Skip to content
Part 10 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Zaune yake a falo daga shi sai singilet da gajeran wando, lemo mai sanyi yake sha yana hira da Haidar a waya. Zuciyarsa ƙal jin cewar Haidar din yana Airport alokacin zai taso zuwa 9ja. Salma ta shigo ta riskeshi a hakan, ganin irin yanda yake sakin murmushi sai abin ya burgeta ya kuma yi mata dadi. Zama ta yi har ya kammala wayar ta dubeshi da kulawa.

“Yau ɗan nawa da alama yana cikin nishaɗi, ina fatan da surukata kake waya?”

Dariya ya yi.

“Mum kenan, ni ba wannan ne a gabana ba. Haidar na hanyar zuwa 9ja.”

Ta saki fuska sosai.

“Kai masha Allah, amma na ji dadi. Ko ba komai zan dinga samun ganinka time to time ko don Haidar me son girkina.”

Ya yi murmushi kawai. Gani tayi wannan ce damarta don haka ta fiddo waya ta lalubo hoton wata budurwa ta miƙa mishi.

“Karɓi wannan ka gani.” Ya ɗan dubeta sai kuma ya sa hannu ya kar6a. Kyakkyawar budurwa Black Beauty, sanye take da riga doguwa ta Atamfa wanda ya kamata sosai har kirjinta ya fito ta sama. Ta yi daurin ture kaga tsiya. Ta wani turo baki wanda ya sha pink lipstick. Ya hade girar sama da ta ƙasa ya mika mata wayar gami da jan guntun tsaki.

“Please Mum, yanzu bani da lokacin aure. Duka-duka yaushe ma aka haifan wai?”

Ya ƙarashe da gatse, ta yi yar dariya.

“Fu’ad ɗana na kaina. Allah dai Ya shiryamin kai. Shikenan, nima ba aurennaka ne yanzu a gabana ba. So nake na ga ka zama namiji ka amshi kamfaninka da kanka ka ci gaba da kula da shi. Zama hakan ba zai yiwu ba tunda karatun nan ka kammala. Wannan kuma budurwar da kake gani ƴata ce, diyar Hajiya Murja Aminiyata, Sa’adah.”

Tun soma maganar har kammalawar bai ko kalleta ba, hankalinsa na ga wayarsa yana kallon wani Film. Ta fahimci hakan, ranta kuwa ya ɓaci. Hannu ta sa ta warce wayar, ya dubeta a harzuƙe sai kuma ya waske gami da jan guntun tsaki.

“Wai menene haka? Me kike so bayan zuwan da kika tursasani na yi? Please, kar ki ɓatan farin cikina.”

Salma ta hadiye maganganun da wai ɗan cikinta ne ke furtawa gareta.

“Wata alfarmar za ka ƙara yimin a karo na biyu, idan na isa kenan amma.”

Ya kalleta a hagunce, ta ci gaba da magana.

“Zuwa za ka yi muje gidan su Hayat, tun..”

“No Mum! Ba zan dauki wannan rainin wayon ba fa. Kin nuna bakya so naje wurin grandies ɗina, na fasa zuwa. Yanzu kuma ki yimin maganar zuwa wurin wasu villagers? Ba zan je, kar ma ki soma tursasani.”

Ta dubeshi sosai ta tabbatar da cewar iyakar gaskiyarsa ya faɗi mata, ta san Fu’ad, yanzu idan ta rantse sai ta shawo kansa to sai su ɓata lokaci su na abu ɗaya. Wayar kawai ta ajiye mishi tana murmushi.

“Shikenan My son, a sha zama lafiya. Idan kana bukatar zuwa wani wurin, kawai ka kirani. Ni zan wuce.”

Ya gyada kai, ya ji dadi da bata takura mishi ba. Sai da ta fice ya dauki wayarsa, Hanan wacce tun ɗazu take faman kiransa bai ɗauka ba kuma bai bi baya ba, ita ya kira.

