Skip to content
Part 28 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Binta ba ta shirin biki tabbas, amma kowa a dangi yana shirin wannan biki ciki har da Nabila wadda take nuna ta fi kowa murna.

A boye ita ta siyo kayan lefe Mujahid ya je ya dauka ya kai garinsu sannan aka kawo gidansu Binta daga can. Har kayan suka yi kwanakinsu a gidan ko kallonsu Binta ba ta taba yi ba.

Danginta babu irin nasihar da ba sa yi mata game da yadda take son bayar da kunya amma tamkar ta bayan kunneta komai ke zuwa ya wuce. Haka ma ake ta faman yi wa Mujahid wannan nasihar, shi da bai kai Binta zafi ba, face suna ganin shi a wanda bai dage da rarrashin Binta ba, duk da an ga ya dage da hidimar gyaran gidansa, har ma da sake sabuwar mota, sai dai iyakar walwala kenan a hidimar gabansa ko ta wasu mutane ba Binta ba, har ma aka fara zunden maganar a dangi ana ganin cewa shi ma fa ba ya son auren nan.

Takanas qanwarsa Ummi ta saci jiki zuwa dakinsa ta kwashe masa zargin tare da roqonsa don Allah ya sassauta ya janye wasu abubuwan.

Dayake yana cikin tsananin haushin yadda suka yi da Binta, sannan yana ganin cewa Ummi tana yawan damuwa da alakar da ke tsakaninsa da Binta ko da Nabila saboda rashin sanin abinda ke akwai, kawai sai ya kwashe labarin komai ya bata, qarshe cikin bacin rai ya rufe da cewa,

“Ummi kuna jiran na dinga goyata ne ko kuma ina kwantawa tana bi ta kaina? Allah ne ya sa min sonta, kuma ban taba fatan ya cire min ba, amma fa ba zan taba daukar raini da ya wuce haka daga gareta ba”.

Ummi ta tausaya masa qwarai, har ma sai da ta yi masa qwalla, cewa ta ke,

“Wallahi Yaya babu wanda ya taba fahimtar haka a tsakaninku, kowa baibai yake kallon lamarin”

Yana dariyar kore damuwa ya ce,

“Kar ki damu, ke ma wannan maganar da muka yi da ke ta zama sirri tsakaninmu don Allah, kar ki yarda na ji ta a bakin kowa. Binta matata ce kuma wadda nake so, ko me ta zo da shi na aibu dole na boye don zamowarta iyali kuma abin so… a bar ta ta yi haukanta ta gama, in ta ga zata tsufa cikin damuwa da kanta zata nemawa kanta mafita.”

Ummi ta yi kasaqe sannan ta ce,

“Amma dai Yaya Mujahid, ka shirya wata dabarar ta qoqarin ta fahimceka, wannan dauke wutar ba zai sa ta fahimce ka ba.”

Ya sake dariya,

“Fahimta? Binta yarinya ce kamar ke? Ki zuba ido ki gani ba wannan ne a gabanta ba, abinda ke gabanta na sani yanzu shi ne tanadin abinda zata shiga gidana da shi na baqanta rai, wannan ne abinda ya kamata na fuskanta ba wai na nace sai ta fahimci ina sonta ba”.

Sai Ummi ta qara tsorata, don ba ta zaci mummunar shaidar da zai wa Binta ta kai haka ba.

Da sanyin jiki ta fice daga dakin ta shiga cikin gida.

Kamar Mujahid ya sani.

An je an yi shiryawa Binta gida kamar aljannar duniya a gidansa. Sama da qasa ne gidan amma saman bai kammala ba, ya rage fenti da qyele-qylen bandakuna, qasan kawai yana da dakunan bacci uku, falo biyu da sauransu, nan aka mamayewa Binta abinta.

Ana gobe za a kai ta wato rana yini kenan har daki Alhaji ya zo ya sami Mujahid. Tun a nan Mujahid ya fara shirin jin abu mara dadi daga Binta, kasancewar in ya ga Alhaji a dakinsa tabbas muhimmin abu ne.

