Skip to content
Part 50 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Shekaru uku kenan da auren Maarouf da Amina, tana goyon danta na biyu mai sunan Baban Maarouf wato Habib da suke kira ABBA. Wanda ya biyo bayan danta na fari Masud. (Hanif). Maarouf na gab da sauka daga kujerarsa don haka komai ya cakude musu, ba ya samun zama ko kadan, suna yawon kamfen gari-gari don neman samun kara hayewa gwamnatin Bauchi a karo na biyu.

Sosai suke kewar sa a gidan musamman Hanif da yayi mugun sabo da mahaifinsa. Hatta wanka in yana gida shi yake masa. Abba dan maman sa Hanif dan Abbansa.Kullum haka rayuwarsu take cike da soyayya tatacciya kamar Zuma. Sabuwa take komawa a ledar ta, kullum cikin mararin junansu suke.

To komai yayi farko zaiyi karshe. Yau shekarunsu hudu ba wata uku akan karagar mulki. Tenure tazo karshe sai fafutukar yadda zaayi a cigaba. Kai ya dau zafi komai ya cushe musu babu lokacin iyali ko kadan.

A irin wadannan lokutan Amina na yiwa mijinta uzuri, bata damunsa, bata nanike masa, bata binshi da korafin rashin zamansa a gida. Mayar da hankali take kan ibada da rainon yayanta tana kuma binsa da kyakkyawar addua.

*****

A daya gefen tsohon kwamishinansa na kananan hukumomi da mai ba shi shawara kan ci gaban karkara da ya sauke sun dade da fito da sabuwar jamiyyar adawa (opposition party) da suka sanya wa suna NRC (Northern Region Congress) sun fito da karfinsu suna yakar (NPC) ta karkashin kasa da ta duk sauran hanyoyin da zasu iya.

Tsohon kwamishinan Abdallah Ganjuwa da tsohon mai bada shawarar Yushau Saminu sun tsaya neman kujerar gwamna da ta mataimakinsa.

Lokacin da Maarouf ya samu wannan labarin daga bakin Turaki da sauran kwamishinoninsa a dakinsu na zartarwa bai yi mamaki ba, in kanna siyasa ba abinda bazaka gani ba, sun ci gaba da kulla wadda za ta fishshe su ne kawai ba su sanya su a lissafinsu ba balle har su dame su.

Amma abin mamaki abin da kuma yaa kada yan hanjinsu shi ne yadda alummar jihar da dama suka soma karkata zuwa (NRC). Lokacin da aka yi (primary election) Maarouf ne ya ci, a can su kuma Abdallah ne ya ci. Allah kadai ya san irin kulle-kullen da suke yi wa (NPC) har da bin bokaye da yin kazafi iri-iri gare su. A cewarsu, mabiya jamiyyar (NPC) masu ruwa da tsaki dukkansu sumumu-kasau ne, wai macijin sari-ka-noke, kasancewarsu tsofaffin jiga-jigan jamiyyar suka rinka fidda sharri kala-kala da suka shirya musamman da rahotanni na karya da alkawurra iri-iri masu ban mamaki ga alummar jihar.

Da yawa an karkata gare su tunda Maarouf din ai dan Adam ne kamar kowa dole a wani fannin yana da kasawa. Duk da kokarin su Ilya na shiga birni da kauye suna karyata zargin da ake yi wa jamiyyarsu da kare gwamnatinsu an ce wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, Abdallah da Yushau ba rana daya suka fito ba, kwanton bauna suka yi wa (NPC) suka rarake kasansu kamaryadda suka ci alwashi. Sannan bokayensu sun dade suna shiri a kan wannan lokacin kan Maarouf da magoya bayansa.

Lokacin da zabe ya matso ya zama ko lokacin gidansa ba ya da shi, ya shiga damuwa. Yadda ya shiga damuwa haka iyalinsa, hatta Abba da ake goyo ya san rayuwar gidansu ta sauya. Amina sai ta kwashe sati guda cur bata sanya Maarouf a idanunta ba.  Hakan baya damun ta addua kawai take ba dare ba rana, idan mulkin nan alkhairi ne a gareshi Allah ya maimaita masa, in babu alkahairi tana rokon ubangiji ya fitar dashi daga ransa ya huta suma su huta.

