Skip to content
Part 6 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Tun daga waje Binta ta tattara bacin ranta ta yi jifa da shi, ta shiga gidan da walwala aka yi ta murnar dawowarsu.

Fiye da mintuna goma sha biyar da shigowarta  amma ba ta sanya Nabila a idonta ba, sai da ta sa baki ta tambaya.

“ni fa ban ga Nabila ba

Amina ta yi caraf ta amsa.

“Mun dawo a katari, Yaks ya shigo kawai ta yi alwala ta shige daki har yanzu ta qi fitowa”.

“Bari na ganta”.

Binta ta fada tare da miqewa, cikin rashin qwarin jiki ta doshi dakin.

Ga mamakinta sai ta tarar da Nabila dunqule a gado, yanayinta na nuna tana cikin tsananin damuwa qila ma kuka ta ke.

Ta zauna gefen gadon cikin sanyin muryar ta ce,

“Ba dai bacci ki ke rub da ciki ba a wannan almurun, na shigo tun dazu ban ganki a ‘yan maraba ba?”

Da gaske Nabila kukan ta ke saboda kokawar ta rage dunqulen takaicin da ya ke kawo wa qirjinta naushi. Da qyar ta yi dabarar goge hawaye ta tashi zaune tana wuri-wurin alamun farkawa daga bacci.

“Lah Anti ban ji shigowarki ba, cikina ke ciwo na kwanta shi ne bacci ke son sace ni..”

Binta ta qura mata ido cikin shakku tamkar za ta bi ta a yadda ta kamfato, amma tuna nata qalubalen wato Mujahid sai ta ganta a fagen nazari cikin kallon Nabila kallo irin na qurulla.

“Kuka fa ki ke?”

Ta ce da Nabila.

Ita kuma Nabilan ta tsargu da kallon, sai ta ji wani kukan na neman qwace mata, amma sai ta shanye shi.

“Eh, ai na fada miki cikina ke ciwo”.

“Ban yarda ba”.

Kai tsaye Binta ta fada.

Kawai sai Nabila ta zura mata ido ba tare da ta tanka ba, ta san da gaske qarya ta ke ba ciwon ciki ba ne, sai dai gaskiyar ba za ta taba faduwa ba.

“Menene matsalarki?”

Binta ta katse mata tunaninta.

Nabila ta kaxo kai wanda ya taimaka mata zuqe hawayen da ya danno idonta, ta kawar da kai daga kallon Binta.

“Ban fahinci abin da ki ke nufi ba, ni ba ni da wata matsala da ta wuce ciwon cikin da na fada miki”.

Dabara ta so qwace wa Binta amma ta cafko ta.

“Yaks ya zo ko?”

Ba ta jira amsar Nabila ba ta cigaba.

“Mun hadu lokacin da na ke shigowa”.

Ko motsi Nabila ba ta yi ba domin jin Binta ta yi kidanta ta yi rawarta.

“Yanzu Yaks ba matsala ba ne a rayuwarki?”

Nabila ta ji katsaham Binta ta yi mata tambayar, amma ita ce eh Yaks matsala ne a rayuwarta, amma dai kasancewar cin fuska babu dadi tunda dan uwan Bintan ne ita ce ma Bare a cikinsu, sai ta yi saurin girgiza kai tana cewa.

“Haba dai, ta ya ya Yaks zai zama matsala a rayuwata? ko ina da tabbacin za a aura min shi bisa dole ai bai kamata na salwantar da rayuwar tawa ba har ya yi galabar hana ni sukuni…”

Binta ta katse ta tana dariyar hada bara da bana cikin zuciyarta.

“Ina son mutum mai jarunta irinki, amma kin sa ba a ko’ina ba yake zama jarumta a ce mutum ya boye abin da ke qarqashin zuciyarsa.

Da sauri Nabila ta yi mata duban mamaki cike da zargin kai, ko ta yi wani abu ne da ya fallasa muqamin Mujahid a zuciyarta? Kai tana shakkar in an yi hakan don ko ita da zuciyar tata ba ta yarda su dinga tattauna suna son Mujahid bare har wani daga nesa ya canko, don haka ta ci gaba da yi wa Binta  kallon mamaki.

“Ban gane nufinki ba Anti”.

Binta ta yi dariyar basarwa.

“In ba ka son mutum ba zai zama matsala a rayuwarka ba? Na zaci qiyayya na damun zuciya tamkar yadda soyayya ta ke”.

Cikin wata wawuyar ajiyar zuciya Nabila ta koma ta kishingida, duk da ba ta gama gamsuwa da yadda Binta ke tattamqe ta da jijiyoyin jikinta ba.

Tana ta faman sheqar dariyar son ta kori hirar ta ce.

“Mu yara ne, bai kamata mu yarda soyayya ko qiyayya ta dami rayuwarmu ba”.

Binta ta dan kai mata bugu suna dariya duka, ta ce mata.

“In dai yarintarki ba ta isa hana ki aure ba, ai kuwa ba za ta hanaki soyayya ba. Kada ki manta na ji boren da a ke da kakarki na cewa ba za ki shiga wata makaranta ba bayan kin kammala sakandare sai da aurenki.

Nabila ta bata rai, alamar an tuno mata da wani abu mara dadi.

