ya taba tsintar kanshi cikin irin halin da take ne kawai zai iya fahimta.

Ciwon hauka abune mai cike da tausayi da abubuwa kala-kala, rasa hankali abu ne da ko maƙiyinka ba za ka yi ma fata ba.

Kanshi Dawud ya ɗora a jikin Ummi, yana jin yadda nashi hawayen yake zuba shima. Yanayi ne na jarabawa suka shiga da yake gwada imanin su ta fanni mai wahalar cinyewa.

Kusa da su Tayyab ya matso, kafaɗar Dawud ya dafa, ya ɗago ya sauke idanuwanshi da suka canza kala saboda kukan da yayi ranar kan fuskar Tayyab da har ta kumbura.

Shima kukan yake, yasan lallashi yake buƙata, shi kanshi yana da buƙatar mai taya shi fifita ciwukan da yake ji, ga nashi ga na halin da yake ganin su a ciki.

Hannu ya sa ya goge fuskar shi, yana danne abinda yake ji. Hannun Tayyab ya kama yana matsewa cikin nashi. Durƙushewa Tayyab ya yi a wajen yana sakin kuka mai sauti.

Jikinshi ɓari kawai yake yi, Ummi kallon su kawai take yi, bata san me zata yi musu ba don haka ta ƙyale su, kukan ma sauƙi ne. Su yi kukan halin da ‘yar uwar su take ciki.

“Me yasa hakan ke faruwa da rayuwar mu?”

Zulfa ta faɗi tana wani irin kuka mai cin rai. Ummi ta kasa magana balle ta bata amsa, kallonta kawai ta yi ta kauda kai gefe hawaye na sake zubo mata.

Ɗago Zulfa Dawud yayi daga jikin Ummi yana zaunar da ita. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. A tausashe ya ce,

“Akwai abubuwa da yawa da ba za ki gane ba sai kin ƙara girma….”

“Ina son in gane Yaya…. Ina son in gane me yasa hakan ke faruwa da mu.”

Sauke numfashi Dawud yayi yana son samun kalaman da zai yi amfani da su don fahimtar da ita.

“Akwai abinda ba za ki fahimta ba yanzun Zulfa sai nan gaba. Kin taɓa kula a makaranta karatu na canza muku? Da kun wuce wani aji, na gaba ya fi wuya?”

Daƙuna fuskarta da ke jiƙe da hawaye tayi, kamar ta kasa gane meye alaƙar tambayar shi da abinda ke faruwa da su.

“Eh kam, musamman Maths.”

Ta amsa muryar ta a dishe. Kai ya jinjina.

“Kin san me yasa?”

Da sauri ta ce,

“Saboda mun ƙara girma, kuma to make us better.”

“Good girl. To haka rayuwa take tafiya a wajen wasu, suna ƙara girma tana ƙara wahala, kamar yadda ajin nan yake da wahala a wajenku, amma in kuka dage, kuka yi ƙoƙari i sai ki ga kun wuce ko?”

Hannuwanshi da ke fuskarta ta sa nata tana dumtsewa, idanuwanta na sake cika da hawaye, kafin ta ce,

“Har da kyauta ma ake ba wanda suka fi ƙoƙari.”

Zuciyarshi ta sake karyewa.

“To haka zai faru da mu Zulfa, yanzun rayuwar mu tayi wuya, sai dai in muka jure, da addu’a za mu wuce wannan jarabawar har ma mu samu kyauta.”

“Hakan na nufin Sajda zata warke? Zata daina hauka?”

Runtsa idanuwanshi yayi yana buɗe su, ƙarshen abinda zai yi shi ne yai mata alƙawari da ƙaddarar da bashi da iko akanta. In zai kula da su gaba ɗaya ta hanyar da ya dace gaskiya ce ta kamata ta dinga shiga tsakanin su komin zafinta.

Sai da ya haɗiye wani abu da ya tsaya mishi a wuya sannan ya ce,

“Lafiyar sajda ba a hannuna take ba Zulfa. Allah ne yake bada lafiya, shi za mu roƙa ya ba ma Sajda.”

