Skip to content
Part 21 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Indai yana gida bai taɓa setting alarm ba. Bai kuma san yadda ake ba, yana ɗauka in kasa abu a ranka ne kawai. Ƙarfe huɗu saura ya farka. Gefen shi ya fara dubawa ya ga Mamdud na nan. 

Banɗaki ya shiga yayi wanka ya ɗaura alwala. Sannan ya wuce kitchen, ya ɗibi dankali ya soma ferewa. Yana gamawa ana soma kiran sallah. Cikin ruwan ya barshi ya koma ɗaki ya tashi Mamdud. 

Tare suka je sallar Asuba suka dawo, Mamdud ya taya shi suka soya dankalin, waje biyu ya haɗa, ya dafa ƙwai a ɗayan gas ɗin. Suna gamawa ya ɗora ruwan wanka a kettle. 

Sai da ya shiga ɗakin Zainab ya haɗa mata ruwan wanka sannan ya tashe ta ya fito, su Asad na ƙwanƙwasa musu yayi, ya tabbatar sun tashi tukunna ya wuce ya duba arif da yake ta bacci abinshi. 

Ɗakin Zainab ya sake komawa don ta fi kowa wahalar shiryawa, ya buɗe closet ɗinta ya fito mata da uniform ya ajiye mata akan gado.

Har socks da takalma sai da ya fito mata da su. Yana nan ta fito wanka. 

“Ina kwana.”

Ta gaishe da shi. Ya amsata yana ɗorawa da, 

“Ya jikin ki?”

“I am fine, yunwa nake ji.”

“Dole ki ji yunwa, ba abinda ke cikinki sai ice cream Zeezee. Me za ki ci?”

“Kome su Ya Asad za su ci.”

Kai Labeeb ya ɗaga yana sauke numfashi, don inta faɗi wani abun daban zata ɓallo mishi aiki. 

“Ka tafi yaya, ni shiryawa zanyi.”

Yana dariya ya ce, 

“To, karki daɗe dai.”

Ya fita daga ɗakin. Ɗakinshi ya koma ya ce ma Mamdud, 

“Ka yi wanka, duk tare zamu fita…”

Miƙewa Mamdud yayi, ya shiga banɗaki, Labeeb kam changing room ɗinshi ya shiga, ya buɗe closet ɗaya na kayan shi ya dudduba su. Duk wasu sababbin kaya dake ciki ya bari ya cire wanda ya taɓa sakawa ya sake musu waje. 

Yana nan ya ji ya fito, kiranshi yayi. 

“Duka kayan dake nan su ne naka, sababbi ne, wanda yayi maka kaɗan sai ka faɗa min. Ka gwada takalma gasu can ko size ɗin mu ɗaya.”

Yana ƙarasa magan ya raɓa Mamdud da ke tsaye yana kallon shi ya rasa abinda zaice, da gudu labeeby ya fice daga ɗakin saboda ya ji kukan Arif. 

Ɗakin Arif ɗin ya ƙarasa ya ɗauke shi yana faɗin, 

“Good morning Arif, ka tashi zaka cika mana kunne da kuka ko?”

Shiru Arif yayi, kamar yasan abinda Labeeb ɗin yake cewa, kitchen ya koma ya ɗauko ruwan wankan shi ya fito. A falo ya ga Mamdud. 

“Kawo shi in mishi.”

Ba musu Labeeb ya miƙa mishi Arif, inda Allah ya ƙara taimakon shi, Arif baya ƙyuya, kowa yarda yake da shi. Ba kaman Zainab ba, da take da wahalar sabawa da mutane kuma har yanzun. 

Mamdud yayi mishi wanka ya shirya shi tsaf cikin riga da wando. Ya saka mishi takalman shi. Ya sauke shi ya kamo shi suka fito. 

“Ina son kai shi makaranta, amma har yanzun ko jagwalgwalon surutun yara arif baya yi.”

“Wasu yaran basa fara magana da wuri.”

Mamdud ya faɗi. Girgiza kai Labeeb yayi. 

“Anya ba kurma bane.”

Abin ya ba Mamdud dariya, shi kanshi Labeeb dariyar yake yi. 

“Seriously, baya cewa komai fa banda kuka.”

“Ba kurma bane, kawai bai fara magana da wuri bane, ka sani ko kaima haka kayi?”

Girgiza kai Labeebyayi. 

“Buzz off Malam, ni surutu tun ina shekara ɗaya na fara.”

“Kaine ka tuno ko labari aka baka?”

Hararar Mamdud Labeeb yayi, ya nufi kitchen ya kwaso musu kayyyakin da za su yi amfani da su ya kai dining table ya shirya musu. 

Zainab ta fara fitowa jikinta sanye da uniform. Kujera ta ja ta zauna, ta ƙasan idanuwa take kallon Mamdud. Kamar baya wajen ƙasa -ƙasa ta ce ma Labeeb, 

“Is he staying with us?”

