Skip to content
Part 25 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Gadan-gadan Ilya ya shiga aiwatar da aikin amanar da Amina ta damka masa. Sai da ya kammala komai, madaidaicin ‘apartment’ din Goggo mai jan rufi ya kammala, mota kirar (E-Class) ta iso. Matsala daya ilya ya samu, wato dole Goggo ta je a yi mata fasfot da daukan hoto. Daga baya dabara ta zo masa, ya je ya samu Goggo ya ce ta yi shiri su je wani waje za a yi musu takardar zama ‘yan kasa, kuma dole sai an dauki hoto.

Goggo ba ta yi musu ba suka je aka yi mata fasfot ba da saninta ba. Aka dauke ta hoto, ba ta sa wa ranta komai ba, Ilya ya je ya biya kudin kujerar hajjin, Goggo aka yi mata ‘visa’ da komai aka sanya musu ranar tashi, sannan ne ya zo ya gaya wa Goggo komai ya damka mata fasfot dinta.

Goggo don dadi sai hawaye. wai ita ce za ta je dakin Allah karkashin inuwar ilmin Amina. Lokacin Amina na government house, Goggo ta kira ta a waya.

“Sai kuma na ji wannan alheri haka? Aminan Goggo Allah ya yi miki albarka, Ya ba ki miji na gari wanda zai tallafi maraicinki, ya rike ki da kauna ta gaskiya”.

Dadi ya rufe Amina, cewa ta ke, “Amin Goggo, Goggo Allah ya bar min ke”.

Ranar juma’a su Goggo suka tashi zuwa aksa mai tsarki. Don haka wannan satin Amina ta yi zamanta ba ta zo gida ba, ta ci gaba da kula da Ameena.

Idan Goggo Hauwa tana dawafi a ka’aba ba abin da ta ke roko, sai miji na gari ga Amina. Idan sujjada ta yi a maqama Ibrahima addu’ar da ke kan halshenta kenan. Idan safah da marwa ma ta ke roqon Allah ta ke ya fiddo wa Amina miji na gari cikin gaggawa. Wannan shi ne kadai sauran burinta a rayuwa, sai neman cika wa da imani.

Goggo na can Makkah, Amina na dakinta na gidan gwamnati tare da patient dinta, wadda ke kwance kan cinyoyinta tana mata ‘messaging’ a gabobinta. Sai kawai Ameena ta yunkura ta tashi zaune.

Dr. Amina ta ce, “Mene ne Amina?”

“Fitsari zan yi.”

Kafin ta yi wani motsi na taimaka mata don mikewa, Ameenar ta mike da kanta a kan kafafunta (all of a sudden). Ta yi hanyar bayan gida.

Amina Mas’ud Shira ta rasa abin da za ta fara yi don farin ciki. Sai kawai ta sauko daga gadon ta yi lullubi ta gurfana gaban mahaliccinta ta yi sujjadah.

“Tsarki ya tabbata gare Ka sarkin mulkin da bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba. Ba dabara ta ba ce, ba iyawa ta ba ce, ba gwanintata ba ce, iko da buwayarKa ne. Wanda in Ya ce, ‘kasance’ sai ya kasance. Tsarki ya tabbata gare Ka zuljalali wal ikrami.”

Ta dago ta karanta fatiha ta shafa, ta mike ta bi bayan Ameena bayan gida.

Ameena ta yi fitsarinta, ta yi tsarki ta dubi Dr. Amina da ke tsaye bakin kofa, da murmushi ta ce, “Mama yau na yi tafiya da kaina babu karfe.”

Da sauri Amina ta karasa ta rungume ta na mintuna, sannan ta kamo hannunta suka fito. Karo na biyu a tsayin zamanta tare da su da ta ga ya kamata ta kira Ma’arouf Habibu Ji-kas a waya.

Yan fadar shugaban kasa tare da sauran gwamnonin Najeriya gaba daya na Kudu da na Arewa suna tattaunawa a kan yadda za a magance matsalar almajiranci a Arewacin Najeriya. Kiran Amina ya shigo wayarsa da ke aljihu, wadda ya manta bai kashe ba kafin shiga taron.

