Skip to content
Part 15 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Washegari da Gwoggo ta haɗa wasu garuka na gyaran mata ta takura Hamida sai da ta sha, tana gama sha ta ɓalle da amai, kamar wasa amai ya miƙe ya ƙi tsayawa tun tana yi da ƙarfinta har jikinta ya fara saki.

Hankalin Gwoggo ya yi masifar ɗagawa, hankali tashe ta kira Nurse Saratu da ta zo allurar amai ta haɗa za ta yi mata amma Hamida ta yi tsalle ta dire ta ƙi yarda, idan suka taro ta nan sai ta yi can tana yarfa hannu.

Haka ta yi ta wahalar da su suna zagaye falon.
Sallamar Abdurrashid ta sanya su kallon ƙofar suna amsawa Gwoggo da Nurse Saratu, Hamida da ke tsaye bayan kujera sai ta duƙa ta kuma maƙalewa kawai. Ya shigo ya zauna yana gaida su Gwoggo Nurse Saratu ta mike ganin zuwan Abdurrashid “Bari in je gida Haj Indo. “To yanzu ya za mu yi Maman Maama? Kin ga aman bai tsaya ba, Hamida ki fito a yi miki allurar nan.”

Sai sannan Abdurrashid ya dago kai “Me ya same ta? Ta ce “Tun ɗazu take amai.” a hankali ya furta “Subhanallah me ta ci? Sai Gwoggo aka kama dabur -dabur “Ok ina allurar? Ya tambaya Nurse Saratu ta miƙa wa Gwoggo ita kuma ta matsa ta ba shi “Fito nan Hamida.” Abdurrashid ya faɗi cikin dakewa, ƙara maƙalewa ta yi don idan dai ba mantawa ta yi ba yau shi ne karo na farko da ta ji ya ambaci sunanta ba.

Ina take? Ya tambayi Gwoggo da hannunta ta nuna mishi inda take ya miƙe ya nufi wurin, Nurse Saratu kuma ta yi amfani da damar ta bar falon “Fito kawai.” Ya ce mata ya yin da yake tsayawa a gabanta ta fito tsamo tsamo har da hawayenta don ta san ba makawa sai ta sha allura, tuna shi ɗin likita ne na Sojoji wandon Sojojin da ke jikinsa ya sa jikinta ƙara ɗaukar rawa.

“Mu je.” Ya ƙara ba ta umarni ta wuce zuwa inda Gwoggo Indo take, cikin turo baki ta ce “Ni zan sha ruwa.” Gwoggo ta wuce da sauri ta kawo mata, tana gama sha ta fara yunƙurin amai da gudu ta yi dakinsu a toilet sai da ta dawo da ruwan ta fito Gwoggo na riƙe da ita suka koma falon ya ce “Zan yi mata allurar aman yanzu, sai mu je Hospital in duba ta.” Hawaye Hamida ta fara ganin yana nufo ta ita kuma Gwoggo ganin ya nufo Hamidan sai ta yi waje.

Yana zuwa kuma kamata ya yi zuwa kujera, ya zauna sai ya ɗora ta a cinyarsa jikinta sai rawa yake wai ita ce yau a kan cinyar Soja, ita gabadaya ma wani namiji bai taɓa mata haka ba.
Hannuwansa ya zagayo kan cikinta “Me kika ci ya sa ki amai? Ya faɗa kamar mai raɗa saitin kunnenta, wani yar ta ji har cikin cikinta.

“Maganin sanyi Gwoggo ta ba ni.” ta samu kanta tana ba shi amsa. “Me ya sa ba ki son allura? Ya faɗa cikin wata murya da har ta fi ta farko sa ta shiga wani hali. Hannunsa da ta ji ya sa cikin jikinta yana shafa bayanta ya sa ta ƙoƙarin tashi ta gudu ya riƙe ta riƙo mai kyau, tilas ta sallama ba ta ankara ba sai dai ta ji allurar ya tsira mata.
Ga mamakinta ba ta ji zafi ba, ya sa hannunsa yana liliya mata wurin ai tana jin ya sassauta riƙon da ya yi mata sai ta tashi ta gudu kujerar nesa da shi ta rufe fuska.

Ya daɗe zaune yana taɓa wayarsa kafin ya miƙe ya fita ta bi bayansa a gindin bishiya suka ga Gwoggo, ta ce “Har ka fito, ba za ku Asibitin ba? Ya ce “In sha Allah ma zai tsaya, idan kuma ta ƙara sai a kira ni.”

