Skip to content
Part 22 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Graduation ɗinmu ne fa. Amma kalli yadda gaba ɗaya makarantar hankalin kowa ya koma kan Yaya.”

Asad ya ƙarasa maganar yana dariya. Da murmushi a fuskar Aseem ya ce, 

“Nasan abinda zai faru kenan ai.”

Agogon hannun shi Mamdud ya duba, lokaci na ƙurewa, shi kanshi so yake ya wuce tasu makarantar. Inda Labeeb yake yana gaisawa da mutane ya ƙarasa. 

“Ina son wucewa school ɗinmu.”

Daƙuna mishi fuska Labeeb yayi. 

“Ka bari muyi hotuna kawai, sai mu wuce tare mana. Bana son su Asad su ji kamar bana nan.”

Sosai Mamdud ke kallon shi. Har ranshi baisan me yasa ranshi ya sosu da maganar Labeeb ɗin ba. 

“Nah, ka barshi kawai. Ka zauna nan din har a gama, muma ba wani abu za muyi ba. Hotunan ne kawai.”

Sauke numfashi Labeeb yayi. 

“Ka tabbata?”

Kai Mamdud ya ɗaga mishi. 

“Kuma mota ɗaya muka ɗauko. Ko in sauke ka in dawo?”

‘Yar dariya kawai Mamdud yayi ya juya yana faɗin, 

“Karka damu fa”

Su Asaad ne suka hango zai tafi. 

“Come on. Ina za ka je kuma?”

“Makarantar mu.”

Aseem ne ya karɓe zancen da faɗin, 

“Makarantar ku is lame, ka tambayi Yaya. Ka zauna nan mana.”

Murmushi kawai yayi, bai ce musu komai ba ya wuce abinshi. Mashin ya tare yayi makarantar su. Harya isa yana jin yadda ranar ke da muhimmanci a wajen shi. 

Saboda ya taka wani mataki a rayuwar shi da bai taɓa zaton zai zo cikin sauƙi ba. Amma baida kowa da zai yi murnar ranar da shi. 

“Mamdud Ibrahim Maska.”

Ya furta a hankali yana yin ɗan murmushi. Labeeb da yai alƙawarin zama ɗan uwanshi, abokin shi, ko shi baya tare da shi a wannan ranar. 

Ya nuna mishi banbacin jini da bare. Baya son jininshi su ji kamar baya rayuwar su. Ranshi ƙara ɓaci yake. Ko da ya shiga cikin makaranta kowa ka gani da walwala da fara’a a fuskarshi. 

Wasu mata guda biyu ‘yan ajinsu da sukan gaisa sosai suka ƙaraso wajen shi. 

“Mamdud, ya Rabb, ina El-Maska? Ka ga yadda na gama yi ma yayyena kuri muna class ɗaya da kai. Yau har hoto za muyi da shi. Please karka ce min ba zai zo ba.”

Cewar Fadila. Amina ta jinjina kai tana ɗorawa da faɗin, 

“Wallahi nima na sa rai. Ka ga yadda nake crushing akan shi kuwa. Time ɗin yana school ɗin nan tsoro ke hana ni zuwa in gaishe da shi.”

Kallon su kawai Mamdud yake. Maganganun su kamar tunzura shi suke yi. Su kaɗai ne yake ɗauka suna mishi magana don shi. 

Sai yau ya gane duk kulashin da suke saboda Labeeb ne. Kamar duk wani wanda zai zo kusa da shi a aji basuda zance sai na El-Maska. Wata tambayarsu, wani komai El-Maska dai. 

Ko wanda ba ‘yan ajin su ba. Zasu zo suna mishi tambayoyi. Babu abinda ya fi mishi ciwo irin yadda suke tambaya sun san kaf ‘yan gidan su Labeeb. Sun rasa inda yai fitting. 

“Ba zai zo ba.”

Ya amsa su can ƙasan maƙoshin shi. Yana kallon yadda ko kaɗan basu ji daɗin amsar shi ba. Juyawa suka yi suka yi tafiyar su ba tare da sun ce mishi komai ba. 

Su Ahmad ya hango suna ɗaukar hotuna don haka ya taka ya ƙarasa wajen su. 

“Hey Maska, what’s up?”

Samuel ya tambaya yana miƙo mishi hannu suka gaisa. 

“Nothing much.”

Ya amsa. Suna gaggaisawa da su Ahmad. Kafin suka soma ɗaukar hotuna. 

“Maza ina El-Maska? Ba zai zo ba?”

“Yep.”

“Oh man. Kasan class ɗaya suka yi da sister ɗina. I am a big fan. Na so yau mu gaisa.”

Mamdud bai amsa su ba. Kawai barin wajen yayi. Ya gaji da jin yadda duk wanda zai nufo shi ba shi da wanda zai kira sai El-Maska. 

