Skip to content
Part 7 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Wanke wanke ta gama ta fito daga kitchen ɗin. Don bata jin tana da nutsuwar zuwa wajen aiki shi yasa ma bata fita ba. 

Sallama ta ji. Zuciyarta ta doka. A sanyaye ta amsa shi tana kallonshi. Mafarkin da ta yi jiya yana ƙara faɗo mata a rai. 

Tama kasa ce mishi komai. Ƙarasowa yai inda take ya kama hannunta. Bai damu da yadda hakan ya sa shi jin wani ƙunci ba. 

Abinda ya kusan faruwa tsakanin shi da Beeba yake son mantawa. Janta yai zuwa falo. Binshi kawai take ya ajiye jakarshi kan kujera ya jata zuwa bedroom ɗinsu. 

*****

Kwance take tana kallon Auwal. Tana mamakin shi ne yaita abubuwan da yayi a kwanakin nan. Yanzun yadda yake kwance kamar auwal ɗinta. 

Ba tare da ya kalleta ba ya ce, 

“Aisha aure zan ƙara!”

Tana jin yadda maganar shi ke mata yawo cikin kunne tana samun wajen zama a zuciyarta da wani irin kishi mai zafi. 

Shiru ta yi saboda in ta yi magana kishi zai sa ta faɗi abinda zata yi da-na-sani. Bata taɓa zaton haka zafin kishi yake ba sai yau. 

Tana ganin rashin hankalin matan da ake cewa suna haukacewa in mijinsu zai ƙara aure. Sai yanzun ta gane abinda ake ji. 

Shima ko kallonta bai yi ba ya sauka daga kan gadon ya shiga banɗaki. Kuka mai cin rai ya ƙwace mata. Ji take ‘yan awannin nan da suka shiga tsakaninsu. 

Kishi ya rufe su. Ya rufe duk wata soyayya da ke tsakaninsu. Ya rufe yarda da sonta da yake yi. Don a yanzun ji take inda yana sonta zata ishe shi. Ba zai yi sha’awar ƙara auro mata wata ba. 

Yana fitowa daga banɗaki ya shirya. Ya fice bai ce komai ba. Miƙewa ta yi ta shiga banɗaki. Tana wanka tana kuka. 

Har ta fito wunin ranar ba zata ce ga yadda ya zo ya wuce mata ba saboda tashin hankali.

**** 

Yau sati ɗaya kenan da maganar ƙara auren Auwal. Wani abu da ya danganci hakan bai sake haɗa su. Asali ma babu abinda ya shiga tsakaninsu. Abin ƙara gaba yake yi. Addu’a take ba dare ba rana. Ɗan zaman da suke da dare ma yanzun baya yi. Da ya dawo sallar Isha’i yake wucewa ɗaki ya kwanta. 

Kwana biyu kenan yaran ma basa zama. Kowa na ɗaki. Gidan yayi wani irin shiru. Duk wata walwala tasu da nishaɗi kamar an yi ruwansu an ɗauke. 

In dai ka san su a da. Kallo ɗaya zakai musu yanzun ka san wani abu ya sauya a tattare da su. Yanzun ma zaune take a falo ita kaɗai da tunani barkatai a zuciyarta. Sajda ta shigo. 

“Ummi ina Abba?”

A sanyaye ta amsa ta da. 

“Bacci yake. Me kika kawo a bashi?”

Haɗe fuska Sajda ta yi tare da girgiza mata kai. 

“Abba baya hira da mu yanzun Ummi. Mun yi laifi ne? Wallahi ina ƙoƙari sosai a makaranta. Ki ce Abba yayi haƙuri zan sake zuwa na ɗaya in sha Allah.”

Wani abu Aisha ta ji yai mata tsaye a ƙirjinta mai zafin gaske. Kamo hannun Sajda ta yi tana janta jikinta. Cikin taushin murya ta ce, 

“Kin san yanzun Abbanku aikin kasuwa yake ko?”

Kai sajda ta ɗaga mata. Fuskarta da alamar bata ga abinda ya haɗa kasuwar Abba da daina hira da su ba. 

“To aikin kasuwa akwai gajiya. Da ya dawo jikinshi ciwo yake shi yasa yake bacci da wuri.

Ba ku yi laifin komai ba. Ammanl zan mishi magana ya dinga samar muku lokaci kin ji ko?”