Ilai kuwa, bayan kewaye-kewaye Alhajin yace,

“Jiya da dare na zauna da Binta har tsawon awa daya, ta yi alqawarin yi mana biyayya daga qarshe kuma ta nemi wata alfarma, sai dai ban san yadda zaka karbe ta ba don ban san yadda kake son iyalinka su kasance a wannan bangaren ba”

Mujahid ya dinga gyada kai tamkar qadangare yana jira baqin cikin Binta ya fado masa qirji, ya sha sharafinsa ya gama don ya san duk qarfinsa dai ba zai iya kashe shi ba.

Alhaji ya gyara murya ya ce,

“Ta ce min tana sha’awar fita aiki, don Allah tana roqon alfarmar na tambayar mata kai”.

Qwaqwalwar Mujahid ta koma can baya tuno lokacin da yake lissafawa Binta abubuwan da ba ya so a matarsa, ashe su ta kame ta ke so daya bayan daya ta hukunta shi da su? Yanzu ya gane illar ka nuna wa ko wanne dan Adam ba ma wai mace ba abubuwan da ba ka so, in ya zama maqiyinka sai ya nemi kashe ka da su.

Yana ta kwarara murmushin yaqe ya cewa Alhaji,

“Ai babu matsala, na yarje mata dari bisa dari, Allah ya taimaka, ko ni kuma zan bincika mata…”

Alhaji ya dinga gode masa sannan ya dora da cewa,

“Ai kar ka damu ma, Yaks yana da hanya ta sanar da ni cikin sati daya zai iya samo mata”.

Mujahid ya ji wani tashin hankali ya karci qirjinsa, amma jarumtarsa ta shanye murna ce kawai ke wanzuwa a fuskarsa yana daga kai,

“A shikenan ma an huta dawainiyar nema, Allah yayi musu albarka”.

Cikin jin dadi Alhaji ya ce,

“Amin,  kai ma Allah yayi maka albarkar ya ba ka abinda kake nema duniya da lahira”,

Sai lokacin Mujahid ya ji wata ‘yar salama ta leqo zuciyarsa, da niyyarsa har zuciya ya amsa,

“Amin, na gode.”

*****

Hajiya da sauran dangi sun kwashi shagalin bikinsu, an yi kamu da yamma, da dare aka yi dinner iyaye, washegari aka yi yini, daya washe garin aka tattara amarya aka miqa dakinta.

Amaryar da ba ta yi kama da Amaren ba saboda rashin walwalarta, ko kunun kanwa ya rufa mata asiri wajen fara’a, sannan wajen kyan da amare suke ma fiye da rabin ‘yan bikin ma sun fi ta kyau, duk da an matsa mata an yi asarar kudi a gyaran jiki, kuma ana matsa mata ta saka sabon kaya duk da haka sam ba ta kyau, hotunan bikin duk haka ta fito komai babu armashi.

Qarfe sha biyun dare an watse an bar ta da dukan zuciya, duk tsaurin idonta da yadda take jin ta fara qwarewa a iya tura wa Mujahid haushi sai da ta sami kanta cikin tsananin tsoron abinda zai zo ya biyo baya.

Ta saqa wannan ta saqa wancan, amma don qarfin hali ta qi bari falon, ta hakimce sosai da zarar ta jiyo motsi sai ta shiga cin magani tana yamutse fuskoki, tare da shirin rashin mutunci kala-kala.

Wasa! Har qarfe biyu babu Mujahid, daga nan sai ta fara karaya tana jin wani ciwo da ba ta san dalilin tasowarsa qirjinta ba.

Da kyar ta lallaba ta kulle qofar falon sannan ta zarce cikin daki kai tsaye idanuwanta na yajin bacci da damuwa.

Wannan Man din ashe ya shirya sa qafar wando daya da ita? Gaba yake son su yi ta yi yadda zata yi ta yi masa abin haushi bai san ta yi ba ko me yake nufi? Ita ba zama ta zo gidan nan ba, hayaniya ta zo cikinsa wadda zata yi sanadin gille igiyar auren ta yi gaba abinta.

Ranar na sai bayan sallar asuba ta sami runtsawa, inda bata farka ba sai kusan sha biyun rana, shi ma bugun qofa da muryar kanne Hajiya ce ta farkar da ita.