Kai ta ɗaga mishi, tana sauke hannayenshi daga fuskarta ta matsa sosai ta kwanta jikinshi tana sauke ajiyar zuciya. Gyara mata kwanciyar yayi a hankali yana matsawa ya zauna tsakiyar Ummi da Tayyab.

Hannun Ummi ya kamo.

“Ya isa haka Ummi, kar kanki yayi ciwo, babu abinda ya gagari Allah, zamu ƙara addu’a yau, muna da kusanci da Ubangiji shi yasa rayuwar mu take cike da jarabta.”

Ɗayan hannunta ta sa ta goge fuskarta, tasan me yake yi, ƙoƙarin sharing pain ɗinsu yake don su samu sauƙi, hakan kawai yana sake taɓata ta yadda ba zata iya misaltawa ba.

Sakin hannun Ummi yayi, ya juya ya kalli Tayyab da kanshi yake haɗe da gwiwa, hannunshi ya kai ya dafa kafaɗarshi yana ɗago shi.

Kai ya girgiza masa alamar kukan ya isa, miƙewa Tayyab yayi yana barin falon. Har inda suke suka jiyo doko ƙofar da ya yi.

Miƙewa Dawud zai yi a sanyaye Ummi ta ce,

“Kabar shi”

Tunanin kalar ciwon da Tayyab yake ji a yanzun kawai yasa zuciyar Dawud ɗaukar wani zafi na daban.

“I don’t want him alone ummi”

“Ba zaka iya kare shi daga komai ba Dawud, wannan na ɗaya daga cikin su.”

Bai sake cewa komai ba, shiru suka dukansu har aka kira magariba, sannan Dawud ya ɗaga Zulfa daga jikinshi yana miƙewa.

Ɗakin su ya nufa ya ɗauro alwala, tare da Tayyab suka fita masallaci suka yo sallah suka dawo.

****

Sai da suka yi sallar isha’i tukunna suka dawo. Suna dawowa kai tsaye Dawud ya wuce kitchen. Babban plate ya samu ya zubo musu abinci a ciki ba don yana jin yunwa ba.

Asalima tunanin saka wa cikin shi wani abu har amai ya ji yana ji. Ya zo ya ajiye ya koma ya ɗauko musu ruwa a fridge ɗin da ke kitchen ɗin, cike yake da drinks kala-kala.

Kuma yasan akwai wasu da ko taɓa su ba a yi ba, wannan duk aikin Labeeb ne. Ya dawo ya zauna.

“Ku taho mu ci abinci.”

Ya buƙata, Ummi ma juyowa ta yi , tasan ko ita bata buƙatar abincin ɗan da ke cikinta na da buƙata, ba zata cutar da shi ba.

Zulfa ma matsowa ta yi. Idanuwa Dawud ya kafa ma Tayyab. Can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Bana jin yunwa.”

“Nima ban ce kana jin yunwa ba. Ko cikinka baya buƙatar abinci jikinka yana buƙata.”

Yasan yi ma dawud musu aikin banza ne, don haka ya matso ya ɗauki cokali ya soma cakuɗa gabanshi. Zulfa ta saka cokali ɗaya a bakinta, da alama ko taunawa bata yi ba ta haɗiye shi.

Dawud ta kalla idanuwanta na yin rau-rau.

“Ba za akai ma Sajda ba?”

Ɗan abinda ya dira cikinshi ya ji yana barazanar fitowa. Kai ya soma girgiza mata yana haɗiye abinda ke taso masa kafin ya samu ya ce,

“Bacci take, an bata magani. Sai gobe in Allah ya kaimu zata tashi.”

Da alama amsar da ya bata ta zauna mata. Don haka ta maida hankalinta tana ci gaba da cin abincin.

Ko rabi basu ci ba, kowa ya ajiye cokalin. Dawud ya ɗauka da kanshi ya mayar kitchen, yana shirin fitowa ya ga Tayyab ya dawo da kofunan da suka sha ruwa da su.

