Ranar juma'a da aka tashi makaranta turowa ya yi aka kai ta gida don yana da aiki.
Sai da ta canza kaya ta ci abinci Aunty Karima ta kira ta a waya ta ce ta zo ta yi baƙuwa, ta isa sasan sai Gwoggonta ta gani daɗi ne ya lulluɓe ta ta zauna kusa da ita tana gaishe ta, ita ma cikin farin cikin take amsawa yadda ta ga Hamida.
Hamida ta ce ta zo su je wurinta, falon da ya nuna mata ya ce za ta iya kai baƙinta ta kai ta, ta bu. . .