Murmushi labeeb yayi, Zainab ta fi yin turanci fiye da yadda take Hausa, gaba ɗaya gidan babu mai kalar ƙwaƙwalwarta, har Anees. Don ma Labeeb na hanawa, makaranta su mata double promotion da yanzun JSS3 take kamar su Anees, maimakon JS1. Kallonta yayi, shima ƙasa yayi da murya. 

“Yeah, a nan zai zauna tare damu.”

“Ba zai barmu ba? Ba zai dinga tafiya kamar Mummy ba?”

Mamdud Labeeb ya kalla don baya son yima Zainab alƙawarin da baida tabbas akanshi. 

“Ina nan in shaa Allah.”

Mamdud ya amsa mata, kai ta ɗan ɗaga mishi tana miƙa ma Labeeb plate ɗinta don ya zuba mata dankalinta a ciki. Suna fitowa Asad ya jama Zainab ɗankwali. 

“Yaya kaganshi ko?”

“Asad ka ƙyaleta, karka sa ni surutu da safen nan.”

Anees zama yayi yana gaishe da Labeeb ɗin da Mamdud. 

“Kanka baya ciwo dai ko?”

Labeeb ya tambaya. Hannu Anees yasa ya taɓa plaster ɗin da ke goshin shi. 

“Zai warke, bakwai saura fa, ku yi sauri.”

Ya ƙarasa maganar yana ɗaukar kofi ya soma haɗa tea ɗinshi, a gurguje suka ƙarasa karyawa, Labeeb ya koma ɗakinshi ya ɗauko mukullin mota ya fito. 

Anees ya ba kuɗinsu na makaranta ya sauke su, Zainab ta sumbaci kuncin shi, shi da Arif sannan ta ruga cikin makaranta. 

“Love you, ku kula, banda hawa bishiya, banda faɗa Asad. Ku kula da Zeezee.”

“Love you too. Zamu dawo gida mu sameka?”

Anees ya faɗi, kai Labeeb ya ɗaga mishi. Asad kam har ya shige cikin makaranta. 

“Thank you.”

Anees ya faɗi yana wucewa, kamar dawowa gidan da zai yi ya samu Labeeb na nufin abu babba a wajenshi. Su dukkansu kulawa suke buƙata. 

Mota Labeeb ya koma, ya ja su zuwa makarantar da yake ta Essence International. Suna shiga ya ɗauki Arif don su yi sauri suka nufi office ɗin principal. 

Bayanin Mamdud Labeeb yayi mata. 

“Gaskiya yanzun kasan munci term har biyu, muna kan na uku, sai dai in zai jira mu ƙarasa term ɗin sai ya fara daga SS1 ko kuma ya fara daga JSS3 ya ƙarasa tare da su.”

Girgiza kai Labeeb yayi. 

“No, in dai akwai hanya, ya fara daga SS1.”

“Zan fara daga aji ukun, babu damuwa.”

Mamdud ya faɗi, girgiza kai Labeeb yayi. 

“No Mamdud, level ɗin su Asad ne fa.”

Murmushi Mamdud yayi. 

“Ba a girma da karatu ai, zan fara daga aji ukun.”

Girgiza mishi kai Labeeb ya sake yi, bai ga dalilin da zai sa ace Mamdud ya fara karatu daga aji uku ba.

“Ba kuna exams ba, ku yi mishi mana?”

Sosai Mamdud ya kalle shi. 

“El-Maska zan fara daga aji uku, babu komai fa.”

Ba don Labeeb ya so ba, ware idanuwa Mamdud yayi jin dubu arba’in da biyar kuɗin saka shi makaranta da komai. Haka Labeeb ya ɗauko a aljihunshi ya ƙirga ya bayar. 

Gabanshi aka cike komai da komai da Mamdud Ibrahim Maska. Ɗari biyar Labeeb ya bashi ya ce ya ci wani abu, kuma ya hawo mashin ya koma gida in an tashi. 

Bai ce komai ba har Labeeb ya fice. Alƙawari ɗaya yaima kanshi, dama ce ya samu, chance ne rayuwa ta bashi da ba zai taɓa wasa da shi ba. 

Alƙawari yaima kanshi zai zama wani abu a rayuwarshi, za a daina mishi kallon marar asali, zai ce matsayin da asalin shi ba zai damu kowa ba saboda yana da abinda za’a duba fiye da wannan. 

Da alƙawarin adane a ƙirjinshi aka auna shi uniform, da shi a ƙirjinshi aka raka shi ajin su. Da shi a ƙirjinshi ya soma first class ɗinshi a makarantar da ko burinshi bai taɓa hango mishi takawa ba. 

**** 

Gidan Uncle Labeeb ya fara wucewa ya ko yi sa’a yana nan. Ya faɗa mishi ba zai samu zuwa ba a satin, a ci gaba da shooting na wasu parts ɗin ai holding ɗin nashi. 