“Sannu da aiki.”

Mmmm

Ya ce mishi ba don komai ba sai don ya kori yanayin da suke ciki ko da na minti ɗaya ne. Kai kawai Tayyab ya ɗan ɗaga mishi har lokacin. Remote ɗin ummi ta ɗauka tana canza channel ɗin.

Wrestling ake, wani abu ya soki zuciyarta yana tsaya mata a maƙoshi. Shirin da baya wuce su duk sati. Tare suke kallonshi da Auwal.

Tasan da wahala in baya can yana kallo, saita samu kanta da son kallon shirin. Ko ba komai zai ɗan rage mata mugun kewar mijinta da ke damunta.

“Na tsani shirin nan.”

Zulfa ta faɗi, muryarta ɗauke da wani yanayi. Kallonta Ummi take da mamaki, tasan ita da Tayyab sun fi kowa jin daɗin shirin da Abbansu.

“Nima na tsane shi.”

Tayyab ya faɗi yana kauda kanshi daga kallon TV ɗin. Muryar Ummi na rawa ta ce,

“Yaushe kuka fara tsanar shi? Tare kuke kallo da Abban ku fa.”

“Saboda Abba nake kallo. Ba ya kore mu daga gidanmu ba? Na tsani shirin nan Ummi, na tsani Abba ma.”

Zulfa ta ƙarasa maganar tana miƙewa da gudu ta nufi ɗakinsu, Dawud Ummi ta kalla tana son ya taimaka mata.

“Tashi muje mu kwanta Tayyab.”

Ya faɗi, da sauri Tayyab ya miƙe ko saida safe bai ce ma Ummi ba ya wuce. Ba tare da Dawud ya bari sun haɗa idanuwa ba ya ce,

“Sai da safe Ummi.”

Bai jira amsarta ba ya wuce abinshi.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, Allah ka ganar da su Abban su ba shi da wani zaɓi, Allah karka bari tsanar shi ta samu wajen zama a zuciyar su……”

Ta ƙarasa kuka na sake ƙwace mata, saboda ta ga kamar ta makaro da addu’arta, tana iya karantar tsanar Auwal a idanuwan ‘ya’yan shi.

Duniya kenan, duniya ba komai bace ba, ta sake tabbatar da hakan a yanzun. Allah na nuna Ikon sa a ko da yaushe, ɗan Adam ne yake rufe idanuwa yana ƙin gani.

Tun a duniya kenan, ‘ya’ya sun tsani mahaifin su, wanda ya ɗauki shekaru yana kula da su kafin ƙaddara ta ɗauki wata hanyar da hakan. Tun a duniya kenan da suke da zaɓi guda biyu.

Su yafe mishi ko akasin hakan. Ina ga an je lahira? Inda kowa ta kanshi yake yi. Ɗa na nema wajen mahaifanshi su ma suna nema a wajen shi, haka kowa zai wuce ba tare da ya ba wa ɗayan abinda yake nema ba.

Tsoro ne na daban ya shigeta. Wanda bashi da alaƙa da abinda yake faruwa da rayuwar su. Tsoron lahirar ta da abinda ta ƙunsa.

Da ta tuno da hakan sai ta ga abinda yake faruwa da ita ba komai bane ba. Babban tashin hankali rashin sanin makomarta. Hawayenta ta share, tana miƙewa.

Wannan tunanin da take yi ba amfanin da zai yi mata sai cutarwa. Ɗaki ta shiga, Zulfa har ta yi bacci. Gyara mata rufa ta yi, ta zauna gefen gadon.

Drawer ɗin gefe ta janyo. Hardcover ɗin da ta sa Tayyab ya siyo mata ne shekaranjiya a ciki guda biyu da biro. Ɗauko littafi ɗaya ta yi.

Da biron ta kishingiɗa da gadon, ta soma rubutu a ciki.

