Skip to content
Part 5 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo a bayan kallon da Mujahid ya yi mata ya cika ta qwarai, dole ta shiga saqa da warwara har suka yi tafiya mai tsawo kowa bakinsa a dinke.

Mujahid ya ce yana sonta, daidai ne da albishir din ranar mutuwarta, in kallon da ya ke mata daga mahudar soyayya ya hudo ta ina za ta bi ta kubuta?

Maganin kar a yi, to kar a soma, ta shawarci kanta wannan azancin, kuma nan take ta yi fuska ta fuskance shi ta ce masa.

“kadaici na taka rawa a wannan zafin kan naka Yallabai, ka ba ni hadin kai na nemo maka abokiyar zama mana”.

Ya juyo ya dube ta da kyau cikin murmushin yaqe, sannan ya kawar da kai yana kallon hanya muryarsa a sarqe ya amsa mata.

“Da ra’ayoyinmu sun zo daya zan iya kasadar ba ki zabo min mata, amma mun saba a yawancin zabenmu, ko kuma abin da ke burge mu”.

Ita ma ta qura wa hanya ido tana murmushi.

“Na san yawancin abin da ke burge maza”.

Ya juyo ya kalle ya cikin zaro ido.

“Da gaske? In dai ina cikin mazan da ki ka san abin da ke burge su haqiqa sai na yi miki kyauta”.

Tana dariya ta ce.

“Ka bar kyautarka, ni don Allah zan yi, kuma don ita ma matar da na yi maka na fahimci  tana ra’ayin namiji irinka, ba don kar in bayar da mata ba ma sai in ce sonka ta ke”.

Ya san mawuyacin abu ne Binta ta furta masa soyayya in bai taqala a matsayinsa na namiji ba, amma zuciya da saqe-saqe sai ta dinga raya masa wadda Binta ke kwatance ita kanta ce.

Cikin doki da son tabbatar wa ya ce mata.

“Wace ce haka?”

Kai tsaye ta amsa masa.

“Nabila ce!”

Nan take ya murtuke fuska tamkar kakkaurar gasarar da ake watsa wa ruwan zafi. Ya fara kokawa da numfashi.

Ba  kallon jiran amsa kawai Binta ke masa ba, kallo ne na nazarinsa gabadaya tare da alqanta rayuwarsu tare idan hasashenta ya zama gaskiya na zaton ita ya ke so, ya ce yana so, ina za ta iya kai wannan qaddarar? Da kafin ranar yau ne ya ce yana sonta za ta iya karbar sonsa a matsayin laba’asa, amma a yanzu karin maganar Hausawa ne kawai ya ke ta kuwwa a kunnenta, wato gado marin da, kuma da gaske shi zai sa ta yi wa soyayyar tankwabar da ba ta taba yi wa kowa irinta ba idan ya miqo.

Ta nisa da qyar cikin gauraya tunani da qarfin hali, ta yi dariya ta ce masa.

“Bai fa kamata ka bar ni shiru ba, ni ba game na zo mu yi ba, duk abin da na ke fada wallahi da gaske na ke”.

Ya dan ja fasali kafin ya juyo ya kalle ta cikin sanyin jiki.

“Duk lokacin da Nabila ta gama boye-boyen son da ke kadai ki ka fuskanci tana yi min, idan ta furta ki sanar da ita ni ba na sonta, ban taba mafarkin son irinta ba, kuma ba zan zahirantar da shi a filin rayuwata ba”.

Ta jima tana kallonsa cikin mamaki, sannan ta kada kai ta kawar.

“Nabila ta fi qarfin wani namiji mai saka hula ya ce ba ya so… Allah wannan ban yarda ba”.

Kamar zai tare ta a zafafe saboda tsabar quluwar da ya ke saboda kuranta Nabilan nan da ba ta isa samun kowaccen irin shimfida a  zuciyarsa ba, amma mashin son Bintan na zare masa idon yi mata tsawa, kawai sai ya koma laqwas cikin kada kai da murmushi ya bi titi da kallo.