*****

Yau ne ta kama ranar Kamu da yini a gidan su Nuriyyah. Wuri sosai mai kyau da tsada Hajiya Hafsatu ta kama. Haduwar wurin ta burge mutane da yawa. Kwalliyar white and blue aka yiwa wurin. Ƴanmatan Amarya sun sha ankonsu na Atamfa blue mai surkin baƙi da yellow kadan a jiki. Yayinda yara akai musu ankon doguwar riga ta atamfa blue mai ratsin fari. Cikinsu har da Humaira da Jamila, idan ka kallesu yanda fatarsu ta murje ta yi kyau sai ka rantse ba mazauna Kauyen Cinnaku bane. Sun yi kyau sosai sun yi ƙiba hakan yasa suka saje da mutan birnin.

Dab da za’a soma taro, Maryam da su Inno suka ƙaraso wurin. Tawagar Hajiya Hafsatu kenan, gaba daya suke tare har ƙawayenta da wasu cikin ƴan uwanta, su ma ankonsu daban ne. Maryam komai ta kalla burgeta yake, ta kasa kauda idonta daga kan Humaira. Yarinyar ta yi saurin girma a cewarta. Duk sadda za ta jima wurin kallon fuskarta, sai ta ji wani iri a jikinta. Tana so ta tuna ainahin mai fuskar sai dai babu damar haka. Gudun kada ta zurfafa a tunani ne ya sanya ta saurin kauda idanunta akan Humairar.

Wuri na musamman suka zauna daga gaba-gaba. Su Inno ba ka ce ita ce wannan Dattijuwar ta kauyen Cinnaku ba, ta yi kyau don har ƴar kwalliya Hajiya Hafsatu ta sa akai musu. Duk a cikinsu babu mai kuruciya sai Maryam, girma ya ɗan kama su kaɗan. Ita kuwa duka duka bata kai shekara arba’in ba ma a duniya. Wannan ta sanya Hajjo kanwar Hajiya Hafsatu wacce bata wuce sa’ar ta ba, tasu ta fi zuwa ɗaya. Yanzun ma tare suke a zaune suna ƴar hira sama-sama. Hajjon ita ce mai surutun da jan mutum a jiki, anan ne Maryam ta gane inda Nuriyyah ta dauko magana. Don Hajiya Hafsatu bata da yawan kwaramniya sai kirki.

Ba jimawa da zuwansu, sai ga Amarya da angonta, wannan sabon salo ne da ake yayi a zamanin da ake ciki, Amarya da Ango sai abokansa haka ake zuwa wurin biki. Nan da nan Dj ya umarci da a fita a tarbi Amarya da Ango. Daga yara kananun har ƴanmatan masu anko suka fita.

Huzaifa ya sha dakakkiyar shaddarsa Getzner blue. Hakanan itama Amaryar ta yi adon wani leshinta blue mai hudi-hudi. Naɗin kanta silver sai purse dinta da Takalmi. Ta yi kyau sosai, banda murmushi ba abinda take wanda hakan ya ƙara fidda tsantsar kyawunta.

Abokan ango na jere a baya, cikinsu har da Adam. Ya ci adon golden shadda, Kyau kam ba’a ma magana. Ba ya so ya jima a taron, ba don Umma da ta matsa akan rakiyar Huzaifa ba, da babu inda zai je don ji ya yi kawai ya fasa. To ganin Huzaifan ma bai ji dadin yanda ya coge ba hakan yasa dole ya lallaɓa ya fito. Khady ce ta soma hangoshi, nan da nan ta zunguri Hidaya.

“Kee, ga Handsome can ya zo!”

Yanda ta yi maganar da ɗan karfi ya sanya Ameena da ke gefensu duban inda Khady ke nunawa da ido. Ya ilahi! Wani abu ta ji ya taso mata tun daga yatsun kafa har zuwa kai. Ta tabbatar yau ta samu mijin aure, koda wasa ba za ta bari ya kufcemata ba. Wannan dai idan ta aureshi tana  ji a jikinta ta kerewa Nuriyyah. Ba ta so su Khady su ɗagota, dole ya sanya ta kauda idanunta daga kanshi, tana kara ji yanda suke zuzutashi. Kasan ranta banda zaginsu ba abinda take yi. Ita kanta ta gefen ido take bibiyarsa da kallo.