Uncle bai matsa mishi ba, don yasan Labeeb bai taɓa ƙin zuwa aiki babu dalili mai ƙarfi ba. Bai wani jima ba ya fito, gidan su Dawud ya wuce. 

Da sallama ya shiga. Ummi ta fito da fara’a a fuskarta. 

“Labeeb, ka shigo mana…..”

Takalmanshi ya cire, yana ƙarasawa falon, ta karɓi Arif ta zaunar da shi kusa da ita. Gaisawa suka yi da Ummi. 

“Baka je makaranta ba Labeeb?”

“Babu wanda zan barma Arif, Mummy bata nan, ‘yar aikinmu kuma na koreta jiya. Arif nata kuka fa, wallahi Ummi tana zaune tana shan ice cream.”

Girgiza kai Ummi tayi. 

“Mutane sai haƙuri Labeeb, kuma da ka kawo Arif ɗin nan ai, tunda ba rigima yake da ita ba.”

“Yanzun ma biyowa na yi ince ko za ki dubo mana wata mai aikin, bansan wa zan sa ba kuma, duk wanda ake samowa sai addu’a.”

Ɗan jim Ummi tayi. 

“In sha Allah zan samo mai hankali. In baka makara ba kabar Arif dine ka je ka shirya.”

Girgiza ma Ummi kai yayi. 

“Sai dai gobe in Allah ya kaimu kuma Ummi. Su Dawud suna makaranta ko? Ina Sajda?”

“Suna makaranta, Sajda surutu, an sata makaranta itama.”

Dariya Labeeb yayi. 

“Arif ma so nake ya fara magana, in kai shi.”

“Ka barshi ya ƙarasa shekara uku dai.”

Jinjina kai Labeeb yayi yana miƙewa.

“Bari in wuce Ummi, sai na je kasuwa na yi cefane…..”

“Ka dawo wajen sha biyu ka karɓar muku abinci Labeeb.”

Sauke numfashi yayi. 

“You are a life saver Ummi.”

Dariya kawai tayi. Yai mata sallama ya wuce, har ƙasan ranshi yake jin ina ma ace a gidansu Dawud yake. Yadda Ummi take nan a rayuwarsu yana burge shi matuƙa.

Nan kawai yake zuwa wasu lokutan ya ci abinci, ko ya zauna yaita kallo, yakan samu natsuwa, ga nasihohin Ummi, ko su Dawud take yima a gabanshi yakan ji sun shige shi. 

Sai da ya biya ta oasis ya kwashi shirgin lemuka da ice cream, biscuits da chocolate saboda Zainab sannan ya koma gida. 

**** 

Watan Mamdud ɗaya kenan tare da su, Labeeb zai iya cewa ƙaunar Mamdud bashi kaɗai yake da ita a zuciyarshi ba. Zuwa yanzun har Zainab da take da wahalar sabo ta shaƙu da Mamdud. 

Ko Mummy da ta dawo, Labeeb yai mata bayanin Mamdud ɗin, sai dai sanin halinta yasa shi ce mata iyayenshi rasuwa suka yi, baya jin daɗin inda ake riƙonshi. 

Sosai ta kalli Labeeb ɗin, 

“Kwashe-kwashe ne bana so ka sani Labeeb.”

“He is great Mummy, i promise, don Allah karki ce a’a, shi kaɗai ne yake tare danir tsakani da Allah, i need some normalcy.”

“Yara da yawa masu shekarunka za su yi komai don su zamo a matsayin da kake, bansan me yasa kakeyin kamar matsayin da kake da shi wani abune marar kyau ba.”

Yasan Mummy ba zata taɓa fahimta ba. 

“Kasan yawan kuɗin da ke account ɗinka kuwa? Kasan garuruwan da fina-finanka suke zagayawa? Kana da fans all over Nigeria, wa ya sani ko harda wajenta ma.”

So yake ya ce ma Mummy ba fans yake buƙata ba, bai damu da yawan kuɗin shi ba, bai damu da ɗaukakar shi ba. Iyaye yake so, da suka damu da shi da matsalarshi. 

Maimakon ya faɗa mata abinda yake ranshi sai ce mata yayi, 

“I need a friend, Mamdud ne Mummy, ba sai kin yi accepting ɗinshi ba. Kiyi approving kawai ya zauna tare da mu.”

Sauke numfashi Mummy tayi. 

“Allah Ya sa kar kayi dana sani. Mutum mugun icce, wanda kaima rana shi zai maka dare.”

“Mummy mana, please.”

“Fine…..”

Ta faɗi tana juyawa. 

“Zai iya zama?”

Kai kawai ta ɗaga ma Labeeb ta shige ɗakinta. Murmushi nasara Labeeb yayi. Kuma gashi ita kanta in ta zo yakan ga ta amsa gaisuwar Mamdud ɗin da fara’a. 

Musamman da ta ga yadda yake ɗawainiya da Arif. Wannan satin da ta dawo yayi dai dai da tafiyar da Labeeb zai yi zuwa Zaria, kuma ya zo a weekend. 

