Washegari da Gwoggo ta haɗa wasu garuka na gyaran mata ta takura Hamida sai da ta sha, tana gama sha ta ɓalle da amai, kamar wasa amai ya miƙe ya ƙi tsayawa tun tana yi da ƙarfinta har jikinta ya fara saki.
Hankalin Gwoggo ya yi masifar ɗagawa, hankali tashe ta kira Nurse Saratu da ta zo allurar amai ta haɗa za ta yi mata amma Hamida ta yi tsalle ta dire ta ƙi yarda, idan suka taro ta nan sai ta yi can tana yarfa hannu.
Haka ta yi ta wahalar da su suna zagaye falon. . .