“Wai me ki ka dauki so Binta?”

Ta yi fuska tana fadin.

“Bai bambanta da yadda masana falsafa suka kalle shi ba, amma kar ka manta muna maganar son aure ne ba wai na jin tashen balaga ba”.

Ya ji shiga maganarta tamkar ya juyo ya dube ta cikin mamaki, sai kuma ya shanye ya yi fuska kamar ita.

“Sai ki bambance min na tashen balagar da kuma na auren, wataqila na zabi wanda zai fi dacewa da ni”.

Kai tsaye ta amsa masa.

“Shi son tashen balaga shi ne irin wanda ka ke so ka ce min kana yi wa matar da ka ke so, son in ba ke ba sai rijiya, ko ba haka ka ke so ka ce min ba ne?”

Yanzu ya bar mamakin ya sha sharafinsa a fuskarsa, cikinsa ma ya juyo ya kalle ta yana murmushi.

“Yanzu ke har yanzu ni ne ban wuce shekarun tashen balaga ba, da ma da ni ki ke?”

Ta kebe baki ta kawar da kai.

“Burbushinsa ke damunka, to in ba da kai na ke ba, da wa na ke? Na ga ai a kanka mu ke magana”.

Ya kada kai yana ta faman dukan sitiyari a hankali cikin kallon titi alamar ya rasa abin ce mata, sai can cikin dariya ya ce.

“To ja mu je na ji yadda son auren ke kasancewa”.

Ta fara magana cikin yarfa hannu.

“Son aure sai mu kalli zabin da Manzon Allah (S.A.W) ya ba ku a mata. Nabila ta hada abu biyu cikin zabin, wato kyau da addini, na tabbatar in an zabe ta hannun ba zai turbaya ba”.

Ba tare da ya kalle ta ba cikin kada kai ya ce.

“Manzon Allah ya yi mana umarnin auren wadanda muke so in bai mana iyaka da wadanda muke so ba, bai kamata tashen balaga ya yi mana ba”.

Ta ji haushi na neman kashe ta har ta kasa boyewa, murya a sarqe ta ce.

“To mu bar maganar”.

“Don me?”

Shi ma ya yi fuska, ba tare da ya jira ta amsa ba ya ci gaba da magana.

“Ban san me ya sa ki ke son ki yi min auren dole ba, sai ka ce kin ga alamun zan ce ke na ke so”.

Yanayin maganarsa bai nuna wasa ba, amma ita dole ta mayar da abin wasa don ba za ta taba son ya zama gaske ba, cikin dariyar yaqe ta ce.

“Haba! tatsuniya ma ke nan ka ce kana sona, Yaya Mujahid ai ni na fi qarfinka, na yi maka yawa”.

Batunta ya shige shi, amma babu yadda ya iya haka ya bar maganar a wasa shi ma..

“In kin min yawa sai a qara ni mu yi daidai ko a rage ki mu yi daidai…”

Ta ci gaba da magana cikin wasan.

“Tunda na budi ido na ga na zama budurwa na sha yi wa kaina tanadin miji, in an dube ka daga sama har qasa, ko daya ba ka rabi sharuddan da na gindaya wa mijin aurena ba”.

Yanzu dariyar yaqe ya ke domin bai dauki maganar da ta yi wasa ba, duk kuwa da a cikin wasan ta yi ta. Cikin nuna qarfn hali ya amsa mata da cewa.

“Da kyau! Daidai ke nan da ma, ai ni ne namiji, ni ne shugaba, ni ya kamata na kafa sharudda ko na dade ina zabi kamar yadda na dade ina zabo ki”.

Da sauri ta qara bata rai tana daga masa hannu.

“Don Allah mu bar wannan wasan duk da wasa ne, wallahi yana sosa min zuciya. Haba Yaya Mujahid ina zan kai ka a matsayin miji? Ni sam ma ba na sha’awar auren zumunci”.