“Ameena’s Doc” ke yawo a kan fuskar wayar in bai manta ba, tsayin watanni goma sha daya da suka yi tare wannan ne karo na biyu da ta taba kiransa a waya. Wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa da shi kansa ya ba shi mamaki. Tsam ya mike ya fito daga dakin taron zuwa harabarsa ya amsa kiran da sallama.

“Ameena’s Doc, ya ya aka yi ne?” Ya fada cikin taushin murya.

Amina bakinta har rawa yake, ga in’ina ta kasa fadin takamaiman dalilin kiranta. Dadi da farin ciki da suna kisa, da yau sun kashe ta.

“Um-um-um Ameena ce…”

“Me ya samu Ameenar?” ya fada cikin jin faduwar gaba.

“In ba a nesa ka ke ba, ka zo ka gani da kanka zai fi. Mu wuni lafiya”. ta kashe wayarta.

Ma’arouf Ji-kas ya dade rike da wayar a hannunsa, ya kasa tantance yanayin da ke cikin sautinta, farin ciki ne ko tashin hankali? Ya ji ‘yar damuwa ta ziyarce shi. A sanyaye ya juya ya koma dakin taron.

Haka aka karasa taron da shi a daddafe ba tare da ya kara fahimtar abin da ake cewa ba.

Bai kwana ba kamar yadda ya tsara, a daren ya nemi jirgi ya taho Bauchi.

Amina da Ameena sun yi wankan barcinsu. Amina ta sanya wa ‘yar tata kayan barci, ita kuma ta nemi doguwar rigar atamfa da kallabinta ta sanya suka bi gado suka kwanta, suka rufa da bargo bayan Amina ta gama ba ta magungunanta. Carbi ne a hannunta tana ja, idonta a lumshe. amma ba ta kai ga yin barcin ba.

Knocking aka yi, ta tashi zaune ta yi lullubi, sannan ta bada izinin shigowa. Ya shigo cikin jamfa da wando na shadda ‘Excelsior’ ruwan makuba, babbar rigar da ya cire rataye a kafadunsa. kansa babu hula kamar koyaushe, ba ya tara gashi a kansa. Akwai ‘yar damuwa a kan fuskarsa amma ya yi kokari kwarai wajen boye ta. Daga bakin kofar ya tsaya, idonsa ya sauka cikin na Dr. Amina.

“Me ya faru?” Ya tambaya cikin tsaka-tsakin yanayi. Babu fargaba kuma babu farin ciki.

Kawai sai Amina ta dan girgiza Ameena karama. Yarinyar ta bude ido nan da nan, da ma barcin nata ba wani nisa ya yi ba. Ta nuna mata bakin kofa.

“Je ki Daddy ya dawo”

Ta kalli Babanta, sai ta tsallako daga gadon da gudu, ta nufe shi ta rungume.

“Daddy yau ka ga ina takawa da kafata, babu karfe.”

Ma’arouf ya tsaya standstill, ya kasa ko da motsi. Domin bai amince idonsa biyu ba ya fi gasgata mafarki yake yi, Ameena rungume ta ke da kafafunshi tana ta ba shi labarai. Yawanci dai duk na abubuwan da Mamanta ta yi mata ne, wanda ke sa ta farin ciki, irin su danwake, kai ta bakin ruwa a wheel-chair da sauransu.

Lokaci ya ja, in mafarki ne ya kamata zuwa yanzu a ce ya farka, amma shiru! Don haka ya sanya hannuwa a kan ‘yar tasa yana shafawa a hankali. Daga bisani ya rage tsawo ya zama daidai tsawonta ya rungume ta.

Sunkuyar da kai ya yi ba tare da ya saki Ameena ba, sai kuma ga hawaye suna disa a bayan Ameena. Ya zarce da fuskantar alkibla ya yi sujjadah. Ameenah karama da ta ga ya dago daga sujjadar, sai ta kai ‘yan kananan yatsunta tana share masa hawaye, tana tambayarsa.

“Daddy me ye ka ke kuka? Daddy na warke fa”.

