Skip to content
Part 18 of 37 in the Series Shirin Allah by Maryam Ibrahim Litee

Ranar juma’a da aka tashi makaranta turowa ya yi aka kai ta gida don yana da aiki.

Sai da ta canza kaya ta ci abinci Aunty Karima ta kira ta a waya ta ce ta zo ta yi baƙuwa, ta isa sasan sai Gwoggonta ta gani daɗi ne ya lulluɓe ta ta zauna kusa da ita tana gaishe ta, ita ma cikin farin cikin take amsawa yadda ta ga Hamida.

Hamida ta ce ta zo su je wurinta, falon da ya nuna mata ya ce za ta iya kai baƙinta ta kai ta, ta buɗe fridge ta samu akwai lemo da ruwa ta ɗauko ta ajiye gaban Gwoggon.

Hira suke a hankali Gwoggo tana ba ta labarin jarin ta ya yi ƙasa saboda hidimar bikin nan, hakanan dai take rurrumawa Hamida ta miƙe ta ce tana zuwa ɗakinsu ta koma ta ɗauko hand bag ɗinta ta dawo wurin Gwoggonta.

Ta tura hannunta cikin jakar ta ciro duka kuɗin da ke ciki wanda yake ba ta ba tare da ta ƙirga ba ta miƙa wa Gwoggo su duka.

Sai da ta ƙirga ta ce “Waɗannan fa ba ta ko numfasa ba ta ce “Ba ni yake kullum idan ya sauke ni makaranta.”

Gwoggo ta taɓe baki ” Mai hali dai bai fasa halinsa, duk wannan uban arziƙin ji abin da aka samu a wurin ki, shi dai na rasa abin da ya sa yake ƙanƙamo.

Hamida dai ba ta ce komai ba duk da ta ji ba daɗi ranta ya sosu da yadda ta aibata shi.

Wata kwalba Gwoggo ta ciro cikin jakarta sauyoyi ne a ciki sai aka zuba ruwan turare “Kin ga wannan Hamida duk dare in za ki kwanta ki ɗan tsiyaya a hannunki ki yi Bismillah ki shafa wa fuskarki, zuwa ƙirjinki har zuwa mararki, namiji duk taurin ransa ya yi amfani da ke sai ya yi ladab, sati mai zuwa zan zo in ƙarɓi kuɗinsa.

Ban da ba ki son na sha an kawo kala daban daban masu kyau kina amfani da su kwana nawa za ki kama shi a hannunki, kina dai ganin yan’uwanki dubi dai Laila yadda Ahmad ya zama kamar bawanta, ba kuma boka ba Malam, kayan nan dai na mata nake kai mata duba ki ga yadda sasan su ya zama daban a gidanmu.

Aina da aka kai jiya jiya da ta ce in turo Acc no dubu dari biyu ta sanyo min, amma ke Hamida duk uban wannan arziki sai tarkacen canjin makaranta.

Ta ciro wani garin magani a farar leda “Ki daure Hamida ki sha wannan da madara yanzu a gabana.
Fuska Hamida ta ɓata tuna maganar Nurse Saratu ta ce “Ba na sallah Gwoggo.

Cikin rashin jin daɗi Gwoggo ta miƙo mata “Ki tabbatar kin sha kina gamawa.”

Ta gyaɗa mata kai ta je ta ɓoye ta dawo Gwoggo ta ce za ta tafi suka fito tare tana mata rakiya, hango Mami Haj Mariya tsaye da wata mata ya sa su nufar inda suke, sai da Gwoggo ta gama gaishe su Hamida ma ta bi sahu sai suka wuce har gate ta raka Gwoggon nata ta juyo za ta gifta su Mami ta yafuto ta ta isa ta tsaya “Ba ki taɓa zuwa kin gaishe ni ba, ko da yake wannan miskilin banzan ai ba zai ce ki zo ki gaishe ni ba.” Ta taɓe baki Hamida dai ta tsaya shiru sai matar da suke tare ta ce “Tafi yarinya.”