Hakan yasa yace ma Mamdud ya shirya su tafi tare. ‘Yar aikin da Ummi ta samo musu babbar mace ce, tana kula da gidan yadda ya kamata. 

Hankalin Labeeb a kwance yake ta wannan fannin, don yasan da Mummy na cikin gidan da bata nan, bambancin ɗan kaɗan ne.

Kulawar gidan da ta su Arif yana hannun mai aikin. Aikam tare da Mamdud suka tafi. 

**** 

KANO

Sosai Mamdud yake mamakin hayaniya da yawan mutanen da suke location ɗin da suka tafi shooting. Gara ma na waje, amma cikin gida da suka shiga. 

Ji yayi numfashin shi na sama-sama, dole ya fita waje, cikin ɗakin da ake shooting scene ɗin yawan mutane yasa fankar ɗakin kamae bata aiki, ga zafi ga rashin wadatacciyar iska. 

Har kusan Magariba basu zauna ba, sai dai sallah, sai in an yi cutting a ci abinci, wanda ko kaɗan Mamdud bai ga Labeeb ya ci ba, suna gama aikin ranar kuma mutane suka yi ma su Labeeb da wasu cikin Jaruman maza da mata caaa kamar kowa na son gutsirar wani ɓangare ya tafi da shi gida. 

Basu samu sun tafi Daula Hotel inda suka sauka ba a nan cikin garin Kano sai wajen takwas da rabi. Suna cikin mota Mamdud ke cema Labeeb, 

“Haka kuke fama? Ko da yaushe? Ka ji jirin da na dinga ji?”

Dariya Labeeb yayi. 

“Zaka saba, a watan nan ka ga rayuwar El-labeeb. Barka da zuwa rayuwar El-Maska.”

Jinjina kai Mamdud yayi. 

“Lallai kam, rayuwar El-Maska cike take da abin mamaki.”

Jingina kanshi Labeeb yayi da kujerar motar har aka ƙarasa da su hotel ɗin aka sauke su. Ɓangare ɗaya ne akai musu booking na satukan da zasu yi.

Suna shiga, wanka Labeeb yayi, ya fito ya sake kayan jikinshi zuwa jeans da plain T-shirt mai laushi. Tun yana jin ciwon jiki in sun yini aiki har ya saba.

Nan ya ɗauki Telephone ya kira room service aka kawo musu abinci, suka ci, ko da Labeeb ya ce ya ci abinci, ɗan kaɗan Mamdud ya ci. 

Kwaciya yayi Labeeb ya ce, 

“Wai me za ka yi? Dalla tashi fita za mu yi.”

Juya baya Mamdud yayi yana jan mayafi ya rufe jikinshi. 

“Ina kuma? Kasan yadda jikina ke ciwo? Bacci zan yi, saika dawo.”

Ƙafarshi Labeeb ya kama ya janyo shi. 

“Party za mu je, rayuwar El-Maska za ka gani, inka yi bacci mun dawo ne.”

Ƙafar da ya riƙe Mamdud yasa yana ture shi da ita, saiya sake shi ya ɗauki robar ruwan da suka sha ya buɗe ya ɗiba a hannu yana yayyafa ma Mamdud a fuska. 

Ba shiri ya miƙe.  

“Innalillahi, ba dai za ka ƙyaleni ba ko?”

Dariya Labeeb yayi, dole Mamdud ya miƙe suka fita, Labeeb ya ja ɗakin, ba tare da ya damu da ya kulle ba, wani part suka nufa duk a cikin hotel ɗin. 

Wajen ya ƙawatu sosai, party ake kamar ana biki, maza da mata kala-kala an cakuɗe, wasu na rawa, wasu na shan lemuka, wasu na hira. Hayaniya sosai. 

Mamdud ya gane fuskokin wasu daga ciki don ya gansu a wajen shooting da Labeeb, gaggaisawa suka sake yi da Labeeb kafin ya bar Mamdud nan tsaye yana kallon ikon Allah. 

Glasses ya dawo da su guda biyu, ya miƙa ma Mamdud ɗaya, ya kafa nashi a baki ya shanye tas. Bakin shi Mamdud yakai nashi kofin, ba arziƙi ya janye kanshi da glass din yana yamutsa fuska. 

Dariya Labeeb yayi. 

“Meye wannan?”

“Rayuwa da kanta, ka sha ka ji”

Mamdud na yamutsa fuska ya kai kofin bakinshi, yana kurɓa ya furzo da shi, saboda taste ɗin daya kama mishi harshe da wani ɗanɗano marar dadi. 

“El-Maska meye wannan?”

Dariya Labeeb yayi, ya karɓi kofin hannun Mamdud ya shanye. Wani cikin wanda suke yawo da uniform a wajen Labeeb ya taɓa ma kafaɗa. 

“Kawo mishi coke, normal coke zalla.”

