Skip to content
Part 35 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Barrister Abeed ya yi shiru bayan ya miƙa wa Salma duk takardun da ya kyautu ta sa hannu kafin zuwan matar da ake son itama ta saka nata hannun. Ganin yanda ita kanta Salmar fuskarta ta nuna kamar ba’a son ranta bane ya sanyashi kasa barwa cikinsa har sai da ya fesar.

“Wai nikam Hajjaju, mene fa’idar yin abinda ranki bakya so? Meke faruwa ne?”

Ta kalleshi ranta a ɓace.

“Ba ruwanka da dalilina, ba don haka nayi kiranka ba. Don haka ka kama bakinka.”

Ya numfasa gami da ɗan jinjina kai ba tare da ya dora uffan ba. Ba jimawa suka ji sallamarta. Suka dubi hanyar shigowa falon. Kallo ɗaya ya yi mata ya san ba karamar ƴar duniya bace. Sai bayan zuwanta suka gaisa da Barrister, ta dubi Salma tana mai taunar cingam da sakin dariyar rainin wayo.

“Sannu Hajiya Salma, ana ta hada-hada?”

Murmushin yaƙe Salma ta yi tana mai jin kamar ta shaƙeta, ta miƙawa Barrister takardun.

“Ok, yanzu ina shi yaron?”

Tambayar Barrister ta sanya suka dubeshi. Ganin basu fahimta bane ya sanya ya yi musu bayani.

“Kin san sai da sa hannunsa shima a matsayinsa na mallakin wuraren.”

Salma ta dubi Halima cike da bakin ciki.

“Kinji ai.”

Halima wacce tuni ta yi saranda cikin faɗuwar gaba ta ɗan sauya fuskarta. Ta tuna abinda Hanan ta ce mata game da Adam. Ta tabbatar ba wata hanya. Tana huci ta dubi Salma.

“Ko zamu iya magana?”

Salma ta kalli Barrister wanda ke ƙare musu kallo yana nazari, kamar babu alamun yarda.

“Ba komai.” Fadin Salma fuska a ɗan sake.

Suka mike suka nufi ɗakinta.

“Salma! Ba dukiyar Fu’ad na nemi ki bani ba, daga cikin abinda kika mallaka a karan kanki za ki bani! Salma ki fita idona wallahi tun ban tonamaki asiri ba. Kalli shaidar zan iya komai.”

Ta ciro waya ta bude whatsapp gami da nunamata hoton da Gwaska ga turo. Yana tsaye daidai kofar gate din gidan Alhaji Zakariyya mahaifin Haisam. Salma ta maida duba ga Halima cike da tashin hankali.

“Naji! Sai dai ki sani ba zai kai yawon na Fu’ad ba saboda kusan gaba daya dukiyar tasa ta fi yawa.”

Gudun kada ta yi biyu babu ta amince. Suka koma aka sauya shawara. Barrister yace dole zasu yi hakurin zuwa gobe don ya shirya takardun da ya kamata. Dole Halima ta amince da hakan aka sulhunta.

Barrister Abeed na shiga mota ya dulmiya cikin kogin tunani, meyasa Salma ke son bayar da dukiyar maraya? Mene dalilinta na sauya shawara da aka ce lallai sai da sanya hannun Fu’ad?

“Hakan na nufin gayen ba shi da masaniya a kitumurmurar da mahaifiyarsa ke shiryawa?” Ya furta a fili, ya tuna sadda aka damƙa mishi amanar dukiyar Fu’ad a hannunsa bayan an karɓe daga hannun Barrister Munir. Ya taɓa fadamasa cewar Alhaji Haisam ya so su hadu ya ce akwai maganar da yake son yi da shi Barrister Munir din sai dai lokacin yana Abuja. Koda ya dawo sai labarin mutuwarsa ya ji. Ya ji ciwon rashin sanin taƙamaiman abinda zai ce. Sai dai jikinsa ya ba shi ko mene ya shafi dukiyarsa.