****

Yau tashin Tayyab yayi suka yi sallolin tare, sun jima suna karatun Ƙur’ani kafin su gabatar da addu’o’in nemar ma sajda sauƙi.

Nan kan kafet ɗin Tayyab ya bar Dawud ya koma ya kwanta, tashi Dawud ɗin yayi shima ya hau gadon, kwata-kwata shi da bacci sun yi sallama.

Yanajin shi duk wani iri, baya jin daɗi gaba ɗaya. Shi kanshi inda zai samu ganin likita yana da buƙatar hakan ko don rashin baccin nan da yake fama da shi.

Yasan yanzun sanin ba shi kaɗai bane a ɗakin shi ya hana bacci ziyartarshi. Amma har da rana haka yake kwanciya yai ta raba idanuwa ba tare da baccin ya zo ba.

“Sajdaaaaaa!”

Tayyab ya faɗi da ƙarfi yana sakin wani gunjin kuka, riƙe shi Dawud yayi yana girgiza shi, kwanan nan haka yake fama da mafarkan nan. Yau maimakon ya kira Abba kamar yadda yake yi.

Sajda ya kira, a hankali Dawud ke jijjiga shi yana mishi Addu’o’i har ya samu ya nutsu tukunna ya gyara mishi rufa ya juya shima.

Kan kunnen shi aka kira sallar Asuba. Ya tashi Tayyab ɗin yayi alwala, ya riga shi fitowa. Da sallama ya ƙwanƙwasa ɗakin Ummi, gyaran murya ta yi mishi don yasan ta tashi sannan ya juya.

Suka fita masallaci shi da Tayyab ɗin. Suna idar da Sallah Ummi ta gama azkar ɗin safe ta miƙe daga dardumar. Littafin da ta kusan cikawa da rubutu ta ɗauka ta janyo inda ta ɗauko shi ta mayar.

****

Shirin makaranta su Tayyab suka yi. Dawud ya shiga kitchen ya haɗa musu abin kari. Sai da yaima Tayyab faɗa sosai ma sannan ya ɗan sha ruwan tea.

Ya basu kuɗi wadatattu ko da za su ci wani abun a makaranta. Gidan ya sake yin wani irin shiru. Kwanonin duk da suka ɓata ya wanke.

Ya gyara kitchen ɗin ya fito ya samu Ummi zaune a falo. Cikinta ya tsufa sosai, da ƙyar take ko miƙewa balle kuma wasu ayyukan.

“Sannu da aiki Dawud. Allah kar yasa ka taɓa wulakanta a rayuwarka. Allah ya baka yaran da za su yi maka fiye da abinda kake min.”

Kallonta yayi. Tana kallon yadda ɗan nata ya canza sosai, fara’a na wahalar bayyana a fuskar shi, bata da yadda zata yi da hakan.

Murmushi tai mishi. A sanyaye ya ce,

“Amin ummi. Kema sannu da zama.”

Shi ya share gidan gaba ɗaya, ya gyara ko’ina tukunna ya wuce ɗakinshi ya yi wanka. Baƙin wando ya saka sai plain T-shirt fara. Ya taje sumar dake kanshi ya fito. Inda ya bar Ummi nan ya sameta. Ya zauna kan hannun kujerar da take.

“Yaushe za ki koma asibiti?”

“Sai na ji wani ciwo tukunna, basu bada rana ba.”

Jinjina mata kai yayi.

“Za mu je wajen Sajda tare ne?”

Girgiza mishi kai ta yi. Tunda suna tsaye akan Sajda ɗin ba sai ta je ba, bata son furta ma kanta dalilin ƙin fitarta, hakan zai sake tabbatar da sakin da Auwal yai mata.

Miƙewa yayi da faɗin,

“Bari in je Ummi. Karta tashi kuma tana buƙatar wani abu.”

A sanyaye ta ce,

“A dawo lafiya. Allah ya bata lafiya.”

Ya amsa da amin. Sai da yayi addu’a tukunna ya fice daga gidan. Ta sauke wata irin ajiyar zuciya.