Cikin idanuwa ta kalli Ummin tata ta ce 

“Za ki yi masa magana? Zai dinga hira da mu kamar da?”

“In sha Allah.”

Murmushi Sajda ta yi. 

“Na tafi in kwanta Ummi. Yaya Zulfa ke min wata tatsuniya mai daɗi.”

‘Yar dariya Aisha ta yi. 

“To maza kije. Karku manta da Addu’a dai.”

Fita Sajda ta yi da gudun ta tana barin ɗakin. Aisha ta sauke numfashi mai nauyi haɗe da miƙewa ta nufi ɗakin baccin su. 

Kamar kullum a kwanakin nan. Kwance yake can ƙarshen gadon. Ya bata baya. Tasan idonshi biyu ba bacci yake ba. 

Banɗaki ta shiga ta watsa ruwa. Ta fito ta sa rigar baccin ta. Ta hau gadon gefen shi ta zauna. Muryarta babu ƙwari ta ce, 

“Abban sajda…..”

Shiru yayi ya ƙyaleta. 

“Na sanba bacci kake ba fa.”

Muryar shi cike da alamun ta takurashi ya ce, 

“Meye kuma?”

“Hmm. Ka yi haƙuri idan na takuraka. Don Allah alfarma nake nema a wajenka.”

Juyowa yayi ya kalleta. 

“Saboda Allah ba za ki iya bari saida safe ba? Zaki dame ni yanzun da daren nan.”

Tana jin yadda hawaye ke son zubo mata. Ta tarbesu. 

“Da safe yanzun ko karyawa baka tsayawa ka yi. Yaushe na samu lokacinka?”

Sake tamke fuska yayi ya ce, 

“Ina jinki. Menene?”

Kallon shi take. Tana neman Auwal ɗinta da ta aura. Auwal ɗinta da ko yaushe fuskarshi take ɗauke da fara’a a cikin gidanshi. 

Wanda yake mata magana da taushin murya, ƙauna da girmamawa. Ba wannan Auwal ɗin da yake nuna kwanciyarshi kusa da ita kawai takura ce a rayuwar shi ba.

Kasa haƙuri ta yi ta ce, 

“Me nai maka? Don Allah Abban Sajda idan na maka wani laifi ne da kake horani ta wannan hanyar ka yafe min . Ka yi haƙuri ka kuma gaya min dan kar in sake aikata shi. Wallahi na hukuntu…..”

Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata.

“Mtswwwww. Kina da matsala wallahi.”

Ya faɗi yana juya mata baya. Da mamaki take kallonshi. Tsakin da yayi ya fi komai bata mamaki da ɓata mata rai. 

Tunda suke wannan cin fuskar bai taɓa shiga tsakanin su ba. Yau ita ce tai magana Auwal yai mata tsaki. Hannu ta kai ta goge siraran hawayen da suka sake zubo mata. 

Bata gaji ba dai ta ce, 

“Ka yi haƙuri. Idan ni na maka wani laifi ne da ban sani ba kake hukuntani. Bai kamata ya shafi yaranka ba. Suna kewarka sosai. Gidan babu walwala gaba ɗaya. Don Allah ko ba za ka yi hira da ni ba. Ka ci gaba da mu’amala da su kamar yadda kake yi a da. 

Bana son dangantakar ku ta samu rauni. Musamman su Sajda da ba hankalin kirki gare su ba.”

Tana gama magana ta zame jikinta ta kwanta. Kamar yadda ta zata kuwa bai bata amsa ba. 

Kuka take marar sauti. Tana jin gaba ɗaya duniyar ta mata ƙunci. Idan haka ƙara aure yake. Dole mata su dinga jin tsoron shi. 

Irin wannan wulaƙancin tun kafin ta shigo kenan. Tana tsoron shigowarta gidan. Don tasan abinda ya fi wannan shi ne zai faru inhar ta shigo gidan. 

Koma wacece wannan da zata ganta da ta roƙeta da ta ji tsoron Allah karta kai Auwal ga halaka. A haka bacci ya ɗauke ta cike da ƙunci da ɗacin zuciya. 

**** 

Yasan akwai abinda ya kamata ace yana ji a game da Aisha banda rashin son ganinta da jinta kusa da shi. 

Akwai gaskiya tattare da maganganunta amma sun ƙi tasiri akanshi. Asalima ya ƙagu ne gari ya waye don safiyar litinin ɗin za a ɗaura mishi aure da Hajiya Beeba. 