Tafiya take tana yi tana waige, burinta itama ta karasa ta tsaya a layi. Hannunta dauke da cingam da ta siyo a wurin mai dan tebur a kofar shigowa event center din. Bata kaunar ace an shiga an barta, ba ta yi aune ba ta bangajeshi wanda hakan ya yi sanadin zubar cingam din daga hannunta ya faɗi ƙasa.

Adam ya kalleta, ganin yarinya da ba ta fi Amirarsu ba, ya sanya ya danne ɓacin ransa.

“Lah Sori dan Allah.”

Yanayin yanda ta furta sorry din sai ya so ya yi dariya, ga dukkan alama ba kwararriyar ƴar makaranta ba ce. Ita kuwa ta rantsewa Jamila daman ba zata bari a rainata a wurin bikin nan ba. Hakan yasa take ta cakula turanci itama a dole ta faso gari a dauketa ƴar gaye. Durkusawa ya yi ya shiga tayata tsintar cingam din. Yana murmushi ba tare da ya kalleta ba yace.

“Yanzu duka wannan chewing gum din za ki ci? Ba kya tsoron ya jaza miki ciwon haƙori? Ba fa a son shan zaƙi da yawa.”

Ta dago kai sakaka tana dubansa, tunda ya furta chewing gum ta ji wani mugun zaƙi a ingilishinsa. Ba ta san sadda ta yi ƴar dariya ba. Alokacin ya miƙe tsaye, itama ta mike tana miƙa mishi hannu alamar ya bata. Kallonta ya ɗan yi, nan da nan ta faɗo ranshi.

‘Oh, yarinyar da ya hadu da ita ne a Mall. Mai tsoron tinted glass.’ Ya yi murmushi, ta maida martani.

“Ɗan biyutiful, tanku.” (Thank you)

Tana fadi tana yanga da ƴar muryarta, ta ware hannunta alamar ya bata cingam din. Ita fa ba raini,ta buga turanci ta kece rainin. Adam bai san sadda ya yi dariya ba. Girgiza kai ya yi.

“Gorgeous, turancinki dadi da sa dariya. Which class are you?”

Ta ɗan zaro dara-daran idanunta tana dubanshi. Ya ji wani yamm har bai san sadda ya kauda idanunsa ba. Class ta fahimta, nan da nan ta tuni da Class 2B ajin su Bilal.

“Class 2B.”

Ya yi murmushin da fararen haƙoransa suka bayyana kafin ya miƙa mata cingam din.

“Keep it up, wataran za ki zama abar alfahari in Sha Allah.”

Ta kuwa ji dadin maganarsa, ita kam ba ta so ya daina turancin nan, dadi take ji. Har ta yi gaba sai kuma ta juyo ta dubeshi. Shima kallonta yake yi. Tunawa ta yi da hakan rowa ce babu kyau, sai ta dawo baya da sauri ta tsaya gabansa. Lokacin har tawagar Amarya da Ango sun soma nufar ciki. Su Khady hankalinsu ya gaza daukewa daga kan Humaira da Handsome. Ameena da ke ji kamar ta je ta shaƙeta, tun ranar da aka fita da yarinyar ta zauna a gida ita kuma adalilinta ta ji ta tsaneta.

“What happen?”

Ya jefomata tambaya, Humaira dadi kasheta. Ta wangale haƙoranta kananu wadanda suke a jere tas. Abin ya burge Adam, har lokacin bai bar murmushi ba. Ya kuma gane, turancin ke burgeta.

Hannu ta ware mishi.

“Filis ka ɗibi chuuwiiin goma! Na tuna Mama ta hana ni rowa babu kyau.”

Ta mugun ba shi dariya ta kuma yi mugun shiga ransa. Ya dara sosai ita kuwa ta saki baki tana kallonsa, ta rantse da Allah kyakkyawa ne wannan.

“Ɗan Biyutiful.” Ta furta baki a washe. Ya dakatar da dariyar wacce ya manta rabonsa da ita.

“Na gode Gorgeous, kina da abin dariya. I like you.”

Murmushi ta yi wannan karon don bata fahimta ba. Sai dai ta amsa

“Lah, ba sunana gorjoyos ba, sunana Aishatul Humaira.”