Ya tsane hawayensa da tissue da ke kusa da shi, ya yi mata murmushi. Ya rike dukkan hannayenta, “kukan farin ciki nake yi Ameena, ko ba ki ga kafafunki sun warke ba? Da taimakon Allah da na Dr. Amina”

Ameena ta dubi kafafun nata, “Ai kuwa tun dazu na watsar da karafan Daddy, na ce Mama ta yi maka waya ta gaya maka ta ce za ka zo, Daddy na warke”.

“Ce ne alhamdu lillahi Ameena, mun gode wa Allah, mun gode wa Dr. Amina”.

*****

Kwana uku bayan nan Dr. Amina ta soma hada tarkacenta don barin gidan gwamna Ji-kas, bayan ta kara tabbatarwa a lafiyar Ameena karama babu sauran kalubale.

Sai dai kuma abin da ya ba ta mamaki, duk yadda ta kai ga murnar komawa gaban Goggonta abin da ta fi so a rayuwarta, jikinta a matukar sanyaye yake. Ta fara samun kanta cikin wannan sanyin jikin bayan murnar warkewar Ameena, ga wata irin damuwa da zuciyarta ta shiga in ta tuna lokacin rabuwa ya zo da Ameena da babanta, Baban Amina kuma ? Wata zuciyar ta tambaye ta, ba wani mugun sabo ta yi da shi ba a tsayin shekara guda da suka yi tare, amma Ma’arouf Ji-kas ya samu wani irin muhalli a zuciyarta da ba za ta iya fasalta shi ba. Ta dade tana nazarin halaye irin nasa masu wuyar samu a wannan zamanin. Ga nagarta, ga tsare mutuncin duk wanda ke karkashinsa da tsare nasa mutuncin a kan kansa. Shugaba abin koyi wanda kowane talaka ya bude baki a jihar Bauchi, alheri yake fadi a kansa. Su da ke cikin gidansa ma sun shaida hakan. Ma’arouf ya tsaya a zuciya da ruhinta da matsayin da ba ta san wane iri ba ne. Tana jin rabuwar nan har cikin bargonta ba zuciyarta kadai ba.

A hankali ta ke ciro kayanta daga wardrove tana ninkewa tana jefa wa a ‘trolley’ dinta, Ameena na gefenta tana cin abinci, ta ce, “mama yau ba juma’ah ba ce, ina za ki je? Don Allah ki tafi da ni.”

Amina ta dube ta idonta cike taf da kwallah. Ta kasa ce mata komai, ta dau diyar Gwamna ta kai gidansu a wane dalili? Yaushe ta kai wannan matsayin? Amma ko da zai ba ta da ya yi mata babban adalci. da duk wannan damuwar hamsin bisa dari ta kama gabanta. Tana tare da jinin Ji-kas, ai kamar ji-kas ne suka ci gaba da rayuwa tare. Watakila watarana har ta ganshi a dalilin diyarsa.

A’ah! Wai me ke damuna ne Amina Mas’ud?” Ta tambayi kanta, “Ji-kas! Ba tun yau ba sunan mutumin nan yake yi mata wani irin nauyi a zuciyarta. Tun sanda ta fara jin sunansa ba ta iya fade saboda girmamawa. Amma a yau bayan girmamawa ta fahimci akwai wani al’amarin daban mai girma da ya mamaye zuciyarta a kansa da ba za ta iya fassarawa ba. Wasu hawaye suka ziraro daga idanunta na kewa da sabo. Ta daura hannu a kan Ameena tana shafawa a hankali. Daga bisani ta ture akwatin gefe ta rungume ta kuka ya kwace mata.

An yi (knocking) har sau biyu Amina da Ameena ba su ji ba dukkaninsu kuka suke yi. Ameena Ma’arouf ta gane Mama barinta za ta yi, ita kuma ba za ta iya zama da Anty Laila ba.

Cikin kuka ta ke fadin, “Mama ni binki zan yi, wallahi ba zan zauna da Anty Laila ba.”

Amina ta ce, “Cool down Ameena, da Daddy za ki zauna ba da Anty Laila ba…”

“Kullum ba ya nan, Mama ni ma ba zan zauna ba…” Sai kuka.

Amina ta rasa abin da za ta ce mata, sai ta biye mata suka dunkule suna ta rera abinsu.