Washe garin da ya faɗa ma Aisha ya gaya ma Yaya Ibrahim, fatan alkhairi yai mishi. Tare suka tsaida ranar da za a ɗaura aure tunda ba wata budurwa bace ba. 

Tambaya uku kawai yai mishi. Cewae Hajiya Beeba ‘yar mutunci ce, su waye iyayenta ya ce sun rasu kamar yadda ta faɗa mishi da ya tambayeta. Za su karɓi aurenta ne hannun kawunta. 

Sai kuma ya tambaye shi ko ya faɗa ma Aisha ya ce ta sani. Sunyi da ita a gidanta zata tare ya dinga zuwa can. Da wannan saƙe-saƙen bacci ya ɗauke shi. 

**** 

Kayan da suka gama karyawa ita da Auwal ta kwashe ta kai kitchen. A ranta take tunanin in Huzai ta zo yau zata sa ta nemo mata ‘yar aiki. 

Don wahalar wanke wanken nan ya soma isarta. Bata damuwa da girkin indai Auwal ne zaici kowacce wahala zata iya masa ita. 

Da yake ba yawa gare su ba. Nan da nan ta ɗauraye ta dawo falon. Tana zama ta ji sallamar Huzai. 

“‘Yar duniya. Yanzun nake zancenki a zuciyata.”

Ƙarawa tayi ta samu waje ta zauna. 

“Amaryar Auwal. Na ga har wani haske kike ƙarawa.”

Dariya Hajiya Beeba ta yi sosai. 

“Bana son iskanci. Ya zancen mu. Kinsan fa anjima ne. Kin dai samu wanda za su min wakilcin ko?”

Harararta Huzai tayi. 

“Me kika mayar da ni wai? Ai angama tun jiya. Dama su harkarsu ce. Ba zamu samu wata matsala ba.”

“Beeba ba kowa bace a garin Kaduna in bake a kusa da ni aminiyata.”

Murmushi Huzai ta yi. 

“Nifa mamaki nake. Wai kece za ki yi aure yau. Abin dariya. Gaskiya kinci amanar bariki Beeba.”

Hannu Beeba ta kai mata suka tafa tare da yin shewa. 

“Haba aminiya. Kinsan ni da bariki mutu ka raba ai.”

Sauke murya Huzai ta yi. 

“Kina nufin babu abinda za a fasa kenan?”

Juya idanuwanta Beeba ta yi da ke nuna ‘Ke da kika sani’. Huzai tayi wata shewa tana tafa hannayenta. 

“Shegiya aminiya. Baki da kyau wallahi.”

Murmushi ta yi. 

“Shi yasa nace masa a gidana zan tare. Don ina zan iya zama wannan gidan nashi ɗaki ɗaya kuma?”

Zaro idanuwa Huzai ta yi. 

“Amma bansan ke banza bace sai yau. Baki gama kama shi a hannunki ba zaki tare a gidan ki?

Kin manta matsayin matarshi a wajen shi. Da bakinki kikace yana mugun sonta a alamun kawai da kika gani. Ba don aikin malam ba ko kallon arziƙi baki ishe shi ba.”

Jikinta ta ji yayi sanyi. Duk wani ɗoki da take ji ya dishe. Da damuwa ta ce, 

“Ya kike so in yi to? Nifa nace ma Malam inda hali ya raba shi da tsinanniyar matar nan. Ya zama nawa ni kaɗai.”

Gyara zama Huzai ta yi. 

“Yau kice masa kina son tarewa a gidanshi. Kisa ido kiga yadda kusancin shi da iyalinshi yake. 

Ta hakane kawai za ki samu damar tsigeta daga gidan. Inma wani turare ne ko maganin barbaɗawa in kina kusa kin fi saka shi. Ki shirya ma muje wajen Malam mu ji ya ake ciki.”

Jinjina kai Hajiya Beeba tayi. Tana tunanin yadda akai bata kawo duk abubuwan nan da Huzai ta lissafa mata ba. 

Bata san matar Auwal ɗin nan ba. Amma kishin da take ji nata bazai misaltu ba. Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe ta shiga ɗaki . 

Shiryowa tayi. Ta ɗibi kuɗi, ta ɗauko mukullin motarta ta dawo. Suka fice ita da Huzai zuwa gidan Malam ɗin. 