Ko mintina biyar baiyi ba ya dawo da wani glass cup ɗin daban. Labeeb ya karɓa ya bama Mamdud da yake kallonshi da mamaki. 

Saboda wannan ɓangare ne na Labeeb da bai taɓa gani ba a kwanaki talatin ɗin da yayi da shi. Gaba ɗaya wajen ma gani yake a shekarun su bai kamata ace suna wajen ba. 

Wata yarinya da kallo ɗaya za ka yi ma yanayin shigarta kasan ƙabila ce, ba kuma musulma ba kuma zata girme su ta zuro hannuwanta kan ƙugun Labeeb tana rungume shi ta baya. 

“El-Maska…..”

Ta faɗi da ɗan ƙarfi saboda kiɗa da hayaniyar da ke wajen, ɗan juya wuyanshi yayi, sumbatar ta yayi a baki tare da faɗin, 

“Ruby”

Ware idanuwa Mamdud yayi, Labeeb ya juya ya kama hannayen yarinyar da ya kira da Ruby suka soma jujjuyawa da kiɗan da ke tashi. 

Sosai Mamdud zai ce Labeeb ya iya rawa, yana kallo ya kai bakinshi saitin kunnen Ruby ya faɗa mata wata magana, kai ta ɗaga mishi ta wuce. 

Glass cup ya sake ɗauka da aka zo wucewa da shi, na huɗu kenan Mamdud na lissafawa. Tangaɗin da ya ga Labeeb ya soma ne ya tabbatar mishi da zargin da yake na abinda ke cikin kofin. 

Wani ya ga ya sake ɗauka, ya kai bakinshi, ya ƙarasa ya karɓi kofin. 

“Ya isa haka. Wannan ba kai bane ba.”

Kofin ya kai hannu zai karɓa, Mamdud ya ture hannunshi. 

“Meke damunka haka? Meye wannan ɗin?”

Dariya Labeeb yayi. 

“Rayuwar El-Maska kenan Mamdud, in zan yi aikin nan gobe i need this.”

Ƙasa Mamdud ya ajiye kofin ba tare da ya damu ba, hannun Labeeb da ke tangaɗi ya kama yana janshi suka nufi hanyar fita daga wajen. 

Wata yarinya ce da fitsararriyar shiga a jikinta ta kama ɗayan hannun Labeeb ɗin. 

“El-Maska tun ɗazu nake nemanka.”

Tsayawa Mamdud yayi, ya kama hannun yarinyar yana cire na labeeb daga ciki. 

“Baki ga bai damu da ke ba? Da ya nemoki ai, matsa dalla!”

Kaucewa ta yi tana watsa ma Mamdud wani mugun kallo, Labeeb kam dariya yayi. Bai mishi musu ba ya ja shi suka fita daga wajen gaba ɗaya suka nufi hanyar da ɗakinsu yake. 

Yasa hannu ya tura dakin ya shiga da Labeeb ɗin ciki. 

“This is my life Mamdud….. I hate acting bana so….bana sooo…. Ina so inje makaranta kamar kowa, inyi yawo a hanya babu wanda ya damu da ni.”

“Na ji, ka zauna, yanzun ma za ka yi yawo babu wanda zai damu da kai.”

Mamdud ke faɗi, yanayin muryar Labeeb yasan magana yake a buge, da wahala da safe ya tuna maganganun da yayi, koma duk abinda yayi, don ba a cikin hayyacin shi yake ba. 

Zaunar da shi yayi kan gado, ya kama ƙafafuwanshi ya cire mishi takalma, ya ajiye su gefe, ruwa ya ɗauka ya zuba a kofi ya ba Labeeb ɗin da ya ture hannunshi. 

“Ba za ka gane baaa….. Kullum da daddare sai ta shigo ɗakinaaa….. She… She is so big….. She raped me…. Mummy bata damu ba, bata nan… Kullum kullum Mamdud, ba zai sake faruwa ba, ba mace bace zata ɓata ni….. Ni ne zan ɓata ta…. Bazai sake faruwa ba…..”

Shiru Mamdud yayi, bai taɓa zaton maza za su iya fuskantar matsala irin haka ba, ya kuma tsorata har ranshi, tunanin abinda ya faru da Labeeb ɗin kawai yake yi. 

Miƙewa yayi daga zaman da yayi, yana kallon fuskar Labeeb dake ɗauke da wani irin yanayi. 

“Amai….amai nake ji.”

Ya faɗi yana miƙewa da ƙyar, kamashi Mamdud yayi suka nufi hanyar toilet, kafin su ƙarasa har ya fara aman, ya ɓata kayanshi da wajen, da ƙyar Mamdud ya ja shi ya ƙarasa cikin banɗakin. 

Shi ya kamashi ya cire mishi rigar da ya ɓata ya bar mai singlet ya wanke mishi fuska da hannuwanshi, da ƙyar yake iya buɗe idanuwanshi. Ya kamashi ya fito da shi, kan gado ya kwantar da shi ya ja mishi mayafi ya rufe shi. 

