Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Rumfar Kasuwa by Murja Na'ikke

بسم الله الرحمن الرحيم
Allah ka ba mu albarkacin Annabi

“Ke Maryam ki raba kanki da kutsawa cikin motocin can, kinga dai wallahi yawancin direbobin nan ni ban yarda da su ba kina kallo ranar suka cirewa wata mai abinci hijabi ni dai duk wanda ba zai zo inda nake ya siya sana’ata ba to sai dai ya hakura ni ma in hakura.”

Cikin tsiwa ta dubi Zinatu tace “ke dalla can tafi can yo in ba ki kutsa kin kai sana’arki ba ya za a yi su san kin zo? Ko so kike kunun ya buga ne? Kina kallo yau qanqarar ma dakyal muka samu shida shida kuma kunun ya fi na dubu hudu,to ni kinga na shiga in kaima su Lawali can lungun ‘yan dabino.”

“kar ki je Maryam wallahi in kika je sai na fadawa Inna kina zuwa gurin maza.”

“hm lallai yarinya to bari ki ji da zafi zafi akan daki karfe inji hausawa sannan sun ce motsi ya fi la6ewa,shin wai idan mun zauna anan waye zai san mun zo? Sai fa wadanda suke wucewa amma idan muka shiga muka nuna cewa mun fa iso ai mu warkan,domin kuwa zama zaunewa inji hausawa ke da kike wannan maganar ai kin san irin gwagwarmayar da ake kafin a hada kudin da za a kai gida (wato idan mai abinci ko kunun aya ta yi kwantai sai ta samu wani daga cikin direbobi ya ďan sha lungu da ita ya mammatseta don ta samu abin toshe bakin uwarta) duk ranar da ba a samu abin kirki ba.”

Galala Zinatu tayi tana kallon sarautar Allah daga bisani ta ce “wal iyazu billahi kuma ni Allah ya tsareni da samun kudin da ba na halal ba wallahi Maryam ke dai kin shiga ukku,da ace Inna ta san irin yadda ake hada kudin kunun ayar nan na tabbata ba za ta barmu mu zo kasuwa asabar da lahadi ba.”

Ta karashe zancenta cikin rawar murya da alamun tana dab da fashewa da kuka.

Ido daya Maryam ta kanne tare da matsowa daf da Zinatu tace “in kin fada mata sai me? Ina ce ita ta turo mu don mu nema mata kudi ko? To wlh ko kin fada mata kinyi aikin banza in kuma ta nemi ta yi min fada itama na san me zan fada mata ehe.”

Ba ta tsaya sauraronta ba ta yi gaba abinta rike da murfin bokitin da ta dora kunun aya akai.

“Abokina yarinyar nan da nake ba ka labarinta fa wlh mun hadu.”

Lawali ya kalli abokinsa Umar yace “kai dan Allah ka ce min har ka kashe arnan kawai”

Dariya suka yi gaba daya Umar yana ba shi labarin wata yarinya da ya yaudara mai abinci satin da ya gabata ,suna ganin Maryam duk suka nutsu kowa yana sak’a abu a ransa.

Fara ce mai kyau komai naya madaidaici ga kugunta duk girman hijabi idan ta saka tana fara tafiya sai an ga shatinsa kirjinta ma a cike yake fam tana tafe tana girgiza,

Tana karasowa ta ajiye murfin tace ga shi da sanyinsa na kawo muku don na ga yau ana zabga rana kuma dai in ba haka nayi maku ba ai ba za ku san mun hallara a kasuwar bakuna nan kuna bushe bushenku” (shan taba sigari).

Umar yace “lallai kema kin ce wani abu.”

Ya dauki daurin kunun aya guda biyu ya duqa ya shige karkashin babbar mota inda suke hutawa idan sun kawo aya da dabino.

Lawali ya kalli Maryam yace “wai ke nifa duk ba wannan ba idan kunu ne ai na san gurin zamanku zan iya zuwa in kar6o,shin wai sai yaushe ne za ki amince da bukatata?”