A bakin gate ya ci karo da motar Labeeb. Tsayawa yayi da mamaki har suka yi parking. Suka fito, har da Zainab da ta kalle shi. 

“Menene kake kallon mu haka?”

“Bai ɗauka zamu zo bane.”

Asad ya faɗi yana ɗaga ma Mamdud gira. Cikin sanyin murya Mamdud ɗin ya ce, 

“Da baku zo ba. Really ba wani babban abu bane ba. Nima tafiya zanyi yanzun.”

“Yaya ka ji shi fa. Wallahi ku sa a ranku, wanda bai zo wajen graduation ɗina ba kar ya sake min magana. 

Kasan yadda nake so in ga na gama saka uniform kuwa?”

Zainab ta tambaya tana ware idanuwa. Da murmushi Labeeb ya ce, 

“Babban abune family su zo ranar big day na ɗan uwansu. Ka fara sabawa da hakan.”

Buɗe baki zai yi yai magana ‘yan ajinsu suka baibaye su suna son yin hoto da Labeeb. Dole ya je wajen su. Su Asad suna gefe suna hirarsu shi da Aseem. 

Zainab ta zagaya ta buɗe motar. Ta fito da gifts guda shida a hannunta anyi wrapping ɗinsu. Asad ta fara bawa guda biyu, tare da sumbatar kuncin shi. 

“Happy graduation. Allah ya sanya alkhairi.”

“You are the best sis…. The best in the world”

Murmushi kawai ta yi, ta ba Anees nashi da ta zo sumbatarshi ya tare ta. 

“Zaki shafamun jan baki Zee Zee. Kalla fuskar Asad.”

Da sauri Asad ya ware idanuwanshi yana sa hannu da goge fuskarshi. 

“O. M. G zeezee….”

Dariya suka kama yi mishi su dukkansu, kafin Anees ya sumbaci goshinta. 

“Thank you.”

Daƙuna mishi fuska tayi, mota ta sake komawa ta buɗe, ta ƙara ɗauko wani babban gift ɗin ta haɗa da biyu na hannunta. 

Ta dawo ta ba Mamdud.

“Zee Zee really…..shi guda uku fa.”

“Ba kwa taya ni assignment. Girkinku. O. M. G ban shirya wankin ciki ba.”

“Anees kana ji ba. Na janye kalamaina. You are the worst.”

Juya mishi idanuwa tayi. 

“Ko me ka ce. Yaya Mamdud congrats. Kai ne best bro ɗina, my fav…..”

“I am so jealous.”

Asad ya faɗi. Mamdud kam kallon zainabU yake ya rasa abinda ya kamata ya ce. Yana jin bai kyauta ba da yai musu mummunar fahimta ɗazu. 

Karamcin nan da suka yi mishi, bai da kalaman da zai fassara muhimmanci shi. Akwai wani ɓangare tattare da zainab da ba kowa yake gani ba. 

Yasan ta ƙara mishi gift ne saboda ba zata iya sumbatarshi kamar yadda taima su Anees ba. Bata kuma so ya ji bambancin. 

“Na gode Zee Zee.”

Murmushi ta yi tana maida hankalinta kan Labeeb da yake ta ɗaukar hotuna da mutane. Takawa ta yi ta ƙarasa inda yake, murmushi tai ma mutanen har duka haƙoranta suka bayyana sannan ta kamo hannun Labeeb tare da faɗin, 

“Family time Yaya.”

Bai yi musu ba ya bi Zainab ɗin. Ya ji daɗi, don ya gaji dama. Hayaniyar ta soma damunshi. Hotuna suka yi da su Mamdud sannan suka shiga mota suka yi gida abinsu. 

***** 

Bacci yake mai ƙarfi yaji ana ɗirka mishi duka. Da ƙyar ya iya buɗe idanuwanshi da suke cike da bacci ya sauke su kan Zulfa da ke zaune gefen gadon shi. 

“Ka tashi…”

Ta faɗi, juyawa yayi, yana jan mayafi ya rufe fuskarshi. Mayafin ta kama ta ja. 

“Allah zan koma gida in baka tashi ba.”

Yamutsa fuska Labeeb yayi. Baccin da ya samu da daddare ba shi da yawa. Shi yasa suna dawowa ɗazu ya kwanta. Da tunanin Zulfa ya kwanta. 

Yasan yana ƙaunar su Zainab, amma Zulfa waje take da shi daban a zuciyarshi da ba zai faɗu ba. Zai iya cewa tun tana da shekaru biyu a duniya. 

Ita tasa yake yawan zuwa gidan su. Dalilin ta yasa ya shaƙu da ummi. Ita ce take cike mishi wasu wajajen da Mummy ta kasa cikewa. 

“Me zanyi idan na tashi?”