A lokacin ya sake ma kanshi wani alƙawari, ba zai taɓa shan wani abu da zai gusar mishi da hankali ba, ƙwaya, giya, ko makamancin hakan. Bazai taɓa buguwa ba in har haka ake komawa. 

Wajen da Labeeb ya ɓata ya wanke, bai ji ƙyama ko wani abu ba, ya ga abinda ya fi haka a gidan marayu. Babu wani abu kuma da yake tunanin zai ɗaga mishi hankali. Da sabulun wankan da ke ajiye ya wanke rigar Labeeb ya shanya cikin banɗakin tukunna ya watsa ruwa ya fito. 

Bacci mai nauyi Labeeb yake yi, Mamdud ya hau gadon ya kwanta a gefe, yau ya ga kuɗi ba komai bane, kuɗi wani abu ne kawai da suke sauƙaƙa zaman duniya da rayuwa. A da gani yake in kana da kuɗi baka da matsalar komai, ko ranar farko da Labeeb ke faɗa mishi shi yake kula da ƙannen shi, daga mumynshi har dadynshi basu da lokacin su. 

Da ya ga kalar suturar su, kalar abincin su, gani yake Labeeb ba shi da godiyar Allah ne. Tunda yana da wanda zai kira iyaye ko suna nan ko basa nan babu wani abu. 

Sai yau ya ga illa ɗaya na rashin su, sai yau ya ji abu guda ɗaya cikin wanda yasan akwai su da suka faru da Labeeb akan rashin kulawar mumynshi. 

Da wannan tunanin a zuciyarshi yai bacci, cike da mafarkai masu tsoratarwa. 

**** 

Da safe Labeeb ne ya tashe shi suka yi sallah, sai bayan sun idar ya kalli Mamdud. 

“Na maka shirme jiya ko? Ya Rabb, bansan me zance ba wallahi.”

Ya faɗi yana tallabe kanshi da ke mugun sarawa kamar zai faɗo ƙasa, ya kuma san giyar da ya sha ce jiya. Har ƙasan zuciyarshi yana son bari. 

Sai dai kamar yadda baisan dalilin dayasai ya fara ba, haka ya kasa samun dalilin da zai bari. 

“Ba sai ka min bayani ba, har yanzun akwai abubuwa da yawa na rayuwata da ban maka bayani ba…”

Kai Labeeb ya jinjina. 

“Ka ga rayuwar El-Maska ko? Banda dalilin dazan bar ta. Zan iya zama El-labeeb saboda su Zainab, suna buƙatar El-labeeb…..”

“Zaka iya zama El-labeeb kawai.”

Ɗan ɗaga kafaɗa yayi. 

“Perhaps wata rana, yanzun kam bansan ko ta yaya ba.”

Shiru Mamdud yayi. Kafin can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Abinda ya faru da kai, abinda ‘yar aiki….”

Da sauri Labeeb ya katse shi da faɗin,

“Bana son maganar Mamdud, ba yanzun ba, ba ko da yaushe ba, har abada banason maganar. Ba zai sake faruwa ba, shi ne maganar kawai.”

Kallonshi Mamdud yayi. 

“Karka bari ya canza ka.”

Wata irin dariya Labeeb yayi yana miƙewa.

“Tun shekaru biyu da suka wuce. Bacci zan koma nikam, kaina ciwo yake, ƙarfe goma zamu fita.”

Ya ƙarasa maganar yana kwanciya abinshi. Shi ma Mamdud ɗin komawa yayi ya kwanta, sai dai maimakon yai bacci kallo ya ci gaba da yi abinshi.

****

BAYAN SHEKARU UKU

A shekarun nan in akwai abinda Labeeb zai ce ya canza a shekaru goma sha takwas da ‘yan watanni da yake dasu a duniya shi ne girman ƙannen shi. 

A yanzun Mamdud ya zame mishi wani ɓangare na rayuwar shi da baisan ya zata kasance ba in baya cikinta. Makaranta kuwa yana gab da gama level one a KASU inda yake karantar Mass Communication saboda kawai Mummy ta matsa mishi. 

Don bai yi niyyar ci gaba ba daga Secondary, bai ga me zai yi da karatun ba, da taso ya zaɓi Career da ta barshi yayi hankalin da zai yi hakan, sai dai kamar yadda ta saba, tana bayyana ta nuna ta damu da rayuwarshi ne a lokacin da take tunanin ya mata. 

Yanzun haka kwance yake a gidanshi da yake saukar baƙi ko abokan da suke tare da shi saboda ɗaukakarshi. Ko ‘yan matanshi. 

Don banda Mamdud babu wanda yasan yana gari, party yayi cikin gidanshi daren jiya. Haske da ya ji cikin idanuwanshi shi ya farkar dashi. 

“Oh shit!”