Fari tayi da ido tace “haba Lawali lokaci yana zuwa karkayi garaje mana ni dai kawai ka bar zancen nan mu cigaba da yin abinda ya fi sauki a garemu, (yab matse matse da tsotse tsotse) kuma wai shin idan na amince maka a ina za mu yi?”

A Cikin Garin Katsina

kofar kaura layin Kanikawa

Cikin zafin rai ta banka kofar dakin ta shiga tare da fadin “wai yarinyan nan rainani kika yi hala? Ya ina maki magana tun dazu ki fito ki tafi gurin suyar awarar nan kin wani tsaya sallarki ta munafurci? To wlh duk abinda za ki yi yau sai kin saya da ita tas don ba zan lamunci a dinga dawomin da ragowa ba.”

Addu’a ta shafa sannan ta mike cikin ladabi tace “kiyi hakuri Umma na gama fita kawai zanyi.”

Tsoki ta ja tare da harararta ta fita ita kuma ta bi bayanta tana gyada kai.

“Ke dalla malama ki zubo min tun dazu nake jiranki kin wani shanya ni anan in ba za ki siyar ba ki fadawa mutane sai wani jan aji kike kamar wata yar gwamna”

“Kayi hakuri wanda suka riga ka zuwa su nake sallama kafin layi ya zo kanka”

“To a zubo min dai uzuri gareni”

Tunda take sayar da awara a bakin layinsu ba a ta6a fada mata maganar da ta yi mata ciwo irin na yau ba,don me zai ce mata kamar wata yar gwamna? A tunaninsa ‘ya’yan masu da shi su kadai suka iya tsukewa gayu fuska? Ko su kadai suka iya jan mutumcinsu don kada a raina su?

Cikin sa’a kuwa yau ana gama sallar magariba awarar ta kare tas ,godiya tayi ma Allah kamar kullum ta kira almajiri ya kwashi kayan suka nufi gida.

Shewa Umma ta dinga yi tana fadin “ko ke fa? Ana ga yaki kina ga k’ura, idan kina fita da wuri irin haka har yaushe ciniki zai ke wuce mu? Amma kin wani tsaya iyayi sallah a gidan biki sai ki je ki dauki abincinki ga shi can acikin mazubi ki ci kafin mahaifinki ya dawo ya tarar da ke anan kin tasa kayan awara a gaba har ma ki sa ya gano cewa mun karya masa doka.”

Sunanta Halima yarinya ce ‘yar kimanin shekaru goma sha biyar, anan aka haifeta a kofar kaura da ke garin Katsina.

Mahaifinta Alhaji Isa mai albasa sai mahaifiyarta Hajiya Suwaiba duk haifaffun garin katsina ne kuma auren zumunci suka yi.

Alhaji Isa manomi ne noman damina da na rani suna rayuwa cikin rufin asiri wanda suka je aikin hajji a tun shekaru ashirin da suka shude baya.

Halima tana aji na biyar a makarantar gaba da firamare wato, Ulul albaab Primary and secondary school, da ke nan cikin Kofar Kaura.

Yarinya ce wankan tarwaďa wato ba fara ba kuma ba bak’a ba,tana da kyau daidai misali sannan a fanin karatun addini da na boko fitacciya ce domin ba ta ta6a tsallake na ďaya ba tun daga firamare har zuwa yanzu.

Yau ma kamar kullum Umma ta gyara komai har Halima ta fita bakin layi gurin soya awara kwatsam sai ga baban Halima yayi dawowar bazata irin wadda bai ta6a yi ba.

A k’a’ida sai bayan sallahr isha’i yake dawowa daga kasuwa amma yau karfe shida sai ga shi.

Tunda ya shigo da sallamarsa ta karanto tsantsar 6acin rai da masifa a idanunshi amma hakan bai hana ta gabatar masa da abin shimfida da ruwa a tsakar gidan ba kasantuwar ana ďan ta6a zafi a garin.