“Labari za mu yi…Yaya Labeeb ka tashi!”

Miƙewa yayi ƙasa-ƙasa yake faɗin, 

“Oh God.”

A fili kuma ya ce, 

“Zanzo yanzun.”

Dariya ta yi da ta bayyana murmushi a fuskarshi. 

“Karka koma bacci fa.”

“Bazan koma ba, wanka zanyi in zo.”

Miƙewa ta yi ta fice da faɗin, 

“Tam kai sauri.”

Wankan yayi, sai da ya fito yake mamakin yamma da tayi haka. Sallar Asr da baiyi ba yayi, tukunna ya fita falo. Kowa na nan banda Arif. 

Ta ɓangaren Zainab za a iya cewa surutunta da shiga mutanenta sai wanda ta zaɓa. Miskilanci ne kawai, Arif kam haka halittarshi take. Kwaramniya bata dame shi ba. 

Ba kuma ya son hayaniya. Ƙarasawa Labeeb yayi ya zauna kan kujera kusa da Zulfa. 

“Wai me kuke kallo haka? Kowa ya nutsu?”

“Yaya kai shiru mu ji.”

Zainab ta faɗi. Shirun yayi ya kai hannu ya ɗauki cookies ɗin da Zainab ke ci guda ɗaya. Janye kwalin tayi ta mayar da shi ɗayan ɓangaren. 

“Zeezee rowa. Guda ɗaya zaki bani kika hana ni.”

Anees ya faɗi. 

“Bana ce in baka kuɗi ka siyo ba. Harma ka ƙaro mana ka ƙi? I don’t share my cookies.”

“Ku ƙyale min ƙanwa. Kun cika kwaɗayi. El-Maska mayar mata da abinta.”

Mamdud ya faɗi yana kallon Labeeb. Gutsuran cookies ɗin yayi. 

“Ku biyun duka marowata ne ai. Ni bazan mayar ba.”

Miƙa ma Zulfa sauran yayi, cookies ba damunta yayi ba. Ta karɓa ta gutsura ta mayar mishi. 

“Cinye duka.”

Girgiza mishi kai tayi tana daƙuna fuska. Karɓa yayi ya saka sauran a bakinshi duka. Sallama suka ji. Da gudu Asad, Anees da Zainab suka miƙe suna tarar Mummy kamar yara ‘yan shekara uku. 

Dariya Mummy tayi da Labeeb ya ji har cikin zuciyar shi. Shi kanshi kula yayi ya miƙe tsaye bai kuma san lokacin da yai hakan ba. Zai iya alaƙanta shi da cewar ya kusan wata biyu bai ganta ba. 

Kewarta waje take da shi a zuciyarshi da wanda ya san ma’anar rashin uwa ne kawai zai fahimta. Yanzun ganinta bai taɓa ko’ina na ɓangaren ba, sai ma ƙara mishi ciwo da yayi. 

“Mummy mun yi missing ɗinki sosai. Don Allah karki koma. Please… Pleaseeeee.”

Asad ya faɗi yana sumbatar kuncin ta. 

“Yes please. Mummy karki koma.”

Zainab ta faɗi kamar zata yi kuka. Anees ya kasa daina murmushi.

“Ku kam. Ko hutawa bata yi ba. Mummy sannu da zuwa.”

Labeeb ya faɗi, da murmushi a fuskarta ta sauke idanuwanta akanshi. 

“Labeeb. Yawwa, Zulfa ana nan kenan, Mamdud.”

Sannu da zuwa Zulfa da Mamdud suka yi ma Mummy. Takalmanta ta cire tana sauke numfashi a gajiye. Takawa ta yi tana nufar hanyar ɗakinta. Su Zainab na manne da ita kamar zasu koma cikinta. 

“Mummy graduation ɗinmu kika zo ko? Wallahi na ɗauka kin manta”

“Ba wani graduation. Ai angama, real party ance a bari result ya fito. Mummy zata yi spending time ɗin duka da mu ko?”

“Mummy ki ƙyale su Yaya Asad. Kinsan last exam ni na karɓi duka gifts ɗin da aka bayar na ‘yan class ɗinmu. Ban bude ba na ce sai kin dawo.”

Su dukkan su magana suke yi a lokaci ɗaya. Babu mai bari wani ya gama, duka so suke ta basu hankalinta. So suke ta saurare su. Shi kanshi labeeb dake tsaye yana binsu da kallo hakan yake so.

Hira yake so su yi da Mummy ko na minti sha biyar ne, su zauna waje ɗaya, suyi labari, ya ji muryarta, dariyar ta. Basu Zainab kaɗai ke buƙatar kulawarta ba.

Arif ne ya fito, kallon su Anees da mumy yayi. Ya ɗan sauke numfashi. 

“Sannu da zuwa.”