Ya faɗi yana ture yarinyar da ke kwance a jikinshi, in akwai abinda yafi tsana bai fi ace yayi asarar sallah akan lokaci ba, agogon shi da ke ajiye gefe ya ɗauka, bakwai saura. 

“Mtswwww.”

Ya faɗi yana saukowa daga kan gado, toilet ya nufa ya soma tsarkake jikinshi tukunna yayi wanka da sabulu ya ɗaura alwala ya fito. Ɗan dafe kai yayi. 

Yasan da kunya a ganshi da ranar nan ya fita masallaci, ba dai lokacin walha bane balle. Gaba ɗaya najasar gidan yake gani, bai yarda da ko’ina a ciki ba balle ya ce zai yi sallah.

Da wahala ma idan da darduma a cikin gidan, wani tsaki ya sake ja, ya ɗauki pillow ya buga ma yarinyar da ke kwance kan gadonshi da ko sunanta bai sani ba. 

“Tashi dalla.”

Ya faɗi yana jin tsanarta da tsanar abinda suka aikata, da ƙyamatar kanshi. Buɗe idanuwanta tayi, tana mishi murmushin da yaji ya sake tsanarta, wandonshi da ke ajiye gefe ya ɗauko. 

Ya laluba cikin aljihunshi ya ɗibo kuɗin da baiko ƙirga ba ya watsa mata. 

“Fita zanyi, tashi ki tafi.”

Ware idanuwanta tayi da mamaki, kafin wani yanayi dake nuna yai hurting ɗinta ya bayyana a fuskar ta. Bai dame shi ba. Ba sake ganinta zai yi ba, in tana zaton wani abu banda kwana ɗayan da ta samu kanta ya kwance. 

El-Maska baya ajiye mace fiye da kwana ɗaya. 

“Get out!”

Ya faɗi yana haɗe fuska, bata ce komai ba ta ɗauki doguwar rigarta da ke gefe ta miƙe tana sakawa, kauda kanshi yayi gefe a zuciyarshi ya ce, 

“In na bugu banda class, wannan mai kalan t-square ɗin kuma na tsinto.”

Yana kallonta ta ɗauki mayafinta ta kwashe kuɗinta ta nufi ƙofa. 

“Sai yaushe kuma?”

Ware idanuwa yayi.

“Yaushe me?”

Kallon tambayata kake tai mishi kafin ta ce, 

“Zamu sake haɗuwa.”

“Uhum seriously? Dalla fita!”

Jan ƙofar ta yi ta fita tana dokota, cike da son huce haushinta akan ƙofar, closet ɗin ɗakin ya buɗe ya ɗauko jallabiya ya zurama jikinshi, yasan ba wasu kuɗi yake ajiyewa ba. 

Mukullan gidan dana mota ya ɗauka, yana fita daga bedroom ɗin ya ga yadda gaba ɗaya aka lalata gidan, kwalaye da robobin lemuka dana take away, bama yaso ya shiga kitchen balle ɗayan bedroom ɗin balle ya ga ƙazantar da ke ciki. 

Fita waje yayi ya kulle gidan, ya shiga motar shi. In yaje ya faɗa ma Mamdud, shi yasan wanda yake kira a gyara gidan in ya ɓata shi haka. 

Steering wheel ɗin ya doka da faɗin, 

“Crap……”

Haba shi yasa Mamdud ya tafi da wuri jiya, ya manta ya ce mishi ranar suke last paper ɗinsu. Gaba ɗaya ya manta, jan motar yayi zuwa gida. 

***** 

Yana shiga ya ji daɗi da bai samu kowa a falo ba, ɗakin shi ya wuce yayi sallah, tukunna ya sake yin wanka, ya fito ya shirya kanshi cikin blue jeans da riga ja, da ta dan kama shi. 

Gaban mudubin ɗakin ya tsaya yana taje kanshi, turaruka ya feshe jikinshi da su sannan ya fito. Zainab ya ci karo da ita, da kwalin cookies a hannunta, jikinta sanye da three quarter da ƙaramar riga. 

Kanta babu ɗankwali. 

“Zeezee baki je makaranta ba?”

Idanuwanta manya da sak irin na Mumynsu ne ta juya mishi tare da faɗin, 

“Hutu muke yi, oh ka manta fa ko? Kamar yadda ka manta ranar graduation ɗinmu…”

Ta ƙarasa tana ɗaukar cookies guda daya ta gutsura. Ɗan runtsa idanuwanshi yayi ya buɗe su. 

“Sau nawa zan baki haƙuri?”

“Ban sani ba nima, Mummy bata je ba, na fahimta saboda kullum bata nan dama. Kuma sai gashi baka manta na su Yaya Asad ba… Excuse me if am hurt.”

Ta ƙarasa tana wuce shi ta koma kan kujera ta zauna, ta mayar da hankalinta kan TV ɗin da ya tabbatar ba kallo take ba. 

Takawa yayi ya zauna kusa da ita. 