Tsaye yayi k’ik’am kamar itace a gurin yana kallon yadda duk jikinta ke rawa ,a yayinda ita kuma ta gama sarewa da shiga ukun da za ta yi ,tabbas ya ga Halima a bakin layinsu tana soya awara dalilin shigowarsa cikin fushi kenan.

Karfin hali tayi ta matsa kusa da shi tace “Sannu da dawowa ka zauna ga shimfida nayi maka ga shi kuma ko…”

Ba ta karasa ba ya katseta cikin fada “kin bani mamaki Suwaiba ,yanzu ke Suwaiba dokar da na kafa miki a gidan nan ita kike karyawa idan ba na nan?”

“Tsakaninki da Allah menene ba na kokarin yi muku a gidan nan? menene ku ka nema ku ka rasa da har kike tura mun yarinya k’waya ďaya da na mallaka a bakin layi tayi tallar awara? shin so kike duniya ta zageni ne a ce na kasa daukar nauyinku ke da ita?”

Shiru ya biyo bayan tambayoyin Alhaji Isah babu amsa ko guda daga bakin Umma Suwaiba sai murza yatsun hannunta da take tana hararensa da gefen ido,

Tsawa ya daka mata “ko ba tambayarki nake ba?”

“Dan iska kika maidani ne ko sakaran namiji kike son maisheni?”

Matsowa yayi dab da ita ya nuna ta da yatsa yace, “Wallahi wallahi idan kika kuskura kika sake tura Halima tallar awara a gidan nan sai munyi abinda ko zamanin k’uruciya ba mu yi irinshi ba a gidan nan sakarya mara godiyar Allah kawai.”

Daga haka ya kada kai ya nufi dakinsa ransa yana kuna ainun yadda Umma Suwaiba ta kasa bin dokarsa abin yana ci masa tuwo a kwarya.

Dama yana dan jin labari sama sama to bai yi magana ba ne sai yau da ya gani da idonsa kuma dalilin dawowarsa da wuri kenan.

Umma Suwaiba kuwa ba karamin razana tayi da kalamansa ba amma wani sashe na zuciyarta sai tunzurata yake kawai ta shareshi ta ci gaba daga inda ta tsaya ai dai yanzu a buge aka ce ya bugeta ba zai yi ba ko don ganin idon tilon ďiyar da Allah ya ba su.

Zama tayi ragwab a gurin tana sakawa da warwarewa har aka kira sallah (idan mijinki ko abokin zamanki yayi fushi to kada ki je gurinsa ki ďan ba shi tazarar mintuna kafin ya dan huce ya dawo hayyacinsa).

Mikewa ta yi ta zuba mashi ruwan alwala ta nufi dakinsa gabanta yana dukan ukku ukku,

Da sallamarta ta shiga ya amsa ba tare da ya kalleta ba ya ci gaba da 6alle bitiran hannun rigarsa ta yi saurin kar6a ta karasa cire masa tare da ajiyewa gefe tace
“Dan Allah dan annabi ka yi hakuri wallahi sharrin shaidan ne da zuciya in sha Allahu ba zan sake ba.”

“Allah ya sa haka”

“Amin” ta amsa sannan ta ce “na zuba maka ruwan Alwala ga shi can”

Hannunta ya saki ya nufi kofa.

Ita kam zaunawa tayi tana zullumin abinda zai je ya dawo domin ga dukkan alamu hakurin da ta ba shi bai amsa duka ba in aka yi duba da yadda ya amsa ďin.

Babban ma abin tashin hankalin shi ne,yanzu idan ta yi abinda dangi kowa ya ji ai ta shiga ukku domin ta ko ina ‘yan uba ne suka zagayeta sannan iyayenta sun rasu a gidansu Alhajin aka riketa har Allah ya kaddara aure tsakaninsu.