Ya wuce Gwoggo na mishi a sauka lafiya. Hamida ƙin bin sa ta yi don kunyar cinyarsa da ya sa ta.

*****

Wannan kenan. Abdurrashid ya ci gaba da zuwa wurin Hamida, duk kuma bayan kwana biyu yake zuwa.

Family ɗinsa shirye-shirye kawai suke na bikin tarewar, ba wanda ya koma ta kan angon da ya ƙi bayar da haɗin kai, don shi kam bai shirya ma a ga yar ƙaramar yarinyar nan kamar Hamida a ce ita ya aura, sai tsiya Daada ke mishi ta ce “Ita san da aka yi mata aure shekaru sha biyu ne da ita, amma ta yi biyun hamida a girma, dan dai hamida ba ta da ƙiba ne shi ya sa yake raina girmanta.
Duk kuma ƙin shi akwai Dinner da mahaifinsa ya shirya za a yi a daren da aka kawo Hamida ɗakinta, manyan mutane ne za su halarta saboda rashin sanar da su ɗaurin aure.

*****

Ana gobe za su wuce Daura idan kuma sun je kwana daya za su yi a juyo da ita Kano, Abdurrashid ya iso da yammaci.

Bai shiga ba da wayarsa ya yi amfani ya kira ta.
Ba ta cikin shiri don aiki take taya masu aikin Gwoggo tuni suka koma abincin sayarwar su wanda Gwoggo Indo ta ce ba ta ga dalilin zama har sai Hamida ta tare kafin ta koma sana’arta ba, daga Abdurrashid ba ɓanɓaruwa yake ba.

Cikin sauri Hamida ta shiga ta watsa ruwa wata doguwar riga ta zura ta yane kanta da gyalen rigar sai ta fita, yana cikin mota bai fito ba ta san miskilancin na kai kenan indai ya ƙi fitowa, ta zagaya ta buɗe motar ta shiga ta gaishe shi “Fita za mu yi, zan buɗe miki account saboda tafiyar da zan yi in bar ki zan dinga sanya miki abin da za ki yi amfaninki da shi.” Ta ɗaga mishi kai. Daga haka motar ya tada suka bar wurin, har kuma suka isa bankin babu wanda ya yi ko tari a cikin su.

Ba wani ɓata lokaci aka gama komai, muhimmin abin da ya sa ya zo da ita ma ATM da za a yi mata don an riga da an yi mata komai.
Da suka fito ji ta yi kamar ta roƙe shi ya kai ta gidan su Walida duk da sanin da ta yi Walidar na nan tafe da yamma za ta kwana gidansu washegari su wuce Daura.

Sai dai suna rabuwa da Abdurrashid wanda yana sauke ta ya wuce Walidar ta samu zaune ta iso, suka shiga murnar ganin juna Walida ta ce “Ya za a yi da ƙawayena da na gayyata masu son zuwa Daura? Daidai nan Gwoggo ta shigo, ta cafe “Ai ba za ta iya mishi magana ba, shi kuma ba taɓuwa yake ba.” Nan Gwoggo ta yi ta surfa uban faɗa kan rashin ba Hamida komai na game da biki da Abdurrashid bai yi ba. Hamida ba ta ji daɗi ba saboda Walida na zaune amma ba yadda ta iya.

*****

Abdurrashid shi ya bayar da motar da ta kai su Daura su biyar. Daga Hamida da walida sai Gwoggo da wata aminiyarta sai Laila.
Taran biki suka samu a na yi, yan’uwa duk sun iso dan su iyalan gidan ma kawai Malam, suka ɗauki hanya.

Sun kusa shiga Kano Aunty Zainab wadda ita ta wakilci sauran yan’uwanta zuwa Daura, ta ciro wayarta jin shigowar saƙo *Ka da ku kai yarinyar nan part ɗina, jama’a za su ɓata min wuri Aunty na roƙe ki.

Saƙon da ta gani kenan daga Abdurrashid ɗan murmushi ta yi “Ja’iri za ka shiga hannu.” Ta faɗi a hankali.

*****

Wani keɓaɓɓen wuri cikin part ɗin Aunty Karima aka sauki amarya da yan’uwanta. Sai da suka ci abinci suka yi sallah a ka zo a ka tafi da Hamida don shirya ta zuwa wurin Dinner.