Ranar zabe duk suna (polling unit) na mazabarsu shi da iyalinsa, Amina rike da hannun Hanifa Abba yana kwance a kafafunta, anyi-anyi a karbe shi ya ki sai kuka yake yi, ta zauna don ta shayar dashi ya ki yarda ya kama nonon sun rasa abinda ke damunsa, Dr. Turaki ne yayi nasarar karbar sa ya fita daga wajen dashi, Amina ta rasa abin da zatayi ta rasa me ke mata dadi kawai sai ta tsugunna ta soma kuka.

cikin tawagar harda Goggo, Kaka Maryama, Inna zulai, Dr. Zainab Turaki da nata iyalin, Ilya da iyalinsa,  yaransa biyu shima, Hajiya Saude wadda aka fi sani da Hajiyan Ji-kas, Alhaji Mansur da daukacin iyalinsa, Uwa uba mahaifin da ya haifeshi Mallam Habibu, Dr. Umar Bolori da family din gidansu duka, da duk wani makusancinsa suna tattare a rumfa guda anan suka jefa kuriunsu.

Aka taru akan Amina ana lallashin ta wadda baa san kukan me take ba, ita kanta bata san kukan me take yi ba ko me ya sanya ta kukan, ta san danta lafiyarshi kalau yanada damuwa ne irin ta kananan yara ga iyayensu har suka dawo gida, amma da tayi tsam da zuciyarta sai ta fahimci Maarouf take tausayawa, tausayi mai dumbin yawa domin jikinta ya gama bata zaben nan basu da nasara.

Suka dawo gida suka zauna gaban radio.

Aka tafka zabe aka gamaa karo na biyu, Maarouf Habibu Ji-qas ya fadi. Wato ya sha kaye daga abokin karawarsa Abdallah Ganjuwa. A lokacin da zuciyarsa ta afu ga son ci gaba da kujerarsa!

Bai san yana son mulkin har haka ba, sai lokacin da kafafen yada labarai suka bayyana an kayar da shi. Kayarwa daga abokin takarar da bai taba zato ba.

Ya shiga damuwa ba yar kadan ba, Amina dake gefe ta kashe radion, ta shiga karfafa masa gwiwa tana tunatar da shi muhimmancin yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi, tana ankarar da shi tarin niimomin Ubangiji a gareshi, kada ya butulce, ta cigaba da tuna masa; sanda ya bashi mulkin nan fa ba kokarin sa bane ko na magoya bayansa, ya gode maSa, ya karbi sauyin da hannu bibbiyu.

Ya bude ido yana kallon ta,wani irin kallo mai tsayi da zurfi, a zuciyarsa yana fadin ko da ke kadai na tsira zan iya rayuwa a duk inda na tsinci kaina. Sabo ne turken wawa!

A fili ya rinka maimaita kalmar Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Har sau uku. Wata irin nutsuwa ta zo masa. Ya runtse idonsa ya bude su a kanta, ya mika mata tafukan hannayensa biyu ta kama ta mikar dashi tsaye. Toilet ya nufa ya dauro alwala ya tada sallah. Amina ta mara masa baya ta hanyar janyo hijabinta ta bishi sallahr.

Sosai suka samu nutsuwa, da gaske ne samun mata ta gari shine cikar rabin addini. He thank ALLAH for this blessing, yana rokonsa ya tashe su tare har a gidan aljannah.

Ya kwantarda kai a kafadunta, ta rike shi sosai a jikinta. Tuni ya manta da komai.

Sauyin Rayuwa

Suna ji suna gani ranar wata asabar suka tattara suka fito daga gidan gwamnati, Amina kullum cikin kwantar wa da maigidanta Maarouf hankali ta ke har ya ware ya saba da sabuwar rayuwarsa. Suka share gidansa na Fati Muazu, sabuwar rayuwa ta fara.

Ameena little ta gamaprimary a shekarar. Mahaifinta ya kai ta makarantar sakandire ta kwana ta Nigerian Turkish dake Kanoaka sanya ta a J.S.S 1. A shekarar ne kuma Amina ta kara haihuwar yarta mace mai kama da ita a komai. Ta roki Maarouf alfarmar ya sanya mata sunan kakarta da ta rasu a wannan shekarar, mahaifiyar Goggo, wato Maryama, suna kiranta Maryam.

Amina ta koma bakin aikinta a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBU Teaching Hospital), da taimakon Dr. Turaki. Maarouf ya koma (contract) din gine-ginensa, saidai samun kwangilar gine-ginen ya ja baya ba kamar da ba, tunda gwamnatin dake bada kwangilar ba tasu bace.

Sauyin rayuwar da suka samu za su iya cewa mai yawa ne. Abin da za a ce shi ne ba sojoji babu bodyguards da masu take baya, babu (security), babu maids rututu da sauransu, bayan wannan babu ta inda rayuwarsu ta canza ba su nemi komai sun rasa ba sai mulki da abin da ke zagaye da shi.