*****

“Aiki yana tafiya yadda ake so kenan?”

Malam ya tambaya yana wata dariya. 

“Sosai ma malam. Yanzun ‘yan uwanshi nake so su shigo hannuna kamar yadda ya shigo. 

Har matansu ma. Kowa nashi nake so ya karɓeni.”

Ta ƙarasa tana kallon Huzai da ta karɓe zancen da faɗin, 

“Kar su ga laifinta ko da shi Auwal ɗin ne da kanshi zai faɗe shi kuwa malam. Sannan ita ma matar nan tashi haka.”

Dan farantin yashin shi ya ɗauko. Ya zana ƙasa ya goge ya kai sau biyar kafin ya ajiye ya kalle su. 

“Gaskiyar magana. ‘Yan uwanshi za su zo hannunki yadda kike so. Kwalli zan baki da za ki shafa. Da kun haɗa ido shikenan. 

Amma matarshi tun jiya nake bincike akanta na kasa ganin komai. Yanzun ɗin ma haka abin yake. “

Kallon juna Huzai da Beeba suka yi. Kafin huzai ta ce, 

“To yanzun malam ya za a yi kenan?”

Nisawa yayi da fadine,

“Sai dai shi ta ɓangaren Auwal ɗin. Amma ta nata bana jin akwai abinda zai yi tasiri in har bana ganin komai akanta. 

Zan baki laya kisa a ƙarƙashin filon da zai dinga kwanciya. Sannan kuma da turaren da za ki dinga shafa mishi a fuska. Za ki bani labari.”

Ya ƙarasa maganar yana wata ‘yar dariya. Murmushi suka yi. Suka karɓi duk magungunan da ya ce ɗin. Ta sallame shi suka tafi. 

Gida ta fara sauke Huzai sannan ta wuce nata. Kayan kawai ta kai ɗaki ta shiga kitchen don tasan Auwal zai dawo cin abincin rana wajenta. 

Tana aiki tana murmushi. Nishaɗi take ciki marar misaltuwa. Nan da ƙarfe huɗu zata kira Auwal da nata. Daren yau nasu ne su kaɗai.

**** 

Zaune take inda tai sallar Asr tana karatun Qur’ani. Ta ji ƙarar mashin ɗin Auwal. Ta yi mamakin dawowarshi a dai dai wannan lokacin. 

Sai da ta kai aya sannan ta rufe. Ta mayar da Qur’anin inda take ajiye shi. Da hijabinta a jikinta take fitowa. 

Tana zuwa falo ta ji yana ƙwala mata kira. Sauri ta ƙara tana fita tsakar gidan. 

“Sannu da zuwa.”

Maimakon ya amsa ta sai cewa ya yi, 

“Ina dawud?”

Da mamaki ta ce, 

“Ya fita. Lafiya dai ko Abban Sajda?”

Kallonta ya yi.

“An ɗaura min aure ƙarfe huɗun nan. Ɗakinshi ya fi na Tayyab girma. Ina so ya kwashe kayanshi ne su haɗe waje ɗaya. A ɗakin zata tare.”

Lumshe idanuwanta ta yi. Wani azababben kishin Auwal da fargaba na ziyartarta. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un take karantawa a zuciyarta. 

“Magana nake fa. Kina jina kinyi shiru.”

Idanuwanta ta buɗe akan fuskar shi. Muryarta a dishe ta ce, 

“Kasan Dawud tun da aka yaye shi baya iya bacci da motsin wani a kusa da shi. 

Bazai iya haɗa ɗaki da kowa ba. Ka yi haƙuri tunda ɗakin su Sajda ya ma fi nashi girma. Sai su dawo nawa ta zauna a ciki.”

Kafaɗa ya ɗan daga alamar matsalarta ce. Kafin ya ce, 

“Duk yadda kika gani. Ina son samun empty ɗin ɗaki zuwa jibi.”

Bai jira amsarta ba ya juya. Idanuwanta kafe kanshi har ya hau mashin ɗinshi ya ja shi yana fita daga gidan. 

Nan inda take tsaye ta durƙushe tana haɗe kanta da jikinta ta saki wani gunjin kuka. Gaba ɗaya duk wani abu da ta dinga haɗiya ne take amayarwa yau. 

Cikin sati uku duniyar ta birkice mata. Kuka take ba tare da ta samu wanda zai lallashe ta ba. Bata ji sallamar Dawud ba. 