Da sigar rarrashi Binta ta ce,

Kar wannan ya dame ki Nabila, matuqar kin sami wanda ya kwanta miki kuma kin tabbatar yana da halin kirki ki yi aurenki kawai, mu ba gashi ba da muka tsaya jiran karatun mun bar wadanda muke so masu halin kirkin sun wuce suna neman barinmu da alaqaqai, sannan ita ma Inna tana da gaskiya, tsufa kullum sallama yake mata rauni na qara riskarta, in mutuwa ta rufe idonta a halin yanzu, zata bar rayuwarki cikin mawuyacin hali hannun Mominki

Nabila ta dan kebe fuska alamar jimami, sai dai ba ta tanka ba.

Suka jima cikin shiru kafin Binta ta cafko abin cewa a zuwan shawara ta ke ba wa Nabila.

“Lallai ki tanadi mutumin kirki a hannunki kafin kammala makarantarki, hakan zai miki amfani biyu”.

Sa mata ido Nabila ta yi qirjinta na faman lugude.

Binta da kanta ta qarfafa wa kanta gwiwa ta furta abin da ta yi niyya.

“Na san Yaks bai kamace ki ba, amma Mujahid mutumin kirki ne, ya dace da ke”.

Ba don Nabila ita ma ta qarfafa wa kanta gwiwa ba sumewa za ta yi a wajen, saboda farin ciki da dokin jin abin da tun tunin kunnuwanta suka sha mafarkin su ji. To da alama in ba ta sume ba ma ta yi mutuwar ido biyu, domin ta kasa tanka wa Binta.

“Kin yi shru kina kallona”.

Binta ta nemi farfado da ita daga duniyar da ta so zuqe ta.

Da qyar cikin sassarfar harshe ta tanka idonta cikin na Binta.

“Kun yi wata magana da shi ne?”

Binta ta so sheqar qaryar cewa eh, amma da ta tuna yadda suka yi da Mujahid sai ta yi saurin kauce wa wannan tunani, cikin dakewa ta girgiza kai ta ce.

“A’a, kawai dai na ga alamu ne na ke share masa fagen, tare da fatan kar ki tankwabar da mutumin kirki idan ya nuna kansa gare ki…”

Dukkan murnar Nabila ta koma ciki har sai da fuskarta ta bayyana hakan, tana shakkar idan abin da Binta ta fada gaskiya ne, in Mujahid na sonta ya kamata a ce ita za ta fi kowa ganin alamu, to tsakaninta da shi, mu’amala ce da ba ta fice gaisuwa ba, gaisuwar ma ta daga nesa wadda tamkar murmushinsa ma sai ta siya,sai dai babu ‘yar musu ko jayayya tsakaninta da Binta, kawai sai ta bige da murmushin yaqe cikin amsa mata,

“Ba na gaggawa a lamarina Anti, har kullum ina miqa wa Ubangiji zabi nagari…”

Binta cikin daurewa kar ta karaya ta tare Nabila da fadin.

“Ba addu’a kawai Ubangiji ya ce ki kwanta ki yi ba, Ya umarce ki da aiki don ko aljanna ba ta samuwa sai da aiki…”

Nabila ta ji wani haushi na son ya kashe ta, amma ta daure ita ta kashe shi, a sanyaye ta ce.

“Aikin shi ne in fara cewa ina son Yaya Mujahid Anti?”

Binta ta yi qoqarin ta fadi abin da ya fi A’a” ta kasa, sai ita din ta furta sannan ta ja baki ta tsuke zuciyarta na saqe-saqe.

Nabila kuma ta ci gaba da qarfin halin dorewa da magana.

“Ya ma zan yi da Yaya Mujahid Anti? Ai ya yi min yawa”.

Ta qare maganarta da dariya.

Binta ta yi qoqarin ta yi dariyar ita ma, amma ta kasa sai ta sami kanta da duban Nabila cikin alamun tunani..

“Wai ba ki yarda cewa na ga alamun cewa, Mujahid na sonki ba?”

“Ba musawa na yi ba Anti”.

Kai tsaye Nabila ta amsa a fatar baki kawai domin zuciyarta qaryata bakin nata ta ke.

Cikin kada kafada Binta ta miqe tana cewa.

“Tun da kin yarda ina roqon alfarmar idan ya furta ki karbi tayinsa domin kun dace da juna”.

Duk yadda Nabila ta yi qoqarin ta yi wa zuciyarta dole akan tankwabe roqon Binta saboda gudun bayar da kai, sai ta kasa. Muryarta a raunane ta amsa.

“In ya furta zan karbe shi Anti”.

Sai da hawaye ya so ya zubo wa Binta lokacin da kalaman Mujahid a kan Nabila suka fado mata, inda ya ke cewa.

‘Duk lokacin da Nabila ta gama boye-boyen son da ke kadai ki ka fuskanci tana yi min, idan ta furta ki sanar da ita ni ba na sonta. Ban taba mafarkin son irinta ba, kuma ba zan zahirantar da shi a filin rayuwata ba’.

Da kalmar godiya babu qaqqautawa Binta ta hadiye tausayin Nabila da ya cika maqogwaronta, wato ashe hasashenta ya zama gaskiya, Nabila na son Mujahid, shi kuma ba ya sonta? To wai ita da ta kinkimo wannan jidalin ta ina za ta sauke shi?

Da wannan hargitsin zuciyar ta fice daga dakin sakamakon kiran sallar magriba da  ta jiyo an qwala. Yadda ta fice da sauri haka ma Nabila ta miqe da sauri ta shige bandaki da zummar dauro alwala ta gaida mahalicci yadda za ta yi saurin raba zuciyarta da tuntunin hada asara da riba a soyayyar da zuciyarta ba ta shawarce ta ba kafin ta kimsa mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 5Rigar Siliki 7 >>

1 thought on “Rigar Siliki 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×