Ya lumshe idanu ya bude a kanta.

“Sunanki mai dadi, amma ke kyakkyawar ce don haka tun ganina da ke na sanyamaki Gorgeous. Ko ba kya so?”

Ta girgiza kai tana dariya.

“Ina so.”

Sai a sannan hankalinta ya kai ga Amarya da har sun kai tsakiyar fili. Ido waje ta dubeshi, da sauri ta janyo tafin hannunsa ta juyemishi cingam din gaba daya.

“Ɗan biyutiful, ka ɗiba ka ajiyemin. An shiga babu ni!” Tana maganar tana tafiya da gudu-gudu. Mafarkinta na neman rushewa ba ta jera da Amarya ba. Tana zuwa ta bi sahun yaran, Jamila ba ta kusa da ita don haka babu damar surutu dole ta ja baki ta yi tsit aka ci gaba da tafiyar.

Mutuwar tsaye ya yi, murmushin ya ƙi yankewa a saman fuskarsa. Ya dubi hannunsa, a aljihu ya zuba sannan ya bi bayan tawaga yana mai jin wani irin sanyi da annashuwa a zuciyarsa.

Sai bayan an zauna ne suma abokan suka zauna wurin da aka tanada musamman dominsu.

Humaira da sauran sa’anninsu suka zauna wuri guda. Sai sannan Jamila ke tambayar inda ta shiga. Nan da nan ta tuno da Biyutiful da cingam dinta. Ta mike a hanzarce.

“Ke na manta cingam ɗina, bari na amso yanda muna cin abinci sai mu tauna kada muyi warin baki.”

Da wannan fi’ilin ta yi hanyar inda abokan ango ke zaune. Daidai lokacin da Ameena ta nufi teburin da Adam yake da zummar kai kayan abinci kasancewar su masu anko su ne masu rabon. Ko yaya ne tana so ta kulashi, tana ji a jikinta ba zai ga irinta kyakkyawa kuma haɗaɗɗiya ya kyale ba.

Gudun kada Mama ta ganta tayi faɗa ya sanya ta yin zagaye. Sai raba idanu take tana duban bangaren abokan Ango. Sarai ya ganta domin tun tasowarta idanunsa a kanta, sai murmushi yake ganin yanda take rarraba idanu. Tsintar kansa ya yi da shagaltuwa wurin kallonta har da harɗe hannu a kirji. Ameena dake takowa ta gama matowa da ita yake, jikinta har wani mazari yake tsabar kwarjinin da ta ga ya yi mata. Ta kara sauya salon tafiya tana wata rausaya. Ita a lallai ta kere mata, ta ɗan saci kallon  bangaren da su Hidaya ke hada-hadar rabon abinci, ta ga  hankalinsu ba ba’a kansu yake ba. Wannan ya fi komai ba ta haushi don ba haka ta so ba.

Koda ta karasa ta ajiye ko kallonta bai yi ba, sai a lokacin ta waiga ga inda hankalinsa yake. Humaira ta gani tana nufoshi, lokacin ta hangeshi sai washe baki take yi itama tana kara tabbatar da cewa ya cika ɗan biyutiful.

Tana zuwa ta  tsaya gami da ɗan rike haɓa da zaro ido.

“Kaga sai na manta ban karɓi ajiyata ba ko ɗan biyutiful? Allah Ya so ba’a soma cin abinci ba ma.” Ta ƙarashe tana ware ido can kan teburinsu, ta ga an soma kai abinci. Ganin shiru bai ce mata uffan ba sai ta kara dubansa. Ya ɗan basar ya kauda kwayar idanunsa. Hannu ya sa ya ciro mata cingam din a aljihu ya ajiye mata saman hannun, ba  da niyya ba, hannunsa ya gogi nata. Wani irin laushi ya ji a tafin hannun da ya shayar da shi mamaki. Ya kara kallon tafin hannun, har wani ja ja yake yi, ko da ido an san zai yi taushin. Da sauri ya kauda shaidan a tunaninsa.

Ita kuwa tsayawa ta yi ta kirga.

