Skip to content
Part 9 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Tafe take a tsakar filin wani irin fili, da ta yi gabas ta ji ta ci karo da gini, hala ta juya ta dawo yamma nan ma ta kara bugar gini._ _Ta yi kudu nan dinma karo ta kara ci, kirjinta ya shiga bugu, ta soma kallon sararin samaniya ganin yanda ya kara turnukewa wanda hakan ke nuni da saukar ruwa a kowane lokaci._ _Kallon gabas da za ta kara yi ta ga ginin nan ya tarwatse ta hangi wani ginin gida babba mai yalwar fitilu masu haske. Da wani irin sauri ta soma tafiya tana nufar gurin, sai dai ba ta yi aune ba ta ji ta taka wani karfe mai tsini, sukar da ta ji shi har tsakar kanta._ _Ta yi azamar cire kafarta a wurin tana kiran sunan Allah. Haka ta ci gaba da tafiya dakyar jini na ɗiga. Ba zato ta ji tsayuwar mota a gabanta. Kafin ta yi wani yunkurin ta cikin motar ta bude kofa ta fito._ _Wani irin kibiya ne mai tsinin baki a hannunta ta nufota ta saita a daidai kirjinta. Ta shiga magana a tsawance._

“Maryam! Na fi karfinki har abada wallahi! Yau kuma ni zan zama ajalinki. Sai na kashe ki na kashe banza saboda ba ki isa ki raba ni da farin cikina ba. Ba ki isa ki kwacemin abinda yake mallakina ba! Har abada nawa ne!”

Cikin kuka Maryam ta amsa.

“Kar ki kasheni Salma, kar ki wannan yunkurin. Ki ji tsoron Allah, ki tuna da rai da mutuwa a hannunSa take._ _Ba ki isa ki rabani da numfashina ba muddin lokacina bai yi ba.”

Wata iriyar dariya Salma ta saki sannan ta ɗaga kibiyarnan ta yi kanta gadan-gadan.

Jijjigata take tana kuka da kiran sunanta ganin yanda take sharara uban gumi tana ambaton Innalillahi.

Wannan kuka na Humaira ya tashi Inno da Jamila da ke jan munshari. Ganin yanayin da Maryam ke ciki duk suka yo kanta. Inno ce ta yi karfin halin tofamata adduoi a karshe suka ga ta rage jan numfashi, a hankali kuma ta buɗe idanunta tana duban mutanen dakin. Wani irin gumi ke zuba daga saman fuskarta.

“Kaina ciwo.” Shi ne abinda ta furta. Inno ta mike, ta duba yar jakarta ta fiddo maganin ciwon kai da kusan ba ta rabo da shi duk domin Maryam din. Duban Humaira ta yi.

“Maza dauko ruwa a kicin. Za ki iya ko?” Humaira na kukan ta gyaɗa kai sannan ta mike ta fito. Fitilu a kashe kowa na bacci, a hankali ta bude kofar ta dauki ruwan mara sanyi.

Sai bayan Maryam ta sha sannan Inno ta sa ta mike ta kara dauro alwala ta kakkaɓe makwancin ta sauya ɓarin kwanciya. Bacci ya yi awon gaba da ita bayan ta yi addu’a. A lokacin ne su ma suka koma bacci, Humaira ta naniƙe kusa da mahaifiyarta tana jin duminta. Itama riƙon ta yi mata sosai har abin ya ba Inno tausayi. Karshe suka kashe fitila kowannensu ya koma bacci.

Washegari da safe Maryam cike da damuwa ta dubi Inno.

“Na kasa tuna komai, duk sadda nayi yunkurin na tunano, sai na yi munanan mafarkai na wata mace mai suna Salma. Sai na farka da ciwon kai. Haka zan ci gaba da rayuwata ba tare da na tuna asalina ba?”

Sai ta kara sanya kuka, Humaira da ke gefe su na karyawa tare da Jamila, itama ta shiga hawaye, ta kasa gane me Mamanta ke kokarin tunawa. Ta rasa gane bakin zaren. Hankalinta bai kai ta yi wannan tsinkayen ba muddin ba fitowa akai aka yi mata bayani dalla-dalla ba.

“Hakuri za mu yi Maryam, In Sha Allah komai zai zo karshe. In sha Allah ba za’a rasa mafita ba da yardar Allah. Mu dai dage da addua komai zai zo karshe.”