Ajiyar zuciya Barrister Abeed ya sauke, toh ina hujjar take? Ba shi da hujjar komai tunda duniya ta san Fu’ad shi kadai ne ɗan Alhaji Haisam. Ba zai iya tunkarar Fu’ad ya ce bai yarda da takun mahaifiyarsa ba. Ya share zancen kwata-kwata tunda dai an fasa taɓa dukiyar marayan.

*****

Bayan tafiyar su Engineer da sauran manyan iyayen. Wadanda kawai suka rage, Malam Kabiru sai Gwaggo Rakiya, Umma da Baba Yaha. Sai kuwa Humaira wacce ke tare da Maryam. Anyi hotuna tamkar kada a rabu, Hajiya Rasheedat ji tayi kamar ta bi mahaifinta don ganin sauran danginsa, sai dai Prof ya musu alkawarin da zarar sun dawo daga Kano zasu zo. Inno da Jamila na nan bata wuce ba domin a Kano za ta yi jiran Malam Zakari da yayanta su wuce Dambatta wurin yan uwansu.

Hashim na zaune suna hira da iyayen, wayarsa ta yi ƙara. Ganin Adam ne ya sanyashi dauka.

“My son, fatan ka isa lafiya?”

Adam ya amsa dakyar. Kafin ya nemi yi mishi magana a sirrance. Jin haka Hashim ya fice daga ɗakin zuwa ƴar barandar shiga falon Prof.

“Na’am, ina sauraronka. Lafiya kuwa?”

Ya zayyane mishi dukkan abinda ke faruwa, Hashim bai san sadda ya soma gumi ba.

“Anya Hayat jininmu ne? Idan kuwa jininmu ne to ina da tabbacin yana da cuta a ƙwaƙwalwa. Watakila yana shaye-shaye a ɓoye ba da saninmu ba.”

Babu wasa a maganar Hashim,  dagaske iyakar abinda ya hango yake faɗa. Jin Adam ya yi shiru ya sanyashi fadin

“Ka kwantar da hankalinka, kada ka dau hukunci a hannunka. Ka bari zan zo, ƙararsa zamu kai. Wannan maganar dole ta je kunnen iyayenmu. Allah Shi zai sakawa Bilkisu akan wannan abin da Hayat ya yi mata. In Sha Allah sai ya ga fiye da abinda ya aikata gareta. Amman abinda ban fahimta ba, mene hadinsa da Maryam? A ina ya santa? Ka tabbatar ita suke nufi? Humaira suke nufin sacewa?”

Adam ya amsa.

“Eh Uncle. Fu’ad Bai ɓoyemin ba, nima kuma nayi mamaki.”

“Shikenan, wannan din dai bamu da cikakken bayani a kai, don haka muyi shiru har Allah Ya bayyana. Batun Fu’ad kuwa da kaina zan haɗawa Baba Malam, shi zai san yanda zai ɓullo wa Bilki da zancen.”

Suka yi sallama bayan ya ƙara gargadinsa akan ya kula kada ya dau kowane hukunci a hannunsa.

*****

Adam na ajiye waya ya tashi motarsa ya soma tafiya. Kiran Dr Ibrahim wanda tun yana waya yake shigowa bai ɗauka ba, yanzun ya hakura ya ɗaga.

“Adam duk inda kake ka zo, yaron nan jikinsa ya tashi sosai.”

Jin haka hankalinsa ya tashi, ya katse kiran ya karawa motar gudu.

Koda ya isa ya tarar sun dukufa a kansa, kasancewar ba fanninsa bane ya sa bai iya komai ba. Ya tsorata ganin yanda Fu’ad aka sanya mishi robar oxygen.

Dr Ibrahim ne ya fito ya tareshi da sauri.

“Me ya sameshi?”

Cike da tsananin tausayi ya ce.