Hamida ta juya, Haj Mariya ta kuma taɓe baki “Ai duk shegen jin kansa ya ɗauko inda za a bi da shi.” Waccan matar ta ce “Me ya sa kika ce haka? Ta ce “To mariƙiyarta waccan da ta fita ba ƙaramar hatsabibiya ba ce wurin sanin maganin mata masu kyau, duk inda zan zaga in saya sai na dawo wurin ta don nata ne kawai zan yi amfani da shi in rikita Alh, ga shi ta yi kitimirmirar shigo da diyarta gidan nan, dole ina ji ina gani zan haƙura da maganinta.”

Waccan ta ce da ba ki yi saurin sarewa ba ki sa a yi miki bincike inda take sarowa ki fantsama can, don yanzu da ma ba za ki haɗa sirri da su ba.”

Ta ce “Kin kawo shawara zan gwada yin hakan.”

Da Hamida ta koma ɗaki Innawuro ta kira a waya, har Innarta sai da Innawuro ta tilasta ma wa ta karɓi wayar, Hamida ta gaishe ta.

Tana gamawa yau wanka ta yi da wuri ta yi kwalliya da wasu riga da skirt da suka yi matuƙar karɓarta na cikin kayan aurenta, ta sanya wani siririn gyale ta rufe kanta ta zura takalma ta fita da niyyar zuwa part ɗin Aunty Karima.

Fitowarta ta hango Abdurrashid da abokinsa Usman waɗanda suka ba ta baya ta wuce abin ta sai dai tana zama ta dai gaida su Aunty Zainab da ba su daɗe da shigowa gidan ba kiran Abdurrashid ya shigo wayarta tana ɗagawa faɗa ya kama mata wa ya ce ta fita yana kashe wayar ta miƙe tsam Aunty Safiya ta ce “Ina kuma za ki daga shigowa?

Murmushi ta yi Momi Binta ta ce “Yi zaman ki Daugter ga kilishi nan da Zainab ta sanya aka kawo ki ci.” Ta sunkuyar da kai “Shi ya ce in dawo.” Ƙwafa ta yi tana cije baki “Ban da tafiya zai yi da sai na saɓa wa ja’irin yaron nan, ya bar yarinya ta shiga mutane sai ya ce kullum tana can ɗaka ƙunshe ba sai ya bar ta da Karima ba ta samu abokiyar hira ita ma.”

Mai aikin Aunty Karima ta kira ta ce ta ɗebo kilishi ta kawo, da ta dawo aka ba Hamida ta yi godiya ta fita.
Yanzun ma tsayen ta gifta su shi da abokin nasa Usman ya yi dariya “Ka ga abokina ina tausaya ma idan yarinyar nan ta ƙara girma, don ba ƙaramin juya ka za ta yi ba.”

Ya harare shi “Sai ka ce wani kai Allah ya kyauta.”

Ya ce “Shi kenan ai muna nan, Allah ya nuna mana, bari in barka ka bar yarinya ita kaɗai.”

Suka yi musabaha ya faɗa motarsa Abdurrashid ya shiga ciki zaune ya same ta riƙe da wayarta bai amsa sannu da zuwan da take masa ba illa tambayar ta da ya yi “”Me kike karantawa a waya ne da ba ki gajiya da riƙe ta? Ba ta amsa ba illa ƙara sunkuyar da kai da ta yi.

“Ba ni wayar.”. Ya ce yana kallon ta, ta tashi a hankali don idonsa da ke kanta sai ta miƙa masa a tsayen yake dubawa ganin novel ne take karantawa ya dago “Me ya sa ba ki dagewa wurin duba takardun ki na Sch sai ki dage kan wannan shiriritar?

Ta ce “Ina dubawa.” Kai ya kaɗa ya wuce ya cire kayansa.

Yau bai yarda sun zauna wuri guda ba don yadda shigar ta ta rikita masa lissafi ya ce su je part ɗin Aunty Karima su yi ma su Aunty Safiya hira.

Suna can har sai da Aunty Zainab ta ga Hamida ta kwantar da kanta a hannun kujera ta ce “Kai yarinyar nan ta kwanta Abdurrashid.”