Ya faɗi ya raɓa su ya wuce kitchen, ya ɗauko lemo ya sake raɓa su ya wuce. Kwata-kwata babu shaƙuwa tsakanin shi da Mummy. Shi kamar ma bai damu ba. Banda gaisuwa babu abinda yake haɗa su har ta koma. 

Bai taɓa zuwa ɗakinta ba tunda ya fara hankali. Da idanuwa Mummy ma ta bishi har ya sha kwanar da zata kaishi ɗakinshi. 

“Mummy me za ki ci? Ni zan dafa miki.”

Zainab da Anees suka kwashe da dariya. Kallon su yayi. 

“Really guys? Ni abin bai bani dariya ba.”

Zainab tana dariya ta ce, 

“Mummy sai kin yi sati bakinki bai daina ƙauri ba.”

Duka Asad ya kai mata ta maƙale a bayan Mummy tana ihu. Hannuwa Mummy ta saka ta toshe kunnuwanta tare da faɗin, 

“Ku ji ni. A gajiye nake, jikina ciwo yake yi. Bacci zan yi.”

“Nooooooo!!!”

Suka faɗi a tare da ƙarfi, sake toshe kunnuwa Mummy tayi tana girgiza kai. Da sauri ta taka ta nufi ɓangarenta ta barsu a wajen. 

“Kun kore ta.”

Zainab ta faɗi tana hararar su.

“Ke kika koreta.”

Suka haɗa baki, suna zuba ma Zainab idanuwa. 

“Yaya kai musu magana.”

Zainab ta faɗi idanuwanta na cika da hawayen da basu da alaƙa da su Asad. Ƙarasawa labeeb yayi inda suke ya kama hannun Zainab. 

“Ku bari ta tashi bacci, sai ku bata duk labarin da zaku bata. Ba ku ga yau kwananta nawa bata gida ba? Kunsan akwai gajiya right?”

Ƙwace hannunta Zainab ta yi daga na Labeeb. 

“We are not four Yaya. Bata da lokacin mu. Bamu da muhimmanci. Ni dama gidan su Zulfa nake. I hate this house!”

Ta ƙarasa tana rugawa ɗakinta. Su Asad Labeeb suka kalla kafin Anees ya ce, 

“I need a fresh air.”

“Me too.”

Yana kallon su suka wuce suna ficewa daga ɗakin. Hannu yasa ya murza idanuwanshi yana jin kanshi ya soma ciwo. Da zuwan Mummy kaɗai yake bayyana shi in yana gidan. 

Yasan har ta tafi ba zai gane kan ƙannen shi ba. Kamar ciwon rashin Mummy da ke damunsu na lafawa ne in bata nan. Amma da ta zo duk sai ta tayar musu da shi ta birkita mishi su. 

Wani ɓangare na zuciyarshi ya ji daɗin zuwanta, ya ji daɗin ganinta. Amma wani ɓangaren can ƙasa yana jin wani abu na daban da bazai fassaru ba. 

Yana jin abinda rashinta yayi musu, yana kuma jin abinda zuwanta yake musu. Yana nuna musu abinda sai dai su kalla daga nesa yawun su ya tsinke don ba zasu taɓa samu ba. 

Juyawa yayi, ya kalli Zulfa dake zaune hankalinta na kan TV ita da Mamdud. Hannunshi yakai kan goshin shi. A hankali yake faɗin, 

“Zulfa na nan. El-Maska kai haƙuri har zuwa dare. Zaka manta wannan ya faru, yanzun, right now you can be El-labeeb, you need to be El-labeeb.”

Numfashi ya ja yana sauke shi da sauri-sauri. Yana jin jikinshi har rawa yake saboda buƙatar abinda zai sa komai ya ɓace. mace, ƙwaya, giya, ko me ya samu a yadda yake jin nan dai dai kenan. 

Inda yake kusa da zulfa ya koma ya zauna. Ganin yadda jikinshi ke ɓari a hankali yasa Zulfa kai hannu ta taɓa goshin shi. 

“Yaya zazzaɓi kake ko?”

Mamdud ya juyo da sauri ya kalle su. Girgiza ma Zulfa kai yayi. Wannan zazzaɓin ba irin wanda ta sani bane. 

“In ji wa. Lafiyata ƙalau, ɗauko mana lemo a fridge ɗin kitchen.”

Da sauri ta miƙe tana nufar kitchen ɗin. Mamdud ya kalli Labeeb. 

“Lafiyar ka kuwa?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa yayi. 

“Usual drama ɗin da zuwan Mummy yake haifarwa ne. I need some buzz.”

“No you don’t. El-Maska sau nawa zan maka maganar nan? Wannan ba…..”

Zulfa ce ta dawo hakan yasa Mamdud yin shiru yana ma Labeeb kallon da ke fassara basu gama maganar ba. Juya mishi idanuwa kawai Labeeb yayi. 