Ya jima cikin shiru saboda rudun zuciya, tabbas ya san Binta da gaske ta ke ba ta sonsa, ba don zuciyarsa ba ta kinkimo son Binta da wasa ba sai ya share maganar a zuwan wasan ne a tashi a haka, ya ci gaba da jan girmansa. To ko kusa ko alama ba zai iya ba, yadda ya ke jin son Binta a illahirinsa yana tsammanin ba haka aka saba son sauran mata ba.

Sun jima kowa cikin shiru, shi cikin kama tashoshi suna ballewa, ita kuma cikin nadamar yadda ta fito masa da maitarta afili tun ma kafin ya furta mata ita ya ke so.

Can dai wata tashar da ya kamo ta kasa subucewa a kwanyarsa, sai ya kinkima ya tunkare ta cikin yanayin nutsuwa da nuna babu wasa cikin lamarinsa.

“Bayan Nabila tana da kyau, me ki ka tabadar mata kafin ki ga dacewarta a aurena?”

Ta rakito fara’ar duniyar nan ta maka wa zuciyarta da fuskarta.

“Tana da kyau, kuma tana da sanyin hali”.

Ya kebe baki yana girgiza kai.

“Duk ba sa burge ni”.

Ta kafa masa ido cikin haushi da mamaki.

Ba tare da ya yi dakon cewarta ba ya dora idonsa na kallon titi.

“Tun farko ma ya kyautu ki tambaye ni kyau na burge ni, kuma sanyin hali na burge ni? Duk zan hada amsar da zan ba ki da hujjoji”.

“Yanzu na tambaye ka”.

Tana gyara zama ta fada cikin nuna azarbabi tare da gajiyawa.

Shi kuma ya shiga amsa mata kai tsaye.

“Kyau ba ya burge ni, domin ina da kishi, ko budurwa ta ba na so wani namiji ya kalla balle matata. Wannan dalilin ya sa ban taba sha’awar cewa ina son wata mace da na laqanci tana da dabi’ar tara samari ba…  Bayan haka kyawawan mata sun cika hadari, qalilan ne mazajensu ke iya juya su, wasu ma har ha’intar mazan nasu suke, saboda haka mace mai kunya da mai kwwalliya ba sa burge ni”.

Da wannan bayanin nasa kadai Binta ta gama yarda ita zai ce yana so, domin ita dai ba za a sanya ta a layin kyawawa ba, sannan kowa a gidansu ya shaida da adawarta da mata masu sauraron samari alhali ba aurensu za su yi ba, ashe… ashe wannan qudirin nata shi zai janyo mata mutumin da bai cancanta ba ya kawo mata banzar soyayyarsa wadda ba za ta taba amfanarta ba.

Amma dai haka ta ci gaba da yaqe, cikin yanayin hadiye qosawa kuma ta ce masa.

“Gaskiya kana da tsari mai kyau, to batun sanyin hali fa, me ya sa shi ma ba ya burge ka?”

Yana jin qumaji ya amsa mata.

“Son da na ke wa yarinyar da na ke son aure ba ya jiran wani sanyin hali da zafin kai, ke ko ta fi ashana zafin kai haka na ke sonta, kuma haka zan ci gaba da sonta”.

“Hmm”.

Da qyar Binta ta daure ta dan yi nishi saboda yadda qofofin kanta suka kulle a haushi da jin neman mafita idan hasashenta ya zama gaskiya, mafitar da ba ta jima tana nema  ba ta ji ta zo kanta a guje. Sai ga ta tana murmushi tun daga zuci zuwa kan fuska… Ai Mujahid ya gama kuskure, tunda ya haska mata ra’ayinsa a mace.

Sun iso gida kowa jugum-jugum, suna shiga harabar gidan, Yaks na fitowa daga gidan da alamun tafiya gida.