****

Kwance ya samu Sajda tana bacci, sai dai ya ji daɗi da bai ga sun ɗaureta da komai ba. Kuma likitan da ke dubata yace mishi sun bata yoghurt da sasafe da ta tashi.

Ta karɓa ta sha, sannan suka yi mata allura don ƙwaƙwalwar ta na buƙatar hutu. Kujera ya ja kusa da gadon da take ya zauna.

Kanshi ya ɗora a jikin gadon yana ma Allah godiya daya soma karɓar addu’arsu. Ga mamakin shi ji yayi idanuwan shi na lumshewa.

Abin ya so ya bashi dariya. Yau kwanan shi nawa yana neman bacci ya ƙi zuwa sai yanzun, a asibiti kuma. Ɗago kai yayi ya ga Sajda baccinta take ba tare da ta san duniyar da take ba.

Maida kanshi yayi ya kwantar. Bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi. Baisan me ake ba balle yasan iya tsawon lokacin da ya ɗauka yana bacci.

Sa’adda ya buɗe idanuwanshi yana jin wata ‘yar nutsuwa, ɗago kanshi yayi ya sauke idanuwanshi kan Sajda. Kamar daga sama ya ji an ce,

“Har ka gama minsharin?”

Juyawa yayi ya ga Labeeb zaune kan kujera.

“Banyi minshari ba.”

Ya faɗi yana yamutsa fuska.’ Yar dariya Labeeb yayi ya ɗan ɗaga mishi kafaɗa alamar duk yadda ka ce.

“Da gaske banyi munshari ba fa.”

Dawud ya sake faɗi. Dariyar dai Labeeb ya ƙara yi.

“Ni da kai waye yake musu?”

Bayan hannuwanshi Dawud ya sa yana murza idanuwa.

“Ban ji shigowarka ba.”

Kai Labeeb ya ɗaga mishi.

“Na gani ai. Baka bacci ko?”

Ya buƙata.

“Ba laifina bane, baya zuwa min ne, kuma bansan dalili ba.”

Ba alamun wasa a fuskar labeeb ya ce,

“Ka ga likita.”

Girgiza kai yayi.

“Na yi bacci yanzun. Ka gani ai.”

Shiru ya yi ya ƙyale shi. Suna nan wata likita ta shigo ta dudduba Sajda ta gyara mata kwanciya ta fita. Miƙewa suka yi. Kowanne ya sumbaci Sajda a goshi sannan suka fice suna jan ƙofar a hankali.

*****

“Rabon da in nutsu in ci abinci haka har na manta.”

Labeeb ya faɗi yana ajiye plate ɗin da ya gama cin abinci da shi ya ɗauki sprite yana buɗewa.

“Shi yasa ga ka nan kamar a hure.”

Cewar Ummi. Dariya Labeeb yayi.

“Mutane fa Ummi. Da ka zauna da an kiraka. Shi yasa.”

“Kuna ma ƙoƙari ai. Allah ya taimaka ya tsare mana ku.”

Ya buɗe baki zai yi magana wayarshi ta hau ruri. Yasan Mamdud ne don haka ya miƙe yana faɗin,

“Ummi na tafi.”

Kallonshi ta yi, ƙoƙarin shi na bata mamaki. Kamar yadda a kullum bata gajiya da kalar yadda baya gajiya da musu karamci.

“A kula dai. Allah ya tsare.”

Ya amsa da amin yana ficewa da sauri. A ƙofar gida ya samu Dawud a zaune.

“Har ka fito?”

Rausayar da kai Labeeb yayi.

“Wallahi kuwa. Za mu fita da Mamdud ne, ka kira ni in kana buƙatata.”

“Allah ya tsare. Sai kun dawo.”

Cewar Dawud. Hannu kawai Labeeb ya ɗaga mishi yana wucewa ya shiga motarshi.

****

Yau nauyin cikin take ji fiye da ko yaushe. Tana jin yadda ya dunƙule ya koma waje ɗaya. Haka ta kwanta dashi.