Mamdud baya gajiya da hana shi shan kayan maye. Musamman giya da yake ganin illa zata yi mishi nan gaba. 

“Guess me? Mu je mu sha ice cream.”

“Yeeeeeeeeee. I love you.”

Zulfa ta faɗi tana miƙewa da gudu ta ruga ɗakin Zainab. Takan kwana nan wasu lokutan in ta zo, tana da ɗakinta a gidan. 

“Ki taho Ya labeeb zai kaimu mu sha ice cream.”

Saukowa Zainab ta yi daga kan gadon ta saka hannu ta goge fuskarta da har ta yi ja saboda kukan da ta yi. Abinka da farar fata. Muryarta a dishe ta ce, 

“Minti biyar. Yanzun zan fito.”

Kai zulfa ta ɗaga mata, ta wuce ɗakinta ita ma don ta sake kaya. Labeeb kuma ɗakin Arif ya nufa. Sai da ya ƙwanƙwasa ya ce mishi ya shiga tukunna. 

Yana zaune a ƙasa da drawing book yana zane. Ƙarasawa Labeeb yayi ya tsugunna gefen Arif yana kallon abinda yake zanawa. 

“Na kasa getting fuskan right tun ɗazu. Na kasa connecting da ita.”

Arif ya faɗi yana wasa da pencil ɗin da ke hannunshi. Littafin Labeeb ya ɗauka yana jin yadda zuciyarshi ta matse gefe ɗaya. Sak kayan dake jikin Mummy ne, shigarta da ta dawo da ita, har da takalman da ke ƙafarta. 

Amma bai ƙarasa ba, fuska kaɗai ta rage, ba kyan zanen bane ya tsaya mishi. Yasan arif, yana kuma kula da ya fi yawan yin zane in Mummy na nan fiye da in bata nan. 

“Arif….”

Ya faɗi a hankali. Girgiza mishi kai Arif yayi. 

“Why Yaya? Saboda me zan kasa connecting da ita, Mummy na ce, kowa a class ɗinmu yana faɗan yadda yake son Mummyn shi. 

Komai Mummy. Komai Mummy, saboda me ni ma bazan zama kamar su ba? Mummynsu na kaisu school wasu time ɗin, Mummy bata san makarantar da nake ba.”

Runtsa idanuwa Labeeb yayi ya buɗe su, zama yayi babu shiri. 

“Don bata san makarantarku ba baya nufin bata damu ba kamar Mummyn ‘yan ajinku. Taka Mummyn is a very very busy Mummy…”

Katse shi Arif yai da faɗin, 

“Bana son busy Mummy, normal Mummy nake so Kamar nasu. Idan bazan samu ba na haƙura.”

Shiru Labeeb yayi yana jin yadda yake mugun buƙatar abinda zai mantar da shi duk wannan abin da ke faruwa. Kallon Arif yake da siraran hawaye suka zubo mishi, ya sa hannu da sauri yana goge su. 

“Wannan shi ne rayuwa. Ba ma iya samun duka abubuwa……”

Pencil ɗaya cikin wanda Arif ya zube a ƙasa Labeeb ya ɗauka. Ya ajiye littafin da ke hannun shi a ƙasa. Zanen da Arif bai ƙarasa ba ya yi wa wani irin kai.

Gefe ya sake zana wani abu da zai rantse ko kusa bai yi kama da mutum ba, ko cartoon bai taɓa gani mai kalar zanen ba. 

“Me kake yi?”

Arif ya buƙata da murmushi a muryarshi. 

“Zane nake yi.”

Hula yayi akan abinda ya gama zanawa, sannan a gefe ya ƙara zana wasu. Sunaye ya rubuta a jiki, da Arif ya kwashe da dariya. 

“Banyi kama da wannan ba.”

Hannu Labeeb yasa ya ɗan daki kafaɗar Arif. 

“I am not that bad, wannan sunyi kama da su Anees.”

Sosai Arif yake dariya. 

“Mummy zata cire maka kai in ta ga fuskar nan.”

Dariya Labeeb yayi. 

“Shi yasa ba zamu faɗa mata ba.”

Cleaner Labeeb ya ɗauka ya riƙe a hannu, fuskarshi babu alamun wasa yace ma Arif, 

“Duka nan mune, family ɗinmu ne, Dady, Mummy, ni, Asad, Anees, sai kai.”

Cleaner ɗin ya miƙa mishi, yana tura mishi littafin a gabanshi. 

“Goge Mummy da Dady.”

Da wani irin faɗuwar gaba Arif ya kalle shi.

“Saboda me zan goge su?”

“Saboda su duka basa zama tare da mu, su duka are very very busy Mum and Dad. Sai mu goge su saboda baka son very very busy Mummy. 