Haka Inno ta yi ta nusar da ita har a karshe ta ji hankalinta ya kwanta ta samu suka fita domin karyawa.

*****

Dukan kofar dakin ta ke yi sai dai ko gezau bai yi ba. Yana zaune daya cikin kujerun falon ya harɗe kafa yana girgizawa, cikin kwanciyar hankali yake busa hayaƙin sigarin yana kallon kofar.

“Fu’ad, ni za ka yiwa haka? Fu’ad kana manta cewa ji mahaifiyarka ce! Nace ka budemin kofa!”

Ya yi wata ƴar shaƙiyiyar dariya kafin ya mike ya bude kofar. Hajiya Salma ta watsa mishi wani mugun kallo, daurin ɗankwalinta har ya toge. Za ta soma masifa ya dora hannunsa saman leɓensa.

“Shii! Kinsan me nake buƙata, shi za ki bani kawai.”

Ta fashe da kuka.

“Fu’ad yau kai ne ke son zuwa wurin mutanen da basu kaunata. Mutanen da ba su ƙi su wayi gari su ganni a mace ba. Yau kai ke son zuwa wurinsu? Wa ya ta6a nemanka a cikinsu?”

Ya ta6e baki gami da girgiza kai.

“Nifa ba wannan na tambaya ba, ban damu da ko suna sona ba ko basu yi, wannan matsalarku ce keda su. Kawai ina son zuwa wurinsu. Kuma ya zama dole ki bani address dinsu idan kuwa ba haka ba nima za ki rasa ni.”

Ganin yanayin da ya furta maganar ta kara tabbatar da gaskiyarsa. Wannan ne dalilin da ya jawo mata tashin hankali saman fuskarta.

“Shikenan, naji zan bayar. Amman sai ka daukarmin alkawarin babu uban da za ka nunawa hanyar gidana domin bana bukatar ganinsu.”

Ya ɗan dafe kai.

“Kar ki sa min ciwon kai mana Mum, na fadamaki wannan ba damuwata ba ce. Bukatar ganinsu nake.”

Ta jinjina kai ta juya zuwa dakin, rainin da Fu’ad ya yi gareta har ya bar bata mamaki sai tsoro. Nan gaba tana gudun wani abu ya biyo baya. Ta daure ta ɓoye fargabanta, takarda ta dauka da biro ta rubuta mishi kwatance yanda ko wa ya faɗawa zai fahimta. Miƙa mishi ta yi, yana karɓa ya ɗan rungumeta yana murmushi.

“Ko kefa, shiyasa bani da kamar ki a duniya. I love You so much.”

Ta yi murmushin yaƙe, akan idonta ya fita. Waya ta dauka ta dannawa aminiyarta Hajiya Murja waya.

“Ran manya ya dade.” Cewar Hajiya Murja daga ɗaya ɓangaren.

Hajiya Salma a rude ta katse ta.

“Murja akwai matsala, kina ina?”

“Ina gida amma kinsan na fadamaki zan je gidan biki anjima. Ina fatan ba allura ke shirin tono garma ba?”

“Um um Murja, mun kashe maciji ne ba tare da mun sare kan ba. Wajenki zan zo sai na samu rakiyarki wurin Kumurci. Ko me akwai, zan faɗamaki.”

Da haka suka yi sallama. Ba ta yi wata wata ba ta dau abinda za ta bukata ta fice daga dakin a hargitse. A falon su ka yi kiciɓus da Hayat wanda nashi ran a ɓace yake. Kallon kallo suka hau yi kowanne fuska dauke da alamar tambaya. Ta kauda kanta.

“Gidan Hajiya Murja zan je, akwai maganar da zamu tattauna.”

“Wata ƙurar ce ta taso?” Ya jefamata tambayar.

“Fu’ad ne matsalar.” Jin an ambaci Fu’ad ne ya sanya shi tattaro dukkan nutsuwarsa.

“Me Fu’ad ya yi?” Nan ta labarta mishi dukkan abinda ya faru. Sai ta ga ya yi wani murmushi.

“Hayat, na faɗamaka matsalata ka yi dariya? Me hakan ke nufi?”