“Lah ai ba ka dauka ba.” Ta shiga kirgowa har guda biyar ta ajiye saman teburin don hankalinta ya tafi kan abincin da za’a kawo kada a zo bata samu an ajiyemata ba. Tana dire mishi ta yi gaba, sai ta tuno bai yi godiya ba ta dawo baya. Ganin  kiɗa ya soma tashi ya cika wurin ta ɗan russuna kadan wurin kunnensa yanda zai ji da ɗan karfi ta ce.

“Ka dinga godiya ɗan biyutiful, Mama ta ce mu dinga godiya idan an mana abu. Nima nagode da ka ajiyemin.” Daga haka ta yi gaba abinta da sauri.  Ameena tuni ta bar wurin tsabar takaici da bakin ciki. Ita ba yarinya bace, tuni ta fassara kallon da Adam ke bin Humaira da shi. Yarinyar da yanzu ta soma ƙirgar dangi ita kuwa gatanan da diri don tun tsayuwarta sauran mazan ke kallonta. Idan kuwa kyan fuskar ce ya ja hankalinsa itama fa ba abinda ta rasa. Ta dai daure iyakar daurewa ta bar wurin. Adam ya kasa magana, shirunsa bisa dalilai da yawa ne. Ya dubi cingam din ya kwashe ya zuba cikin aljihu. Yana cin abincin yana kallon Humaira, motsinta, da yanda take loma tana wani motsa bakin cike da yanga (a cewarsa) ya burgeshi kwarai. Karshe ya saita kansa daga barin kallonta yana murmushi kawai.

Koda aka kira su yin rawa da zumuɗi ta fita, Jamila na riƙota ta harareta.

“Lallai ma, cabɗin, ke ba abinda zai hana ni rawa. Kin manta Anti Nuriyyah ta ce za ta yi mana liki.”

Da haka ta shiga, ta soma rawarta mai abin dariya a English song, Amarya da Ango na daga tsakiya su kuwa su na zagaye da su. Adam ya tsinci kansa  da yi mata hotuna kala-kala. Ai kuwa Nuriyyah na hangota ta shiga yi mata kari. Maryam daga can girgiza kai ta yi da addu’ar neman diyarta shiriya. Abin ita kanta ya bata dariya. Inno me za ta yi banda dariya.

Adam ya mike cak ya karasa ya shiga yi mata liƙi. Humaira ta dubeshi tana washe haƙora, ba zato ta kalli gefen da Mamanta take, wata uwar harara ta yi gareta wanda ya sanyata ficewa daga filin ba shiri. Ya juya ga amarya da ango ya yi musu kari sannan ya koma mazauninsa.

Fuskarsa ta tuna mata da wata fuska da ta kasa tantancewa, kirjinta ya shiga dukan tara-tara. Nan da nan ta haɗa zufa, duk iyakar kokarinta don ta tuna wani abun ta kasa. Nan da nan kanta ya soma riƙewa, ba ta daina bin Adam da ido ba har ya fice daga taron gaba ɗaya.

“Maryam, lafiya?” Hajjo ta jefamata tambaya, ta girgiza kai tana yaƙe. Ganin haka Hajjo ta miƙa mata gorar ruwa.

“Karɓi ki sha.”

Ba musu ta karɓa ta sha da yawa kuwa.

Da kyar ta samu nutsuwa ta daidaita kanta sai dai hakanan take jin faduwar gaba da bata san dalilinsa ba.

Haka akai taro aka tashi lafiya sumul. Ana tashi kowa ya fito waje. Sun je dab da motar da ta kawo su suka tsinci muryarsa.

“Gorgeous.” Suka waiga suna dubansa. Wannan karon ya saka wani arnen baƙin gilashi da ya kara fiddo da cika da haibarsa.

“Thank you so much.”

Daga nan ya juya ya nufi motarsa. Baki galala suke kallonsa, Humaira turancin ke bala’in kasheta. Nan ta ba Jamila labarin duk yanda sukai, suna labarin suna shan dariya.

“Tafiyarsa ma abar kallo ce.”  Fadin Khady alokacin da suke bin Adam da kallo. Ba su yi aune ba sai ganin Ameena suka yi da sauri-sauri ta nufi inda yake.