Ko sallar dare ta kasa tashi ta yi saboda yadda take jin cikin ba zata iya ba. Bacci ya soma fisgarta sama-sama.

Amsawar da bayanta yayi yasa ta miƙewa babu shiri tana salati. Sakkowa ta yi daga kan gadon ta zauna ƙasa kan kafet.

Ji take kamar ƙasusuwan da ke bayanta suna kakkaryewa suna canza mazauni. Wanda yasan yadda azabar zafin naƙuda take ne kawai zai fahimci halin da take ciki.

Numfashinta ta ji har sama-sama yake saboda ciwo. Kiran sunan Allah take tana dafe ƙugunta. Allah ya jiyar da Zulfa ta ko sakko daga gadon tana faɗin,

“Ummi lafiya? Ummi…..”

Ina! Ta kasa mata magana saboda zafin ciwon da take ji. Da gudu Zulfa ta fita daga ɗakin zuwa ɗakin su Dawud. Bubbugawa take kamar zata karya ƙofar.

Dawud ne ya zo ya buɗe mata. Sai maida numfashi take.

“Yaya… Ummi……”

Ai bai jira ta ƙarasa maganar ba da gudu ya nufi ɗakin Ummi. Samunta yayi tana gunji tana kiran sunan Allah. Haihuwa ta biyar kenan amman wannan naƙudar kalarta dabance da sauran.

Kiranta yake amma bata jinshi. Da gudu ya fita daga ɗakin. Wayarshi ya ɗauko ya shiga lalubar lambar Labeeb. Bugu ɗaya ya ɗauka.

“Dawud lafiya dai ko?”

Numfashi yaja sannan yace

“Ummi……”

“Gani nan zuwa.”

Kawai Labeeb ya faɗi ya kashe wayar. Aljihu Dawud ya zira wayar ya bubbuga Tayyab ya tashe shi. Bai jira ya watsake ba ya koma wajen Ummi.

Ji yake kamar ya cire mata ciwon da take ji ya dawo da shi jikinshi. Tayyab ne ya shigo ɗakin. Hankalin shi a tashe yace ma Dawud,

“Me ya sameta?”

“Ƙila naƙuda ne. Ban sani ba Tayyab, na kira El yana hanya. Mu kaita asibiti.”

Gefe Tayyab ya koma yana jingina da bangon ɗakin, zuciyarshi na ci gaba da dokawa. Ƙwanƙwasa gidan suka ji ana yi. Da sauri Tayyab ya fita ya buɗe.

Labeeb ne, jikinshi sanye da pyjamas da alamu ko tsayawa sake kaya bai yi ba ya fito. Da gudu ya ƙarasa cikin gidan shi da Tayyab. Kama Ummi Dawud da Labeeb suka yi da ƙyar take taka ƙafafuwanta.

Tayyab ya buɗe bayan motar suka shigar da ita. Zulfa ta zauna a gefenta. Shima Tayyab zagayawa yayi. Dawud baida zuciyar ce musu su zauna.

Ko ba komai in suka tafi tare hankalinshi ba zai rabu gida biyu ba. Ciki ya koma ya ɗauko mukullai ya kulle gidan sannan ya shiga motar suka tafi.

******

“I don’t care da cewar ba a nan take awo ba. Ba kuɗina zan biya bane? Saboda me za ku dinga faɗa min duk maganar da kuke so?”

Ƙoƙarin fahimtar da Labeeb likitan yake cewar basu da kowanne bayani akan Ummi. Tunda a Harmony take awo, shi kuma ya kawo ta Dialogue.

“Dole ku koma asibitin da take awo ku zo mana da file ɗinta.”

Ganin Labeeb ya gama ƙulewa yasa Dawud kamo shi. Bata faɗa suke ba, ta lafiyar Ummi suke yi yanzun. Tun tana kiran sunan Allah a fili suna ji har ta yi shiru.