“Ba matsala ba ce ai, ke kanki kin fi ni sanin abinda ya kyautu. Matsalata ta fi taki zafi, sai dai ni ban wani dauketa matsalar ba balle kuma naki da bai taka kara ya karya ba.”

Ba ta da lokaci, ta dubi agogo cikin sauri da ƙaguwa ta ce.

“Wacce ce ta ka?”

“Bilkisu, ta kai ƙara wurin iyayenmu cewar bana kyautata ba.”

Tsaki Hajiya Salma ta ja.

“Ina da abinda ya fi wannan muhimmanci, idan na dawo sai na saurari zancen borarka.”

Daga haka ta yi gaba, iyakar gaskiyarta ta fada don ba ta dauki Bilkisu mace ba. Ba ta dauketa macen da za ta tsaya kishi da ita ba. Saboda mijin bai ta6a nunamata ita din mace ce ba mai daraja da kima ba.

*****

Tun sadda ya bubbuga ƙasar ya kurawa wuri guda ido kafin ya dubesu fuska a daure.

“Akwai matsala!”

Hajiya Murja da  Salma suka kuramishi idanu, baki na rawa Salma ta ce.

“Wace irin matsala?”

“Mutuwa da Rayuwa!”

Ya furta da kwarin gwuiwa.

Ƴan hanjin cikin Salma ya shure wuri.

“Matacciya tana dab da zama rayayya. Mutuwa ce ba zan ce komai akai ba! Sai dai ki saurari fallasa nan ba da jimawa ba!”

A rude Salma ta ce.

“Ka taimakeni Kumurci, ka yimin bayanin da zan gamsu. Na shiga ruɗani.”

Ya yi wata dariya.

“Matar tsohon mijinki da ki ka ɓatar tana dab da dawowa hayyacinta. Bincike ya nunamin tana dab da inda kike. Dawowarta ba zai miki da kyau ba, ba ma ke kadai ba har da mijinki.”

Gumi ya shiga karyomata ta ko’ina.

“Ka taimakeni Kumurci, idan ba kai ba bansan wurin wanda zan je ba. Me ya kamata ayi? Wallahi ko menene zan biya na maka wannan alƙawarin. Idan da hali a raba ta da numfashinta ma kwata-kwata.”

Sai kuka, Murja ta rike hannunta alamar rarrashi. Ta kara da fadin.

“Kumurci ka san kudi ba matsalar Salma ba ce, ba yau ne farkon da ka soma yi mata aiki ba. Don haka ko nawa kake so za ka samu matukar aiki zai yiwu.”

Ya yi murmushi.

“Nasan bani da wannan matsalar, sai dai aikin yana da matukar hatsari da kuma takatsantsan. Idan har aikin bai ci ba to ina ma tabbatarmaki ni kaina ba zan tsira ba.”

Hajiya Murja ta girgiza kai tana wata ƴar dariya.

“Ballantana ma ba zai fi karfinka ba. Anyi aikin shekaru ma ta ina wannan zai fi karfinka.”

Ya yi wata iriyar dariya.

“Ke Murja! Mutuwa gaskiya ce! Yanzu dai me kuke so a yi?”

“A kashe ta!” Salma ta furta a hanzarce.

Ya girgiza kai.

“Ba zai yiwu ba! Domin na rantse sai ta dawo.

Suka dubi juna, suka yi shiru can kuma Salma da hanzari ta dubeshi.

“A kurumta ta, yanda koda ace ta dawo ba zata iya bayyanawa duniya komai ba.”

Ya yi wata shu’umar dariya yana mai daga hannu alamar jinjina.

“Kai Salma! Kefa shaidaniyar gaske ce. Ko ni wannan tunanin bai zo min ba. Kar ki samu damuwa, wannan kamar anyi an gama.”

Jin haka ta yi dariyar cin nasara ta goge hawayen fuskarta. Jaka ta rarumo ta ajiye mishi maƙudan kuɗaɗe. Ya kalli bandir din dubu har uku ya yi dariya.

“Wannan aiki ki tabbatar kamar an yi shi an gama. Maryam ba za ta kara ji ba ballantana ta amsa!”

Hajiya Salma ta ji wani irin dadi. Sai a sannan ta yi maganar Fu’ad da yanda take so a raba shi da tunanin dangin mahaifinsa.

“Wannan matsalar ba wata mai yawa bace. Koda kwanaki biyu ne dai ya yi a wajen garin nan, kafin ya dawo aiki ya kammalu.”