Yaks dan yayar mahaifiyar Binta ne, wanda ya yi rashin sa’ar baturen uba mai sakar wa ‘yayansa ragamar kansu da sunan ‘yanci, duk qoqarin mahaifiyarsa don ba su irin tata tarbiyyar ya ci tura, kasancewar mahaifinsa yana tsananin nuna wa iyalansa so, bai qi ya zagi uwarsu ko ya dake ta a kansu ba, har ma akwai lokacin da ya taba yi mata saki daya a kan yaran.

Wannan ne dalilin da ya sanya tarbiyyarsu ta yi rauni, musamman Yakubu Sagiru, wanda ya sauya wa kansa suna da Yaks. Yana da son sharholiya da jarabar dora ido a kan mata, yau ya latsa waccan, gobe ya yaudari waccan, kuma ba ya boyewa a gaban kowa hatta da qannen uwarsa da yayyenta wadanda ya mayar ma tamkar kakanninsa, don in Hajiyar Binta na yi masa nasiha sanya ta a gaba ya ke ya yi ta faman tuntsira dariya yana shegantaka. Ga shi Allah ya hada jininsa da gidansu, kasancewar gidan taruwar dangi ne musamman ‘yammata da suka fi tsone masa ido.

A nan ya hadu da Nabila wadda ta tsone masa ido fiye da duk wata mace da ya taba gani a rayuwarsa, kyawunta da gayunta komai ya yi masa, saboda haka ya nade qafar wando ya shiga cusa kai tsawon kusan shekara, amma da alama Nabila ba ta tsani kowa ba sama da yadda ta tsane shi, in zai je gidansu sau goma ba za ta fito ta ganshi ba, sai dai ya shammace ta ya ganta anan gidan. Shi ma babu magana mai dadi, in ma ya sami jin ta bakin nata, kowa a gidan ya san halin da suke ciki in ka dauke Mujahid, an san kuma kalar son da Yaks ke wa Nabila ya bambanta da wanda ya saba yi wa ‘yammatan da ya sha yi wa a baya, amma halayyarsa da aka sani ya sanya babu wanda ya damu da tausaya masa ko taya shi yaqin yada manufa a kan Nabila.

Duk wani salo na jawo hankali yana qoqartawa a kanta, kama daga kyautar ido rufe da kuma tsabar iya taku a gayu, tunda ya gane ita ma ‘yar tsana haka ta ganta a kan kwalliya, ga shi dai shi ba wani kyakkyawa ba ne, don gajere ne, baqi wuluq mai faffadan hanci, amma gayunsa da iya kwalliyarsa ya sanya ba za a yasar da shi dalilin muni ba.

Tun daga nesa Binta ta qura masa ido saboda ganinsa ya fito fuskarsa fiye da ta kunu a murdewa.

Ita kuma Mujahid ya qura mata ido wasu dunqulallun abubuwa masu shegen yaji suna naushinsa a maqogwaro da qahon zuciya. Allah ya sani yanzu a filin duniya ba wanda ya tsana sama da Yaks, na farko ya tsane shi domin halayyarsa. Na biyu kuma ya tsane shi ne domin kyakkyawar alaqar da ke tsakaninsa da Binta, ganin Mujahid irin su Yaks quda ba ka haram ne, ko ya ya suka sami qofa za su iya nuna halinsu, kai ko Binta tana da tarbiyyar da ba za ta iya biye wa Yaks ba, shi Mujahid yana qyashin Yaks ya kalle ta ya hadiyi yawu, da Mujahid na da iko haqiqatan sai ya hana Yaks shigowa gidan nan, amma babu yadda ya iya, ko da kuwa na nuna ba ya qaunarsa a fuska.

Binta ta fita daga motar da sauri, sai Mujahid ma ya sami kansa da saurin fitowa ya rufe motar ya bi ta a baya. Suka yi kacibus da Yaks ya yi musu maraba cikin murmushin yaqe.