“Bayan tafiyarka ba jimawa ya suma, wallahi mun jima kafin mu samu ya farfaɗo, to kuma yana tashi sai bugun zuciyar ta sauya, numfashin ma dakyar yake fita. Ciwon zuciya ne, sai an tayashi da addu’a. Kuma don Allah a rage sanyashi a damuwa. Yaron na cikin matsala fa. Allah kaɗai zai taimakeshi.”

Dafe kai  Adam ya yi yana jin inama bai tafi ba, ya tuna sadda Fu’ad din ke kiranshi akan ya dawo bai dawo ba. Ji ya yi Dr Ibrahim ya dafa kafaɗarsa.

“Haka Allah Ya ƙaddara, kada ka damu. Ka kira iyayensa, ya dace su zo su ga halin da ɗansu ke ciki suma.”

Gyada kai kawai Adam ya iya bai ce komai ba.

Bayan awa ɗaya ya shiga gurin Fu’ad, dakyar yake buɗe idanunsa. Fu’ad ya dubeshi hannunsa ɗaya a saitin zuciyarsa inda nan azabar take.

“Kada ka je wurinsa don Allah.”

Ya furta, ba don kusancinsu ba da ba lallai ya ji me yake faɗi ba.

Hannunsa na hagu ya riko gam yana murmushi ga hawaye saman fuskarsa.

“Ban je ba, ba zan je ba. Ka daure ka tashi, zan tayaka addu’a. Ko ba ka son ganin Umma?”

Duk da yanayin da yake ciki sai ya tsinci kansa da murmusawa.

“Ta san ni ɗanta? Ta karɓeni?”

Tausayinsa ya kama Adam ganin yanda yake maganar kamar takura kai. Ya gyaɗa masa kai da murmushi.

“Uncle Hashim ya sani, gobe zasu zo wurinka.”

Fu’ad ya yi ƴar dariya mai karamin sauti kafin ya lumshe idanu ya juya kai. A hankali kuma bacci ya yi Awon gaba da shi, ganin haka Adam ya gyara mishi lulluɓi ya fita zuwa Dr Ibrahim.

“I am sorry Dr, ban taɓa yi maka katsalandan a harkar rayuwarka ba. Sai dai a yau zan yi. Matsayina na amini kuma ɗan uwanka, bana tunanin akwai wani abu da za ka yimin ɓoyonsa a duniya. Fu’ad na cikin mawuyacin hali wanda yake bukatar taimakon gaggawa. Abinda na ɓoyemaka bansan ko kana da masaniya ba, koda dai shi kansa Fu’ad din ya sanarmin cewar yana sha sigari a baya amman yanzu ya bari. Toh gaskiya ya yi affecting zuciyarsa. Da dama za ka ga an fi wanyewa da ciwon huhu ga mashaya. Amman akwai cutar da ake kira Coronary Artery Disease.  Damuwarnan da ya shiga ya ƙara bayyanar da cutar.”

Adam ya girgiza sosai, ya kara jin tsanar Salma da Hayat.

“Ba hawaye za ka tsaya zubarwa ba Dr, addu’a Fu’ad ke bukata daga garemu. In sha Allah zai warke.”

Adam ya gyada kai, sam bai da masaniyar hawayen yake yi. Ya daure ya ba Dr Ibahim labari iyakar abinda ya san zai iya fadi. Tausayi da kaunarsu ta ƙara kama Dr Ibrahim.

“Shakka babu dole ka kalli Abba a wanda ya yi muku ba daidai ba. Sai da duk lalacewar uba, uba ne. Hannunka bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba. Muna fatan Allah Ya shiryeshi.”

“Ibrahim ba abinda ya fi damuna kamar yanda suka lalata rayuwar yaronnan, kaga a wurinsu gani zasu yi ko yanzu sun ci riba tunda sanadiyyarsu ga abinda ya faru da Fu’ad. Allah kaɗai Yasan for how long Fu’ad ke shaye-shaye domin kuwa tun tasowarmu daga Salma har shi (Hayat) ma’abota shan sigari ne. Ban kuma sani ba ko har yanzu ko kuwa sun bari.”