Alamu Dr. Amina ta ji na an zauna a gefensu. Ta yi saurin bude ido, ta juya inda ta ji alamun zaman mutum din da kamshin turarensa na koyaushe. MA’AROUF JI-KAS ne.

Hadiye kukan ta yi baki dayansa ta saki Ameena ta ba shi baya. Ba ta so ya ga hawaye a idonta ba kada ya yi zargin tana kuka ne don za ta bar Government House.

“Kukan naku ya yi yawa…” Ya fada a hankali.

Ba ta ce komai ba, ya koma kan diyarsa.

“Kukan me ki ke yi Ameena?”

Ta share hawayenta da tafukanta biyu, kafin cikin shessheka ta ce, “Mama ce za ta koma gida yau, Daddy ni ma ba zan zauna ba, Anty Laila dukana za ta dinga yi. Mama zan bi daddy…”

Ya janyo ta jikinsa, ya aza a gefensa yana lallashinta, “Ameena makaranta zan sanya ki, wadda ake kwana, Dr. Amina ta gama aikinki za ta koma asibiti, za ta yi aure ta haifa maki kanne. Ba kya son wadannan ci gaban ga Mamarki?”

Ta yi sharbe, “Ina so Daddy. Amma ita zan bi, bana son makarantar kwanan…”

Rigima sosai Ameena ta ke yi, ta birkice musu, hatta Dr. Amina ta tsorata da borin da yarinyar ke yi, ta juyo ta kamo ta tana nata lallashin. Amma Ameena ta tubure.

Ya kai hannu ya cire hular kansa ya ajiye a gefe, sai gumi yake duk da na’urar sanyaya daki da ke aiki ba kakkautawa. Idanunsa sun kada don ko fushin Ameena ba ya so balle kukanta, shi ma ya san zamanta da Laila ba zai yiwu ba, Ji-kas ne waje na farko da ya yi tunanin maida ita ta zauna wajen Hajiya. Amma lokacin shiga makarantarta ya yi har ya wuce, ya kamata a ce tana Primary 1 amma ko nursery ba ta fara ba, shekarunta shidda. Abin da ba ta sani ba shi ne, ya fi ta jin tafiyar Dr. Amina.

Wata mace guda daya da ta shigo cikin rayuwarsa, ta sauya ta. Rana daya ta yi fatali da bulullukan da ya gina rayuwarsa a kai na auren mace daya. Ya dade yana nazarinta kafin wadannan bululluka su ruguzo. Bai taba haduwa da mace mai kyawawan halayenta da nasibobinta ba hatta AISHA. Amina Mas’ud Shira ta dade da canza wannan tunanin, kullum yana kwana ya tashi da tunanin ta inda zai tunkare ta ne ya kasa. Ba wai ba zai iya gaya mata ya yanke shawarar hada rayuwa da ita ba ne, a’ah! Azancin fadar hakan ne babu, tunda ya gama cika duniya da furucinsa na mace daya ta ishe shi rayuwa, a talabijin ne, a jaridu ne, a radiyo ne da sauransu. Shi ya sa ba a so mutum ya ce ya tsara wa kansa rayuwa, muna namu Allah na naSa, rayuwarmu tun haihuwarmu tana rubuce a allon lauhul mahfuz. Ya nisa a hankali ya dan saci kallon Dr. Amina.

“Ki daure ki kara kwana daya ban gama sallamarki ba ai, tun jiya ban zauna ba”.

Ta girgiza kai, “Na riga na yi waya da Goggo, na fadi mata yau zan koma…”

Ya bude idanu sosai ya dube ta daga kankance su da yake yi a baya.

“Sai ki fadi yadda za a yi da Ameena…”

Da sauri ta dago ta dube shi, shi ya kamata ya fadi wannan ita ya za a yi ta sani shi da ‘yarsa?

Ya karanci abin da idanunta suka fadi, ya kara janyo Ameena jikinsa duk sai suka ba ta tausayi. Ba ta san lokacin da ta bude baki ta yi magana ba.

“In za ka ba ni ina so, da ma Goggo ba ta da wadatar ‘ya’ya. I’m sure za ta hada mu ta rike da amana”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 24Sanadin Kenan 26 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×