Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Rumfar Kasuwa by Murja Na'ikke

Duk abinda yaran suke idon Inna akansu.

Maryam ta zo ta wanko bireziya manya guda shida ta fito da su ta shanya a tsakar gida.

Daurin kirji ne tayi wanda ya bayyana ainihin zubewar kirjin nata,

Ido Inna ta sake zuba mata yayin da ta fito da takalmi kusan kala takwas ta zube tsakar gida tana fadin “Idan wannan ‘yar rainin hankalin tana so sai ta dauka.

Zabura inna tayi tace “Ke zo nan”.

Kusa da innar ta tsaya tana wasa da gefen zaninta.

Inna tace “na ga takalmin da kika sawo jiya kusan kala hudu ,waye ya ba ki kudin da kika sayesu?”

“Kai Inna,asusuna ne fa na fasa jiya shi ne na siyo takalmi da sauran kayan kwalliya”.

Inna tac e “to in banda abinki Maryam kudi ne kika kashe sun tasarwa dubu shida,kina ganin hakan shi ne daidai?”

“Ai ina ce yanzu kin fara sanin ciwon kanki za ki fara tanadin abin bukata naki na kanki ba wai kayan kwalliya ba ,tunda ina ba ku kudi ku sawo duk abinda ba ku da shi.”

“Toh saidai a tari gaba Inna kudin nan kam na riga na kashe su”.

“Allah ya kyauta” in ji Inna .

Maryam ta amsa tana daukar bokiti da ke gefenta.

Suna cin abinci bayan sun taso makarantar boko wanda yanzu suka shiga aji na hudu.

Zinatu tace “Inna, kinga Mama Rabi ta siyo mana BULUGUL MARAM ni da Yusrah ‘yar wajen Rabin wanda na ce miki an ce kowa ya siyo kafin sati na sama.”

“Aaa lallai kun gode sai a maida hankali ga karatun”.

Ta kalli Maryam da ke faman hararen Zinatu tace “Ke kin sawo littafin ko sai sun yimaki irin bugun da suka yi maki tukuna?”

Kauda kanta ta yi gefe ta ce “na ma riga su sawowa,don ban kaunar wannan shegiyar bulalar”.

Inna ta saki baki tace “au dama ba don Allah kika sawo ba don bulala?”

Shiru tayi su kuma suka dinga yi mata dariya domin a duniya tana daga cikin dalibai wanda suke kiyaye dokar makaranta don tsoron bulala.

Al’amari ne wanda ya zama ruwan dare a duk inda ka shiga za ka samu mutane na gari da na banza.

Haka abin yake a k’auyukan da suke kan iyaka da najeriya da nijar da kuma iyakokin da suka hada da na kebbi da jamhuriyar Benin.

Kauyukan da suka zagaye jihar katsina musamman wanda suke kusa da iyakar da ta raba katsina da zamfara ,

Sun fi ko ina yawaitar yara mata masu shigowa da man k’uli da fura don yin talla. Akwai masu kawo dafaffen rogo da albasa kwano kwano.

Yara ne ko kuma muce matasa tun daga masu shekara goma sha biyu zuwa shekara ashirin,

Hakan take a garesu domin wasunsu suna zuwa talla ne a bisa lalura ta talauci da rashi.

Yayinda wasunsu suke zuwa don cika burin iyayensu na neman abin duniya.

Suna shiga gidaje da kasuwanni har ma da shaguna don tallata kayansu, yayinda zasu ba ka abin sana’arsu sai su tafi talla.

Idan yamma ta yi sai su dawo suna bi shago shago gida gida don kar6ar kudadensu,

Yayin da suka had’a sai su yi ayari su tafi gurin masu aca6a don komawa gida.

A zahirin gaskiya wasunsu suna ta6a iskanci a shaguna har ma da rumfunan kasuwa yayinda wasunsu suke she’ke ayarsu da masu aca6an da ke daukarsu zuwa gida.

Allah ka yi wa k’warya makama abin ya k’azanta ya munana da yawa wanda har ya kai suma jami’an da suke tsaro akan iyakokin suna ta6a masha’a da wadannan yara.

Abin da zai ruguza tunanin mutum shi ne yadda uwa da ‘ya suke yin shiri a ci ado kitso da lalle a Sha maganin Mata an ci bilicin an Yi d’au d’au,Haka za su jeru a shiga motar haya.idan an zo gate din da samarin ‘yar suke a fad’a ma direba akwai Mai sauka a nan.ita Kuma uwar sai a k’arasa da ita cikin gari ita ma ta tafi sharholiyar ta Idan marece ya Yi su had’e gida ko Kuma uwar ta gaya ma direba Idan an Kai gate kaza zan dauki mutum daya.

Sun gama jarabawa lafiya, wasu sun fara tafiya gida yayinda wasu suka fara daukar hotuna maza da mata.

Halima tana cikin jerin masu fita daga makarantar kai tsaye.

Domin ko dama can ba mai hayaniya ba ce kuma ba ta kawaye saidai a gaisa kawai.