“Allah Ya kyauta. Amman wannan ba rayuwa bace. Ba’a kyautata Umma ba.”

Fadin Dr Ibrahim.  Haka suka ɗan taɓa hira, dakyar Adam ya wuce ofishinsa, dakewa kawai ya yi ya ɗan kama aiki sai dai ransa babu dadi ko kaɗan.

*****

“Ya akayi Hashimu? Da magana ne?”

Malam Kabiru ya jefawa Hashim tambaya ganin ya yi tsugunne a gabansa sai dai bai ce uffan ba. Hashim bai san ta inda zai faro ba amman ya zame mishi dole  ya faɗi.

“Baba akwai matsala ne.”

Jin haka Malam ya gyara zama yana mai duban Hashim dakyau.

“To, wace irin matsala?”

Ya labarta mishi komai. Salati Malam Kabiru ya maimaita har sau uku yana mai jin ciwon abin.

“Lamarin Hayatu na bani tsoro don ya daina bani mamaki. Wane irin son zuciya ne haka? Me ya aikata? Wallahi nayi nadamar aurar da ɗiyata Bilki…”

“A’a Baba  Malam, a’a don Allah. Ku ne masu gyaramana idan mun yi kuskure, ku yi hakurin dai da ku ka saba.”

Baba Malam ya soma zubda hawaye.

“Kaddarar Bilkisu kenan, ita kuma a haka ta zo mata. Shikenan, Allah Yasa hakan ya zamemata alheri. Tashi ka turomin ita.”

Hashim bai fita ba har sai da ya shawo kan Malam Kabiru ya bar zubda hawaye.

Umma tana duban fuskar Hashim ta ji gabanta ya faɗi, babu abinda ta kawo a ranta sai mutuwar Adam.

“Ki zo Baba yana kira.”

Ya furta kafin ya juya ya bar ɗakin. Jikinta ya yi sanyi.

“Allah Yasa lafiya.” Maryam ta furta ganin yanayin Hashim din da kuma firgicin da ya sauka saman fuskar Bilkisu.  Murmushi Umma ta yi wanda ya fi kuka ciwo. Kirjinta banda bugu ba abinda yake, ta zura hijabinta ta fita.

Sallama ta yi ta shiga ɗakin. Suka dubeta suna masu amsawa. Malam Kabiru tunda ya kalleta ya sauke kansa bai ƙara ba saboda tsantsar tausayi.

“Bilkisu.”

“Na’am.” Ta amsa cikin faduwar gaba, ta mance rabon da Malam din ya ambaci sunanta haka kai tsaye.

“Kin yarda da Allah?”

Sai da ta dubeshi, ta kara saddakarwa Adam ne ya rasu. Idanunta suka cika da kwalla. Ta amsa.

“Kenan kin yi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau?”

Ta runtse idanu kafin ta amsa murya a bude wannan karon har rawa muryar take.

“Ki yi hakuri da dukkan abinda za ki ji Bilkisu, ki ƙaddara kaf duniya ba bawan da ya isa ya yi miki hakan face Ubangijin da Ya isa da ke, Ya kuma ce zai jarrabemu, mu masu imani.”

Ranta ya ɗan yi sanyi. Ta kara miƙa tawakkalinta ga Ubangiji.

“Na yarda Baba.”

Ya ɗan yi murmushi, Hashim dai na kallon ƙasa don ba ya son ma ganin yanayin Bilkisu. Ji yake kamar ya tashi ya fita su yi maganar da Baba Malam sai dai ya hanashi.

“Za ki iya tuna ɗan da kika haifa ya mutu bayan haihuwar Adamu?”