Sai hannunshi ta ji ya dafa kafaɗarta. 

“Ummi….. A rana kike? Menene? Me akai miki?”

Ɗagowa ta yi ta kalli ɗan nata. Kanta zata mayar. Ya sa hannuwanshi kan kafaɗarta yana riƙeta. 

“Ummi ki faɗa min menene?”

Ta kasa magana saboda ɗacin da zuciyarta ke mata. Hawaye kawai ke zubar mata wani na bin wani. Sai sauke ajiyar zuciya take.

Hannuwanshi ta kama tana haɗe su da fuskarta. Comfort take nema. Bata da wajen wanda zata juya daya damu sai ‘ya’yanta. 

Miƙewa dawud yayi. Ya kamo Ummi ya ɗago da ita. Falo ya jata. Ya zaunar da ita kan kafet sannan ya fito zuwa kitchen.

Ruwa ya ɗiba a kofi ya koma ya zauna kusa da ita. 

“Ummi ga ruwa.”

Karɓa ta yi ta shanye duka ta ajiye kofin tana maida numfashi. Cikin taushin murya Dawud ya ce, 

“Ki faɗa min ko menene.”

Yanayin da ta ji a muryarshi ya sa ta saka hijabinta ta goge fuskarta. Muryarta a dakushe saboda kukan da ta yi ta ce, 

“Bansan me yasa abin yake damuna ba. Ba abin ɗaga hankali bane. Abban ku ya ƙara aure. 

Zata tare jibi.”

“What?!!! Abba yayi me? Bana ganewa Ummi?”

Duk da a nutse yai tambayar akwai tashin hankali cikin muryarshi. Murmushin takaici ta yi hawaye na zubar mata. 

“Aure dawud. Jibi zata tare.”

Ya kai mintina biyar yana tauna maganarta da tunanin abinda hakan yake nufi.

“Rayuwar mu zata canza da auren nan Ummi.”

“Na sani. Na sani sosai. Ta riga da ta canza tun satika uku da suka wuce.”

Shiru ya sake yi kafin ya ce, 

“Kar kisa damuwa a ranki. Karki bari halayyar Abba ta dame ki. Kwanciyar hankalinki da lafiyarki na da muhimmanci a wajenki. 

Karki saka mana su a haɗari Ummi. Mun rasa Abba. Muna…..”

Girgiza mishi kai take tana katse shi da faɗin, 

“In ji wa ya ce maka kun rasa abban ku? Don ya ƙara aure baya nufin kun rasa shi.”

Runtsa idanuwanshi yayi ya buɗe su. 

“Muna ganin shi ne kawai. Yau sati nawa rabon da ya zama Abban mu? Yai mana abinda muka san yana cikin rayuwar mu? 

Bama sanin fitarshi. Ko sallah ya daina tashin mu da Asuba. Ummi baya hira da mu. Baya jin damuwar mu. Ya daina damuwa. In bamu rasa shi ba me muka yi?”

Yanayin da ya ƙarasa maganar da shi ta sake karya mata zuciya. Muryarta na rawa ta ce, 

“Allah yana tare damu. In ba mu saki addu’a ba ba za mu rasa ƙarfin zuciyar cinye wannan jarabawar ba. Allah ya sauya mana ƙaddarar nan da mafi alkhairi.”

A sanyaye ya amsa da amin. Yana ɗorawa da, 

“To ki daina kukan nan. Bana so Ummi. Duk hawayenki da ke fita yana goge min Abba ne.”

Ware idanuwanta ta yi kan Dawud. Babu wasa ko dana sani a maganar da yayi. Tana karantar yadda matsayin shi ya fi mata na kowa a duniya. 

Hannu ta sa. Sosai take goge fuskarta. Duk da jarabawar nan da take ciki. Da yadda duniyar ta birkice mata tsakaninta da mijinta inta duba sai ta ga kyautar da Allah yai mata. 

Tana da yara har huɗu. Ga dawud a gabanta da zai yi komai da tasan bai saɓa ma addinin shi ba don farin cikinta. Ko da Allah ya ƙwace mata farin ciki ta ɓangaren mijinta don ya jarabata. 

Sai ya buɗe mata ƙofar samun wani ta hanyar ‘ya’yanta don ta samu ƙarfin cinye jarabawar. Murmushi ta yi da ya kai har zuciyarta. Tana ma Allah godiya. 