Dandazon dalibai ne a kofar makarantar suke tare abin hawa suna wucewa gida yayin da wasu kuma suke shiga motocinsu na gida.

Ta fi minti biyar a tsaye tana tare abin hawa amma ba sa’a duk wanda tare ya cika.

Har ta hakura ta gangara ta fara tafiya sai ta ji karar mota a bayanta,

To sanin ba ta da alaka da wata mota a wannan lokacin shiyasa ma ba ta waiwayo ba.

Tafiyarta take a nutse sanye take da doguwar farar hijabi da dogon wando ruwan k’asa wanda ya d’an kama k’asan k’afarta, yayinda k’afafun nata suke sanye da farar safa da takalmin makaranta sandal bak’ake masu adon fararen duwatsu wanda daga ganinsu za ka gane an yi su ne da zallar fata.

Ba ta yi aune ba ta ga mota a gabanta,cikin firgici ta yi baya yayin da ta dafe bakinta da ke shirin sakin ihu.

Ta yi tsaye cak ba ta ko motsi don tsabar razana,

Shi kuwa cikin farin ciki ya zuge gilashin motar ya leko yace “Sannu kura uwar tsoro,da farko da na yi naki ham ai k’in waiwayowa kikayi”.

Ya sake sakin murmushi ya ce “Au,na fa manta ban miki sallama ba”.

“Assalam alaikum ‘yar k’anwata”.

Tunda ya fara magana jikinta yake rawa domin wani bala’in tsoron mutane da yake damunta tun faruwar abin nan.

Jin ya yi sallama ne ya sa ta amsa masa yayin da ta yi gaba ta fara tafiya.

Kalar tausayi ya yi, ya ce “Haba mana k’anwata a k’alla dai ko gaisheni kya yi kafin ki tafi ,don ke fa na tsaya anan da tuni na kai inda za ni”.

Sai nasihar Abbanta ya fado mata a rai inda yake “kada ki raina babba ko waye shi,sannan girma ba shi da kadan domin ko da minti daya mutum ya girmeki to ya girmeki har abada”.

“Ki yi amfani da iliminki a inda ya dace kada ki yarda ki yi abinda zai zubar miki da k’ima a idon mutane duk da cewa su mutane babu mai iya musu.”

Kalar tausayi tayi da fuskarta itama tace “Kayi hakuri dan Allah ina kwana.”

Dariya yayi sosai yace “yawwa ‘yar kanwas lafiya,ko ke fa amma da za ki wani tafi ki barni”.

Jin zai jawo wani labarin ne ya sa tace masa “ka yi hakuri daga makaranta nake za ni gida,sai an jima.”

Daga haka ta tsaida wani adaidaitan ta yi shigewarta ,shi ko yana sake da baki kamar lefen sakarai har suka dan fara nisa.

Saurin saita kansa ya yi ya fara bin bayansu.

“Umma mun gama jarabawa yau sai ki min addu’a Allah yasa in samu sakamako mai kyau.”

“Allah ya bada sa’a yasa ki fito da sakamako mai kyau Halima.”

“Amin” ta amsa sai kuma suka yi shiru.

Ita Umman yanzu ma duk ta tsargu da kanta ,a ce wai saboda son zuciya babu abinda ta rasa wai amma ta dinga dorawa yarinya talla har a nemi yin lalata da ita sau biyu?

Ta tuna yadda zamansu yake da Baban Halima yanzu wanda gaisuwa kawai ke had’a su.

Halima ta lura da halin da Umman ta shiga shiyasa ta matso kusa da ita tace “Umma,Abba fa ya ce ya yafe miki wallahi dazu, yace dama ba fushi yake da ke ba.”

Murmushi ta saki ta tuna irin soyayyar da ke tsakaninta da Baban Halimar ta san ba karamin so suke wa juna ba.

“Aikinki ne Halima na sani, Allah ya miki albarka ya sa ki gama da duniya lafiya.”

“Je ki gyara jikinki ki zo ki fara hada abin da Abbanki zai yi buda baki da shi yau alhamis.”

“To Umma.”

*****

Alale da kunun aya suka hada sannan suka soya doya da kwai, a gefe kuma ga ‘ya’yan itace an gyara su cikin mazubi mai zurfi ga kuma tuwon dawa da miyar busasshen kubewa da ya ji man shanu da kifi.

Da sallamarsa ya shigo ya jingine mashin dinsa da ya canza sabo dal a ranar ,roba roba ne mai kalar ja kirar MOTOBI.

“Sannu da zuwa Abba.”

“Yawwa sannu da gida Halima,ina ita Umman ta ki take?”

“Sallah take idarwa yanzu za ka ganta ta fito.”

“Lahhhh Abba, sabon Amarya muka yi?”

Halima ta nufi mashin din tana zagayawa sai murna take tana shafawa.

“Kai amma dai ya yi kyau Abba Allah ya tsare ya karemin kai daga sharrin komai da komai.”

“Amin Halimata.”

Nepa ne suka kawo wuta gidan ya haske ko ina k’al kal ko dama can Umma mace ce mai tsabta ga iya girki.