Ta ɗago kai ta dubeshi da dukkan nutsuwarta. Ina za ta manta ɗan da take yawan mafarkinsa yana kuka? Ba wanda ta taɓa faɗawa don tana zaton sanyashi a rai da ta yi ne ya sanya take mafarkinnasa. Sai kuma koyi da ta yi da faɗar Annabi s.a.w na a ɓoye mafarki musamman idan marar kyau ne.

“Na tuna Baba.”

“Toh ɗanki bai mutu ba Bilkisu, mijinki Hayat ne ya sa aka sanarmiki da mutuwarsa domin ya damƙashi hannun Salma a sadda take gidan mijinta Haisam.”

Kanta ya kulle, kamar wata wawuya take duban Baba Malam. Ta kara tsintar muryar Hashim yana bata labari tiryan-tiryan yanda Adam ya fadamasa.

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Allahumma ajir ni fee musibatii wakhluf li khairan minha! Wai ni Bilkisu wae irin zunubi na taɓa yiwa Hayat? Me na tsare mishi? Baba ka faɗamin me na rasa? Me nayi? Bani da kyawun hali? Ina na kuskuro? Baba dama ana tsanar mutum har haka? Yanzu Fu’ad ɗana ne? Hayat ya rabamu da shi? Ya sa ya daukeni banza, yana kallo Fu’ad ke zagina yana kirana Bora? Ashe ɗana ne?”

Tana maganar tana kuka, idan ta kalli Baba Malam sai ta maida kai ga Hashim ta kalla. Ba wanda ba ta sa hawaye ba cikinsu. Ta ci gaba da maimaita salati, tun suna jin maganganun da take har suka ji ɗif. Da sauri suka yo kanta su na salati. Ruwa Hashim ya yayyafamata har suka samu ta farfaɗo. Tana ganinsu ta ci gaba da kukan. Malam ya shiga yi mata nasiha mai ratsa zuciya da kuma falala da ladan da ke cikin yafiya a wurin wanda aka zalunta kuma yake da karfin ramawa.

“Baba Ina son zuwa ga Fu’ad. Ya jikinsa?”

Ta zaɓi ta katseshi ta wannan hanyar don a yanda take ji ba za ta iya kyale Hayat ba. Kotu ce za ta rabasu!

“Ki yi hakuri, Adam yana  tare da shi, gobe idan mun je sai ki ganshi.”

Ta amsa da toh tana mai jin zafi a kirjinta ga kanta dake bala’in sarawa. Ashe shiyasa take yawan mafarkinsa da fuskar jarirai yana kuka? Nan ta sanarwa Baba Malam mafarkin ya yi murmushi don ya san ishara ce ake mata cewar ɗanta yana raye.

*****

Maryam ce a ɗakin ajiyarsu, takardun makarantarta ne jibgi guda cikin akwatina waɗanda aka kwaso daga gidan aurenta. Humaira ce ta yi mata rakiya, da zarar ta ɗago littafi, sai ta karɓa tana dubawa da murmushi, kusan rubutunsu iri ɗaya ne sai ita nata ƙananu ne akan na mahaifiyarta.

Zuciyar Maryam ta cika da fargabar rashin ganin abinda take nema, har ta soma gajiyawa sai ta hango wani envelope ruwan ƙasa. Nan da nan ta buɗe ta zazzage litattafan dake ciki, English novels me sai kuwa Allah Ya taimaketa ta hango Diary din a ciki. Ta ɗaga tana mai jin sanyi a ranta, kakkaɓeshi ta yi, yana nan yanda yake, ga dukkan alamu ba wanda ya buɗe shi. A hankali ta bude ta karanta, rubutun mijinta na shekara da shekaru. Hawaye suka zubo a saman kuncinta.

“Mama mene wannan din?” Cewar Humaira tana duban littafin.

Maryam ta dubeta tana murmushi mai ciwo.

“Da wannan littafin zan sa hukuma ta hukunta duk wanda keda hannu a kisan mahaifinki. Ki tayani da addu’a domin muyi nasara.”