“Ya zan yi in gyara?”

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, 

“Don’t miss my birthday.”

“Bazan yi missing ba. I promise, yaune ranar ƙarshe da zan sake jin tsegumin JSCE party ɗinku. Kin yarda?”

Da murmushi a fuskarta ta ɗaga mishi kai. Tashi yayi ya fice daga gidan ta bishi da kallo, kwalin cookies ɗin ta zuba ma idanuwa kafin ta miƙe ta nufi ɗakinta. 

Jakarta ta makaranta ta ɗauko ta buɗe, kwalaben tutolin ɗin da ke ciki guda huɗu ta fiddo ta zuba ma idanuwa. Nadiya ta bata su da alƙawarin in tayi trying shi ne best feeling a duk duniya. 

“Zaki manta ke kaɗai ce a gida, zaki manta Mumynki bata nan, ke zaki manta duk wata damuwa, zaki manta yayanki bai zo party ɗin nan ba. Babu wani abu da zai dame ki. “

Shi ne maganganun Nadiya. Sai dai satin su uku cikin jakarta, tun ranar da ta bata su ta kasa sha, ta rasa abinda ke hana ta. 

Sam bata ji ƙwanƙwasa ɗakin ba, sai turo ƙofar da Asaad yayi, ƙoƙarin ɓoye kwalaben tayi amma ya riga da ya gani. Kwalba ɗaya zata iya bada excuse. 

Bakinshi a buɗe da mamaki ya tura ƙofar yana kulleta, hannu yasa ya ɗauki kwalaben yana juyasu. Kafin ya zauna a gefenta. 

“Ban sha ba wallahi.”

Kallonta yake, tunda take bata taɓa ganin fuskarshi so serious haka ba. 

“Meye wannan Zeezee?”

“Ban sha ba na faɗa maka…”

Ajiyewa yayi ya zauna sosai yana fuskantarta. 

“Tun yaushe?”

Shiru tayi. 

“Damn it Zainab, ki mkn magana. Tun yaushe?! Me yasa?!”

A nutse ta ce, 

“Bana son ana min magana da ihu ka sani, ban taɓa sha ba, inda zan sha da tuni na fara. 

Da ba zaka gansu ba, satin su uku a jakata, ba zama kuke ba, har Arif yanzun, sai in wuni ni kaɗai, zan iya shan duk abinda zan sha Yaya Asaad. 

And you want to know why? Na gaji da zama ni da TV, na gaji da kallo, ba wanda ya damu dani, not mum, not dad and not you, ba za ka gane ba saboda kana da Yaya Anees………just…. Get out of my room.”

Dafe kai Asad yayi, zuciyarshi na dokawa, yasan maganganunta gaskiya ta faɗa. Ba yini suke a gidan ba, tana iya shan duk abinda zata sha ba tare da sun sani ba. 

Hakan kawai ya bashi tsoro, Mummy ta ja musu, da tana nan ba zasu shiga wannan halin ba. Kallon Zainab yayi. 

“I am sorry, na daina fita, zan zauna a gida, mu duka zamu zauna tare da ke. Ba kya buƙatar syrup Zee Zee, shaye-shaye ba option bane, bazai taɓa miki maganin komai ba. 

Yeah zai mantar da ke damuwarki, in ya sake ki fa? Damuwar tana nan, babu inda zata je, za ki ƙara damuwa ne akan taki. Ki min alƙawari wannan ba zai sake faruwa ba. 

Ba zai shigo tunaninki ba, balle ki zo da shi ɗakin ki. Please Zee Zee.”

Kai ta ɗaga mishi tana jin wani abu ya tsaya mata a wuya, hawayen da ke taruwa a idanuwanta take ƙoƙarin mayarwa. 

“I am sorry…….za ka faɗa ma yaya?”

Ta tambaya tana kallonshi idanuwanta cike da hawaye.

“Ina da buƙatar in faɗa mishi?”

Girgiza mishi kai tayi. 

“Ba zai ji ba Zee Zee. Tsakanin mu ne, na yarda bazai sake faruwa ba.”

Ya ƙarasa ya dauki kwalaben ya ɗora mata a jikinta ya tashi ya fita daga ɗakin yana tsanar kalar rayuwar su. Dalilin da yasa ya ji yana son dawowa gida kenan, don Anees ya raka makaranta, shi ya gama exams ɗinshi.

Yana fita daga ɗakin Zainab ta kalli kwalaben, bata ma san me yasa ta karɓa ba, sai yanzun ta ga haukan abinda tayi. Tana son rayuwarta a yadda take. 

Bata son canza komai a ciki, tana da ‘yan uwa da za su yi komai saboda ita, miƙewa tayi ta kwashi kwalaben gaba ɗaya ta fita waje ta zuba su a shara da alƙawarin kwaɗama Nadiya mari duk ranar da ta sake nufo ta da su.

<< Prev | Next >>

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 20Rayuwarmu 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×