“Waccan ba Ameena ba ce? Wurin fa Adam za ta je.”

Suka tsaya kallon ikon Allah da wannan shishshigin.

Har ya bude mota ya ji magana sai dai bai kawo da shi ake ba, yana dab da shigewa ta yi saurin zuwa gami da rike murfin motar. Kallon da ya watsamata ya sanya duk sai ta susuce ta rasa bakin magana.

“Lafiya dai ko?”

Inaa! Ta rasa ta cewa sai rawar murya.

“Amm..dama..” Sai ta yi shiru.

“Excuse me please.” Ya fadi yana rike murfin kofar, ta fahimci manufarsa, bata da zaɓi sai na matsawa ya kuwa rufe murfin ya tayar da motar, can ƙasan ransa tsaki kawai ya ja. Ba yau ne rana ta farko da mata ke mishi wannan rainin wayon ba. Sai a mishi magana kuma ya nemi ba’asi a rasa ta  cewa. Masu karfin hali su fadi abinda ya kawo su, sai dai ya basu hakuri ya bar wurin. Ameena na tsaye sai ƙurar motarsa ta gani, ta ji dariya a bayanta. Su Hidaya ta gani, dariya sosai suke, ta daure ta share kwallar da ta taho mata. Nan da nan ta ji ta tsani Adam da abinda ya yi mata. Ta tuna zasu hadu wurin dinner gobe. Ta sha alwashin sai ta rama. Kwafa kawai ta yi ta wuce ba tare da ta ce musu komai ba.

*****

Gudu sosai yake yi a kan babban titi, daga masu zaginsa sai masu Allah wadai. Ko a jikinsa domin kuwa kiɗa ya ware, fatansa ya samu wurin da zai je ya ɗan shaƙata. Bai kuwa yi aune ba ya ci karo da wata mota wanda ya sanya tashi motar wani irin juyi karshe ya hadu da karfen dake rike da traffic light kansa ya bugu da jikin sitiyari.

Adam wanda bai wani bugu sosai ba, ya yi saurin fitowa daga motar ya isa inda motarnan take. Yana budewa da taimakon mutanen dake wurin suna salati, suka ɗago matashin saurayin wanda jini ya ɓatawa fuska.

“Ya Salam.” Fadin Adam.

“Ko za ku taimaka mu sanyashi a motana?” Ba musu aka taimaka mishi. Daga haka ya dawo motar ya kwashi duk abinda ya san za’a iya dauka sannan ya rufe. Allah Ya taimaka akwai yan sanda a wurin. Biyu suka tsaya wurin motar don a samu a miƙa station. Da taimakon daya Adam ya mika FU’AD asibiti mafi kusa. Ganin da jami’in tsaro ne ya sanya aka karɓesu aka shige ciki da Fu’ad. Wayar Fu’ad din da ke jikin Adam ne ta soma ƙara. Duban wayar ya yi. “Mum.” Abinda ya gani kenan.

“Ai gwara ka dauka idan wani makusancinsa ne a faɗi mishi.” Cewar ɗan sandan. Ba musu ya ɗaga kiran.

“Ka kyauta ka ji Fu’ad, wato shi ne ka shanyani ina ta jiranka, ashe ba za ka zo ba? Hakan da ka yimin shi ne daidai?”

Da jin muryar sai da gabansa ya faɗi. Kamar yasan muryar haka yake ji musamman da ta ambaci Fu’ad. Sai dai kuma wadanda yake zaton ba sa gari. Ya daure ya amsa.

“Ba Fu’ad din bane.”

Da sauri ta ce.

“Waye?”

Ya zarce da abinda ya kamata. Ya labarta mata abinda ya faru.

“Na shiga uku! Shi kadai ne tilon ɗana a duniya. Faɗamin sunan asibitin?” Ta ƙarashe da muryar kuka.

Adam ya bata amsa wannan karon muryarsa a daure. Jikinsa ya gama ba shi ko su waye. Daga haka ya kashe wayar ya nufi dakin da Fu’ad ke kwance da gaggawa don ya tabbatar da zarginsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 9Rumfar Kara 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×