Shiru ta ɗan yi tana nazari can kuma ta ce.

“Wannan ba matsala bace. Zan san abin yi.”

Ya gyada kai.

“To kuwa ki ka yi hakan, muddin ya dawo babu shi ba tuna ko uban nashi balle danginsa.”

Suka yi dariya kafin su tattara su bar wurin cike da jin dadi. Gidan Hajiya Murja ta koma inda direbanta ke jira. Ta dubi Hajiya Murja.

“Kinsan fa ba karamin sa’a muka yi ba, ashe abu ya kusa lalacewa muna zaune?”

Wani murmushi Hajiya Murja ta yi.

“Ke dai bari, sai dai kinga ai Allah Ya rufamana asiri. Domin na tabbatar ba ku kadai ya shafa ba, ni kaina ba zan tsira ba idan Maryam ta yi wani furucin.”

Hajiya Salma ta yi kwafa.

“Ban ta6a kishi irin wanda nake yi akan Maryam ba. Ke na tsaneta ne ma! Bilkisu kallonta nake kamar ma babu ita a duniyar. Ban dauketa a wata aba mai daraja ba. Shiyasa ko yanzu da zan fito maganarta Hayat ya so yimin sai dai ban tsaya sauraronsa ba.”

Hajiya Murja ta karkace ta yi waya dariya.

“Allah Ya ja min da ranki Aminiya. Kina cin karenki ba babbaka wallahi.”

Salma ta yi wani irin murmusawa gami da yin farr da ido.

“Mu din wasa ne Murja? Shekara nawa muna dakon so? Ai kuwa kinga ba zamu bari shukar wasu ta nuna ba. Ko ta wace hanya kuwa.”

Suka yi dariya gami da cafkewa. A karshe suka rabu ta shige mota direba ya ja. Hajiya Murja aka koma ciki don shirin gidan biki.

*****

Taɓe baki take tana girgiza ƙafa yana kwararo mata jawabin yanda suka yi da Bilkisu har da barin gidan da ta yi. Tana jin cewar saki ya tabbata ta yi wata shu’umar dariya.

“Ah, ka cemin Bora kuma an ƙara gaba.”

Haka kawai sai ya ji ya kasa dariyar sai yaƙe.

“Ai da ta ci gaba da zama marar ƴanci.”

Ya share zancen.

“Yanzu dai gobe zan je Yoben, idan ya so sai naji hukuncin da Baba zai yanke.”

“Muje tare.” Ya tsinci maganarta kamar daga sama, wannan ta sa ya dubeta baki a sake. Ya kasa gasƙatawa ya dubeta dakyau.

“Kika ce me?”

Ta yi farr da ido.

“Cewa nayi tare zamu je kuma har Fu’ad. Ko akwai matsala?”

Ya girgiza kai sai dai haka kawai ya ji wata iriyar faɗuwar gaba.

“Shikenan, zan yi waya a gyara maku gidana. Kamar can zai fi muku ko?”

Tana murmushi ta gyada kai kawai, wani irin farin ciki take ciki, ta shirya komai yanda ya dace, Fu’ad wannan karon ba zai ƙi bin ta ba koda kuwa su ya fi tsana a duniya.

Shi kuwa a wannan lokacin yana tare da Hanan su na sheƙa ayarsu. Sai bayan komai ya lafa ne ya miƙe ya shige toilet. Sai bayan ya fito ne Hanan ta zuba mishi idanu. A rayuwarta za ta ce bata ta6a samun wanda ya iya tafiyar da mace kamar Fu’ad ba. Tana ji a jikinta ko aurenta ya ce zai yi to babu abinda zai hana ta aure shi. Za ta iya sadaukar da komai don ya tabbata nata ita kaɗai.

Hura mata iska ya yi wanda ya sanyata kifta idanun, ta sauke ajiyar zuciya ta a dubansa. Ya kauda nashi idanun ya juya mata baya Yana suturta jikinsa. Ganin bai ce uffan ba ne, ya sanya ta miƙewa ta rungumeshi ta baya.

“Ina sonka wallahi.”

 Jin abinda ta ce ya yi wani murmushi da ya kara fidda tsantsar kyawunsa.

“So? Kuma a Bariki? Ban ta6a ji ba.”