Da suka kwanta idanuwansa ya rufe da ƙarfi a fatan da yake barci ya ɗauke shi Hamida ce ta tsaya shiga toilet bayan ta cire kayan jikinta, ta gama abin da za ta yi har za ta fito ƙafarta ta zame ta daki ƙofa sai ta faɗa kan ƙafar wani irin zafi ya ratsa ƙwaƙwalwarta ta fasa kuka lokacin da ta yi ƙoƙarin taka ƙafar ta wuce, sai hawaye wasu na korar wasu.

Abdurrashid da tun fasa kukanta ya buɗe ido ya mike da azama ya yi toilet ɗin yana turawa ya gan ta inda ta faɗi tana kuka “Me ya same ki?

Ya tambaye ta “Zamewa na yi. Ta ba shi amsa ya miƙo mata hannunsa “Tashi to mu je.” “Ba zan iya takawa ba ta faɗi tana cigaba da hawayen hannu ya sa ya sunkuce ta zanen da ta ɗaura ya idasa kwancewa ya faɗi ya bar ta daga ita sai fant da bra haka ya kai ta bisa gado yana soma jan ƙafar ba tare da ya lura da hannayenta da ta sanya gaba daya ta kare ƙirjinta duk da raɗaɗin da ke shigar ta tana hawaye waige waige take inda za ta samu abin da za ta rufe jikinta, sai da ya gama jan ƙafar tana mishi kuka ya shafa mata wani tube mai zafi da ta ji kamar ta saki fitsari.

Ya tashi ya ɗauko mata riga mara nauyi ya ba ta ta sanya ya ba ta magani ta haɗiya sai ta kwanta lamo tana sauraron raɗaɗin da ƙafar ke yi mata gadon ta ga ya hau ya kwanta a bayanta barci ta samu ya ɗauke ta wanda ba ta farka ba sai asuba lokacin har ya fita sallar Asuba, sai dai ta taka ƙafa ta ce ba ta san wannan ba, idon ƙafar ya kumbura suntum, ta sauka ta fara rarrafe sai ga shi ya shigo cak ya ɗaga ta sai toilet ya ajiye ta ya juya sai ya ja mata ƙofa.

Ta gama abin da za ta yi tana tunanin mafita sai ta ji daga jikin ƙofa yana faɗin “Kin gama? Ta ce “Eh” Ya shigo ya kuma surar ta sai kan prayer mat ya zaunar da ita, a zaunen ta yi sallah tana gama addu’ointa ta cusa kanta cikin gwiwoyinta barci ta ji tana ji nan ma sai ji ta yi an yi sama da ita sai kan gado ya ajiye ta ta gyara ta kwanta ya shafa mata magani sai da ya gama raɗaɗinsa ta shiga barci barci sosai ta yi sai goma ta farka Abdurrashid da ke kwance bayanta bai iya barcin ba, sai juye juye duk da yau ɗin weekend ne a ranakun yake samu ya yi barcin safe tana tashi zaune ya ce “Bari in kai ki ki yi wanka.” Ta ɗaga mishi kai sai da ya ajiye ta ya ba ta wuri sai da ta gama wankan ta rasa yadda za ta taka ta ɗauko tawul sai kawai ta yanke ta mayar da rigar da ta cire, ta sanya kenan ya shigo kallo ɗaya ya yi mata ya ƙara faɗawa wani yanayi, bayan rigar kasantuwar ta ba mai kauri ba lemar jikinta ta sa ta manne mata sai ta fidda komai ya dai fito da ita ya zaunar da ita ta yi kwalliya riga ya ciro mata kalarta blue black an matse ta daga ƙirji sai aka ɗan buɗa ta daga ƙasa tsawonta iya gwiwa miƙe ƙafar ta yi ta kwantar da kanta jikin gadon har nan ya kawo mata abin kari ta karya kiran da aka yi mishi a waya ya sa ta bar kallon TV da take yi ta maida hankalinta kan abin da yake cewa a yadda ta fahimta wata daga cikin Aunty nan sa ce take tambayar abin da ya hana su fitowa har yanzu sai yake ba ta labarin faɗuwar da Hamida ta yi da raunin da ta samu a ƙafa.

Ya sauke wayar ya dube ta “Su Aunty za su shigo su duba ki.” Kai ta ɗaga tare da lumshe idonta da za ta iya da ta ce ya ɗauko mata wasu kayan amma su zo su same ta da wannan yar riga kanta ma a buɗe sai calabar ta da ta kwanta kan dokin wuyanta.