Godiyar kyautar ‘ya’yan da yai mata da kuma bata fahimtar ba dukkan farin ciki ta rasa ba. Dawud take kallo. 

Murmushinta ya bayyana wani a fuskar shi. Abinda ta kwana biyu bata gani ba. 

“Yawwa ummi har kin ƙara kyau.”

Dariya ta yi. 

“Allah ya albarkaci rayuwarka da ta ‘yan uwanka. Allah ya haɗa min kanku kar Ya bari komai ya cutar min da ku.”

“Amin Ya Rabb. Allah ya kare mana ke Ummi. Ya baki shekaru masu yawa tare damu cikin lafiya.”

Amsa addu’ar shi ta yi ta ce, 

“Yamma na yi. Bansan me zan dafa bama.”

“Ai mana sakwara Ummi.”

Mikewa tayi tana fadin. 

“Taso ka yo mana cefane.”

Ba musu ya miƙe. Jiranta yayi ta shiga ɗaki ta fito mishi da kuɗin tana faɗa mishi abinda zai siyo mata. Yana tafiya ta sauke ajiyar zuciya. 

“Allah ka bani ƙarfin zuciyar juriya da cinye jarabawar ka.”

Don tasan ‘ya’yan ta na buƙatar kulawarta fiye da koyaushe. Saboda sun rasa ta mahaifinsu a yanzun. Ita kaɗai ta rage musu.

Tsakar gida ta fita ta ci gaba da hidimarta. Tana wa kanta alƙawarin ƙin sake bari damuwar Auwal da kishin shi na zama komai na rayuwarta.

**** 

Tun da ta sauke Auwal kasuwa take dariya kan hanyarta ta dawowa har ta iso gida. A daren jiya ta tabbatar ba zata taɓa iya rabuwa da Auwal ba. 

Soyayyar shi ba mai mantuwa bace. Ta dare ɗaya ta samu amma tunanin rasa ta ba ƙaramar fargaba yake shigar da ita ba. 

Gara komai nata ya ƙare. Amma Auwal ya riga da ya zama nata. Zata kuma ɗaura ɗamarar yaƙi da duk wata barazana da zata iya kawo rabuwar su. 

Zata kuma fara da matarshi. Tunata kaɗai yasa zuciyarta raɗaɗi. Kishi na turnuƙe ta.

Alƙawari ta yi wa kanta daga yau har ranar da zata yi nasarar korarta daga gidan Auwal ba zata sake samun wata kulawa tashi ba.

****

Aisha ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Da duk yaran basa gidan sa’adda aka zo jera kayan ɗakin Beeba. Ba wani abu suka yi ba. 

Kafet suka saka cikin ɗakin. Katifa da kayan kallo sai labule. Ta amsa sallamar su ta gaishe da su. Basu amsata ba, yanayin kallon da suke mata ne yasa ta koma ɗaki ta yi zamanta. 

Ta yi niyyar kai musu ko da ruwa ne. Gudun wulaƙanci yasa ta ƙyale. Suka gama tana jin kulle ɗakin da suka yi da takun tafiyarsu. 

Bata fito ba har yara suka dawo daga Islamiyya. Zulfa ta cire hijabinta ta ce 

“Ummi waya kulle ɗakin mu da kwaɗo?”

“Bana ce muku ba ɗakin ku bane yanzun? Abba ya ƙaro muku wata Ummin ita zata dawo nan yau. Ko kin manta.”

Ɗan ɓata rai ta yi. Bata ce komai ba ta samu waje ta zauna. Sajda ce ma ta ce, 

“Ummi mu bama son a kawo wata. Ko Yaya zulfa?”

Kai zulfa ta ɗaga mata. Tana gudun faɗan Ummi ne shi yasa bata faɗi haka ba. Amma har ranta bata son a kawo musu wata. 

Kuma a rasa inda zata zauna sai ɗakin su. Kallon su Aisha ta yi. Ba su kaɗai bane basa son zuwan wata cikin gidan nan. Ba zata munafunci kanta ba. 

Ko da wasa bata ƙaunar auren nan. Inda za a bata zaɓi zata gujema kishiya komin alkhairin da ke cikin aurenta kuwa. Don kishin da take ji Allah ne kaɗai yasan yawan shi. 