So, sai na ɗauka baka son very very busy Dady. Abinda baka so bana so, haka Zainab, haka Asad da Anees. So ka goge su kawai.”

Girgiza kai Arif yake yana kallon zanen, zanene, zanen da ko kusa bai yi kama da su ba, amma sunayen su da labeeb ya rubuta nasu a jiki ba zai iya goge ko mutum ɗaya ba. 

Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Bazan iya goge su ba.”

Hannu Labeeb yasa ya kama Arif ya juyo dashi. 

“Nasan wannan zanen ko worst cartoon channel ba zasu karɓe shi ba. Amma mu ne Arif, in wani ya ga wannan zai yi dariya. 

Wani ko a hannunshi ba zai riƙe ba, saboda munin zanen, amma kai ka kasa gogewa. Kasan me yasa?”

A hankali Arif ya girgiza mishi kai. 

“Saboda mu jininka ne, family ɗinka ne, muna nan, bama nan, muna da kyau, muna da muni, kana sonmu a haka. 

Muna nan, bama nan, duk inda zamu je da sonka a zuciyar mu, saboda kana tare damu a duk inda muke. Ba ka da normal Mummy, baka da normal Dady, baka da normal yayye, saboda mun girmi normal, kaima ba normal bane, look at you, you can draw cooly, kana da twin brothers. 

Wata rana Mumm zata zauna, Dady ma haka, amma yanzun zamu ci gaba da sonsu, da jiran su har lokacin ya zo.”

Kai Arif ya jinjina da murmushi ya ce, 

“I love you. I love ku dukkan ku sosai.”

Murmushi Labeeb yayi. 

“I love you more. Zamu fita shan ice cream, za ka je?”

Girgiza kai Arif yayi. Labeeb ya miƙe don yasan su Zulfa na can suna jiranshi. Gaba ɗaya ji yake kamar duk energy ɗinshi ya juye ma Arif. 

Lokutta da dama inda zaka tambaye shi ina yake samo kalaman da yake ma ƙannen shi magana da su zai ce maka suna zuwa ne daga ƙaunar su da yake yi. 

In ya zo zaɓi, zai bada rayuwar shi don farin cikinsu. Ficewa yayi ya ja ma Arif ƙofar. Mintina biyar Arif ya bashi kafin ya miƙe ya je kan drawer ɗin gadonshi da ya mayar book shelf ya zaro wani drawing book. 

Ya ɗauki pencils kala uku ya fita daga ɗakin. Ɓangaren Mummy ya nufa, da ƙafarshi bai taɓa takawa ba. Zuciyarshi dokawa take har ya kama handle ɗin a hankali ya tura. 

Tana kwance kan gado ta rufe jikinta da duvet, ƙarasawa yayi inda saitin fuskarta yake ya zauna a ƙasa ya baje littafin shi ya soma buɗe duka shafukan da zanukanta ne babu fuska ya soma ƙarasa su. 

Ɗaya bayan ɗaya, ba tare da ya kula da lokacin da yake tafiya ba. Sai da ya gama tas, sannan ya koma shafin farko inda yake blank ya rubuta ‘MY VERY VERY BUSY MUMY’. 

Yana gamawa Mummy na buɗe idanuwanta a hankali. Ta ɗan yamutsa fuska bisa ganin shi. Murmushi yai mata tare da faɗin, 

“I love you Mummy.”

Muryarta cike da bacci ta ce,

“I love you too.”

Miƙewa yayi ya ɗauki littafinshi da pencils ya nufi ƙofa, yasan yanzu zai iya zana fuskar Mummy ko a ina. Ya samu connection ɗin da yake nema. 

Yana fita ya ja ma Mummy ƙofa, ya ɗan ware ido. 

“Yaya Labeeb you are so normal.”

Ya faɗi yana dariya. Yana jin ƙaunar ɗan uwan nashi har ƙasan zuciyarshi. 

**** 

Wajen ƙarfe goma na dare, suna shiga mota shi da Mamdud ya sa key ɗin a jiki ya kunna yai wata dariya. 

“El-Maska is freeee.”

“Allah ya shirya mana kai. Har wani murna kake yi.”

Jan motar Labeeb yayi yana dariya. 

“Baka san zama El-labeeb da Mummy a gida ba ko? Awa biyu gaba ɗaya energy ɗinka sai ya ƙare. Gida huɗu za ka rabu, su Asad su ja biyu, Zainab da Arif. Goodness dole yau in wanke kaina.”

Girgiza kai Mamdud yayi. Takaici na hanashi magana. Alƙawari ne ya ɗaukarwa kanshi. Ba zai taɓa yin rayuwa irin ta El-Maska ba. El-labeeb na burge shi, yana ƙaunarshi. Yana fatan ya zama shi wata rana. 