An yi knocking daga inda yake zaune yana taɓa laptop dinsa ya amsa sai kuma ya miƙe suka shigo su dukkan su ne ya gaishe su daga inda yake suka zauna Hamida ta gaishe su suka tambaye ta ƙafa ta ce da sauƙi kaɗan suka zauna suka yi mata fatan samun sauƙi suka fita.

Har dare a ranar yana tare da ita ba inda ya je ko magungunan da ya ba ta waya ya kira aka kawo mishi.

Zuwa daren kuma ƙafar ta ɗan saki tana taka ta ta hanyar ɗangyashi, ba ta kwanta da wuri ba don wunin da ta yi kwance har ya zo ya kwanta kan gadon tana kallon shi, chat suke da Hanan da Mimi sai kuma grp na ajin su.

Har dai ta ji ta soma jin barci, wayar ta kashe bayan ta kashe datar ta gyara kwanciya ba ta da wuyar barci don haka nan da nan ya yi awon gaba da ita.

Daɗin barci ya ɗauki Hamida ya ɗora kan jikin Abdurrashid wanda ya samu ya tarairayi kansa ya samu barci ya ɗauke shi, jin ƙirjinta da ya yi a jikinsa ya haifar masa da sake shiga wani hali, hannunsa ya kai ya cire ta jikinsa amma abin da yake ji ya kasa ba shi ƙwarin gwiwar yin hakan, yar rigar jikinta ya cire Hamida da kamar a mafarki ta riƙa ji ana shafa ta ta buɗe ido gane abin da ke faruwa ya sa ta saurin wartsakewa tana neman ƙwatar kanta, ƙanƙame ta ya yi yana ba ta haƙuri cikin ƙanƙanen lokaci ya mayar da komai na ta, dogon lokaci ya ɗauka yana abu ɗaya wanda Hamida ta yi kuka iya son ranta ba tare da ya tausaya mata ba.

Gefe ɗaya ya koma yana mayar da numfashi Hamida ta ci gaba da kukanta har barci ya sace ta sai kuma ya mirgino ya haɗe jikinsu ƙarawar da ya yi ya sa ta ci gaba da kukan, a taƙaice dai bai bar su sun rintsa ba sai daf da shiga masallaci ya samu waya ana nemansa daga wurin aikinsa an kawo Sojoji da suka yi karon batta da yan bindiga.

Gudu gudu ya tsallake ta ya faɗa bathroom ya tsarkake jikinsa ya fito ya shirya inda take kwance ya zo ya ranƙwafa “Hamida! Hamida! Sai ta buɗe idanuwanta da suka kaɗa suka yi jawur suka kumbura.

“Ki yi haƙuri ki shiga ruwan zafi neman gaugawa ake min a wurin aikina, ina gama abin da ya kai ni zan dawo in taimaka miki.”

Kai ta ɗaga mishi ya fice cikin matuƙar sauri ta maida idanuwanta ta rufe tana jin yadda ko’ina na jikinta ke ciwo.

Tana nan kwance har sai da ta ji an tayar da sallah a masallacin da ke cikin Estate din ta yi yunƙurin tashi, a daddafe ta kai kanta bathroom ruwa mai zafi ta tara da dabara da dauriyar da ta sanya ta shiga ruwan tana runtse ido, ga hawaye na gudu kan kuncinta sai da ta ji ya soma sanyi ta zubar ta sake wani, wankan tsarki ta yi sai ta yi wanka da ruwa mai zafi, sosai ta ji dama lokacin da ta fito doguwar riga har ƙasa ta samo ta sanya ta yi sallah ta lallaɓa za ta hau gado ta kwanta ta hango inda jini ya ɓata zanen gadon dole ta yaye shi ta kai shi bathroom ta sanya a laudry ta dawo kamar ta duba wani ta shimfiɗa sarawar da kanta ke yi wanda bai rasa nasaba da kukan da ta sha ga zazzaɓi da take ji zai rufe ta ya sa kawai ta kwanta, barci ya yi awon gaba da ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Shirin Allah 17Shirin Allah 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.