Bata da amsar da zata ba su Sajda da ke kallonta. Don haka ta ce, 

“Ku wuce ku ciro uniform. Ku linke su ku sa a cikin jaka fa.”

Miƙewa Zulfa ta yi. Sajda dama bata zauna ba. Ta sauke numfashi kawai ta wuce. 

*****

Ana idar da sallar Isha’i Dawud da Tayyab suka shigo da sallama. Suka gaishe da Ummi suka zauna ƙasa suna ci gaba da hirar su . 

“Ji nake dama ni ne zan fara WAEC next month. Na gaji da uniform.”

Dariya Dawud ya yi. 

“Yaro da sauranka. Shekara biyu nan gaba.”

Ummi da ke zaune ta ce, 

“In Allah ya kaimu Dawud. Ku yi ta faɗan abu kamar ku kuke da shi a hannunku.”

Murmushi Dawud ya yi. 

“In Allah ya kaimu….”

Buɗe baki Tayyab yayi zai yi magana suka ji sallamar mata. Miƙewa Ummi ta yi ta fita tana amsawa. Mata ne su biyu. Yanayin shigar ɗayar yasa cikinta yai wani irin ƙullewa. Gaskiyar da take ta sharewa ce tun ɗazun ta bayyana a gabanta. 

Tasan ya kamata ko da sannu da zuwa ne tai musu. Amma zafin kishin da ke cinta ya hana. Sakin labulenta ta yi tare da yo baya ta dawo cikin ɗaki. 

“Su waye Ummi?”

Tayyab ya tambaya. 

“Matar Abban ku ce aka kawo.”

Ta bashi amsa cikin muryar da bata gane tata bace ba. Babu wanda ya sake magana a cikinsu. Kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarshi. 

Ta cikin labulen da idon Dawud ke kafe kai ya ga kamar motsin mutum. Nutsar da hankalin shi yayi. Ya ga da gaske mutum ne ƙofar ɗakin su a durƙushe. 

Miƙewa yayi da hanzari ba ma ya jin kiran da Ummi ke masa tana tambayar ina za shi, ya ƙarasa bakin ƙofa. Labulen ya ɗaga . 

Ya sauke idanuwanshi kan Huzai da ke tsugunne tana barbaɗa musu wani abu a ƙofar ɗaki. 

“Me kike zuba mana? Me ma ya kawo ki ƙofar ɗakinmu?”

Ɗago kai ta yi da alamar tsoro na ‘yan daƙiƙu a fuskar ta kafin ta nutsu. Wani kallon banza tai ma Dawud ɗin. 

“Sai na ji makara. Fitsararre.”

Gaba ɗaya yanayin matar bai masa ba. Daga fuskarta da ta ci bleaching da laɓɓanta baƙaƙe. Zubin karuwa sak. Ummi ya ji a bayanshi ta zuro kai tana faɗin,

“Dawud meke faruwa ne?”

Kallom Huzai take yi. Ta gane ta, har da su suke mata kallon banza ɗazu da suka zo jere. Idanuwan Dawud akan Huzai ya ce ma Ummi, 

“Wani abu take zuba mana a ƙofar ɗaki.”

Sosai Ummi ke kallonta. Kishinta bai kai na ta zauna tana musayar yawu da matar da bata ma san matsayinta wajen kishiyarta ba. 

Ita kanta kishiyar bata kai tai musayar yawu da ita ba. Don Aisha mace ce da bata son raini ko kaɗan. A duk inda take tana riƙe girmanta. 

Hannun Dawud ta kama ta janyo shi. Ta gyara labulen. Buɗe baki yayi zai yi gardama Ummi tai masa alama da hannu da yai shiru kar ya ce komai.

Janshi tai ta zaunar dashi inda ya tashi. 

“Ummi wani abu fa ta zuba mana a ƙofar ɗaki. Wallahi na ganta sa’adda na fita.”

Sauke numfashi Ummi ta yi. Bata san me yasa tunanin cewar canzawar Auwal harda asiri a ciki bai zo mata ba sai yau. Ta sake tsorata ba kaɗan ba. 

Sai dai tana dannewa ne. Bata son ko Dawud ya gane tsoron da take ji. 

“Babu abinda zai faru in sha Allah. Duk wanda zai fita daga ɗakin nan yayi addu’a sosai. Kuma ku sake riƙe addu’a fiye da komai. Ka ga bana son tashin hankali da daren nan. Idan hira za ku yi ku zauna abinku. In kuma ba za ku yi ba, kowa ya wuce ɗakinshi. Ku yi addu’a ku kwanta.”