Gidan Labeeb suka nufa, tun da suka yi parking Mamdud ke jin kiɗa da hayaniyar mutane na tashi. Ya sauke numfashi, suka fita. Labeeb ya rufe motar suka nufi gidan tare. 

Mutane ne cike, maza da mata, Musulmai da kiristoci da ba za ka gane bambancin su ba, saboda kusan shigar tasu iri ɗaya ce, kuma sun cure waje ɗaya.

Labeeb na shiga aka ɗauki ihu. Dariya yayi yana ɗaga musu hannu, kiɗan aka kashe gidan yai wani shiru. 

“Party ɗin yau is different. Kunsan me yasa?”

“Nooo!!!”

Suka amsa shi. 

“Saboda yau rana ce mai muhimmanci a wajen Mamdud Ibrahim Maska. So guys to Mamdud…..”

Ihu wajen ya dauka. 

“To Mamdud!!!”

Dariya Mamdud yayi yana rasa abinda zai ce, saboda bai taɓa zaton party ɗin yau nashi bane ba. 

“Music on! Have fun guys!!”

Kiɗa aka kunna, Labeeb ya ɗan dafa kafaɗar Mamdud da ke nufin ya ji daɗinshi. Ya wuce abinshi yana kama hannun wata yarinya suka soma rawa. 

Mamdud har mamakin yadda Labeeb ke rawa yake yi. Sam in ka ganshi wajen gidansu ko wajaje irin haka, ka kuma je cikin gidansu, zaka rantse mutane biyune daban-daban. 

Juyawa Mamdud yayi ya ci karo da wata yarinya da fuskarta kawai zaka kalla kasan ƙaramar yarinya ce sosai. Da glass cups guda biyu a hannunta. 

“Zan yi bumping into you ne yasa na ɗauko cups biyu.”

Murmushi Mamdud yayi, yana karɓar cup ɗin da ta miƙo mishi yana ɗan jujjuyawa, ya ga kamar coke, sai dai in Labeeb na throwing party ba komai yake sha ba. 

Bama koda yaushe yake karɓar drink ko a hannun Labeeb ba, inba suna gida ba. Ɗan daga gira yarinyar tayi. 

“Baka yarda da drink ɗin bane?”

Girgiza kai ya ɗan yi, yana jin kunya da bai san daga inda ta fito ba. Kofin ya kai bakinshi ya kurɓa, coke ne, sai dai yau taste ɗin ya mishi wani iri. 

Hannu ta mika mishi tare da faɗin,

“Siyama.”

Yana jin komai na zuciyarshi na mishi ihu, sai dai ya miƙa hannu suka gaisa, abinda duk shekarunshi da Labeeb bai taɓa yi ba. 

“Mamdud….”

Suka faɗa a tare, dariya tayi.

“Na ji kowa na faɗin sunan ne ɗazu.”

Yadda tai dariya ya sa shi jin wani iri duk jikinshi, ga maƙoshin shi da ya bushe. Lemon da ke hannunshi ya shanye gaba ɗaya. 

“Wow easy handsome.”

Ta faɗi da wani yanayi a muryarta. Wani iri Mamdud yake ji. Kanshi juyawa yake. Ganin ɗakin yake kamar an saka mishi slow. Har Kiɗan da wani irin sanyi da bai taɓa ji ba yake zuwa kunnen shi. 

Yana kallon Siyama ta matso kusa da shi, ta zagaya hannunta kan ƙugunshi tana riƙo shi jikinta. Labeeb ne ya zo wucewa ya kalle su. 

Sosai za ka iya karantar mamakin da ke fuskarshi. Abinda bai taɓa ganin Mamdud yayi ba. Jinjina kanshi yake da kiɗan da ke tashi. 

“Siyama me kike da brother na?”

Dariya tayi. 

“Abinda yake so”

Murmushi Labeeb yayi yana jujjuya ƙugunshi, simple rawa yake, amma ko a yanayin da Mamdud yake jinshi yasan a ɓagare ɗaya yana son zama El-labeeb. A ɓangare ɗaya yana jin kishin El-Maska. 

Yadda yake komai kamar babu wahala. Yadda ko murmushi El-Maska yayi za ka ga har maza suna kallonshi kamar su sace shi. 

“Have fun brother!”

Ya faɗi yana ɗan dukan kafaɗar Mamdud ya wuce yana faɗin, 

“Give him a good time.”

Dariya tayi, har lokacin hannunta na kan ƙugun Mamdud. Haka ta jashi har ɗaya daga cikin bedroom ɗin gidan. Kanshi juyawa yake yi, hakan yasa ya bita babu gardama. 

Jingina yai da bangon ɗakin yana riƙe kanshi. Gaba ɗaya ya rasa abinda yake ji. Jin Siyama ta haɗa jikinta da nashi yasa shi sauke hannunshi ya buɗe idanuwa.