Maganar ta soki zuciyarta, ta daure ta janye jikinta tana murmushi. Daga haka ta shige banɗaki. Ya bi bayanta da kallo. Ba laifi ta yi mishi yanda yake so, amma maganar soyayya tsakaninsu wannan kuma ta zo mishi da rainin hankali. Bai yarda akwai matar da za ta yi soyayya da zuciya daya ba don wata bukata ba. Soyayya ana yi don abu biyu, wato kudi da biyan bukata. Banda wadannan kuma, babu wani abun.

Wayarsa ce ta yi ƙara, ya duba. Text ne da lambar Mum dinsa. Neman gaggawa take mishi, hakan ya ɗan ba shi mamaki a karshe ya ajiyewa Hanan kudi saman gado ya bar hotel din.

Koda ta fito ta ga ba ya nan, ta kai duba saman gadon ta ga ajiyar da ya yi mata. Wani kululun bakin ciki ne ya tokareta. Ya nuna dagaske ba ta da wani amfani wurinsa sai na biya mishi bukata.

“Ba zai yiwuwa ba Fu’ad, ina sonka. Ba boka ba Malam sai ka zama nawa ni kadai. Sai ka aureni!” Ta ƙarashe tana mai jin wani rauni a kasan ranta.

*****

Da kyar da siɗin goshi Salma ta shawo kan Fu’ad ya bi su zuwa Yobe. Sai da ta yi mishi kuka akan bai damu da dukkan farin cikinta ba, ya fi son mahaifinsa akanta sannan ya amince da batun zuwa ba don ya so ba. Ko a motar yna zaune a gaba, fuskarnan kamar an aikomishi sakon mutuwa. Cika kawai yake yana batsewa. Kunnensa toshe da headphone yana jin kiɗa har suka isa. Gini ne na zamani inda suka tsaya sai dai duk haɗuwarsa bai kai rabi rabin wanda suke ciki ba a Kano. Hayat ya dubi Salma.

“Sai ku sauka nan ku dan huta, na sa anyi muku order na girki daga Hotel, za’a kawo nan ba da jimawa ba. Zan karasa can gidan.”

“Ƙauye dai kauye ne! Ba’a sauyawa tuwo suna.” Daga faɗin haka ya fice a motar ya soma nufar cikin gidan. Wani abu ya tsayawa Hayat a kahon zuci, ya dubi Salma ransa a tsananin ɓace.

“Kinsan da cewa akwai ranar dana sani ko? Muddin ba ma so kwa6armu ta yi ruwa, ki gaggauta yiwa tufkar hanci.”

Salma ta yi shiru idanunta a kan Fu’ad har ya shige. Karshe ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta ga Hayat.

“Kar ka damu, sai dai kuskure ne ka furta dana sani a kalamanka, ban ga ranar ta ba. Saboda har abada wanda ya mutu ya mutu.”

Ya yi murmushi.

“Kina wasa kenan, a dai juri zuwa rafi.” Itama murmushin ta yi, kowa ya riƙe fahimtarsa ta fice a motar ganin direban da ke aikin jidar kaya zuwa ciki ya kammala ya dawo.

*****

Falon gaba daya zuri’ar Malam Abdallah ne ciki, daga yaransa har jikokinsa su Bilkisu, Nuhu da sauransu.  Hayat na gefe daya ya sunkuyar da kai, sai ka rantse ko yatsa aka sanya mishi a baki ba zai ciza ba.

Alhaji Bello ya yi gyaran murya ya bude taro da addu’a kafin ya soma magana.

“Alhamdulillah, muna godiya ga Allah Mahaliccin dare da rana, sanyi da zafi, hakanan rani da kuma damina. Hayatu, Bilkisu. Wannan taron da ku ke gani a kanku ne aka yi shi ba kowa ba.”

Ya dan yi shiru, Hayat dama ya san da hakan, Bilkisu da ko kallonsa ba ta kaunar yi ta kara noƙe kanta a ƙasa.

un haihuwar Bilki, na dauki alkawarin aurawa Hayatu ita, sai dai kuma a yau ina mai nadamar wannan haɗi da nayi. Da ace nasan zai zama cutarwa ga ɗayansu, da ban soma ba. Wai ni nayi ne don karfafa zumuntar dake tsakaninta da ɗan uwana da kuma zuri’armu baki daya. Sai dai a yau ina mai tsantsar nadamar abinda nayi saboda yau an wayi gari Hayatu ya saki Bilkisu. Saki mafi muni.”