Cikin fargaba Binta ta dinga jin xokin Mujahid ya wuce ya shige gida, amma ya dogare musu yana wani kalen gaisuwar da ba dabi’arsa ba ce.

“Azumi ka ke ne wai na ganka a jigace?”

Binta ta daure ta tambayi Yaks cikin zolaya wai don ta qirqiri abin da zai sa Mujahid ya wuce cikin gida ya barsu idan ya ji za su yi hira, amma ko a jikin Mujahid sai ya maze ya ci gaba da tsayuwa.

Yaks ya sabo hannunsa a wuya yana lasar lebe alamar bacin rai ya amsa mata.

“Nabila har yanzu ta kasa gane in ta ci gaba da nisanta  kanta da soyayyata kisan kai za ta yi…”

Da sauri Binta ta dubi Mujahid don ganin yadda zai karbi maganar nan da Yaks ya baro, a kan yarinyar da tun dazu ta ke masa magiyar ya aura a  kanta, amma da yanayin farin ciki tare da jefa mata tambaya da ido.

“Matar da ta ke da kifinta a gora ki ke tura ni na nema?”

Binta ta kawar da kai ta basar.

Da alama Yaks bai lura da siyasar da suke masa ba, Ya dora batunsa cikin yanayin raunin zuciya.

“Wai babu mai taya ni nuna wa Nabila irin son da na ke mata, har ke Binta ba za ki taya ni ba?”

Binta ta rasa bakin magana sai faman wuwwurga ido ta ke.

Wani murmushin farin ciki ta keto a kuncin Mujahid, cikin karsashi ya dafa kafadar Yaks.

“Kar ka damu, ni zan taya ka don na san yadda ka ke jin tafasar so a qirjinka, ni ma a cikinsa na ke…”

Kafin ya rufe baki Yaks ya rungume shi cikin godiya da yekuwar murna, lokacin da suka saki juna tuni Binta ta dade da bacewa a wajen cikin wani irin takaici da ba zai lissafu ba.

Duk suka bi hanyar da ta bace da kallo.

Yaks ya kada kai cikin takaici bayan ya dauke ido daga kan Binta wadda tuni ta qule.

“Rashin nasarata yana da nasaba daga kware bayan da na ke samu daga dangina, dubi dai wannan matar yadda ta dauki fushi daga na yi maganar abin da ya kamata a tsaya a taya ni jimami,ko da kuwa ba za a rarrashe ni ba”.

Mujahid yana kallon fuskar Yaks ya gane lallai abin da ya ke fada ya taso ne daga doron zuciyarsa, da ya ke ya san irin ciwon da Yakas din ke ji a ransa, sai ya ji yana tausaya masa.

Ya sake dafa kafadarsa cikin tausasawa ya ce masa.

“Kada ka jona samun nasararka ga wani domin shi ma yana da nasa burin da ya ke fatan nasara akansa, ka ga ke nan sai ka yi jiransa ya gama da kansa sannan ya taimake ka. Abin da na ke son ka riqe shi ne azancin nan da masana suka ce, ‘babu abin da ke miqar da sandarka sai nacin daddanawa…”

Yaks ya fizge kafadarsa ya wuce yana fesa masifa.

“Kawai dai dangina ‘yan iska ne, sun dame ni da batun ina yaudarar ‘ya’yan mutane, yanzu kuma na ga ta aure na ce a aura min in daina yaudarar an bige da fada min ita mutumiyar kirki ce, ni dan iska. Da ma qa’ida ita ce dan iska ya auri ‘yar iska?”

Mujahid bai tanka masa ba, illa ya saki baki ya bi shi da kallo duk da dama Yaks bai yi maganarsa don yana son Mujahid ya amsa ba, illa zallar bacin rai.

Kawai sai ya kada kai ya rungumi nasa bacin ran ya shige cikin gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 4Rigar Siliki 6 >>

1 thought on “Rigar Siliki 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×