Yayansu Momi Binta yammata su suka zagaye Hamida da ana yi mata make-up, su kuma suka zame mata ƙawaye a wurin don Abdurrashid ya hana ta faɗi ma kawayenta na makaranta bai so idan ta koma makaranta a gane ita matar aure ce, da ma ita ba faɗi za ta yi ba Walida ce mai giggiwar faɗin.

Duk kuma abin nan da ake Walida na tare da ita Abdurrashid ma ba da son sa ba abokansa masu tarin yawa sun zo bisa jagorancin Usman wanda shi ya gayyace su.

Manya daga ko’ina tun daga Nigeria har ma da wasu ƙasashen sun hallara.

Da aka dawo Dinner ma yaran su Aunty Safiyan ba su bar Hamida ta kwana cikin danginta ba janye ta suka yi duk da su ɗin ba tsararrakinta ba ne, mutum biyu ne suke kai ɗaya.

Washegari aka yi mata buɗar kai irin na su na mutanen Yola yan Daura sun ga ruwan arziƙi wanda aka tura wa Hamida da mahaifiyarta duk da su ma ɗin tushen su yolan ne hausawa suka ce kowa ya bar gida gida ya bar shi. Su yanzu al’adun Katsinawa suke yi.

Idan wannan ta zo ta bayar da nata wannan idan ta fito sai ta bada sama da haka.

Amarya ta yi kyau har ta gaji, ana tashi yan Daura suka wuce gidan Gwoggo Indo bayan sun sha kyaututtuka daga Engineer da kuma atamfofi da aka raba da dardumai ban da ƙananan abubuwa.
Walida ma ana yin sallar magarib ta yi wa Hamida sallama ita kuma ta miƙa mata wasu kuɗi da ta amsa hannun Gwoggo Indo tare da yi mata godiya.

*****

Ta idar da sallar Isha’i a tafkeken dakin da yammatan suke Aunty Karima ta leƙo ta yafuto ta da hannu Mimi ɗiyar Aunty Zainab ta farko da ke kusa da Hamida tana danna wayarta ta ce “Pls Aunty kar ki ɗauke mana ita.” Yarinyar Momi Binta ta uku da ma su biyun su ne tsararrakinta mai suna Hanan ta miƙe tana haɗa hannaye “Pls kar ki ɗauke mana ita Aunty.” Aunty Karima ta kama baki “Kai ku ji mun yara, dakin mijinta za a kai ta idan kuma a gaya wa Hamman naku kun ce a bar muku ita shi kenan.” A tare suka ɗaga hannaye “A’a ba mu ce ba.” Dan ba ƙaramin shakkarsa suke ba, ko da ba komai yake musu ba sai dan rashin sakin fuskarsa.

Ta bi bayan Aunty Karima har bedroom din Auntyn, ta wuce bathroom ta haɗa mata ruwan wanka da kanta ta fita ta bar ta wankan ta yi ta fito tana jin daddaɗan ƙamshin da take yi.
Tsaye jikin madubi ta samu Aunty Karimar ta ba ta wuri ta ce ta zauna da taimakon ta ta zuba kwalliya , wasu irin kaya da Hamida ta rasa mene ne ta ba ta ta sanya, doguwar riga ce da lulluɓinta ta kama mata hannu suka bar dakin, don ta rufe har fuskarta, wani falo suka shiga wanda Daada ke zaune da ƴayanta, ta zaunar da ita gaban Daada nasiha sosai Daadar ta yi mata game da zaman aure, maganar mahaifiyar Abdurrashid da ta yi dukkan su sai da suka yi ƙwalla, a ƙarshe ta ce su kai ta wurin mahaifin Abdurrashid da Haj Mariya kafin su miƙa ta ɗakinta, Aunty Karima da Aunty Zainab su manyan suka ce su je su raka ta.
Sam barka da suka fara kai ta sasan maigidan nan suka tarar da Haj Mariya har ma da yayarsa Haj Gambo, bayan ƙare gaisuwa fatan alheri kowannen su ya yi suka kuma ba da kuɗaɗen da ake ba amarya idan an kai ta wurin dangin miji.
Sai suka miƙa ta sasan Abdurrashid ta ƙofar da za ta sa da ka da sasan mahaifin nasa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 14Shirin Allah 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.