Bayan barinsu gidan gwamnati Ilya ya zama babban yaron Maarouf shi ke kula da harkokin gidansa kuma ya yanka albashi yana ba shi duk wata duk da bai kai wanda yake karba lokacin da ana gwamnati ba, cike da godiya da kyakkyawar zuciya yake zaune da uban gidansa.

A tsayin shekaru uku na zaman su gidan Maarouf na Fati Muazu Links, Amina ta sake haihuwa, wannan karon ma diya mace  ta haifa. Maarouf ya yi mata kuhtbah da sunan mahaifiyarsa, wato Saudatu.

Shekarunsu biyar kenan da aure yayansu hudu, maza biyu mata biyu da babbar Yayarsu Ameena, wadda ke zana jarrabawar kammala karamar sakandire a wannan shekarar daga Nigerian Turkish.

*****

Gaskiya Dokin Karfe

Shekaru uku kenan da kafuwar sabuwar gwamnatin (NRC) a jihar Bauchin Yakubu, tun kafin a kawo wannan lokacin talakawan jihar suk soma dandana kudarsu a hannun sabon gwamna Abdallah Ganjuwa. Hatta ruwan sha da na amfani ya gagare su, wutar lantarki sai a yi wata ba a kyallaro musu ita ba, jinkirin albashin maaikata da sauransu. Wannan kadan ne in aka yi laakari da yadda rashin tsaro ya bi ya addabi jihar, sata, sane, kwace da fashi da makami, hanyar Bauchi ba ta biyuwa saboda yan fashi da suka mamaye ta kuma gwamnatin ta kasa yin komai akai, haka kebantattun unguwanni basa shiguwa, babu wani kokari dagagwamnatin jihar ta kasa yin komai sai sata da itama ta sanya a gaba.

A yadda talakawa suke tunzure da sabuwar gwamnatinsu da da-na-sani wajen zabenta la-shakka da lokacin mulkin soja ne, sai sun yi mata juyin mulki.

Allah-Allah suke ta gama cin-zalinta ta kara gaba su dawo da gwamnatinsu mai adalci. Ko da wannan (rumours) ya shiga kunnen Maarouf tsaki ya yi, ya ce, ina! Siyasa ya gama ta, ba ya fatanta, ba ya sake kwadayinta.

Matasan Bauchi wadanda suka san sun amafana ne karkashin (Maarouf Foundation) har suka tsaya a kan diga-digansu sun ci alwashin sake tsayar da tsohon gwamnansu duk da ya bayyana raayinsa na ba ya shaawa, ba ya bukata. Ilya ne ja-gabansu suka yi tattaki suka tadda Baba da Alhaji Mansur da kokon bararsu na su shawo musu kan Engineer Maarouf ya yarda da kyakkyawan kudirinsu su sake tsayar da shi takara a karo na biyu.

Baba da Alhaji Mansur suka sanya shi a gaba a wani yammaci, su billo ta nan ya billo ta can wajen nuna ba ya raayi, siyasa sai ta neman aljannah ce ta rage masa.

Su kuma suna fadin jihadi zai yi in ya koma ya ceto alummarsa daga hannun wannan azzalumin shugaba.

Haka yana ki yana komai matasan Bauchi suka yi gangami suka sai masa (form) na tsayawa takarar gwamna a karo na biyu. Ilya ne shugaban kamfen a birni da kauyuka, ya tsaya wa kamfen din da jikinsa, lafiyarsa da aljihunsa, ba su samu kwanciyar hankali ba sai da suka maida shi kan kujerarsa ta gwamnan Bauchi a karo na biyu.

Amina ta hakura da aikin asibitinta a karo na biyu ita ma, Maarouf ya bude mata asibitin kula da masu lalurar shanyewar barin jiki nata na kanta, ta ci gaba da kula da Goggonta da yan uwanta.

A dalilinta sai da dukkan danginta suka baro kauyen Shira suka dawo maraya, ta sama musu abin yi. Wadanda ba sa son zaman marayar sun samu abin yi mai karfi a kauyen, Hassan dan Baffa Bilya na cikin wadanda ba sa son zaman marayar shi da iyalinsa, shi ta nada wa alhakin kula da gidan gonarta na tantabaru da tsuntsayen gida da ke Shira.

A wani hutu da Maarouf ya dauka na karshen shekara Amina ta jajibeshi suka yi Sierra Leone tare. Ya ga tarba ta mutumci da karramawa daga dangin Amina. Yaran duka har Amina karama sun ji dadin hutun su a Sierra Leone sabida basu taba fita daga cikin Africa ba saboda patriotism din mahaifinsu. Gara Amina little taje Saudiyyah sau uku. Maarouf da Amina suna adduar Allah ya basu tsawon rai su cika barinsu akan Aadil (babban dan Dr. Turaki) da little Amina, wanda ke ajin farko a jamia yana karantar medicine.