Bugu da kari kuma duk rashin bin dokar da take masa ba ta son 6acin ransa domin aure ne suka yi na soyayya wanda har gaban abada suna jin ba za su daina son juna ba da shi za su mutu.

“Oh Allah”

Ta fada tare da rafka tagumi tana kuma gyara zama ko alamar tashi ba ta yi ba(tana fashin sallah sannan kuma ta kammala duk wani aiki da za ta yi sai wanka kawai).

“Na fita masallaci” ya fada bayan ya gama alwalar har ma ya fara tafiya bai kuma tsaya sauraronta ba ya fice abinsa.

Har aka gama sallar magariba ba ta dawo ba,shi kuma yana masallaci dama al’adarsa ce ba ya zama gida sai an gama sallar isha’i.

Har ya hado musu kayan tea da sauran abin bukata ya nufo gida babu Halima babu alamunta,

To anan fa ba ita uwar gayyar ba har shi hankalinsa ya fara tashi saidai bai nuna mata ba so yake ya ga yadda wasan zai k’are.

Hawayenta ta share ta dubi sauran awarar da ba ta siyar ba tana hasaso irin masifar da Umma za ta yi mata idan ba ta siyar ba, ta share hawaye sannan cikin ranta tace _”ita fa Umma na lura da ita ba wai rashi ne ta sa take doramun awarar nan ba kawai neman magana ne don ta ga wasu yan anguwarmu suna yi shi ne itama abin ya birgeta kuma ko tsoron Abba ba ta yi hm.”

Firgigit tayi ta maida hankalinta ga yaron da yake daukar mata kaya zuwa gida yayin da yake sanar da ita lokacin tafiyarsa makaranta yayi kada malaminsu ya bugeshi idan yayi latti.

Ba tare da tunanin komai ba tace “kira wadancan yaran ku raba awarar nan mu je ka kai min kayan gida” wannan fa shi ake kira SHAHADAR K’UDA

*****

Yana tafe tana bayansa ya ma ďan yi mata nisa tunda shi har ya kusa shiga layinsu ta ji an janyo hijabinta abinka ga marar k’iba kawai sai jinta tayi a jikin mutum,

Tana kokarin yin ihu ya hade bakinsa cikin nata tare da kokarin tura hannunsa cikin rigarta ,

A yadda take mutsu mutsun neman k’watar kanta ne har ta samu damar cizon le6ensa wanda hakan yayi sanadiyar ďagowarsa ba shiri amma bai daina laluben abinda ke cikin rigarta ba.

Ihu take so tayi amma bakinta ya mata nauyi,

tunani take idan tayi ihu fa sai an gansu a cure guri daya abinda zai janyo mata tsegumi har jikokin jikokinta.

Idan kuma ta barshi zai aikata mata mummunan aiki ne,cikin ikon Allah ta dage ta gantsara masa cizon da yayi sanadin fashewar jijiyar hanunsa ya hankadata babu shiri ta fadi k’asa sai alokacin kuka ya kufce mata.

Kafin tayi hanzarin mikewa ha iso gabata cikin isa da gadara ya sake jan hijabinta tare da mikar da ita tsaye yace “Kin gama yi min kallon banza kin gama fada min bakaken maganganu don kina tak’amar ana miki layi a gurin soya awara?”

“Yau ina masu shaidarki suke mai tireda da mai kalanzir da suke hana a miki magana a gurin sana’arki?”

Cikin kuka tace “Ban zageka ba hakuri nake ba ka ka dinga jira har sai layi ya zo kanka.”

Wata murza da yayi wa abin cikin rigarta ne yasa ta saki wani wawan ihun da ya janyo hanakalin wani mutum da ke tafe.

“Kai kai mene haka ?su waye a nan”

Ko da ya hasko fitilar waya sai ya saketa ya juya a guje ita kuma ta durkushe a gurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Rumfar Kasuwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.