Nan da nan idanun Humaira suka yi rau rau, ta rungume mahaifiyarta tana hawaye.

“Mama ba zan yafewa waɗanda suka  kashe mahaifina ba, na tsanesu da duk mai kaunarsu. Sun kashemin rayuwata. Sun anya ban yi kyakkyawar rayuwa da shi ba. Bai sanni ba.”

Tausayinta ya ratsa zuciyar Maryam. Ta ɗan ja majina.

“Babu komai Humaira, kansu suka yiwa. Allah Ya jiƙan Mahaifinki, Yasa yana aljanna.”

Ta amsa da amin da muryar kuka. Sai da suka yi mai isarsu kafin Maryam ta rarrasheta daga bisani suka bar ɗakin.

*****

Da wani irin farin ciki ta wayi gari, na farko, za ta je garin Kano. Garin da bata taɓa zuwansa ba, za ta ga Yaya Adam. Na biyu kuwa, za’a hukunta wanda ya kashe mahaifinta za ta ga danginsa kuma. Wannan ta sanya tun asuba zumuɗi ya hanata komawa bacci. Ta ɗakawa Amira da Jamila duka akan su tashi.

Fa’iza diyar Alhaji Mujahid, wacce ta kasance sa’arsu ta ja tsaki gami da cillamata filo a fuska.

“Kedai Allah Ya sauwake maki, ƴar kauye kawai. Wai ke baki iya komai a hankali ba?”

Humaira ta kai mata duka ta kuwa kauce da sauri tana ƴar dariya haɗi da miƙar gajiya.

“Ban iyaba! Wallahi Fa’iza ki fita idona. Dallah malamai ku kuma ku tashi ku yi sallah ku shirya, kun manta Umma ta ce da wuri za’a tafi?”

Amira ta ja tsaki.

“Bani da sallah fa.”

“Amman ai kya tashi ki yi wanka.”

Fadin Humaira.

“Wai ke zumudin me kike yi? Ko su Mama dai nasan yanzu suke sallah, kuma ko zasu yi wanka su shirya ba yanzu ba.”

Fadin Jamila dake mutsistsika idanu tana mai miƙewa zaune.

“Kema kya faɗa, wayasani ko ɗan balarabennan take don zuwa gani. Yayannan naku mai aiki a Kano. Mene ma sunansa kuka ce?”

Cewar Fa’iza  sadda ta murɗa kofar banɗaki za ta shiga.

“Au, wai Yaya Adam? Ke Humaira, soyayya ku ke?” Fadin Amira wacce tuni ta ji baccin ya kauracemata.

Harara Humaira ta watsamata, kunya duk ta kamata.

“Allah Ya sauwake, kema dai kin san Yayana ne, babu soyayya a raina. Duka-duka yaushe na cika sha hudu?”

“Ga jikinki kuwa kamar ƴar sha takwas.”

Suka sanyamata dariya wanda ya yi daidai da murɗa kofar dakin da akai, da sauri Fa’iza ga shige banɗaki. Maryam ce, tambaya ta yi musu kan hayaniyar me suke da asuba. Karshe ta umarci kowannensu da shiryawa idan sun yi sallah.

*****

Washegari da misalin karfe uku da mintoci na ranar Alhamis, Barrister Abeed ya damƙawa Salma takardun, bayan sun kammala saka hannu ya miƙa wanda ya cancanta ga Halima. Daga nan ya yi musu sallama ya fice.

Halima na fita daga gidan ta yi wani murmushi, wayarta ta hau ƙara. Ta duba, Gwaska ne, ta sanya a silent ta tashi motarta. Tana yin gaba wayar ta kara daukar sauti, Hajiya Murja kenan. Ta kashe wayar gaba daya. “Zan nunamaku wace Halima.” Ta furta a fili gami da sakin murmushin mugunta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 34Rumfar Kara 36 >>

1 thought on “Rumfar Kara 35”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×