Wadanda basu sani ba suka hau salati. Hayat sai a sannan ya dago idanu a waje yana duban Bilkisu da iyayen. Yaha sai sharar hawaye take daga can gefe guda.

“Ya isa, ya isa hakanan.” Kawu Lawwali ya ɗan tsawatar musu.

“Yaushe akai haka? Bilkisu sharrin da za ki yimin kenan? Ni Hayat da bakina na furta saki gareki?”

Sai kuma kallo ya koma kanshi. Alhaji Bello ya daka masa tsawa.

“Yimin shiru! Waye sa’anka a nan wurin? Kar ka maida mutane kamar wasu jahilai.”

Hayat ya ɗan russunar da kai.

“Ka yi hakuri Abba, amma a iyakar sanina Ni Hayat ban saki Bilkisu ba. Idan kuwa na saketa gatanan ta rantse ta kuma nuna shaida.”

 Jikin manyan ya ɗan yi sanyi banda na Alhaji Bello da  Malam Kabiru wanda suka san kalar sakin da ya yi. Shi kansa Hayat din ya san komai, kawai dai burinsa a yarda da shi.

Bilkisu ta dubeshi tsakar ido.

“Hayat ya sake ni. Ba zan iya karya da..”

“Kar fa ki ɓata bakinki Bilki, nasan komai. Na kuma yarda da ke. Don haka yau ku shaida, kamar yanda Hayatu ya rabu da auren Bilkisu, Ni Bello na cire shi…”

Ai tuni kowa ya soma a’a a’a, Hadiza babbar yayarsu ce ta daka mishi tsawa.

“Injiniya! Kana hauka ne? Kar kusa ka bari ɓacin rai ya sanya ka aikata abinda zamu yi dana saninsa a zuri’ar nan.”

Wannan ne ya kashe bakin Injiniya ya yi shiru yana sauke numfashi yayinda kirjinsa ke wani irin zafi.

A karshe Bilkisu ta kara fadada bayanin yanda akai sakin ya afku da kuma dalilanta masu kwari na saɓawa umarninsa ta shigo da Adam cikin gidan.

Wadanda basu sani ba abin ya ta6a ransu ainun.

“Allah Ya shiryamana zuri’a. ” Shi ne abinda Gwaggo Hannatu ta furta. Hayat dai kasa cewa komai ya yi sai zufa. Ji yake kamar ya tashi ya maƙure wuyan Bilkisu ya kasheta har lahira. Yaha tayi bayanin abinda duk ta sani na zamantakewarsu. A karshe Malam Kabiru ya dakatar da ita. Ya kara da fadin.

“Ba abinda zamu ce gareka Hayat sai fatan Allah Ya ganar da kai, Ya shiryeka. Mun gode sosai da irin riƙon da ka yi ga ɗiyarmu. Sai dai ka sani Bilkisu ta saku, babu batun kome. Ina maka fatan alheri a rayuwa. Sannan ke kuma Bilkisu, ina so ki yafe mishi. Duk abinda Hayat ya aikata ba ke ya cuta ba. Kai kuma Hayat ka ji tsoron Allah, ko ba akan Bilkisu ba. Dukkan hakkoki ya rataya a wuyanka na iyalinka komai kankantarsa dole ne ka sauke. Ka manta cewar dukkanmu abin kiwo ne, kuma za’a tambayemu game da kiwon da aka bamu?”

Malam Kabiru ya shiga nasiha, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba. Gaba daya falon da wadanda ransu ke a harzuƙe, da wadanda ke kokarin aibata Hayat duk suka ji jikinsu ya yi sanyi idan ka cire Hayat wanda ya ke jin nan duniya ba matar da ta tsaneshi sama da Bilkisu tunda har ta haɗa shi da ƴan uwansa. Kwafa kawai yake a zuciya yana saƙe-saƙe.

Haka taron ya watse aka bar Hayat da iyayensu maza yana neman gafara. Dakyar Bello ya furta ya yafe mishi bayan Malam Kabiru sun sanya baki. Bilkisu itama ba ta wani ja ba daman ta yafe.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 8Rumfar Kara 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×