Dawud ya fara miƙewa ya tsaya a bakin ƙofar yana addu’a kafin ya fice. Ranshi a ɓace yake, don ko sai da safe bai ce musu ba. Sannan Tayyab yaima su ummi saida safe shi ma ya fice. 

Sajda ta ce, 

“Ummi bari in ce ma yaya sai da safe in dawo.”

Girgiza mata kai ummi ta yi. 

“Ki ƙyale shi kawai. Ku tashi mu je in muku shimfiɗa kuma ku kwanta. Kun ga gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta ko?”

Tashi suka yi. Tana gama musu shimfiɗa ta tsaya sai da suka yi addu’a suka shafe jikinsu. Sannan ta sake yi musu ta fito falo ta zauna. 

Zuciyarta ke wani irin dokawa. Kamar zata fito daga ƙirjinta. Addu’ar duk da ta zo bakinta ita take yi. Bata san iya lokacin da ta ɗauka a zaune a falon ba. 

Kafin ta ji sallamar Auwal. Ɗago kai ta yi tana kallonshi. Yau kwana biyu kenan rabon da ta saka shi a idanuwanta. Kafin ta ga matar da ke biye da shi. 

Kayan jikinta ta gane. Zuciyarta ta sake ci gaba da dokawa. Kamar ɗakinta haka ta samu kujera ta zauna tana ƙare ma Aisha da duk wani abu da ɗakin ya ƙunsa kallon raini kafin ta taɓe baki. 

Kan hannun kujerar da ta zauna nan Auwal ya zauna yana wani murmushi da Aisha ta jima bata gani ba a fuskar shi. Ikon Allah kawai take kallo. 

Tsoro na sake cika zuciyarta. Gashi nan tana kallon yadda aka gama mallake mata miji. An mayar da shi wata halitta daban. Kamar wanda aka saka ma batiri.

Komai nashi ya sha banban da na Auwal ɗin da ta sani. Fari ta ga Beeba ta yi tana faɗar wani abu ƙasa-ƙasa da ya ba Auwal ɗin dariya. 

Kamun ya juyo yace. 

“Aisha wannan ita ce matata. Hajiya Beeba. Ku dukkan ku ba yara bane balle in ce zan tsaya ɓata bakina wajen yi muku nasiha. Sai ki kiyaye bana son jin wata fitina ta taso daga ɓangarenki ko ta yaranki. Na san Hajiya Beeba mace ce mai kirki da hankali. 

Abinda na zo gaya miki kenan. Sai da safe.”

Ya ƙarasa yana miƙewa da kallon beeba. Aisha kam tun da sunan ‘Hajiya Beeba’ ya ƙaraso kunnenta ta daina gane abinda yake faɗa. Hargitsin da zuciyarta ta shiga ba ɗan kaɗan bane. 

Matar nan da Auwal ke gudu kamar annoba. Matar da ya bar aiki don guje wa faɗawa tarkonta ce yau a cikin gidansu. Take samun nasarar fara tarwatsa musu zama. 

Giccin su kawai ta gani. Don ko saida safen kissar da Hajiya Beeba ta yi mata bata ji ba. Kallon su take, ƙarshen maganar Auwal ɗin kawai ta ji 

“…….ki ƙyaleta. Wulaƙanci ne. Kuma wallahi bazan ɗauke shi ba.”

Kafin ya wuce daga ɗakin rai a ɓace. Kallon sama da ƙasa Beeba ta sake yi ma Aisha tana wani taɓe baki kafin ta bugi cinya ta fice daga ɗakin. 

Da gudu Aisha ta miƙe ta nufi ɗakin baccin ta. Su Zulfa na ta bacci kan katifarsu. Banɗaki ta wuce. Bata damu da hawayen da ke zuba daga idanuwanta ba. 

Ta ci gaba da ɗaura alwala. Wannan hawayen ta san ba na kishi bane. Na damuwa da tashin hankali da tsoro ne. Abin ya fi ƙarfinta. 

Kukanta zata miƙa wajen Allah. Mai komai. Mai kowa, Shi ya ɗora mata wannan jarabawar. Ya fi kuma kowa sanin dalilin ƙaddarar da ke faruwa da rayuwar su. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 6Rayuwarmu 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.