Kamata suka yi suka mayar cikin motar. Dawud ya ce mishi,

“Muje Harmony ɗin kawai, tunda can take awo.”

Ba don Labeeb ya so ba suka wuce Harmony. Suna zuwa aka karɓi Ummi cikin hanzari. Daga Labeeb har Dawud sun kasa zama. Sai kai kawo suke yi.

Gara Zulfa da Tayyab sun zauna kan kujerun da ke waiting area ɗin. Har Asuba babu wanda ya fito yai musu bayanin komai.

Sallah suka je suka yi suka dawo, Zulfa na zaune da alama a tsorace take. Wani likita ne ya fito ya ce, musu,

“Wa ya kawo Aisha Auwal?”

Su dujkansu suka nufe shi. Kallon su yayi. Da sauri Labeeb ya ce,

“Ya’yanta ne mu. Ta haihu?”

Labeeb yai ma nuni da su je office ɗin m. Kallon Dawud yayi, da kai yai mishi alama da ya je kawai. Suna shiga office ɗin ko zama ba su yi ba ya ce,

“Menene? Ka faɗa min, me ke faruwa?”

Zama likitan yayi a nutse ya ke kallon Labeeb da duk ya rikice.

“Naƙudar ta zo mata da complications saboda ciwon da ta samu a ƙashin bayanta. Za mu yi mata tiyata nan da awa biyu.

Muna buƙatar jini da kuma sa hannun mijinta ko wani shaƙiƙinta.”

Wani abu Labeeb ya ji ya ƙulle mishi ciki. Bai ce ma likitan komai ba ya juya ya fice. Dawud yake kallo da yadda har wata rama yayi daga cikin daren zuwa wayewar gari.

Baisan ta inda zai fara gaya mishi wannan maganar ba. Baisan ma me zai ce ba. Ganin shi Dawud ɗin yayi. Da sauri ya ƙaraso yana tambayar.

“El yadai? Ummi fa?”

Ba tare daya kalli idanuwan Dawud ɗin ba ya maimaita mishi abinda likitan ya faɗi. Bai ce komai ba ya raɓa Labeeb ya wuce ciki.

Binshi labeeb yayi ciki. Cikin wata dakushewar murya Dawud ya ce ma likitan,

“A ina zansa hannu?”

Labeeb ya kalla, yai mishi alama cewar ya bashi takardun kawai. Miƙo mishi yayi, da biro yana nuna mishi inda zai saka.

Hannunshi na ɓari ya ɗauki biron, ya ƙura wa takardun ido. Karo na biyu kenan da rayuwa ta bashi zaɓi mai wahalar gaske.

Shekaranjiya barin Sajda a asibiti, yau kuma Ummi za a yi ma tiyata. Yasan su duka biyun zaɓi ɗaya ne yake da shi. Ɗora samun lafiyarsu akan abinda yake ji ya yi.

Zuciyarshi yake ji a bushe, hannu ya saka ya tura ma likitan takardar.

“Sai dai jininta zai ɗan bada wahala saboda O+ ne.”

Dawud baisan yadda zai yi ba. Shi A yake da shi, haka ma Tayyab da Zulfa, Sajda ce kaɗai take da group ɗaya da ummi.

“Ba matsala bane, O+ nake da. Mu je ku yi running test ɗin da za ku yi ku ɗiba.”

Kallon shi Dawud yake yi yana rasa abinda zai ce. Murmushi Labeeb yayi mishi.

“She is my Ummi too.”

Miƙewa Dawud yayi abin ya mishi yawa. Muryarshi a sarƙe ya ce ma likitan

“Za mu iya ganin ta?”

Ɗan nazarin maganar yake sannan ya ce,

“Eh za ku iya ganinta kafin mu gama da yayanka.”

Juyawa yayi ya ƙarasa wajen ƙofar ya riƙe handle ɗin. Abinda zaice ma su tayyab yake tunani, da yadda za su ɗauki maganar.

“Allah ka kawo min tallafi. Bazan iya ba sai da Ikonka.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 9Rayuwarmu 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.