Fitowa tai daga falonta tana dan sunne kai tace “Sannu da zuwa Baban Halima,ka dawo?”

“Yawwa na dawo ,ya gidan”?

“Alhamdulillahi” ta amsa sannam ta ce “Au dama mashin ne aka sabunta nake jin Halima tana cewa sabuwar amarya?”

Ta matsa tana ganin mashin din.

Halima ta ce

“Eh Umma wlh ya yi kyau duba fa ki gani.”

“Ai kam dai ya yi kyau Allah ya tsare ya kiyaye.”

Kauda kansa ya yi gefe lokacin da take waiwayowa gareshi ta ce “mu je ka watsa ruwa sai ka zo mu buda baki.”

Dan kallon gefenta ya yi ya ce “a’a in fara buda bakin dai domin ranar yau ta bigeni na ji k’ishin ruwa sosai.”

Gaba ta yi tana takunta mazaunanta suna dan kaďawa domin dai zahirin gaskiya umma k’iarar halittarta irin wadda mutane suke sifantawa da kwalbar koka kola ne.

Har sai da ta zauna saman abin shimfidar sannan ya dauke idanunsa daga kanta yace,

“Halima, bude Boot din mashin ki debo leda akwai wasu riguna ku duba idan sun yi muku.”

Da murnarta ta kar6i makullin mashin din ta ruga ta dauko.

Sai da suka yi hani’an sannan suka gwada rigunan sannan suka yi godiya tare da fatan alkairi.

Umma tace “Am Baban Halima dan Allah ka…”

Tsam halima ta mi’ke ta d’auke mazubin da sauran ‘yayan itacen suke ciki ta nufi d’akinta don ba za ta so jin mai zai wakana ba kuma kamar ta ďan takura musu ne.

Bin ta ya yi da kallo lokacin da ta furta kalmomin hakuri gareshi ,ji ya yi komai ya wuce a gurinsa ganin yadda duk ta damu cikin yan kwanakin nan har idonta ya dan shiga loko saboda damuwa da rashin bacci.

Jin ya yi shiru ne ya sa ta matso kusa da shi ta kama gefen k’afarsa tace “Dan Allah na ce ka yi hakuri wallahi a baya ma sharrin shaid’an ne amma…”

Bai bari ta k’arasa ba ya d’agota ya rumgume kayarsa.

Ko baccin kirki yau ba su yi ba an raya sunnah yadda ya kamata sannan kuma sun tabbatarwa kansu lallai soyayyarsu daga Allah ne.

Zinatu ta fi awa biyu a zaune tana jiran Maryam amma ba ta zo ba, tana ta zaune tana nazarin rayuwa tana bin mutanen da ke ta kaiwa da komowa cikin kasuwar masu bambancin halaye wasu na gari wasu masu zubin ‘yan daba wasu mutanen kirki. Shiru shiru babu Maryam ba alamunta Haka ne ya sa ta tashi ta Dan Kama ma Iyam aiki tana zuba ma kwastomomi abinci tare da mik’a masu,ta dauki tsawon lokaci tana Taya ta suna Hira jefi jefi.

Ganin haka ne ya sa ta bar wa Iyam kayanta ta ce za ta shiga kasuwa ta sawo kayan hadin kunun ayar kafin ‘yar uwarta ta dawo.

“Lawali wallahi ba zan yarda muyi wannan abin cikin kasuwa ba Haka kawai ka janyo mamu abin fad’i muna zaman zamanmu asiri a rufe,

Kai ni fa bari ka ji wallahi ina sonka amma fa ba zan ba ka kaina a kasuwa ba,nace ka yi duk yadda kakeso da ni amma banda can domin ban shirya daukar ciki yanzu ba,Kuma ko babu komi Ina so in Kai mutumcina dakin mijina kamar ko wace macce.”

Ta ci gaba “kai kanka ka sani a baya ba haka nake ba kaine ka fara koyamin wadannan abubuwan,

Duba fa ka ga yadda kirjina ya fara yin laushi,dududu nawa kake ba ni a sati? Naira dubu biyar fa amma har ka ce kuma sai ka wuce can ciki?”.

Ta girgiza kanta tace “inaaa gaskiya mu cigaba da maleji dai da yan wasanninmu kuma ai kana saka yatsunka suma duk ba su gamsheka ba sai kayi mai gaba daya?”.

Hannunsa ya maida ya cigaba da wasa da kirjinta yace “wlh a matse nake ki bari ko sau daya ne inyi mana ai babu zafi tunda ina dan buda gurin da hannu.”

Hannunsa ta ture duk da irin matsuwar da ta yi ita ma tace “ban fa yarda ba,babu irin dadin da ba na jiyar da kai don haka a tsaya daga nan.”

Sai da Zinatu ta jima da dawowa sannan Maryam ta zo,
Godiya ta yi wa Iyam sosai da karamcin da ta yi mata.

Sannan suka tare adaidaita suka nufi gida babu mai yiwa wani magana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kasuwa 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×