Cikin sauri ta wawuri wardrobe ta zuge kayan baccin jikinta ta canja wasu ta nufi falo da sauri cikin shakkun zuciya,

“Ina Mujahid, kuma a ina ya kwana?” Abinda ta dinga tambayar ranta kenan lokacin da take bude qofar.

Sakina da Amratu yammata ne, kannen Hajiyarta sai kuma Abdullahi qanin Yaks.

Ta rakito fara’ar dole ta karbe su. Suka shigo suna mitar yadda ta garqame gida da falo a taskiyar ranar nan kuma wai tana bacci.

Ita dai ta rasa bakin magana, tana son tambayarsu wanda ya bude musu gidan kuma tana tsoro da shakkun kar ta ji abinda ba zai wa ranta dadi ba, in aka ce daga waje Mujahid ya zo ya bude qofar amsar ita ce bai kwana a gida ba, to ina ya je ya kwana? In kuma aka ce daga cikin gidan ya fito ya bude, to wanne dakin? daya falon na garqame kuma tun jiya ba ta ji motsin an taba shi ba.

Cikin kame-kame ta ce,

“Wanka zan shiga, shiyasa na rufe”.

Cikin mamaki Sakina ta ce,

“Wanka zaki shiga? Amarya guda sai yanzu zaki shiga wanka Binta?”

“Amaratu ta ce,

“Sakina ai na zaci tambayarta zaki yi don zata shiga wanka ga angonta a cikin gida sai ta garqame qofofi?”

Hantar cikin Binta ta yi wani tar! Amma dai ba ta dare ba, ta yi fuska ta share ta hanyar janyo Abdul tana yi masa wasa da bade shi da tambayoyi, a bakinsa ta ji cewa ai tare da Yaks suke kuma yana cikin mota.

Da sauri ta ji wata tsokana ta fado mata zuci, ta dubi Sakina ta ce,

“Amma dai tare kuke da Yaks kuka bar shi a qofar gida kuka yi shigowarku?”.

Amratu ta ce,

“Ko dai ya bar kansa? Hankali qila ya fara don babu yadda ba mu yi da shi ba kan ya shigo ya bijire, wai mu shiga mu fito.”

Da sauri ta kada keyar Abdullahi,

“Kai yi sauri ka ce masa ya shigo.”

Da sauri Abdullahi ya fita.

Yaks na sallama a tsakar gida Mujahid ya sakko daga bene, fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amsa sallamar sannan yayi fuska  yana shirin ganin ikon Allah, shin Yaks ba shi da kunya ne zai quga kai ya shigar masa dakin mata?

Da Yaks din bai yi rashin hankalin shiga dakin kai tsaye ba ya tsaya kallon kare a karofi, sai matar tasa da ta fi Yaks din rashin kunya ta fito tana masa tayin ya shiga.

A nan ne Mujahid yayi fuska ce mata,

“Ki kawo Key din dakin nan mu shiga nan da shi, in kin matsu ya zo gidanki kenan, in kuma ba ki matsu ba ina iya sallamarsa daga nan”

Binta ta firgita da tsoron kar su Sakina su jiyo tijarar Mujahid, Yaks kuma ya ji Muzantar duniyar nan ta rufe shi, shi bai zaci har yanzu Mujahid na adawa da shi ba, bai zaci har yau Binta ba ta kwance layar da ta daura masa ba.

Yana ta faman yaqe ya gaisa da Binta sannan ya cewa Mujahid,

“Babu matsala bari ma na jira su a mota”.

Ba wata damuwa a fuskar Mujahid ya kama qafar bene yana hawa yana cewa,

“To babu laifi, hakan ma ya fi lada.”

Yaks ya fita Binta ta koma dakin da sauri da fargabar kar dai su Sakina su jiyo, amma ta makara, don sun ji komai, hasalima a tsaye ta same su da shirin tafiya, ba su dai fada mata dalili ba, amma sun kafe mata sai sun tafi.

Kanta na juyawa tana bin su da kallo suna ficewa sauri-sauri.

Ta fada kujera ta dafe kai tana ta faman tsinewa Mujahid cikin zuciya, wai duk shirin da ta yi da shi yake quga mata haushi ya zurma ta laifin ya koma kanta, yanzu duk inda maganar ta shiga dangi sai ta sami me dasa mata ayar tambaya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 27Rigar Siliki 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×