Rayuwar Maarouf da Amina ta ci gaba da yin albarka cikin niimomin Ubangiji masu yawa, sun tara iyali masu albarka.

Suka ci gaba da cin gwamnatinsu cikin kwanciyar hankali da burin neman kujerar da ta fi wannan a can gaba idan mai duka ya yarje masu da lafiya da nisan kwana.

*****

Masha Allah laquwwata illa billah.

Nan na kawo karshen littafin

SANADIN KENAN, sai mun hadu a littafina na gaba mai suna:

AUREN  KWANGILA

Taku har kullum.

Sumayyah Abdulkadir Takori.

Dandano Daga

AUREN KWANGILA

Nisawa AbdulAziz yayi, ya sauke numfashi mai nauyi, Ishma, wata musiba ce ta tunkaro ni nake so ka taimaka min. Nikuma nayi maka alkawarin yi maka duk abinda kake so a duniya, zan kuma dinga raba albashina biyu ina turo maka rabi har ka gama karatun ka ka tsaya da kafafunka.

Maganganun sounds funnya kwakwalwar Ismael Dakata. Daga ji ba abin alkhairi Yayan zai nema ba tunda har sai ya biya laada.

Ni kuwa me zan yi maka da har sai ka biya ni Yaya Azeez? Gaya min ko me kake so in yi maka kawai in har na alkahairi ne zanyi. Zan iya fansar da raina don in cece ka. Amma wace irin musiba ce wannan da iyayenmu bazasu iya yi maka maganin ta ba sai ni?

Su suke son jefa ni cikinta ai Ismael subhanallah! Please Yaya kada ka sake fadin haka, nayi amanna bazasu taba jefa ka a musiba ba sai alkhairi ga rayuwarka. Yanzu dai me kake so inyi? A shirye nake da in taimaka in har zai tafiyar da damuwar ka. Wallahi ba sai ka bani komai ba zanyi, nima ka sanya ni cikin damuwa matuka

Abdulaziz ya canza rikon wayarsa daga kunnen dama zuwa hagu, ya juya ya tabbatar babu kowa a cikin dakin kuma babu motsin kowa daga waje.

So nake ka bugo waya wa Mammah, ka ce mata ka dade kana son Hafsat, don Allah a baka aurenta, ka kasa maida hankali kan karatun ka saboda soyayyar ta, ka ce sonta kake tun tana yarinya, ka nuna mata irin wani abu zai iya samun ka dinnan idan baka samu aurenta very soon ba, sauran kalaman ka tsara abinka ai kai ba yaro bane tunda na baka topic din, ka gane?

Mamaki ya gama kashe Ismael a tsaye, sai da ya lalubi kujera ya zauna Yaya wace Hafsat din? Ta gidanku mana? kana nufin Suhaana? nifa Ishma sunannakinnata ba duka na rike ba, kuna kiranta da sunaye barkatai, I dont know! Ta wajen Mammah dai.

Don Allah Yaya muyi magana ta fahimta, Hafsat-Suhaana Addar Mammah?

A ginshire Abdulaziz ya rausaya da kai Eh,  ita, don naji Baba Azumi ma ta ce mata Addar.

Dariya ta kama Ismael amma ya gimtse, yanzu ya gano bakin zaren duk da bai gayamasa ba. Mamakin Yayan nasa ya kama shi matuka, amma tunda bai fito fili ya gaya masa dalilin bukatar tashi gareshi ba, bari ya bishi a hakan.

Yaya akan me to? Akan me zanyi hakan? Akan me zan yaudari Mammah inyi wasa da hankalinta akan abin da ba haka yake a zuciyata ba? Yaya Hafsat mai martaba ce a wajen Mammah damu bakidaya da muka rayu tare muka  san wacece ita, wace irin martaba Allah ya yi mata.

Kasancewar ta ba jinin mu ba, baya nufin bama kaunarta ko don kaunar da mahaifiyarmu ke mata. Yarinya ce ta gari, amana a hannun mahaifiyarmu, ta yaya kake tunanin zan iya playinggame akanta? To akan me ma?

AbdulAziz ya hadiyi miyau, jin makoshinsa ya bushe kyamas, ga dukkan alamu bazai samu nasara a plan 1 ba, amma dai bari ya cigaba da turzawa tunda Ismael dai a kasan sa yake.

Akan duk kaunar da kuke mata bata kai wadda ke tsakanina daku ba!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 49

2 thoughts on “Sanadin Kenan 50”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×