A farkon Gate ɗin Hamida na duban wurin saida abincin Gwoggonta sai ta ji kewarta mai yawa ta kamata. Suka wuce zuwa gida, yana parking sai da ta bari ya fita kafin ta buɗe ta fito. "Mu je wurin Aunty Karima su gan ki waɗannan 'yan rawar kan."Kai ta gyaɗa sai ta bi shi a baya.
Yanzu ma kamar da safe zaune suka same su sai dai ba a falon da suka gan su da safe ba, gaishe su suka yi Aunty Karima ta kira mai aikinta ta ce a kawo musu abinci, kai ya girgiza. . .