Magana zaiyi ta haɗa bakinta da nashi da wani yanayi da ya kasa fahimta, kafin ta kai hannunta takashe switch ɗin fitilar ɗakin. 

******

Idanuwanshi da suka yi mugun nauyi ya buɗe , yana kallon ɗakin, ɗumi yaji a jikinshi, hakan yasa shi maida hankalinshi kan Siyama da ke kwance a ƙirjinshi. 

Girgiza kai yake, yana tuna abinda ya faru jiya. 

“No…. No… Please no…”

Yake faɗi yana jin kamar zai sa ihu, Siyama ya ture daga ƙirjinshi da motsawa kawai ta yi ta juya kwanciyar ta. Jikinshi da yanayin da yake ciki yake kallo. 

Da sauri ya shiga banɗaki, ruwa yasa ya shiga dirje jikinshi amma ya kasa cire abinda yasan ya manne mishi har abada. Ya kuma san ko waye sila.

Kamata yai ace jiya ta zame mishi matakalar da zai bi ya hau zuwa cika alƙawurran da yai ma kanshi. 

“Give him a good time.”

Muryar Labeeb ta daki kunnenshi. Wani zafi-zafi yake ji a ƙirjinshi. Ba tun yau ya kula El-Maska na neman abokin lalacewa ba. Kuma shi ya ga yafi dacewa shi yasa ya janyo shi rayuwar da tun ranar farko da ya ɗora idanuwanshi akai ya tsane ta. 

Fitowa yai daga banɗakin, ya ɗauki kayanshi da suke watse a ƙasa ya saka, ya fice daga ɗakin, a falo kan kujera ya samu Labeeb kwance yana bacci. 

Duka ya kai mishi da saida ya firgita. 

“Tashi….”

Mamdud ya faɗi. Da ƙyar Labeeb ya miƙe yana yamutsa fuska tare da dafe kanshi da hannuwa. 

“Ka daina ihu.”

Ya buƙata, kallonshi Mamdud yake yana jin kamar ya rufe shi da duka. 

“Me ka yi El-Maska? Setting me up da yarinyar nan? Hankalinka ya kwanta? Na yi dare ɗaya cikin irin gurɓatacciyar rayuwar El-Maska. 

Kaji daɗi? Kasan me, daga yau zuwa ko yaushe duk yadda rayuwata ta juya is on you!”

Yana ƙarasawa ya juya ya fice daga gidan. 

“Mamdud me nayi wai? Oh God kaina ciwo yake. Are we fighting?”

Ƙarar rufe ƙofar Mamdud da ya ji ya gane ya fita. Kanshi ya dafe ya koma ya kwanta yana rufe idanuwanshi, wani baccin ne ya sake ɗaukarshi. 

***** 

Bai koma gida ba sai bayan Azahar. Don da wani irin ciwon kai ya tashi. Dole ya wuni kwance a gidanshi. Don bayason su Zainab su gane wani abu na damunshi. 

Yasan akwai abinda ya faru tsakaninshi da Mamdud. Kamar sun yi faɗa amma sam ya kasa tuna akan menene. Koma wanne lokaci sukai faɗan. 

In yana cikin mayenshi ba komai da ya faru yake tunawa ba. Don haka yana shiga gida, hannu kawai ya ɗaga ma su Anees da ke zaune a falon ya wuce ɗakin su shi da Mamdud ɗin, 

A kwance ya samu Mamdud.

“Faɗa muka yi? Na kasa recalling komai”

Girgiza mishi kai Mamdud yayi ya amsa shi da faɗin, 

“Ko kaɗan. Abinda kake so ne ya faru.”

Cike da rashin fahimta yace. 

“Abinda nake so kuma? Wanne? Me yasa kake kallona kamar na maka wani abu?”

Saukowa Mamdud yayi daga kan gadon ya ƙaraso saitin Labeeb ɗin. 

“You are so fake right now.”

Da mamaki Labeeb yake kallonshi har ya raɓashi ya wuce yana buɗe ƙofa. Kiran sunanshi yayi ya juyo. 

“I am sorry. Bansan me nayi ba, na sani El-Maska ba shi da hali me kyau, kaso goma cikin ɗari na abinda nayi jiya kaɗai nake iya tunawa. 

In ba za ka gaya min ko me nayi maka ba shikenan. But am sorry okay. I am.”

Murmushi Mamdud yayi.

“Yeah ok.”

Ya faɗi yana ficewa daga ɗakin. Zama kan gadon Labeeb yayi. Yana tunanin abinda yaima Mamdud haka ya kuma rasa. Bama mutanen da suke da muhimmanci haƙuri a rayuwarshi ba wani abu bane mai wahala. 

Ko menene yayi zai ci gaba da bashi haƙuri har ya haƙura.

<< Rayuwarmu 21Rayuwarmu 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.